Kana Tambaya Kuwa, “Ina Ubangiji?”
“Za su yi nesa da ni . . . Ba su kuwa ce, Ina Ubangiji”?—IRMIYA 2:5, 6.
1. Yayin da mutane suka yi tambaya “Ina Allah,” menene ƙila suke nufi?
“INA Allah?” Mutane da yawa sun yi wannan tambayar. Wasu suna ƙoƙarin su fahimci gaskiya ne game da Mahalicci, watau, ina yake da zama? Wasu kuma sukan yi tambaya bayan wani bala’i ko kuma bayan sun sha wahala ne da ba su fahimci dalilin da ya sa Allah bai sa hannu ba. Wasu kuma ba su ma yi tambaya ba domin sun ƙi ra’ayin cewa Allah yana wanzuwa.—Zabura 10:4.
2. Su wa suke nasara a biɗan Allah?
2 Hakika, da akwai mutane da yawa da suke da tabbaci mai yawa cewa akwai Allah. (Zabura 19:1; 104:24) Wasu cikinsu sun gamsu da kasancewa da wani addini kawai. Amma ƙauna mai zurfi ga gaskiya ta motsa wasu miliyoyi, a dukan ƙasashe su biɗi Allah na gaskiya. Ƙoƙarinsu bai zama banza ba domin “ba shi da nisa da kowanne ɗayanmu ba.”—Ayukan Manzanni 17:26-28.
3. (a) Ina ne wurin zaman Allah? (b) Menene ake nufi da tambayar nan ta Nassi, “Ina Ubangiji?”
3 Yayin da mutum ya sami Jehovah da gaske, zai fahimci cewa “Allah ruhu ne,” marar ganuwa ga idanun mutum. (Yohanna 4:24) Yesu ya yi nuni ga Allah na gaskiya cewa “Ubana wanda ke cikin sama.” Me wannan yake nufi? Cewa inda Uba na samaniya yake, a azanci na ruhaniya, yana da girma kamar yadda sammai da ake gani suke saman duniya. (Tafiyar tsutsa ta mu ce, Matta 12:50; Ishaya 63:15.) Saboda ba ma iya ganin Allah da idanunmu, yana sa ya yiwu mu san shi kuma mu koyi nufe-nufensa sosai. (Fitowa 33:20; 34:6, 7) Yana amsa tambayoyin da sahihai da suke neman sanin ma’anar rayuwa ke yi. Game da batutuwa da ke shafar rayuwarmu, yana tanadin tushe mai kyau don mu san matsayinsa, watau, yadda yake ji game da batutuwan ko sha’awoyinmu sun jitu da nufe-nufensa. Yana son mu yi bincike game da irin batutuwan nan kuma mu yi ƙoƙari sosai mu sami amsoshinsu. Ta wurin annabi Irmiya, Jehovah ya yi wa mutanen Isra’ila ta dā horo domin sun ƙi yin haka. Sun san sunan Allah, amma ba su yi tambaya ba, “Ina Ubangiji?” (Irmiya 2:6) Nufin Jehovah ba shi ne muhimmin abin da ke damunsu ba. Ba sa biɗan ja-gorarsa. Idan kana bukatar tsai da shawara, babba ko ƙarami, kana tambaya, “Ina Ubangiji?”
Waɗanda Suke Biɗan Allah
4. Ta yaya za mu amfana daga misalin Dauda mu biɗi Jehovah?
4 Lokacin da yake matashi, Dauda ɗan Jesse, ya gina bangaskiya mai ƙarfi wurin Jehovah. Ya san Jehovah “Allah mai rai” ne. Dauda kansa ya shaida kāriyar Jehovah. Bangaskiya da ƙauna ga “sunan Ubangiji,” sun motsa Dauda ya kashe gwarzo Bafilisti Goliath. (1 Samu’ila 17:26, 34-51) Amma, nasarar da Dauda ya yi ba ta sa ya dogara ga kansa ba. Bai yi tunanin cewa kome da ya yi yanzu, Jehovah zai albarkace shi. Sau da yawa cikin shekarun da suka biyo baya, Dauda ya biɗi Jehovah yayin da yake bukatar yanke shawara. (1 Samu’ila 23:2; 30:8; 2 Samu’ila 2:1; 5:19) Ya ci gaba da addu’a: “Ya Ubangiji, ka nuna mini tafarkunka; ka koya mini hanyoyinka. Ka bishe ni cikin gaskiyarka, ka koya mini; gama kai ne Allah na cetona; A gareka ni ke sauraro dukan yini.” (Zabura 25:4, 5) Hakika kuwa, misali ne mai kyau don mu bi!
5, 6. Ta yaya Jehoshaphat ya nemi Jehovah a wasu lokatai a rayuwarsa?
5 A zamanin Sarki Jehoshaphat, sarki na biyar a zuriyar Dauda, rundunan al’ummai uku suka haɗa kai za su yaƙi Yahuda. Yayin da ya fuskanci wannan yanayi na gaggawa ta ƙasarsa, Jehoshaphat “ya sa zuciyatasa ga neman Ubangiji.” (2 Labarbaru 20:1-3) Wannan ba shi ne lokaci na farko ba da Jehoshaphat ya nemi Jehovah. Sarkin ya yi banza da bautar Baal ta masarautar arewa ta Isra’ila da suka yi ridda, kuma ya zaɓi ya yi tafiya a hanyar Jehovah. (2 Labarbaru 17:3, 4) Saboda haka, yanzu da ya fuskanci tashin hankali, yaya Jehoshaphat ya ‘nemi Jehovah’?
6 A cikin wata addu’a da ya yi a fili a Urushalima a wannan lokaci, Jehoshaphat ya nuna cewa ya tuna da ikon Jehovah maɗaukaki duka. Ya yi tunani sosai a kan ƙudurin Jehovah da ke bayyane cikin yadda Yake kawar da wasu al’ummai kuma yana ba da wata ƙasa ga Isra’ila gadō. Sarkin ya nuna yana da bukatar taimakon Jehovah. (2 Labarbaru 20:6-12) Jehovah ya yarda ya same shi kuwa a wannan lokacin? Hakika kuwa. Jehovah ya ba da takamammun umurni ta bakin Jahaziel, Balawi, kuma washegari ya ba da nasara ga Mutanensa. (2 Labarbaru 20:14-28) Ta yaya za ka tabbata cewa Jehovah zai yarda maka kai ma ka same shi lokacin da kake nemansa domin ja-gora?
7. Addu’o’in su wa Allah yake saurara?
7 Jehovah ba ya wariya. Yana gayyatar mutane na dukan al’ummai su biɗe shi ta wurin addu’a. (Zabura 65:2; Ayukan Manzanni 10:34, 35) Yana lura da abin da ke zuciyar waɗanda suke roƙonsa. Yana tabbatar mana cewa yana jin addu’o’in masu adalci. (Misalai 15:29) Yana yarda waɗanda ba sa sonsa dā amma da yanzu suke neman ja-gorarsa cikin tawali’u su same shi. (Ishaya 65:1) Har ma yana jin addu’o’in waɗanda suka ƙi bin dokarsa amma da yanzu sun tuba cikin tawali’u. (Zabura 32:5, 6; Ayukan Manzanni 3:19) Amma, idan zuciyar mutum ba ta biyayya ga Allah, addu’o’insa banza ne. (Markus 7:6, 7) Ga wasu misalai.
Sun Roƙa Amma Ba a Ba Su Ba
8. Me ya sa Jehovah bai yarda da addu’o’in Sarki Saul ba?
8 Bayan da annabi Sama’ila ya gaya wa Sarki Saul cewa Allah ya ƙi shi domin rashin biyayyarsa, Saul ya yi sujjada a gaban Jehovah. (1 Samu’ila 15:30, 31) Amma riya ce kawai ya yi. Burin Saul ba cewa ya yi wa Allah biyayya ba ne, amma mutane su girmama shi. Daga baya, Filistiya suka fara yaƙan Isra’ila, Saul ya soma lamunin cewa yana biɗan Jehovah. Amma da ba a amsa masa ba, ya je wajen mabiya ko da yake ya san Jehovah ya haramta hakan. (Kubawar Shari’a 18:10-12; 1 Samu’ila 28:6, 7) A taƙaita batun, 1 Labarbaru 10:14 ta ce game da Saul: “Ba ya biɗi Ubangiji ba.” Me ya sa? Domin addu’o’in Saul ba daga tabbatacciyar bangaskiya ba ne. Saboda haka, daidai yake da rashin addu’a.
9. Menene ba daidai ba a roƙon da Zedekiya ya yi game da ja-gorar Jehovah?
9 Haka nan kuma, da ƙarshen mulkin Yahuda ya jawo kusa, an daɗa yin addu’o’i kuma ana zuwa wajen annabawan Jehovah sosai. Amma mutanen suna dagula bautar gumaka da girmama Jehovah. (Zephaniah 1:4-6) Ko da yake sun yi lamunin biɗan Allah, amma ba su shirya zukatansu ba su ba da kai ga yin nufinsa. Sarki Zedekiya ya roƙi Irmiya ya biɗi Jehovah dominsa. Jehovah ya riga ya gaya wa sarki abin da dole ne ya yi. Amma domin rashin bangaskiya da tsoron mutum, sarkin ya ƙi yin biyayya ga muryar Jehovah, ta haka Jehovah bai ba shi amsar da ƙila zai so ya ji ba.—Irmiya 21:1-12; 38:14-19.
10. Menene ba daidai ba a hanyar da Johanan ya biɗi ja-gorar Jehovah, kuma me za mu koya daga kuskurensa?
10 Bayan an halaka Urushalima, rundunar Babila suka tashi tare da Yahudawa masu bauta, Johanan ya yi shiri ya kwashi ƙaramin rukunin Yahudawa da ya rage a Yahuda zuwa ƙasar Masar. Suka yi shiri, amma kafin su fara tafiya suka ce Irmiya ya yi addu’a dominsu kuma ya biɗi musu ja-gorar Jehovah. Amma, domin ba su sami amsar da suke so ba, sun ci gaba cikin abin da suka ƙudura niyyar yi. (Irmiya 41:16–43:7) Ka ga darussa cikin waɗannan aukuwa da za su taimake ka a lokacin da kake son ka zo gaban Jehovah, har ya yarda ka same shi?
“Kuna Gwada Abin da ke na Yarda”
11. Me ya sa muke bukatar mu yi amfani da Afisawa 5:10?
11 Bauta ta gaskiya ta fi kawai mutum ya nuna alamar keɓe kansa ta wurin baftisma cikin ruwa, da halartan taron ikilisiya, da kuma saka hannu cikin hidimar fage. Ta shafi dukan hanyar rayuwarmu. Kowacce rana muna shan matsi—a kaikaice, wasu kuma kai tsaye—da za su iya kawar da mu daga hanya ta ibada. Ta yaya za mu bi waɗannan? Yayin da manzo Bulus yake rubuta wa Kiristoci masu aminci a Afisus ya aririce su: “Kuna gwada abin da ke na yarda ga Ubangiji.” (Afisawa 5:10) An nuna hikimar yin haka cikin yanayi da yawa da aka rubuta cikin Nassosi.
12. Me ya sa Jehovah ya baƙanta sa’ad da Dauda ya kai sunduƙin alkawari Urushalima?
12 Bayan da aka mayar da sunduƙin alkawari na Isra’ila kuma ya zauna na shekaru da yawa a Kiriath-jearim, Sarki Dauda ya so ya kai shi Urushalima. Ya nemi shawarar hakiman mutanen kuma ya ce za a ɗauki Sunduƙin ‘idan sun yarda kuma idan zai gamshi Jehovah.’ Amma bai bincika sosai ya tabbata nufin Jehovah game da batun ba. Da ya yi haka, da ba za a ɗora Sunduƙin bisa keken shanu ba. Da Kohatawa na Lawi sun ɗauka a kafaɗarsu, yadda Allah ya bayyana sarai. Ko da yake sau da sau Dauda yana biɗan Jehovah, a wannan lokaci ya kasa yin haka a hanyar da ta dace. Sakamakon ya zama bala’i. Daga baya, Dauda ya fahimci cewa: “Ubangiji, ya auko mana, da shi ke ba mu neme shi bisa ga ƙa’ida ba.”—1 Labarbaru 13:1-3; 15:11-13; Litafin Lissafi 4:4-6, 15; 7:1-9.
13. A cikin waƙar da aka rera lokacin da aka yi nasarar ƙaura da Sunduƙin, wace tunasarwa aka haɗa ciki?
13 A ƙarshe da Lawiyawa suka ɗauki Sunduƙin daga gidan Obed-edom zuwa Urushalima, Dauda ya shirya waƙa da aka rera. Ya haɗa da tunasarwa mai kyau: “Ku biɗi Ubangiji da ikonsa; Ku biɗi fuskatasa tuttur. Ku tuna da ayyukan da ya yi na ban mamaki; al’ajabansa kuma, da shari’un bakinsa.”—1 Labarbaru 16:11, 12.
14. Ta yaya za mu amfana daga misalin kirki na Sulemanu kuma daga kuskurensa a rayuwarsa ta gaba?
14 Kafin mutuwarsa, Dauda ya gargaɗi ɗansa Sulemanu: “Idan ka biɗe [Jehovah], yā samu gareka.” (1 Labarbaru 28:9) Da ya hau kursiyi, Sulemanu ya je Gibiyon, inda alfarwar taro take kuma ya yi wa Jehovah hadaya. A wurin Jehovah ya gaya wa Sulemanu: “Ka roƙi abin da zan ba ka.” A amsa roƙon Sulemanu, Jehovah ya ba shi hikima da sani da zai zama alƙali a Isra’ila, kuma ya daɗa masa wadata da girma. (2 Labarbaru 1:3-12) Ta wurin yin amfani da tsarin gini da Jehovah ya ba wa Dauda, Sulemanu ya gina babban haikali. Amma a batun aurensa, Sulemanu ya kasa biɗan Jehovah. Sulemanu ya auri mata da ba sa bauta wa Jehovah. A shekarunsa na gaba, suka kawar da zuciyarsa daga Jehovah. (1 Sarakuna 11:1-10) Ko yaya aka san da mu, mai hikima, ko mai ilimi, muhimmin abu ne muna “gwada abin da ke na yarda ga Ubangiji”!
15. Yayin da Zerah Habashi ya kai wa Yahuda hari, me ya sa Asa ya yi addu’a da gaba gaɗi cewa Jehovah zai ceci Yahuda?
15 Labarin sarautar Asa, tattaɓa-kunnen Sulemanu ya nanata dalilin haka. Bayan shekara 11 da Asa ya zama sarki, Zerah Habashi ya ja-goranci rundunar mutum miliyan guda su yaƙi Yahuda. Jehovah zai ceci Yahuda kuwa? Shekaru 500 a farko, Jehovah ya bayyana abin da mutanensa za su yi tsammani idan suka saurare shi kuma kiyaye dokokinsa da kuma abin da za su yi tsammani idan ba su yi haka nan ba. (Kubawar Shari’a 28:1, 7, 15, 25) A somawar sarautarsa, Asa ya ciccire bagadai da sifofi da ake amfani da su a bauta ta ƙarya. Ya aririce mutanen su “biɗi Ubangiji.” Asa bai jira har sai ya gamu da bala’i kafin ya yi hakan ba. Saboda haka, tare da bangaskiya ga Jehovah, Asa ya yi masa addu’a ya aika dominsu. Menene sakamakon? An ba Yahuda nasara mai girma.—2 Labarbaru 14:2-12.
16, 17. (a) Ko da yake Asa ya yi nasara, wace tunasarwa Jehovah ya yi masa? (b) Lokacin da Asa ya yi wauta, wane taimako aka ba shi, yaya ya yi? (c) Ta yaya za mu amfana a la’akari da halin Asa?
16 Duk da haka, da Asa ya dawo da nasara, Jehovah ya aiki Azariah ya sadu da sarkin kuma ya ce: “Ku ji ni, ya Asa, da kai, da dukan Yahuda da Banyamin: Ubangiji yana tare da ku, muddar kuna tare da shi; idan kun neme shi, yā samu a gareku; amma idan kun yashe shi, shi kuma za ya yashe ku.” (2 Labarbaru 15:2) Da sabuwar himma, Asa ya bunƙasar da bauta ta gaskiya. Amma bayan shekaru 24, da ya sake fuskantar yaƙi, Asa ya kasa biɗan Jehovah. Bai bincika Kalmar Allah ba, kuma bai tuna da abin da Jehovah ya yi lokacin da rundunar Habasha suka yi wa Yahuda hari ba. Ya yi wauta ya haɗa hannu da Suriya.—2 Labarbaru 16:1-6.
17 Domin wannan, Jehovah ya sa Hanani annabi ya yi wa Asa horo. Da Asa ya amfana a lokacin da aka bayyana masa ra’ayin Jehovah a batun. Maimakon haka, ya yi fushi kuma ya jefa Hanani cikin gidan sarƙa. (2 Labarbaru 16:7-10) Abin baƙin ciki kuwa! Mu kuma fa? Muna biɗan Allah amma kuma muna ƙi da gargaɗi? Lokacin da wani dattijo mai lura mai kirki ya yi amfani da Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu domin muna kamuwa cikin duniya, muna godiya ga taimako na ƙaunar nan da aka ba mu domin mu san “abin da ke na yarda ga Ubangiji”?
Kada Ka Manta, Ka Yi Tambaya Ina Jehovah
18. Ta yaya za mu amfana daga kalmomin Elihu ga Ayuba?
18 A cikin matsi, har wanda ma yake da tarihin kirki a hidimar Jehovah zai iya kasala. Lokacin da aka harbi Ayuba da mugun cuta, ya yi hasarar yaransa da kuma dukiyarsa, abokansa kuma suka zarge shi, sai ya shaƙu cikin tunanin kansa. Elihu ya tunasar da shi: “Ba mai-cewa, Ina Allah Mahaliccina.” (Ayuba 35:10) Ayuba yana bukatar ya mai da hankalinsa wurin Jehovah ya yi la’akari da yadda Yake ɗaukan yanayin. Cikin tawali’u Ayuba ya yi na’am da tunasarwar, kuma misalinsa zai taimake mu mu yi haka nan.
19. Sau da yawa menene mutanen Isra’ila suka kasa yi?
19 Mutanen Isra’ila sun san labarin yadda Allah ya yi sha’ani da al’ummarsu. Amma sau da yawa ba sa tunawa lokacin da wasu yanayi sun taso a rayuwarsu. (Irmiya 2:5, 6, 8) Idan suka fuskanci tsai da shawara a rayuwarsu, sai su biɗi nasu annashuwa maimakon yin tambaya, “Ina Ubangiji?”—Ishaya 5:11, 12.
Ka Ci Gaba da Tambaya, “Ina Ubangiji?”
20, 21. (a) Su waye a yau suka nuna ruhun Elisha a neman ja-gorar Jehovah? (b) Ta yaya za mu yi koyi kuma amfana daga misalin bangaskiyarsu?
20 Lokacin da hidimar Iliya ta ƙare, bawansa Elisha ya ɗauki taguwar da ta faɗo daga Iliya, ya je Urdun, ya bugi ruwa kuma ya ce: “Ina Ubangiji Allah na Iliya? (2 Sarakuna 2:14) Jehovah ya amsa ta nuna cewa yanzu ruhunsa yana kan Elisha ne. Me za mu iya koya daga wannan?
21 Wani abu makamancin haka ya faru a zamanin nan. Wasu shafaffun Kiristoci da suka yi ja-gora a aikin wa’azi sun mutu. Waɗanda aka ba wa aikin kula suna bincika Nassosi kuma suna wa Jehovah addu’a domin ja-gora. Suna tambaya koyaushe, “Ina Ubangiji?” Sakamakon haka shi ne, Jehovah ya ci gaba da yi wa mutanensa ja-gora a ayyukansu. Muna koyi kuwa da bangaskiyarsu? (Ibraniyawa 13:7) Idan haka ne, za mu kasance kusa da ƙungiyar Jehovah, muna bin ja-gorarta, kuma muna sa hannu sosai cikin aikin da take yi ta wurin ja-gorar Yesu Kristi.—Zechariah 8:23.
Yaya Za Ka Amsa?
• Da wane nufi za mu dinga tambaya, “Ina Ubangiji?”
• Ta yaya mu a yau za mu sami amsar tambayar nan, “Ina Ubangiji?”
• Me ya sa ba a amsa wasu addu’o’i na neman ja-gora ta Allah?
• Waɗanne misalan Littafi Mai Tsarki suka nuna bukatar mu ci gaba da “gwada abin da ke na yarda ga Ubangiji”?
[Hoto a shafi na 15]
Ta yaya ne Sarki Jehoshaphat ya nemi Jehovah?
[Hoto a shafi na 16]
Me ya sa Saul ya biɗi mabiya?
[Hotuna a shafi na 18]
Ka yi addu’a, nazari, da kuma bimbini don ka san ‘inda Jehovah yake’