Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 3/1 pp. 9-13
  • Tattara Abubuwan Da Ke Cikin Sama Da Waɗanda Ke Bisa Duniya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tattara Abubuwan Da Ke Cikin Sama Da Waɗanda Ke Bisa Duniya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Abubuwan da ke Cikin Sammai”
  • An soma Tattarawa
  • An Karɓe su Cikin Alkawarin Mulki
  • Cin Isharar
  • Tattara “Abubuwan da ke Bisa Duniya”
  • Menene Jibin Maraice Na Ubangiji Yake Nufi A Gare ka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Me Ya Sa Muke Taron Tuna Mutuwar Yesu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Za Mu Tafi Tare da Ku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Garke Ɗaya, Makiyayi Ɗaya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 3/1 pp. 9-13

Tattara Abubuwan Da Ke Cikin Sama Da Waɗanda Ke Bisa Duniya

“Bisa ga yardarsa da ya nufa a cikinsa . . . shi tattara dukan abu cikin Kristi, abubuwan da ke cikin sammai da abubuwan da ke bisa duniya.”—AFISAWA 1:9, 10.

1. Menene “yardar” Jehobah ga samaniya da kuma duniya?

SALAMA A DUNIYA! Wannan ita ce nufin Jehobah “Allah na salama.” (Ibraniyawa 13:20) Ya huri manzo Bulus ya rubuta cewa “yardarsa” ita ce “a tattara dukan abu cikin Kristi, da abubuwan da ke cikin sammai, da abubuwan da ke bisa duniya.” (Afisawa 1:9, 10) Menene ake nufi da aikatau da aka fassara shi ‘tattara duka’ a cikin wannan ayar? Wani masanin Littafi Mai Tsarki J. B. Lightfoot ya ce: “furcin yana nufin jituwar dukan sararin samaniya, da ba za ta haɗa da baren abubuwa ba, amma dukan ɓangarorinta za su samu jituwa cikin Kristi. Zunubi, mutuwa, kuskure da wahala, duk za su shuɗe.”

“Abubuwan da ke Cikin Sammai”

2. Su wanene “abubuwa da ke sammai” da suke bukatar a tara su?

2 Manzo Bitrus ya taƙaita begen Kiristoci na gaskiya sa’ad da ya ce: “Amma, bisa ga alkawarinsa, muna sauraron sabobin sammai da sabuwar duniya, inda adalci yake zaune.” (2 Bitrus 3:13) “Sammai” da aka yi alkawarinsu suna nufin sabon ikon, wato Mulkin Almasihu. “Abubuwa dake sammai” da manzo Bulus ya ambata a wasiƙarsa zuwa ga Afisawa za a tara ne a “cikin Kristi.” Su ne mutane kaɗan da aka zaba su yi mulki da Kristi a sama. (1 Bitrus 1:3, 4) Waɗannan shafaffun Kiristoci 144,000 da aka “fanso su daga cikin duniya,” za su zama masu tarayyar gadō da Kristi a Mulkinsa na samaniya.—Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 14:3, 4; 2 Korinthiyawa 1:21; Afisawa 1:11; 3:6.

3. Ta yaya za a iya cewa shafaffun Kiristoci suna ‘zama a cikin sammai’ ko da yake suna nan a duniya?

3 Da taimakon ruhu mai tsarki an fanshi shafaffun Kiristoci, ko kuma an haife su, don su zama ’ya’yan Jehobah na ruhaniya. (Yohanna 1:12, 13; 3:5-7) Tun da Jehobah ya ɗiyance su su zama “ ’ya’yansa,” sun zama ’yan’uwan Yesu. (Romawa 8:15; Afisawa 1:5) Ko da yake suna nan a duniya, ana cewa ‘ya tashe su tare da shi, ya zamshe su tare da shi cikin sammai cikin Yesu Kristi.’ (Afisawa 1:3; 2:6) Sun sami wannan ruhaniya mai ɗaukaka saboda an ‘hatimce su da ruhu mai tsarki na alkawari, wanda yake shigambiyar gādonsu’ wanda aka keɓe masu a sammai. (Afisawa 1:13, 14; Kolosiyawa 1:5) Waɗannan su ne “abubuwa da ke sammai,” waɗanda ya kamata a tattara adadin da Jehoba ya riga ya naɗa.

An soma Tattarawa

4. Yaushe ne kuma ta yaya aka fara aikin tattara “abubuwa da ke sammai”?

4 Daidai da “wakilcin” Jehobah ko kuma hanyarsa ta gyara abubuwa, za a soma tattara “abubuwa da ke sammai” a “cikar wokatai.” (Afisawa 1:10) Lokacin ya kai a ranar Fentakos ta shekara ta 33 A.Z. A wannan ranar aka cika manzannin Yesu tare da almajiransa maza da mata da ruhu mai tsarki. (Ayukan Manzanni 1:13-15; 2:1-4) Wannan ya ba da tabbaci cewa an fara amfani da sabon alkawari, ya kuma nuna farkon ikilisiyar Kiristoci da kuma sabuwar al’ummar Isra’ila ta ruhaniya, “Isra’ilan gaske na Allah.”—Galatiyawa 6:16; Ibraniyawa 9:15; 12:23 12:23, 24.

5. Me ya sa Jehobah ya halicci sabuwar “al’umma” maimakon Isra’ila ta zahiri?

5 Doka ta alkawari da aka yi da Isra’ila ta zahiri ba ta fitar da “Mulki na firistoci da al’umma mai-tsarki” waɗanda za su yi hidima har abada a sama ba. (Fitowa 19:5, 6) Yesu ya gaya wa shugabannin addinin Yahudawa: “Za a amshe muku mulkin Allah, za a bayar ga al’umma mai-fitowa da ’ya’yansa.” (Matta 21:43) Wannan al’ummar, wato Isra’ila ta ruhaniya, ta ƙunshi shafaffun Kiristoci da aka haɗa cikin sabuwar alkawari. Ga waɗannan, manzo Bitrus ya rubuta: “Ku zaɓaɓen iri ne, Firistoci basarauci, al’umma mai-tsarki, jama’a abin mulki na Allah kansa, domin ku gwada mafifitan halulluka na wannan wanda ya kiraye ku daga cikin duhu zuwa cikin haskensa mai-ban al’ajabi. Ku da ba jama’a ba ne a dā, amma yanzu jama’ar Allah ne.” (1 Bitrus 2:9, 10) Isra’ila ta zahiri ba mutanen alkawari na Jehobah ba ne kuma. (Ibraniyawa 8:7-13) Kamar yadda Yesu ya faɗa, an ɗauki gatar zama cikin Mulkin Almasihu daga hannun Isra’ila ta zahiri aka ba 144,000 waɗanda suke cikin Isra’ila ta ruhaniya.—Ru’ya ta Yohanna 7:4-8.

An Karɓe su Cikin Alkawarin Mulki

6, 7. Wane alkawari na musamman ne Yesu ya yi da ’yan’uwansa shafaffu a ruhaniya, kuma menene ma’anar wannan a garesu?

6 A daren da Yesu ya kafa ranar Tuna Mutuwarsa, ya gaya wa amintattun manzaninsa: “Ku ne waɗanda kun lizimce ni a cikin jarabtuwana; ni ma na sanya maku mulki, kamar yadda Ubana ya sanya mani, domin ku ci, ku sha tare da ni cikin mulkina; kuma za ku zauna bisa kursiyai, kuna yin shari’a bisa kabilan Isra’ila goma sha biyu.” (Luka 22:28-30) Yesu yana nufin alkawari na musamman da ya yi wa ’yan’uwansa shafaffu 144,000 ta wajen ruhu waɗanda za su yi “aminci har mutuwa” su kuma nuna sun yi “nasara.”—Ru’ya ta Yohanna 2:10; 3:21.

7 Waɗannan mutane ƙalilan sun ƙyale begen rayuwa har abada a duniya a rayuwarsu ta mutane masu jiki da jini. Za su yi sarauta da Yesu a sama, za su zauna bisa kursiyai su hukunta mutane. (Ru’ya ta Yohanna 20:4, 6) Bari mu bincika wasu nassosi da suka shafi shafaffun Kiristoci kawai da kuma waɗanda suka ba da dalilin da ya sa “waɗansu tumaki” ba sa cin isharar Abin Tuni.—Yohanna 10:16.

8. Menene shafaffun Kiristoci suke nunawa sa’ad da suka ci gurasar? (Dubi akwati a shafi na 11.)

8 Shafaffun Kiristoci sun sha wuya kamar yadda Yesu ya sha, shi ya sa suka yarda za su mutu kamar yadda ya mutu. Manzo Bulus yana ɗaya daga cikin rukunin nan kuma ya ce a shirye yake ya sadaukar da kansa domin ya “ribato Kristi . . . in san shi, da ikon tashinsa, da tarayyar raɗaɗinsa.” Hakika, Bulus ya yarda ya ba da kansa don “kamantadda [shi] ga mutuwarsa.” (Filibiyawa 3:8, 10) Shafaffu Kiristoci da yawa sun jimre irin “hatsarin kisa, irin kisan da aka yi wa Yesu.”—2 Korinthiyawa 4:10.

9. Gurasa tana nuna alamar jikin wanene?

9 A lokacin da ya kafa Jibin Maraice na Ubangiji, Yesu ya ce: “Wannan jiki na ne.” (Markus 14:22) Yana nufin jikinsa na zahiri, wanda ba da daɗewa ba za a daka a kuma ɓata da jini. Saboda haka gurasa marar yisti ce ta dace da jikinsa. Me ya sa? Saboda a cikin Littafi Mai Tsarki, yisti yana nufin zunubi ko kuma mugunta. (Matta 16:4, 11, 12; 1 Korinthiyawa 5:6-8) Yesu kamiltacce ne, kuma ba shi da zunubi ko kaɗan. Yesu zai miƙa kamiltaccen jikinsa hadaya. (Ibraniyawa 7:26; 1 Yohanna 2:2) Idan ya yi hakanan zai amfani dukan Kiristoci masu aminci, masu begen rayuwa a sama ko a aljanna ta duniya har abada.—Yohanna 6:51.

10. Ta yaya waɗanda suka sha ruwan inabi suke ‘tare a jikin Kristi’?

10 Game da ruwan inabi da shafaffun Kiristoci suke sha a ranar Tuna Mutuwar Yesu, Bulus ya rubuta: “Ƙoƙon albarka wanda mu ke albarkatasa ba zumunta ta jinin Kristi ba ne?” (1 Korinthiyawa 10:16) A wace hanya ce masu shan ruwan inabi suke ‘tare a cikin jinin Kristi’? Babu shakka ba su ba ne suka ba da fansar hadayar, tun da shi ke su ma suna bukatar fansa. Ta wurin bangaskiyarsu da ikon fansa na jinin Yesu, an gafarta masu zunubansu an kuma kira su masu adalci domin rayuwa a sama. (Romawa 5:8, 9; Titus 3:4-7) Saboda darajar jinin Yesu da aka zubar ne aka “tsarkaka” abokan gadon Kristi 144,000, aka keɓe su, aka tsabtacce su daga zunubi don su zama “tsarkakku.” (Ibraniyawa 10:29; Daniel 7:18,27; Afisawa 2:19) Hakika, da jininsa ne Kristi ya “saye ma Allah mutane daga cikin kowace kabila, da kowane harshe da al’umma, . . . [ya] maishe su su zama mulki da [firistoci] ga Allahnmu; suna kuwa mulki bisa duniya.”—Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10.

11. Menene shafaffu suke nunawa ta wurin shan ruwan inabi na Tuni?

11 Sa’ad da Yesu ya kafa ranar Tuna Mutuwarsa, ya miƙa wa manzanninsa masu aminci ruwan inabi sai ya ce: “Dukanku ku sha daga cikinsa; gama wannan jinina ne na alkawari, wanda an zubar domin mutane dayawa zuwa gafarar zunubai.” (Matta 26:27, 28) Kamar yadda jinin bijimi da na rago suke nuna tabbacin doka ta alkawari da Allah ya yi da Isra’ilawa, haka ma jinin Yesu ya nuna sabuwar alkawarin da Jehobah zai yi da Isra’ila ta ruhu, a ranar Fentakos ta shekara ta 33 A.Z. (Fitowa 24:5-8; Luka 22:20; Ibraniyawa 9:14, 15) Ta wurin shan ruwan inabi da take nuna “jinin alkawarin,” shafaffun Kiristoci sun nuna cewa sun shiga cikin alkawari kuma suna ganin amfaninta.

12. Ta yaya shafaffun Kiristoci suka yi baftisma a cikin mutuwar Yesu?

12 An tunawa shafaffun Kiristoci wani abu kuma daban. Yesu ya gayawa almajiransa masu aminci cewa: “Ƙoƙon da ni zan sha, da shi za ku sha, baftismar da za a yi mini kuwa, da ita za a yi muku.” (Markus 10:38, 39) Bayan haka Manzo Bulus ya yi magana cewa an yi wa Kiristoci “baftismar cikin Almasihu [Yesu] cikin mutuwa tasa.” (Romawa 6:3) Shafaffun Kiristoci sun sadaukar da ransu. Mutuwarsu sadaukarwa ce saboda sun watsar da begen yin rayuwa ta har abada a duniya. Baftisma ta shafaffun Kiristoci cikin mutuwar Yesu za ta cika idan suka mutu a cikin aminci kuma aka tashe su a ruhu su yi “mulki tare da shi” a sama.—2 Timothawus 2:10-12; Romawa 6:5; 1 Korinthiyawa 15:42-44, 50.

Cin Isharar

13. Me Ya sa waɗanda suke da begen rayuwa a duniya ba sa cin ishara ta Tuna Mutuwar Yesu, amma me ya sa suke halartar wannan taron?

13 Tun da shi ke raba gurasa da ruwan inabi da ake yi a ranar Tuna mutuwar Yesu ya shafi dukan waɗannan, ba zai cancanta ba idan waɗanda suke da begen rayuwa a duniya suka ci isharar. Waɗanda suke da begen rayuwa a duniya sun fahimci cewa ba sa cikin shafaffu ’yan’uwan Kristi, ko kuwa cikin sabon alkawari da Jehobah ya yi da waɗanda za su yi mulki da Yesu Kristi. Tun da shi ke “ƙoƙon” yana nufin sabon alkawari, waɗanda suke cikin sabon alkawarin ne kawai za su ci wannan ishara. Waɗanda suke da begen zama kamiltattun mutane a duniya har abada a Mulkin Allah ba su yi baftisma cikin mutuwar Yesu ba kuma ba a kira su ba su yi mulki tare da shi a sama. Idan kuwa suka ci isharar, hakan zai nuna wani abin da ba daidai ba ne game da su. Shi ya sa, ba sa ci, ko da yake sun halarci taron Tuna Mutuwarsa don kiyayewa da darajawa. Suna yi wa Jehobah godiya saboda dukan abubuwa da ya yi masu ta wurin Ɗansa, haɗe da yadda ya gafarta masu zunubansu ta wurin jinin Kristi.

14. Ta yaya ne shafaffun Kiristoci suke samun ƙarfi na ruhaniya ta wurin cin gurasa da shan ruwan inabi?

14 Hatimcewar ƙarshen na adadi ƙalilan na Kiristoci da aka kira su yi mulki da Kristi a sama ya kusa ƙarewa. Har sai ƙarshen rayuwarsu ta sadaukarwa a duniya, shafaffun Kiristoci suna samun ƙarfi na ruhaniya idan suka ci ishara ta Tuna Mutuwar Yesu. Suna haɗa kai da ’yan’uwansu maza da mata na cikin Kristi. Cin isharar gurasa da ruwan inabi na tuna masu da hakkinsu na kasancewa da aminci har mutuwarsu.—2 Bitrus 1:10, 11.

Tattara “Abubuwan da ke Bisa Duniya”

15. Su wanene aka haɗa tare da shafaffun Kiristoci?

15 A tsakiyar shekara ta 1930, an sami ƙaruwar “waɗansu tumaki,” waɗanda ba “ƙaramin garke” ba ne waɗanda kuma begensu na rayuwa ne a duniya, sun yarda da shafaffun Kiristoci. (Yohanna 10:16; Luka 12:32; Zakariya 8:23) Sun zama amintattun abokanan ’yan’uwan Kristi, suna taimaka musu sosai ta wurin ‘bisharar mulki’ domin shaida ga dukan al’ummai. (Matta 24:14; 25:40) Ta haka, sun ba da kansu ga Yesu su zama “tumakinsa” da suke “hannun damansa” na alheri sa’ad da ya zo ya yi wa dukan al’ummai shari’a. (Matta 25:33-36, 46) Ta wurin ba da gaskiya ga jinin Yesu za su zama taro “mai-girma,” waɗanda za su tsira daga “babban tsananin.”—Ru’ya ta Yohanna 7:9-14.

16. “Abubuwan da ke bisa duniya” za su haɗa da su wanene, kuma ta yaya dukansu za su sami zarafin zama “ ’ya’yan Allah”?

16 Sa’ad da aka kammala hatimce sauran shafaffu 144,000, za a ƙyale “iskoki” da za su faɗā wa muguwar duniya ta Shaiɗan. (Ru’ya ta Yohanna 7:1-4) A lokacin sarauta ta shekara dubu ta Yesu da abokansa sarakuna da firistoci, babban taro za ta sadu da mutane da babu iyaka waɗanda aka tashe su daga matattu. (Ru’ya ta Yohanna 20:12,13) Waɗannan za su samu zarafi na zama mutanen da za su rayu a Mulkin Almasihu, Yesu Kristi a duniya har abada. A ƙarshen Sarauta ta Shekara Dubu, za a miƙa dukan “abubuwa da ke duniya” ga gwaji na ƙarshe. Waɗanda suka kasance da aminci za su zama “ ’ya’yan Allah” a duniya.—Afisawa 1:10; Romawa 8:21; Ru’ya ta Yohanna 20:7, 8.

17. Ta yaya nufin Jehobah zai cika?

17 Ta wurin wakilcinsa ko kuma ta hanyar gyaran abubuwa, Jehobah zai cika nufinsa ta wurin “tattara dukan abu cikin Kristi, abubuwan da ke cikin sammai da abubuwan da ke bisa duniya.” Za a tattara dukan halittu masu basira da ke sama da waɗanda ke duniya a cikin salama ta sararin samaniya, waɗanda suke yin biyayya ga mulkin Mai Ƙuduri Mai Girma, Jehobah.

18. Ta yaya shafaffun Kiristoci tare da abokansu za su amfana a taron Tuna Mutuwar Yesu?

18 Bangaskiyar shafaffu Kiristoci da suka rage tare da abokansu waɗansu tumaki miliyoyin zai ƙara ƙarfafa sa’ad da suka taru a ranar 12 ga watan Afrilu ta 2006! Za su kiyaye ranar Tuna Mutuwar Yesu, kamar yadda Yesu ya umurce su: “Ku yi wannan abin tunawa da ni.” (Luka 22:19) Waɗanda suka hallara za su tuna abin da Jehobah ya yi masu ta wurin ƙaunataccen Ɗansa, Yesu Kristi.

Domin Bita

• Menene nufin Jehobah ga abubuwan da ke sama da abubuwan da ke duniya?

• Su wanene “abubuwan da ke sammai,” kuma ta yaya aka tara su?

• Su wanene ne “abubuwan da ke duniya,” kuma wane bege ne suke da shi?

[Akwati a shafi na 11]

“Jikin Kristi”

A cikin 1 Korinthiyawa 10:16, 17, an tattauna muhimmancin gurasa na ’yan’uwan Kristi shafaffu na ruhu, Bulus ya yi amfani da kalmar “jiki.” Ya ce: “Dunƙulen gurasa da mu ke karkarye, ba zumuntar jikin Kristi ba ne? Da shi ke fa mu, da mu ke dayawa, dunƙule ɗaya ne, jiki ɗaya ne, gama mu duka muna tarayya daga cikin dunƙule ɗaya.” Sa’ad da shafaffun Kiristoci suka ci gurasar Tuna Mutuwar Yesu, suna nuna haɗin kansu ne ga ikilisiyar Kiristoci shafaffu, wadda kamar jiki take da Kristi ne shugabanta.—Matta 23:10; 1 Korantiyawa 12:12, 13, 18.

[Hotuna a shafi na 11]

Me ya sa shafaffun Kiristoci ne kaɗai suke cin gurasa suke kuma shan ruwan inabi?

[Hoto a shafi na 13]

A tsarin Jehobah, dukan halittu a sama da kuma a duniya za su jitu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba