Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 2/1 pp. 26-31
  • “Ku Bada ’Ya’ya Dayawa”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ku Bada ’Ya’ya Dayawa”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Zarafi Domin Ƙaruwa
  • ’Yar Halayen Kirista
  • Ba da ’Ya’ya na Mulki
  • Ba da ’Ya’ya ta Wajen Yaɗa Iri na Mulki
  • Ba da Abin da Za Mu Iya Domin Darajar Allah
  • Mu Yi Wa’azi Kuma Mu Koyar
  • Nuna Ƙauna Ya Kawo Bambanci
  • Jehobah Yana Kaunar Wadanda Suke Yin Wa’azi da Jimiri
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Ku Ci Moriyar Aikinku
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Abin da Ya Sa Muke Ci Gaba da Yin Wa’azi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Kana Cikin Waɗanda Allah Yake Ƙauna?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 2/1 pp. 26-31

“Ku Bada ’Ya’ya Dayawa”

“Ku bada ’ya’ya dayawa; hakanan kuma za ku zama almajiraina.”—YOHANNA 15:8.

1. (a) Wace ƙa’ida ta almajiranci Yesu ya faɗa wa manzaninsa? (b) Wace tambaya za mu yi wa kanmu?

MARAICE kafin ya mutu. Yesu ya ɗauki isashen lokaci ya ƙarfafa manzanninsa da magana fuska da fuska. A yanzu, dare ya riga ya yi tsaka, amma Yesu, ƙaunar aminansa ta motsa shi ya ci gaba da magana. Sa’an nan, a cikin wannan taɗi, ya tunasar da su wata ƙa’ida da suke bukatar su cika idan za su ci gaba da kasance almajiransa. Ya ce: “Inda a ke ɗaukaka Ubana ke nan, ku bada ’ya’ya dayawa; hakanan kuma za ku zama almajiraina.” (Yohanna 15:8) A yau muna cika wannan ƙa’ida ta almajiranci? Menene yake nufi a “bada ’ya’ya dayawa”? Domin mu fahimta, bari mu koma ga wannan taɗi na maraice.

2. Wane misali ne game da ’ya’ya Yesu ya bayar a maraice kafin ya mutu?

2 Shawarar su ba da ’ya’ya ɓangaren misali ne da Yesu ya ba wa manzanninsa. Ya ce: “Ni ne kuringar anab mai-gaskiya, Ubana kuwa mai-noma ne. Kowanne reshe a cikina wanda ba ya bada ’ya’ya ba, ya kan kawashe shi: kowanne reshe kuma da ya bada ’ya’ya, ya kan tsarkake shi domin shi daɗa bayarda ’ya’ya. Ko yanzu ku tsarkakakku ne saboda magana da na faɗa muku. Ku zauna cikina, ni ma a cikinku. Kamar yadda reshe ba ya iya bada ’ya’ya don kansa ba, sai dai yana zaune cikin kuringar anab; hakanan kuwa ku ba ku iya ba, sai dai kuna zaune cikina. Ni ne kuringar anab, ku ne rassan: . . . Inda a ke ɗaukaka Ubana ke nan, ku bada ’ya’ya dayawa; hakanan kuma za ku zama almajiraina. Kamar yadda Ubana ya ƙaunace ni, ni kuma na ƙaunace ku; ku zauna cikin ƙaunata. Idan kun kiyaye dokokina, za ku zauna cikin ƙaunata.”—Yohanna 15:1-10.

3. Menene mabiyan Yesu dole ne su yi domin su ba da ’ya’ya?

3 A wannan misalin Jehovah ne Manomin, Yesu kuma shi ne kuringar anab, manzaninsa kuma da Yesu yake yi wa magana a lokacin su ne rassan. Idan mazannin sun yi ƙoƙari su “zauna cikin” Yesu, za su ba da ’ya’ya mai yawa. Sa’an nan Yesu ya yi bayanin yadda mazannin za su yi nasara wajen riƙe wannan haɗin kai mai muhimmanci: “Idan kun kiyaye dokokina, za ku zauna cikin ƙaunata.” Daga baya, manzo Yohanna ya rubuta kalmomi makamantan haka ga ’yan’uwa Kiristoci: “Wanda ya kiyaye dokokin [Kristi] cikinsa ya ke zaune.”a (1 Yohanna 2:24; 3:24) Saboda haka, ta wajen kiyaye dokokin Kristi, mabiyansa suna kasancewa cikin haɗin kai, kuma wannan haɗin kan, yana sa su ba da ’ya’ya. Menene wannan ’ya’ya da muke bukatar mu bayar?

Zarafi Domin Ƙaruwa

4. Menene za mu koya da yadda Jehovah yake “kawashe” kowanne reshe da ba ya ba da ’ya’ya?

4 A misalin kuringar anab, Jehovah “ya kan kawashe shi,” ko kuma ya datse reshen da ba ya ba da ’ya’ya. Menene wannan yake nuna mana? Wannan ya nuna mana cewa dukan almajirai ba kawai ana bukatar su ba da ’ya’ya ba amma duka za su iya ba da ’ya’ya, ko yaya yanayinsu yake. Hakika, ba zai jitu da tafarkin ƙauna na Jehovah ba ya ‘datse’ ko kuma ya kawar da almajirin Kristi domin ya kasa cika abin da ya fi ƙarfinsa.—Zabura 103:14; Kolossiyawa 3:23; 1 Yohanna 5:3.

5. (a) Ta yaya misalin da Yesu ya bayar ya nuna cewa za mu iya ci gaba wajen ba da ’ya’ya? (b) Waɗanne ’ya’ya iri biyu ne za mu bincika?

5 Misalin da Yesu ya bayar na kuringar anab ya nuna cewa, dole ne mu nemi zarafin ci gaba a ayyukanmu na almajiranci ko yaya yanayinmu. Ka lura da abin da Yesu ya ce: “Kowanne reshe a cikina wanda ba ya bada ’ya’ya ba, ya kan kawashe shi: kowanne reshe kuma da ya bada ’ya’ya, ya kan tsarkake shi domin shi daɗa bayarda ’ya’ya.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Yohanna 15:2) A kusan ƙarshen misalin, Yesu ya aririci mabiyansa su “bada ’ya’ya dayawa.” (Aya ta 8) Menene wannan yake nufi? Mu almajirai, kada mu zama ragwaye. (Ru’ya ta Yohanna 3:14, 15, 19) Maimakon haka, ya kamata mu nemi zarafin ci gaba wajen ba da ’ya’ya. Waɗanne irin ’ya’ya ya kamata mu ba da da yawa? Su ne (1) “ ’yar ruhu” da kuma (2) ’yar Mulki.—Galatiyawa 5:22, 23; Matta 24:14.

’Yar Halayen Kirista

6. Ta yaya Yesu Kristi ya nanata tamanin ɗiyar ruhu ta farko da aka ambata?

6 Abin da aka ambata da farko cikin “ ’yar ruhu” ita ce ƙauna. Ruhun Allah mai tsarki yana ba da ƙauna cikin Kiristoci, domin suna biyayya ga umurnin da Yesu ya bayar ba da daɗewa ba bayan ya ba da misalin kuringar anab mai ba da ’ya’ya. Ya gaya wa manzanninsa: “Sabuwar doka ni ke ba ku, ku yi ƙaunar juna; kamar yadda ni na ƙaunace ku, ku ma ku yi ƙaunar juna.” (Yohanna 13:34) Hakika, a cikin dukan tattaunawar da ya yi a darensa na ƙarshe a duniya, Yesu ya tunasar da manzanninsa a kai a kai su nuna ƙauna.—Yohanna 14:15, 21, 23, 24; 15:12, 13, 17.

7. Ta yaya manzo Bitrus ya nuna cewa ba da ’ya’ya yana da nasaba da nuna halaye irin na Kristi?

7 Bitrus da yake a wurin a wannan daren, ya fahimci cewa ƙauna irin ta Kristi da kuma wasu halaye ya kamata su bayyana tsakanin almajiran gaske na Kristi. Bayan shekaru da yawa, Bitrus ya ƙarfafa Kiristoci su koyi halaye irin su kame kai, da kuma ƙauna. Ya daɗa cewa yin haka zai hana mu zama “ragwaye ko kuwa marasa-amfani.” (2 Bitrus 1:5-8) Ko yaya yanayinmu, za mu iya nuna ɗiyar ruhu. Saboda haka, mu yi ƙoƙari mu nuna ƙauna, kirki, taushin hali, da wasu halaye irin na Kristi sosai, domin “waɗannan babu shari’a a kansu,” ko iyaka. (Galatiyawa 5:23) Hakika, bari mu “bada ’ya’ya dayawa.”

Ba da ’Ya’ya na Mulki

8. (a) Mecece nasabar da take tsakanin ’yar ruhu da kuma ’yar Mulki? (b) Wace tambaya ce ta cancanci mu bincika ta?

8 ’Ya’ya masu kyakkyawan launi kuma masu zaƙi suna kyawanta itace. Amma, tamanin waɗannan ’ya’ya ya wuce kawai su kyawanta itace. ’Ya’yan suna da muhimmanci wajen yaɗa itacen ta wajen irinsu. Hakazalika, ’yar ruhu tana aikata fiye da kyawanta mutuntakar Kirista. Halaye irin su ƙauna da bangaskiya suna motsa mu mu yaɗa iri na saƙon Mulki da yake cikin Kalmar Allah. Ka lura da yadda manzo Bulus ya nanata wannan nasabar. Ya ce: “Mu kuma muna gaskatawa [ɓangaren ’yar ruhu], domin wannan kuwa mu ke magana.” (2 Korinthiyawa 4:13) A wannan hanyar, Bulus ya ƙara bayani, mu “miƙa hadaya ta yabo ga Allah kullayaumi, watau, ’ya’yan leɓunan”—’ya iri ta biyu da muke bukatar nunawa. (Ibraniyawa 13:15) Da akwai zarafi a rayuwarmu da za mu ƙara ba da ’ya’ya, hakika mu ba da ’ya’ya “dayawa,” mu masu shelar Mulkin Allah?

9. Shin ba da ’ya’ya daidai ne da almajirantarwa? Ka yi bayani.

9 Domin mu ba da amsa da kyau, muna bukatar mu fahimci da farko abin da ’yar Mulki ta ƙunsa. Daidai ne a kammala da cewa ba da ’ya’ya almajirantarwa ne? (Matta 28:19) ’Ya’ya da za mu bayar yana nufi mutane da muka taimaka wa suka zama masu bauta wa Jehovah da suka yi baftisma ne? A’a. Idan haka ne, to yanayin zai kasance da kasala ga dukan ƙaunatattun ’yan’uwa da suke shelar saƙon Mulki da aminci na shekaru da yawa a yankunan da mutane ba sa saurara. Lallai, idan ’yar Mulki da muke bayarwa yana kwatanta sababbin almajirai ne kawai, Shaidu masu ƙwazo za su zama kamar rassan da ba sa ba da ’ya’ya na misalin da Yesu ya bayar! Hakika, wannan ba haka ba ne. To, mecece ce ainihin ’yar Mulki na hidimarmu?

Ba da ’Ya’ya ta Wajen Yaɗa Iri na Mulki

10. Ta yaya misalin da Yesu ya bayar na mashuki da kuma ƙasa iri dabam dabam ya nuna abin da ɗiyar Mulki take nufi da abin da ba ta nufi?

10 Misalin Yesu na Mashuki da kuma ƙasa iri iri ya ba da amsar—amsa mai ƙarfafawa ga waɗanda suke shaida a yankuna da ba sa ba da amfani da yawa. Yesu ya ce irin, saƙon Mulki ne da yake cikin Kalmar Allah kuma ƙasar tana kwatanta zuciyarmu. Wasu irin suka “faɗi a cikin ƙasa mai-kyau, suka yi girma, suka bada amfani.” (Luka 8:8) Waɗanne irin ’ya’ya? Bayan alkama ta tsiro ta ƙosa, tana haifan, ba ƙananan kara na alkama ba, amma sababbin iri. Hakazalika, Kirista da yake ba da ’ya’ya, ba dole ba ne sababbin almajirai, amma sababbin iri na Mulki.

11. Yaya za a ba da ma’anar ’yar Mulki?

11 Saboda da haka, ’yar nan ba sababbin almajirai ba ne kuma ba kyawawan hali ba ne na Kirista. Tun da iri da aka shuka maganar Mulkin ce, ’yar dole ne ta kasance yaɗuwar irin. Ba da ’ya’ya a nan yana nufin yin furci game da Mulki. (Matta 24:14) Ba da irin wannan ’yar Mulki—shelar bisharar Mulkin—za mu iya yin hakan, ko yaya yanayinmu? Hakika, za mu iya! A wannan misalin Yesu ya ba da dalilin haka.

Ba da Abin da Za Mu Iya Domin Darajar Allah

12. Shin ba da ’ya’ya na Mulki zai yiwu kuwa ga dukan Kiristoci? Ka yi bayani.

12 “Wanda aka shuka cikin ƙasa mai-kyau,” in ji Yesu, “ya kan bada amfani, wani riɓi ɗari, wani sattin, wani talatin.” (Matta 13:23) Iri da aka shuka a gona zai bambanta a amfani da ya bayar dangane da irin yanayinsa. Haka nan, abin da za mu iya yi wajen shelar bishara zai bambanta dangane da irin yanayinmu, kuma Yesu ya nuna cewa ya fahimci haka. Wasu za su sami zarafi mai yawa; wasu za su kasance da ƙoshin lafiya da kuma kuzari. Saboda haka, abin da za mu iya yi zai fi ko kuma ya gaza na wasu, amma tun da abin da za mu iya ke nan, Jehovah zai yi farin ciki. (Galatiyawa 6:4) Ko idan tsufa da kuma ciwo suka rage abin da za mu iya yi wajen aikin wa’azi, Ubanmu mai juyayi, Jehovah, babu shakka zai saka mu tsakanin waɗanda suke “bada ’ya’ya dayawa.” Me ya sa? Domin mun ba shi ‘iyakar abin da muke da shi’—hidimarmu da zuciya ɗaya.b—Markus 12:43, 44; Luka 10:27.

13. (a) Menene dalili mafi girma da ya sa za mu ‘ci gaba’ da ba da ’ya’yan Mulki? (b) Menene zai sa mu ci gaba da ba da ’ya’ya a yankuna da mutane kalilan ne suke saurara?—(Ka dubi akwati a shafi na 29.)

13 Ko yaya yawan ’ya’ya na Mulki da za mu iya bayarwa, za mu motsa mu “bada ’ya’ya,” sa’ad da muke sane da dalilin da ya sa muke yin haka. (Yohanna 15:16) Yesu ya ambata dalili mafi girma na yin haka: “Inda a ke ɗaukaka Ubana ke nan, ku bada ’ya’ya dayawa.” (Yohanna 15:8) Hakika, aikinmu na wa’azi yana tsarkake sunan Jehovah a gaban dukan ’yan Adam. (Zabura 109:30) Honor, Mashaidiya mai aminci ’yar shekara kusan 75, ta ce: “Har a yankuna da mutane ba sa saurara ma, gata ce a wakilci Mafi Girma.” Sa’ad da aka tambayi Claudio, wanda ya kasance Mashaidi mai ƙwazo tun shekara ta 1974, me ya sa ya ci gaba da wa’azi, ko da yake mutane kalilan ne a yankinsa suke saurara, ya yi ƙaulin Yohanna 4:34, inda muka karanta kalmomin Yesu: “Abincina ke nan, in yi nufin wanda ya aiko ni, in cika aikinsa.” Claudio ya daɗa cewa: “Kamar Yesu, Ina so ba in fara aikin shelar Mulki ba kawai amma kuma in ƙarasa shi.” (Yohanna 17:4) Shaidun Jehovah a dukan duniya sun yi na’am da wannan.—Ka dubi akwati “Yadda Za a Ba da ’Ya’ya da Haƙuri,” a shafi na 29.

Mu Yi Wa’azi Kuma Mu Koyar

14. (a) Waɗanne abubuwa biyu suke ƙunshe cikin aikin Yohanna Mai Baftisma da kuma na Yesu? (b) Yaya za ka kwatanta aikin Kiristoci a yau?

14 Mai shelar Mulki na farko da aka ambata a cikin Lingila Yohanna mai Baftisma ne. (Matta 3:1, 2; Luka 3:18) Ainihin dalilin haka domin ya “bada shaida” ne, kuma ya yi haka da bangaskiya mai ƙarfi da kuma begen cewa “dukan mutane su bada gaskiya.” (Yohanna 1:6, 7) Hakika, wasu da Yohanna ya yi wa wa’azi sun zama almajiran Kristi. (Yohanna 1:35-37) Saboda haka, Yohanna mai wa’azi ne kuma mai almajirantarwa. Yesu ma mai wa’azi ne kuma malami ne. (Matta 4:23; 11:1) Saboda haka, ba abin mamaki ba ne da Yesu ya umurci mabiyansa su yi wa’azin saƙon Mulki kuma su taimake mutane da suka karɓe shi su zama almajiransa. (Matta 28:19, 20) Saboda haka, aikinmu a yau ya ƙunshi wa’azi da kuma koyarwa.

15. Wane kamani yake tsakanin yadda ake karɓan aikin wa’azi a ƙarni na farko da wanda ake yi a yau?

15 Waɗanda suka ji Bulus yana wa’azi kuma yana koyarwa a ƙarni na farko, “Waɗansu suka gaskata abin da aka faɗi, waɗansu ba su gaskata ba.” (Ayukan Manzanni 28:24) A yau, yanayin haka yake. Abin baƙin ciki, yawancin iri na Mulki suna faɗawa a kan ƙasa marar saurara. Duk da haka, wasu iri suna faɗi a kan ƙasa mai kyau, su yi saiwa su tsiro, kamar yadda Yesu ya faɗa. A dukan duniya, mutane fiye da matsakaicin adadi 5,000 suke zama almajiran Kristi na gaske kowanne mako na shekara! Waɗannan sababbin almajirai sun “gaskata abin da aka faɗi,” ko da yake yawancin mutane ba su gaskata ba. Me ya taimaka wajen saka zuciyarsu ta karɓi saƙon Mulki? Sau da yawa ƙauna da Shaidun suke nunawa ne—ba da ruwa ga sabon iri da aka shuka—ya kawo bambancin. (1 Korinthiyawa 3:6) Ka yi la’akari da misali biyu kawai cikin wasu da yawa.

Nuna Ƙauna Ya Kawo Bambanci

16, 17. Me ya sa yake da muhimmanci mu nuna ƙauna ga waɗanda muka sadu da su a hidimarmu?

16 Karolien Mashaidiya matashiya ce a Belgium, ta je wajen wata tsohuwa da ta nuna ba ta son saƙon Mulki. Hannun matar yana naɗe da bandeji, sai Karolien da kawarta suka je za su taimake ta, amma matar ta ƙi. Bayan kwanaki biyu Shaidun biyu suka sake komawa gidan matar suka tambaye ta yaya jikinta. “Wannan ne ya sake yanayin,” in ji Karolien. “Ta yi mamaki da ta ga muna ƙaunarta da gaske. Ta gayyace mu zuwa cikin gidanta, kuma muka fara nazarin Littafi Mai Tsarki.”

17 Sandi, Mashaidiya ce a Amirka, tana nuna ƙauna ga waɗanda take musu wa’azi. Sai ta duba sanarwar haihuwa a jarida bayan haka sai ta ziyarci iyayen da Littafi Na na Labarun Bible.c Tun da mamar tana gida kullum kuma tana farin ciki ta nuna wa baƙi jaririnta, sau da yawa sai su fara taɗi. “Ina gaya wa iyayen muhimmancin kusantar jaririn ta wajen yi masa karatu,” in ji Sandi. “Bayan haka sai na yi bayani game da ƙalubalen renon yaro a duniya ta yau.” Ba da daɗewa ba domin irin wannan wa’azin, wata uwa da yara shida suka fara bauta wa Jehovah. Fara fita nema da kuma nuna irin wannan ƙaunar za su kai ga sakamako na farin ciki a hidimarmu.

18. (a) Me ya sa ƙa’idar a ‘ba da ’ya’ya da yawa’ bai fi ƙarfinmu ba? (b) Waɗanne ƙa’idodi uku ne da aka ambata a Linjilar Yohanna ka ƙuduri aniyar cikawa?

18 Abin ƙarfafa ne mu ga cewa bukatar mu ci gaba da “bada ’ya’ya dayawa” bai fi ƙarfinmu ba! Yara ko manya, lafiyayyu ko marasa lafiya, ko muna wa’azi a yankin da mutane suna saurara ko babu, dukanmu muna iya ba da ’ya’ya da yawa. Ta yaya? Ta wajen nuna ’yar ruhu cikakkiya da yaɗa saƙon Mulkin Allah gwargwadon ƙarfinmu. Sa’an nan kuma, mu yi ƙoƙari mu ‘zauna cikin maganar Yesu’ kuma ‘kasance da ƙauna ga junanmu.’ Hakika, ta wajen cika waɗannan ƙa’idodi uku masu muhimmanci na almajiranci da aka ambata a cikin Linjilar Yohanna, muna tabbatar da cewa mu “ne almajirai [Kristi] na gaske.”—Yohanna 8:31; 13:35.

[Hasiya]

a Ko da yake rassan kuringar anab na misalin Yesu yana nuni ga manzanninsa ne da kuma wasu Kiristoci da za su gaji Mulkin Allah na samaniya, misalin yana ɗauke da gaskiya da za ta amfani dukan mabiyan Kristi.—Yohanna 3:16; 10:16.

b Waɗanda ba za su iya fita ba daga gidajensu domin tsufa ko kuma ciwo za su iya yin wa’azi ta wajen rubuta wasiƙa, ko kuma idan zai yiwu, da tarho, ko kuma wataƙila sa’ad da wasu suka ziyarce su.

c Shaidun Jehovah ne suke bugawa.

Tambayoyi don Maimaitawa

• Wane irin ’ya’ya ne muke bukatar mu bayar da yawa?

• Me ya sa makasudin “bada ’ya’ya dayawa” bai fi ƙarfinmu ba?

• Waɗanne ƙa’idodi uku ne masu muhimmanci da aka ambata a Linjilar Yohanna muka bincika?

[Box/Hoto a shafi na 29]

Yadda ‘Za A Ba Da ’Ya’ya Da Haƙuri’

MENENE ya taimake ku kuka ci gaba da wa’azin saƙon Mulki da aminci a yankin da mutane ba sa yawan sauraro? Ga wasu amsoshi da sa yi taimako.

“Da yake mun sani cewa Yesu yana taimakonmu wannan yana ba mu ƙarfin gwiwa da kuma dauriya, ko yaya mutane suke aikata a yankinmu.”—Harry, ɗan shekara 72; ya yi baftisma a shekara ta 1946.

“Nassi na 2 Korinthiyawa 2:17 kuma tana ƙarfafa ni. Ta ce muna saka hannu cikin hidima ‘Allah yana gani, tare da Kristi.’ Sa’ad da nake hidima, ina more abokantakar aminai.”—Claudio, ɗan shekara 43; ya yi baftisma a shekara ta 1974.

“Gaskiya, aikin wa’azi a gare ni ba shi da sauƙi. Duk da haka, ina ganin gaskiyar kalmomin da suke Zabura 18:29: ‘Da ikon Allahna ni ke tsallake ganuwa.’ ”—Gerard, ɗan shekara 79; ya yi baftisma a shekara ta 1955.

“Idan na karanta aya ɗaya kawai a hidima, yana gamsar da ni cewa Littafi Mai Tsarki ya bincika zuciyar wani.”—Eleanor, ’yar shekara 26; ta yi baftisma a shekara ta 1989.

“Na ci gaba da ƙoƙarin gwada hanyoyi da yawa na yin magana. Suna da yawa da ba zan iya yin amfani da dukansu ba a raguwar rayuwata.”—Paul ɗan shekara 79; ya yi baftisma a shekara ta 1940.

“Baƙar magana ta mutane ba ta damuna. Ina yin magana da mutane cikin kwanciyar hankali kuma in saurari nasu ra’ayi.”—Daniel, ɗan shekara 75; ya yi baftisma a shekara ta 1946.

“Na sadu da waɗanda suka yi baftisma a baya bayan nan da suka gaya mini cewa aikin wa’azina ya sa sun zama Shaidu. Ba da sani na ba wani ya yi nazari da su ya taimake su suka ci gaba. Yana ba ni farin ciki na fahimci cewa hidimarmu aiki ne na haɗa kai.”—Joan, ’yar shekara 66; ta yi baftisma a shekara ta 1954.

Wanene yake taimaka maka ka ‘ba da ’ya’ya da haƙuri’?—Luka 8:15.

[Hotuna a shafi na 28]

Ta wajen nuna ’yar ruhu da kuma yin shelar saƙon Mulki, muna ba da ’ya’ya da yawa

[Hoto a shafi na 31]

Menene Yesu yake nufi sa’ad da ya gaya wa manzanninsa: “Ku bada ’ya’ya dawaya”?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba