Garke Ɗaya, Makiyayi Ɗaya
“Ku da kuka biyo ni . . . ku kuma za ku zauna bisa kursiyi goma sha biyu, kuna mallakar kabilan goma sha biyu na Israila.”—MAT. 19:28.
1. Yaya Jehobah ya bi da zuriyar Ibrahim, kuma me ya sa hakan ba ya nufin cewa ya ƙi da sauran mutane gabaki ɗaya?
JEHOBAH yana ƙaunar Ibrahim, saboda haka, ya nuna ƙauna ta aminci ga zuriyar Ibrahim. Fiye da ƙarnuka goma sha biyar, ya ɗauki al’ummar Isra’ila da ta fito daga Ibrahim a matsayin mutanensa zaɓaɓu, ‘al’ummarsa keɓaɓiya.’ (Karanta Kubawar Shari’a 7:6.) Hakan yana nufin cewa Jehobah ya ƙi mutanen wasu al’ummai gabaki ɗaya? A’a. A wannan lokacin, an ƙyale waɗanda ba Isra’ilawa ba ne da suke son su bauta wa Jehobah su bi al’ummarsa keɓaɓiya. An ɗauki waɗannan shigaggu a matsayin sashen wannan al’ummar. Za a bi da su a matsayin ’yan’uwa. (Lev. 19:33, 34) An bukace su su yi biyayya ga dukan dokokin Jehobah.—Lev. 24:22.
2. Wane shela mai ban mamaki ne Yesu ya yi, hakan ya ta da waɗanne tambayoyi?
2 Amma, Yesu ya yi wannan shela mai ban mamaki ga Yahudawa na zamaninsa: “Za a amshe mulkin Allah daga hannunku, za a bayar ga al’umma mai-fitowa da ’ya’yansa.” (Mat. 21:43) Su waye ne suke cikin wannan sabuwar al’umma, kuma yaya wannan canjin ya shafe mu a yau?
Sabuwar Al’umma
3, 4. (a) Yaya manzo Bitrus ya nuna sabuwar al’umma? (b) Su waye ne suke cikin wannan sabuwar al’umma?
3 Manzo Bitrus ya nuna wannan sabuwar al’umma sarai. Ya rubuta wa ’yan’uwansa Kiristoci: “Ku zaɓaɓen iri ne, zuriyar firist ba-sarauci, al’umma mai-tsarki, jama’a abin mulki na Allah kansa, domin ku gwada mafifitan halulluka na wannan wanda ya kiraye ku daga cikin duhu zuwa cikin haskensa mai-ban al’ajibi.” (1 Bit. 2:9) Kamar yadda aka annabta, Yahudawa da suka amince da Yesu a matsayin Almasihu ne mutane na farko na wannan sabuwar al’umma. (Dan. 9:27; Mat. 10:6) Daga baya, an haɗa waɗanda ba Isra’ilawa ba ne da yawa a cikin wannan al’ummar, don Bitrus ya ci gaba da cewa: “Ku da ba jama’a ba ne a dā, amma yanzu jama’ar Allah ne.”—1 Bit. 2:10.
4 Su waye ne Bitrus yake maganarsu a nan? A farkon wasiƙarsa, ya ce: “[Allah] wanda ya maya haihuwarmu bisa ga jinƙansa mai-girma zuwa bege mai-rai ta wurin tashin Yesu Kristi daga matattu, zuwa gādo marar-ruɓewa, marar-ƙazantuwa, wanda ba shi yanƙwanewa, ajiyayye a sama dominku.” (1 Bit. 1:3, 4) Saboda haka, wannan sabuwar al’umma ta ƙunshi shafaffun Kiristoci, waɗanda suke da begen zuwa sama. Su ne “Isra’ila na Allah.” (Gal. 6:16) A cikin wani wahayi, manzo Yohanna ya ga cewa adadin waɗannan Isra’ila na ruhaniya ya kai 144,000. An “fanshi waɗannan daga cikin mutane, su zama nunan fari ga Allah da Ɗan rago” don su yi hidima na “firistoci” kuma “su yi mulki kuma tare da shi [Yesu] shekara dubu.”—R. Yoh. 5:10; 7:4; 14:1, 4; 20:6; Yaƙ. 1:18.
An Haɗa Wasu Al’ummai Ne?
5. (a) Su waye ne wannan furci “Isra’ila na Allah” yake nuni? (b) Menene ya nuna cewa kalmar nan “Isra’ila” tana da wata ma’ana?
5 A bayane yake cewa furcin nan “Isra’ila na Allah” da ke Galatiyawa 6:16 yana nuni ga shafaffun Kiristoci kaɗai. Amma, shin da akwai misalai inda Jehobah ya yi amfani da al’ummar Isra’ila a matsayin hoto ko kuma kwatanci, da ya ƙunshi Kiristoci fiye da shafaffu? Za a samu amsar a waɗannan kalaman Yesu ga manzanninsa masu aminci: ‘Na sanya maku mulki, kamar yadda Ubana ya sanya mani, domin ku ci, ku sha tare da ni cikin mulkina; kuma za ku zauna bisa kursiyai, kuna yin shari’a bisa kabilan Isra’ila goma sha biyu.’ (Luk 22:28-30) Hakan zai faru a lokacin “sabonta,” ko kuma sake maidowa, a lokacin Sarauta ta Shekara Dubu na Kristi.—Karanta Matta 19:28.
6, 7. Su waye ne furcin nan “kabilan Isra’ila goma sha biyu” yake nuni a cikin mahallin Matta 19:28 da Luka 22:30?
6 Mutane 144,000 za su yi hidima na sarakuna, firistoci, alkalai a lokacin Sarauta ta Shekaru Dubu. (R. Yoh. 20:4) Su waye ne za su yi wa shari’a kuma bisa su wanene za su yi sarauta? A Matta 19:28 da Luka 22:30, an gaya mana cewa za su yi shari’a bisa “kabilan Isra’ila goma sha biyu.” Su waye ne “kabilan Isra’ila goma sha biyu” a wannan mahallin? Suna wakiltan dukan waɗanda suke da begen zama a duniya, wato, waɗanda suka ba da gaskiya a hadayar Yesu amma ba a haɗa su cikin rukunin sarauta na firistoci ba. (Ba a haɗa kabilar Lawi a cikin tsarin ƙabilu goma sha biyu na Isra’ila na zahiri ba.) Waɗanda ƙabilu goma sha biyu na Isra’ila suke wakilta a wannan mahallin su ne waɗanda za su samu fa’idodi na ruhaniya daga hidimomi na firistoci na 144,000. Waɗannan da ba firistoci ba da za su amfana, su ma mutanen Allah ne, kuma yana ƙaunarsu da kuma amince da su. Ya dace da aka kamanta su da mutanensa na zamanin dā.
7 Ya dace da bayan da manzo Yohanna ya ga Isra’ilawa na ruhaniya guda 144,000 da aka saka wa hatimi na dindindin kafin ƙunci mai girma, ya kuma lura cewa da akwai “taro mai-girma” da ba mai ƙirgawa da suka fito daga ‘dukan kabilai.’ (R. Yoh. 7:9) Waɗannan za su tsira daga ƙunci mai girma zuwa cikin Sarautar Kristi na Shekara Dubu. Biliyoyin mutane da aka ta da daga matattu za su haɗu da su a wajen. (Yoh. 5:28, 29; R. Yoh. 20:13) Dukan waɗannan za su kasance cikin “kabilan Isra’ila goma sha biyu” da Yesu da abokan sarautarsa 144,000 za su yi musu shari’a.—A. M. 17:31; 24:15; R. Yoh. 20:12.
8. Ta yaya abubuwa da suka faru a Ranar Kafara da ake yi kowace shekara take alamta dangantaka da ke tsakanin 144,000 da sauran ’yan Adam?
8 An alamta wannan dangantaka tsakanin 144,000 da sauran ’yan Adam a Ranar Kafara da ake yi kowace shekara. (Lev. 16:6-10) Da farko, ana bukatar babban firist ya yi hadaya da bijimi don zunubi “domin kansa kuma da gidansa.” Saboda haka, za a yi amfani da hadayar Yesu da farko ga iyalin gidansa na mataimakin firistoci, wato, waɗanda za su yi hidima tare da shi a sama. A Ranar Kafara na dā, ana tanadin awaki biyu don zunuban sauran Isra’ilawa. A wannan yanayin da ƙabila na firistoci take wakilta 144,000, sauran Isra’ilawa suna hoton dukan waɗanda suke da begen zama a duniya. Hakan ya nuna cewa kalmar nan “kabilan Isra’ila goma sha biyu” ba ta nufin mataimakan firistoci da Yesu ya shafa da ruhu kawai ba amma ya haɗa da sauran mutane da suka ba da gaskiya ga hadayar Yesu.a
9. Su waye ne firistoci a wahayin Ezekiel na haikali suke wakilta, kuma su waye ne Isra’ilawa da ba firistoci ba ne suke wakilta?
9 Ka yi la’akari da wani misali. An nuna wa annabi Ezekiel wahayi mai girma na haikalin Jehobah. (Ezek., surori na 40-48) A wannan wahayin, firistoci suna aiki a cikin haikali, suna ba da umurni da kuma karɓan gargaɗin Jehobah da gyara. (Ezek. 44:23-31) A wannan wahayin kuma, waɗanda suke cikin ƙabilu dabam dabam sun zo su yi bauta kuma su miƙa hadayu. (Ezek. 45:16, 17) A cikin wannan mahallin, firistocin suna alamta shafaffu, yayin nan kuma Isra’ilawa daga ƙabilu da ba firistoci ba ne suna alamta waɗanda suke da begen zama a duniya. Wahayin ya nanata cewa rukuni biyun suna aiki tare da haɗin kai, kuma rukunin firistoci suna yin ja-gora a bauta ta gaskiya.
10, 11. (a) Wane cikawa mai ƙarfafa bangaskiya na kalaman Yesu muka gani? (b) Waɗanne tambayoyi suka taso game da waɗansu tumaki?
10 Yesu ya yi maganar “waɗansu tumaki” waɗanda ba za su kasance cikin “garke” ɗaya da “ƙaramin garke” na mabiyansa shafaffu. (Yoh. 10:16; Luk 12:32) Ya ce: “Su kuma dole zan kawo, za su kuma ji muryata: ya zama garke ɗaya, makiyayi ɗaya.” Ganin cikar waɗannan kalaman yana ƙarfafa bangaskiya! An haɗa rukunin mutane biyu tare, wato, ƙaramin rukuni na shafaffu da kuma taro mai girma na waɗansu tumaki. (Karanta Zakariya 8:23.) Ko da yake a alamance waɗansu tumaki ba sa hidima a cikin farfajiya na ciki na haikali na ruhaniya, suna hidima a farfajiya na waje na wannan haikalin.
11 Amma idan Jehobah a wani lokaci yana amfani da waɗanda ba firistoci a Isra’ila ta dā da suke wakiltar waɗannan waɗansu tumaki, ya kamata waɗanda suke da begen zama a duniya su ma su ci ishara na tuna mutuwar Yesu ne? Za mu bincika amsar wannan tambayar yanzu.
Sabon Alkawari
12. Wane sabon shiri ne Jehobah ya annabta?
12 Jehobah ya annabta sabon shiri don mutanensa sa’ad da ya faɗa: “Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila bayan waɗannan kwanaki . . . zan sa shari’ata a cikinsu, zan rubuta ta a cikin zuciyarsu: in zama Allahnsu, su zama mutanena.” (Irm. 31:31-33) Ta wurin wannan sabon alkawari, alkawarin da Jehobah ya yi wa Ibrahim zai samu cikawa mai ɗaukaka kuma na dindindin.—Karanta Farawa 22:18.
13, 14. (a) Su waye ne suke cikin sabon alkawarin? (b) Su waye ne za su amfana, kuma yaya suka ‘riƙe’ wannan sabon alkawari?
13 Yesu ya yi nuni ga wannan sabon alkawari daddare kafin mutuwarsa sa’ad da ya ce: “Wannan ƙoƙo sabon alkawali ne cikin jinina, wanda an zubas dominku.” (Luk 22:20; 1 Kor. 11:25) An haɗa dukan Kiristoci a cikin wannan sabon alkawari? A’a. Wasu, kamar manzanni da suka sha daga cikin wannan ƙoƙon a wannan maraice, suna cikin sabon alkawarin.b Yesu ya ɗauki wani alkawari da su su yi sarauta tare da shi a Mulkinsa. (Luk 22:28-30) Za su yi sarauta tare da Yesu a Mulkinsa.—Luk 22:15, 16.
14 Waɗanda za su zauna a duniya a ƙarƙashin Mulkinsa kuma fa? Za su amfana daga sabon alkawarin. (Gal. 3:8, 9) Ko da yake ba sa ciki, ‘sun riƙe’ wannan alkawarin ta wurin miƙa kai ga bukatunsa, kamar yadda annabi Ishaya ya annabta: ‘Baƙi kuma, waɗanda suka haɗu ga Ubangiji, domin su yi masa hidima, su ƙaunaci sunan Ubangiji, su zama bayinsa, kowane wanda ya tsare assabbat, ba ya tozartar da ita ba, yana kuwa riƙe da wa’adina: Su dai sai in kawo su wurin dutsena mai-tsarki, in faranta zuciyarsu a cikin gidana na addu’a.’ Sai Jehobah ya ce: “Za a ce da gidana gidan addu’a domin dukan al’ummai.”—Isha. 56:6, 7.
Su Waye ya Kamata Su Ci Isharar?
15, 16. (a) Ga wane gata ne manzo Bulus ya haɗa waɗanda suke cikin sabon alkawari? (b) Me ya sa waɗanda suke da begen zama a duniya ba za su ci ishara na tuna mutuwar Yesu ba?
15 Waɗanda suke cikin sabon alkawari suna da “gaba gaɗi . . . shiga cikin wuri mai-tsarki.” (Karanta Ibraniyawa 10:15-20.) Su ne waɗanda za su ‘karɓi mulki wanda ba shi girgizuwa.’ (Ibran. 12:28) Saboda haka, sai waɗanda za su zama sarakuna da firistoci a sama da Yesu Kristi ne ya kamata su sha daga “ƙoƙon” da ke wakiltar sabon alkawari. Waɗannan da suke cikin sabon alkawari ne Ɗan Ragon ya yi wa alkawarin aure. (2 Kor. 11:2; R. Yoh. 21:2, 9) Dukan waɗanda suke halartan Tuna Mutuwar Yesu da ake yi kowace shekara, waɗanda ba sa cin isharar, masu lura abin da ake yi ne cikin ladabi.
16 Bulus ya kuma taimaka mana mu fahimci cewa waɗanda suke da begen zama a duniya ba sa cin isharar Tuna mutuwar Yesu. Ya gaya wa shafaffu Kiristoci: ‘Kowane lokacin da ku ke cin wannan gurasa, kuna kuwa shan ƙoƙon, kuna shelar mutuwar Ubangiji har ya zo.’ (1 Kor. 11:26) A wane lokaci ne Ubangiji ‘ya zo’? Sa’ad da ya zo ya ɗauki rukuni na ƙarshe na amaryarsa shafaffu zuwa gidansu na samaniya. (Yoh. 14:2, 3) Hakika, Jibin Maraice na Ubangiji da ake yi kowace shekara ba zai ci gaba har matuƙa ba. “Sauran” zuriyar macen da har ila suke duniya za su ci gaba da cin wannan jibin har sai dukansu sun karɓi ladarsu na samaniya. (R. Yoh. 12:17) Amma, da a ce waɗanda za su yi rayuwa har abada a duniya suna cin isharar, za a ci gaba da cin wannan jibin Tuna Mutuwa har abada.
Za “Su Zama Mutanena”
17, 18. Yaya aka cika annabci da ke rubuce a Ezekiel 37:26, 27?
17 Jehobah ya annabta haɗin kan mutanensa da waɗannan kalaman: “Zan yi alkawari na salama da su: za ya zama madawwamin alkawari da su: zan zamshe su, in riɓanɓanya su, in kafa wurina mai-tsarki a cikin tsakiyarsu har abada. Mazaunin kuma za ya zama wurinsu; zan zama Allahnsu, su kuma su zama mutanena.”—Ezek. 37:26, 27.
18 Dukan mutanen Allah suna iya amfana daga cikar wannan alkawari mai ban al’ajabi, wannan alkawari na salama. Hakika, Jehobah ya tabbatar wa dukan bayinsa masu biyayya cewa za su samu salama. Ɗiyan ruhunsa yana bayane a tsakaninsu. Wurinsa mai tsarki, da ke nuna bauta mai tsarki na Kirista, yana tsakaninsu. Da gaske sun zama mutanensa, don sun yasar da dukan fannoni na bautar gumaka kuma suna bauta wa Jehobah kaɗai.
19, 20. Su waye aka haɗa cikin waɗanda Jehobah ya kira “mutanena,” kuma menene sabon alkawari ya sa ya yiwu?
19 Abin ban sha’awa ne a shaida haɗin kan wannan rukuni biyu a zamaninmu! Ko da yake taro mai girma da suke ƙaruwa ba su da begen zuwan sama, suna fahariyar yin tarayya da waɗanda suke da wannan begen. Sun haɗa kansu ga Isra’ila na Allah. Ta yin hakan, an haɗa su cikin waɗanda Jehobah ya kira “mutanena.” Wannan annabci yana cikawa a kan su: ‘Al’ummai da yawa za su haɗa kansu ga Ubangiji a cikin wannan rana, za su zama jama’ata; ni ma zan zauna a tsakiyarki.’—Zech. 2:11; 8:21; karanta Ishaya 65:22; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.
20 Ta hanyar sabon alkawari, Jehobah ya sa dukan wannan ya yiwu. Miliyoyin mutane daga al’ummai dabam dabam sun zama sashen mutanen Jehobah da aka amince da su. (Mi. 4:1-5) Sun ƙuduri aniya su ci gaba da riƙe wannan alkawari ta wajen amincewa da tanadodinsa da kuma yin biyayya ga bukatunsa. (Isha. 56:6, 7) Ta yin hakan, suna more albarka mai yawa na ci gaba da kasancewa da salama tare da Isra’ila na Allah. Bari ka shaida hakan a yanzu da kuma nan gaba!
[Hasiya]
a Hakanan ma, ana ce da shafaffu a matsayin “ikilisiya.” (Ibran. 12:23) Amma, kalmar nan “ikilisiya” tana da ƙarin ma’ana, tana nuni ga dukan Kiristoci, ko da menene begensu.—Ka duba Hasumiyar Tsaro, 1 ga Mayu, 2007, shafuffuka na 7-10.
b Yesu shi ne Matsakanci na wannan alkawari. A matsayin Matsakanci, bai ci isharar ba.
Ka Tuna?
• Su waye ne “kabilan Isra’ila goma sha biyu” da mutane 144,000 za su yi wa shari’a?
• Menene dangantaka na shafaffu da kuma waɗansu tumaki ga sabon alkawari?
• Ya kamata dukan Kiristoci su ci ishara na tuna mutuwar Yesu?
• Wane haɗin kai aka annabta don zamaninmu?
[Zane/Hotuna da ke shafi na 25]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
Mutane da yawa yanzu suna hidima tare da Isra’ila na Allah
7,313,173
4,017,213
1,483,430
373,430
1950 1970 1990 2009