Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 3/1 pp. 13-18
  • Menene Jibin Maraice Na Ubangiji Yake Nufi A Gare ka?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Menene Jibin Maraice Na Ubangiji Yake Nufi A Gare ka?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Wasu Sun Yi Shi Yadda Bai Dace Ba
  • Halartar Masu Kiyayewa da Daraja
  • Neman “Waɗansu Tumaki”
  • Abin da Ya Sa Wasu Suke Ganin An Zaɓe Su
  • Abin da Ya Sa Suke da Tabbaci
  • Lokacin Bikin Tuna Mutuwarsa —Lokaci ne Mai Albarka
  • Me Ya Sa Muke Taron Tuna Mutuwar Yesu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Tattara Abubuwan Da Ke Cikin Sama Da Waɗanda Ke Bisa Duniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Taro Mai Girma Suna Yabon Allah da Kristi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Me Ya Sa Muke Halartan Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 3/1 pp. 13-18

Menene Jibin Maraice Na Ubangiji Yake Nufi A Gare ka?

“Dukan fa wanda ya ci gurasa ta Ubangiji, ko ya sha ƙoƙonsa, da rashin cancanta, ya zama da laifi cikin jikin Ubangiji har da jininsa.”—1 KORINTHIYAWA 11:27.

1. Wane muhimmin biki ne aka shirya domin shekara ta 2003, kuma menene asalinsa?

MUHIMMIN biki da aka shirya domin shekara ta 2003 za a yi shi a ranar 16 ga Afrilu, bayan faɗuwar rana. A wannan lokacin ne Shaidun Jehovah za su taru domin su yi bikin Tuna Mutuwar Yesu Kristi. Kamar yadda aka nuna a talifi da ya gabata, Yesu ya kafa wannan biki, da aka kira Jibin Maraice na Ubangiji, bayan shi da manzanninsa suka gama bikin Faska na 14 ga Nisan, 33 A.Z. Isharar bikin gurasa marar yisti da jar ruwan inabi ne, suna wakiltan jiki marar zunubi na Kristi da kuma jininsa—hadaya kaɗai da ta fanshi mutane daga zunubi da mutuwa.—Romawa 5:12; 6:23.

2. Wane gargaɗi ne aka rubuta a 1 Korinthiyawa 11:27?

2 Waɗanda suke cin isharar bikin Tuna Mutuwar dole ne su yi haka yadda ya dace. Manzo Bulus ya yi bayani dalla-dalla yayin da ya rubuta zuwa ga Kiristoci a Koranti na dā, inda ba a yin bikin Jibin Maraice na Ubangiji bisa ƙa’ida. (1 Korinthiyawa 11:20-22) Bulus ya rubuta: “Dukan fa wanda ya ci gurasa ta Ubangiji, ko ya sha ƙoƙonsa, da rashin cancanta, ya zama da laifi cikin jikin Ubangiji har da jininsa.” (1 Korinthiyawa 11:27) Menene ma’anar waɗannan kalmomi?

Wasu Sun Yi Shi Yadda Bai Dace Ba

3. Yaya ne da yawa cikin Kiristoci na Koranti suke yi a wajen bikin Jibin Maraice na Ubangiji?

3 Kiristoci da yawa a Koranti sun ci isharar yadda bai dace ba. Suna rarrabuwa, kuma a wani lokaci ma, sukan kawo abincinsu su ci kafin ko kuma a lokacin taro, sau da yawa suna zarin ci har da maye. Ba a faɗake suke a hankali ba balle ma a ce a ruhaniya. Wannan ya sa suka “zama da laifi cikin jikin Ubangiji har da jininsa.” Waɗanda ba su da abinci da suke jin yunwa hankalinsu ya rabu. Hakika, da yawa sun ci ba tare da daraja ko kuma fahimtar dalilin bikin ba. Babu mamakin da suka jawo wa kansu huƙunci!—1 Korinthiyawa 11:27-34.

4, 5. Me ya sa ya dace ƙwarai waɗanda suka saba cin isharar bikin Tuna Mutuwar Yesu su binciki kansu?

4 Yayin da lokaci domin bikin Tuna Mutuwarsa ya yi kusa kowacce shekara, waɗanda suke cin isharar musamman suna bukatar su sake bincika kansu. Don su yi tarayyar da ta dace lokacin jibin, dole ne su kasance lafiyayyu a ruhaniya. Duk wanda ya rena, ko kuma ya yi ƙyamar hadayar Yesu zai shiga haɗarin a ‘kawar da shi daga tsakanin mutanen Allah,’ yadda ya kasance ga Ba’isra’ile da ya ci jibin tarayya da ƙazanta.—Leviticus 7:20; Ibraniyawa 10:28-31.

5 Bulus ya kwatanta bikin Tuna Mutuwar Yesu da jibin tarayya da ake yi a Isra’ila ta dā. Ya ce waɗanda suke ci suna tarayya da Kristi ne kuma ya daɗa cewa: “Ba ku da iko ku sha ƙoƙon Ubangiji duk da na aljanu ba: ba ku da iko ku tara ci daga [tebur] na Ubangiji, da na aljanu ba.” (1 Korinthiyawa 10:16-21) Idan mutum dama ya saba da cin isharar bikin ya yi zunubi mai tsanani, ya kamata ya yi ikirari wa Jehovah kuma ya nemi taimakon dattawan ikilisiya. (Misalai 28:13; Yaƙub 5:13-16) Idan ya tuba da gaske kuma ya yi ayyukan tuba, ba zai zama yana ci da rashin daraja ba.—Luka 3:8.

Halartar Masu Kiyayewa da Daraja

6. Ga su wanene Allah ya ba da gatar cin Jibin Maraice na Ubangiji?

6 Ya kamata ne waɗanda a yanzu suke yin nagarta ga raguwar 144,000 na ’yan’uwan Kristi su ci Jibin Maraice na Ubangiji? (Matta 25:31-40; Ru’ya ta Yohanna 14:1) A’a. Allah ya ba da wannan gatar ga mutane da ya shafa su da ruhu mai tsarki su zama “masu-tarayyan gadō da Kristi.” (Romawa 8:14-18; 1 Yohanna 2:20) To, menene matsayin waɗanda suke da begen rayuwa har abada a aljanna a duniya ƙarƙashin Mulki? (Luka 23:43; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Tun da yake su ba masu tarayyar gadō ba ne masu begen samaniya, suna halartan bikin ne su kiyaye da daraja.—Romawa 6:3-5.

7. Me ya sa Kiristoci na ƙarni na farko suka sani cewa ya kamata su ci isharar bikin Tuna Mutuwar Yesu?

7 Kiristoci na gaskiya a ƙarni na farko an shafa su da ruhu mai tsarki. Da yawa tsakaninsu suna iya amfani da kyautar mu’ujiza na ruhu, ɗaya ko biyu, kamar, magana da wani yare. Saboda haka, ba zai zama abu mai wuya ba ga waɗanda sun sani cewa an shafa su da ruhu kuma ya kamata su ci isharar bikin. Amma, a zamaninmu za a san wannan ta wurin hurarrun kalmomi kamar wannan: “Iyakar waɗanda Ruhun Allah ke bishe su, waɗannan ’ya’yan Allah ne. Gama ba ku karɓi ruhun bauta da za ku sake jin tsoro ba; amma kuka karɓi ruhun ɗiyanci, inda muke kira, Abba, Uba.”—Romawa 8:14, 15.

8. Su wa “alkama” ke kwatanci, su wa kuma “zawa” ke kwatanci yadda aka ambata a Matta sura ta 13?

8 Duk cikin ƙarnuka, shafaffu na gaske sun yi girma kamar “alkama” cikin gonar “zawa,” ko kuma Kiristoci na ƙarya. (Matta 13:24-30, 36-43) Tun daga shekarun 1870, “alkama” ta bayyana sosai, kuma shekaru daga baya an gaya wa masu kula Kiristoci: “Dattawa . . . ya kamata su bayyana wa waɗanda suka taru domin [bikin Tuna Mutuwar] imanin nan,—(1) Bangaskiya cikin jinin [Kristi]; da kuma (2) keɓewar kai ga Ubangiji da kuma hidimarsa, har zuwa mutuwa. Sai su gayyaci dukan waɗanda suke da imanin nan kuma da sun keɓe kansu su sa hannu a yin bikin mutuwar Ubangiji.”—Studies in the Scriptures, Series VI, The New Creation, shafi 473.a

Neman “Waɗansu Tumaki”

9. Ta yaya aka bayyana “taro mai-girma” a shekara ta 1935, kuma yaya wannan ya shafe wasu da suke cin isharar Tuna Mutuwar dama?

9 Da shigewar shekaru, ƙungiyar Jehovah ta soma mai da hankali a kan wasu ban da shafaffu mabiyan Kristi. An sami bunƙasa ta musamman game da wannan a tsakiyar shekarun 1930. Kafin nan, mutanen Allah sun ɗauki “taro mai-girma” na Ru’ya ta Yohanna 7:9 aji na biyu ne na ruhaniya da za su yi tarayya da shafaffu 144,000 da za a ta da daga matattu zuwa sama—watau, abokan amaryar Kristi. (Zabura 45:14, 15; Ru’ya ta Yohanna 7:4; 21:2, 9) Amma a ranar 31 ga Mayu, 1935, a wani jawabi da aka yi a taron gunduma na Shaidun Jehovah a Amirka a Washington, D.C., a wurin an yi bayani daga cikin Littafi Mai Tsarki cewa “taro mai-girma” (“babban garke,” a King James Version) na nufin “waɗansu tumaki” ne da suke rayuwa a lokaci na ƙarshe. (Yohanna 10:16) Bayan taron, wasu da dā suke cin isharar bikin suka daina domin sun fahimci cewa begensu na duniya ne, ba na samaniya ba.

10. Yaya za ka kwatanta bege da hakki na “waɗansu tumaki” na zamanin nan?

10 Tun daga shekara ta 1935 musamman ana ta neman waɗanda suka zama “waɗansu tumaki,” da suka ba da gaskiya ga fansa, suka keɓe kansu ga Allah, kuma suka goyi bayan shafaffu, “ƙaramin garke” a aikin wa’azi na Mulkin. (Luka 12:32) Waɗannan tumaki suna da begen rayuwa a duniya har abada, amma a kowanne fasali, suna kama da raguwar masu gadōn Mulki na zamaninmu. Kamar baƙi a Isra’ila ta dā da suka bauta wa Jehovah kuma suka bi Doka, a yau waɗansu tumaki suna na’am da hakki na Kirista, irinsu wa’azin bishara tare da waɗanda suke cikin Isra’ila ta ruhaniya. (Galatiyawa 6:16) Kamar yadda babu wani baƙo da zai zama sarki ko kuma firist a Isra’ila, babu wani cikin waɗansu tumaki da zai yi sarauta a Mulki na samaniya ko kuma ya zama firist.—Kubawar Shari’a 17:15.

11. Me ya sa kwanan wata na ranar da mutum ya keɓe kansa zai shafi begensa?

11 A shekarun 1930, ya ƙara bayyana cewa a galibi an gama zaɓan aji na samaniya. Misalin shekaru saba’in yanzu, waɗansu tumaki ake nema, da suke da bege na duniya. Idan wani shafaffe ya yi rashin aminci, mai yiwuwa ne cewa wanda ya yi hidima ga Allah da daɗewa cikin aminci daga waɗansu tumaki ne za a zaɓa ya ɗauki matsayinsa tsakanin 144,000.

Abin da Ya Sa Wasu Suke Ganin An Zaɓe Su

12. Cikin wane irin yanayi ne mutum zai daina cin isharar Tuna Mutuwar, kuma me ya sa?

12 Kiristoci shafaffu sun tabbata sarai cewa an zaɓe su domin samaniya. Amma idan wasu da ba a zaɓe su ba suna cin isharar bikin Tuna Mutuwar kuma fa? To, da yake yanzu sun fahimci cewa ba a zaɓe su ba domin samaniya, lallai lamirinsu zai motsa su su daina cin isharar. Allah ba zai yi farin ciki da wani da ya naɗa kansa sarki da firist na samaniya sa’ad da ya sani cewa ba a zaɓe shi ba. (Romawa 9:16; Ru’ya ta Yohanna 20:6) Jehovah ya halaka Kora Balawi domin girman kai da son ya kasance cikin tsarin firistoci na Haruna. (Fitowa 28:1; Litafin Lissafi 16:4-11, 31-35) Idan Kirista ya fahimci cewa yana cin isharar bikin Tuna Mutuwar Yesu cikin rashin sani, ya kamata ta ko ya daina ci kuma ya yi addu’a cikin tawali’u domin Jehovah ya gafarta masa.—Zabura 19:13.

13, 14. Me ya sa wasu cikin kuskure za su aza cewa suna da bege na samaniya?

13 Me ya sa wasu suke ganin an zaɓe su domin samaniya? Mutuwar abokiyar aure ko kuma wata masifa za ta iya sa marmarin rayuwa a duniya ya fita a ransu. Kuma su so begen zuwa sama yadda wani abokinsu na kud da kud yake da shi na Kirista shafaffe. Hakika, Allah bai naɗa kowa ya zaɓi wasu domin wannan gatar ba. Kuma bai shafi magadan Mulki ta wurin sa su su ji muryoyi da saƙo game da haka ba.

14 Ra’ayi na addinan ƙarya na cewa dukan nagargarun mutane za su sama zai iya sa wasu su yi tunanin cewa suna da begen samaniya. Saboda haka, ya kamata mu tsare kanmu daga ƙyale ra’ayin da ba daidai ba ko kuma imaninmu na dā ya rinjaye mu. Alal misali, wasu suna iya tambayar kansu: ‘Ina amfani da wasu magunguna ne da suke taɓa hankalina? Ina tunani ainu ne da zai sa ni tsammanin an zaɓe ni?’

15, 16. Me ya sa wasu cikin kuskure za su kammala da cewa su shafaffu ne?

15 Wasu kuma suna iya tambayar kansu: ‘Ina son na yi suna ne? Ina da dogon buri ne na son iko yanzu ko kuma zama magaji tare da Kristi a nan gaba?’ Lokacin da aka zaɓi magadan Mulkin a ƙarni na farko, ba duka suke da matsayi mai girma cikin ikilisiya ba. Kuma mutane da aka zaɓa domin samaniya ba sa neman girma ko kuma fahariyar zama shafaffu. Sun nuna tawali’u da ake bukata daga waɗanda suka fahimci “nufin Kristi.”—1 Korinthiyawa 2:16.

16 Wasu suna iya tunanin cewa domin sun sami sanin Littafi Mai Tsarki sosai an zaɓe su domin samaniya. Amma shafa mutum da ruhu ba ya kawo yawan fahimta, domin Bulus ya koyar kuma ya yi gargaɗi ga wasu shafaffu. (1 Korinthiyawa 3:1-3; Ibraniyawa 5:11-14) Allah ya shirya tanadin abinci na ruhaniya domin dukan mutanensa. (Matta 24:45-47) Saboda haka, kada wani ya yi tunanin cewa zama Kirista shafaffe ne zai ba shi hikima da ya fi na waɗanda suke begen duniya. Shafa mutum da ruhu ba ya nufin fasaha wajen amsa tambayoyin Nassi, yin wa’azi, ko kuma ba da jawabi na Littafi Mai Tsarki. Kiristoci da suke da begen zama a duniya ma suna da fasaha a waɗannan fasaloli.

17. A shafa mutum da ruhu ya dangana ga me kuma a kan wa?

17 Idan ɗan’uwa mai bi ya yi tambaya game da zaɓen zuwa samaniya, wani dattijo ko kuma Kirista ƙwararre zai iya tattauna batun da shi. Amma, wani ba zai tsai da wannan shawarar wa wani ba. Wanda da gaske an zaɓe shi domin samaniya ba ya bukatar ya tambayi wasu ko yana da irin wannan begen. Da yake shafaffu an “maya haihuwar[su], ba daga iri mai-ruɓewa ba, amma marar-ruɓewa, ta wurin maganar Allah, wadda ta ke rayuwa, ta kuma dawwama.” (1 Bitrus 1:23) Ta wurin ruhu da Kalmarsa, Allah yana shuka “iri” da ke sa mutumin ya zama “sabon halitta,” da ke da begen samaniya. (2 Korinthiyawa 5:17) Jehovah ne kuma ke yin zaɓen. Shafewa ba daga “wajen mai-nufi ya ke ba, ba kuwa daga wajen wanda ya yi tsere ba, amma daga wajen Allah.” (Romawa 9:16) To, ta yaya mutum zai tabbata an zaɓe shi domin samaniya?

Abin da Ya Sa Suke da Tabbaci

18. Ta yaya ne ruhun Allah yake shaida da ruhun shafaffu?

18 Shaidar ruhun Allah ne ke tabbatar wa Kiristoci shafaffu cewa an zaɓe su domin samaniya. “Kuka karɓi ruhun ɗiyanci,” in ji Bulus, “inda muke kira, Abba, Uba. Ruhu da kansa tare da namu ruhu yana shaida, mu ’ya’yan Allah ne: idan ’ya’ya ne fa, magada ne kuma; magadan Allah, masu-tarayyan gadō da Kristi; in da muna raɗaɗi tare da shi, domin kuma mu ɗaukaka tare da shi.” (Romawa 8:15-17) Domin tasirin ruhu mai tsarki ne, ruhun ko kuma halin shafaffu ke motsa su su yi amfani da abin da Nassosi ya faɗa game da ’ya’yan Jehovah na ruhu. (1 Yohanna 3:2) Ruhun Allah na ba su azancin zaman ’ya’ya gare shi kuma yana sa su kasance da bege na musamman. (Galatiyawa 4:6, 7) Hakika, rayuwa har abada a duniya na mutane kamiltattu tare da waɗanda suke cikin iyalai da abokai za ta kasance da armashi ƙwarai, amma ba begen da Allah ya ba su ba ke nan. Ta wurin ruhunsa, Allah ya sa bege mai ƙarfi na zuwa sama cikinsu da ya sa suke a shirye su sadaukar da dukan tarayya ta duniya da kuma bege.—2 Korinthiyawa 5:1-5, 8; 2 Bitrus 1:13, 14.

19. Wane matsayi ne sabon alkawari yake da shi a rayuwar Kirista shafaffe?

19 Kiristoci shafaffu suna da tabbaci game da begensu na samaniya, da aka kawo su cikin sabon alkawari. Yesu ya ambata shi lokacin da ya kafa bikin Tuna Mutuwarsa, ya ce: “Wannan ƙoƙo sabon alkawari ne cikin jinina, wanda an zubar dominku.” (Luka 22:20) Waɗanda suke cikin sabon alkawarin, Allah ne da shafaffunsa. (Irmiya 31:31-34; Ibraniyawa 12:22-24) Yesu ne mai aikin matsaikacin. Ta wurin jinin Kristi da aka zubar ne sabon alkawarin ya kahu, ya kawo ba Yahudawa kawai ba amma kuma daga al’umman mutane domin sunan Jehovah kuma ya sa suka kasance cikin “zuriyar” Ibrahim. (Galatiyawa 3:26-29; Ayukan Manzanni 15:14) Wannan “madawwamin alkawari” ya sa dukan Isra’ilawa na ruhaniya za a ta da su zuwa rai marar matuƙa cikin sama.—Ibraniyawa 13:20.

20. Shafaffu sun shiga wane alkawari ne da Kristi?

20 Shafaffu suna da tabbacin begensu. An saka su cikin wani alkawari, alkawarin Mulkin. Game da yin tarayyarsu da Kristi, Yesu ya ce: “Ku ne waɗanda kun lizimce ni a cikin jarabtuwana; ni ma na sanya muku mulki, kamar yadda Ubana ya sanya mini.” (Luka 22:28-30) Wannan alkawari tsakanin Kristi da abokansa sarakuna zai kasance har abada.—Ru’ya ta Yohanna 22:5.

Lokacin Bikin Tuna Mutuwarsa —Lokaci ne Mai Albarka

21. Ta yaya za mu iya samun amfani mai yawa daga lokacin Tuna Mutuwar?

21 Akwai albarkatai da yawa a lokacin bikin Tuna Mutuwar Yesu. Za mu iya amfana daga tsarin karatun Littafi Mai Tsarki domin wannan lokaci. Lokaci ne kuma musamman domin addu’a, yin bimbini a kan rayuwar Yesu a duniya da kuma mutuwarsa, da sa hannu a aikin wa’azin Mulkin. (Zabura 77:12; Filibbiyawa 4:6, 7) Bikin ma yana tunasar da mu game da ƙaunar da Allah da Kristi suka nuna mana ta wajen hadayar fansa ta Yesu. (Matta 20:28; Yohanna 3:16) Tanadin nan na ba mu bege da ta’aziyya, ya kamata ya daɗa motsa mu mu bi tafarki irin na Kristi. (Fitowa 34:6; Ibraniyawa 12:3) Ya kamata kuma bikin Tuna Mutuwar ya ƙarfafa mu mu cika keɓe kanmu mu bayin Allah kuma mu zama mabiya masu aminci na Ɗansa ƙaunatacce.

22. Mecece kyauta mafi girma na Allah ga mutane, kuma a wace hanya ɗaya ce za a iya nuna godiya dominta?

22 Lallai kyauta ce mai kyau da Jehovah ya ba mu! (Yaƙub 1:17) Muna da ja-gorar Kalmarsa, taimakon ruhunsa, da begen rai madawwami. Kyautar Allah mafi girma ita ce hadayar Yesu domin zunuban shafaffu da kuma na dukan wasu da suka yi imani. (1 Yohanna 2:1, 2) To, yaya tamanin mutuwar Yesu yake gare ka? Za ka kasance cikin waɗanda za su yi godiya dominsa ta halartar taro bayan faɗuwar rana a ranar 16 ga Afrilu, 2003, domin yin bikin Jibin Maraice na Ubangiji?

[Hasiya]

a Shaidun Jehovah ne suka buga amma yanzu an daina bugawa.

Menene Amsoshinka?

• Wa ya kamata ya ci isharar bikin Tuna Mutuwar Yesu?

• Me ya sa “waɗansu tumaki” suke halarta Jibin Maraice na Ubangiji kawai ba tare da cin isharar ba?

• Ta yaya Kiristoci shafaffu suka san ya kamata su ci gurasa kuma su sha giya a bikin Tuna Mutuwar Kristi?

• Lokacin bikin Tuna Mutuwar Yesu lokaci ne mai kyau domin me?

[Graph/Hotuna a shafi na 14]

Waɗanda Suka Halarci Bikin Tuna Mutuwar

MILIYOYI

15,597,746

15

14

13,147,201

13

12

11

10

 9

 8

 7

 6

 5

4,925,643

 4

 3

 2

 1

878,303

63,146

1935 1955 1975 1995 2002

[Hoto a shafi na 14]

Za ka kasance a wurin bikin Jibin Maraice na Ubangiji wannan shekarar?

[Hotuna a shafi na 17]

Lokacin bikin Tuna Mutuwar Yesu lokaci ne mai kyau domin daɗa karatun Littafi Mai Tsarki da kuma sa hannu cikin aikin wa’azin Mulki

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba