Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 6/1 pp. 8-13
  • Kristi Ya Yi Wa Ikilisiyoyi Magana

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kristi Ya Yi Wa Ikilisiyoyi Magana
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Zuwa ga Mala’ika a Afisus
  • Zuwa ga Mala’ika a Samiruna
  • Zuwa ga Mala’ika da ke Birgamos
  • Ka Saurara Abin Da Ruhu Ya Faɗa!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Yadda Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna Ta Shafe Ka a Yau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Ka Koyi Biyayya Yayin Da Ƙarshe Ya Matso Kusa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 6/1 pp. 8-13

Kristi Ya Yi Wa Ikilisiyoyi Magana

“Ga magana da wannan ya faɗi wanda yana riƙe da taurari bakwai ɗin cikin hannunsa na dama.”—RU’YA TA YOHANNA 2:1.

1, 2. Me ya sa ya kamata mu kasance da son abin da Kristi ya faɗa wa ikilisiyoyi bakwai a Asiya Ƙarama?

ƊA MAKAƊAICI na Jehovah, Yesu Kristi, shi ne Shugaban ikilisiyar Kirista. Don ikilisiyar mabiyansa shafaffu ta kasance marar aibi, Kristi yana shugabancinsa ta yaba musu kuma ta yi musu gyara. (Afisawa 5:21-27) Da akwai misalan wannan a Ru’ya ta Yohanna surori 2 da 3, inda muka samu saƙon Yesu mai ƙarfi kuma na ƙauna da ya yi wa ikilisiyoyi bakwai a Asiya Ƙarama.

2 Kafin ya ji kalmomin Yesu zuwa ga ikilisiyoyi bakwai ɗin, an nuna wa manzo Yohanna wahayi na “ranar Ubangiji.” (Ru’ya ta Yohanna 1:10) “Ranar” ta soma sa’ad da aka kafa Mulkin Almasihu a shekara ta 1914. Saboda haka, abin da Kristi ya gaya wa ikilisiyoyin yana da muhimmanci a waɗannan kwanaki na ƙarshe. Ƙarfafarsa da gargaɗi yana taimaka mana mu bi da waɗannan miyagun zamanu.—2 Timothawus 3:1-5.

3. Menene ma’ana ta alama na “taurari,” “mala’iku,” da “fitilu na zinariya” da manzo Yohanna ya gani?

3 Yohanna ya ga Yesu Kristi da aka ɗaukaka, wanda yake “riƙe da taurari bakwaiɗin cikin hannunsa na dama,” da wanda “ya ke tafiya cikin tsakiyar fitilu bakwaiɗin na zinariya,” ko kuma ikilisiyoyi. “Taurarin,” “mala’iku ne na ikilisiya.” (Ru’ya ta Yohanna 1:20; 2:1) Taurari wani lokaci na wakilta mala’iku halittun ruhu, amma Kristi ba zai yi amfani da mutum ba ya rubuta saƙo don halittun ruhu. Saboda haka, waɗannan “taurarin” na nuni ga masu kula ne waɗanda ruhu ya shafe su, ko kuma rukunin dattawa. Furcin nan “mala’iku” yana dangane da hakkinsu na manzanni. Domin ƙungiyar Allah ta riga ta bunƙasa, “wakili mai-aminci” ya kuma naɗa ƙwararrun maza daga “waɗansu tumaki” na Yesu su zama masu kula.—Luka 12:42-44; Yohanna 10:16.

4. Ta yaya dattawa za su amfana daga sauraron abin da Kristi ya gaya wa ikilisiyoyin?

4 “Taurarin” suna hannun dama na Yesu—na ikonsa, cikin ja-gorarsa, tagomashi, da kuma kāriya. Saboda haka, za su ba da lissafi. Ta yin biyayya da kalmominsa ga kowacce ikilisiya bakwai ɗin, dattawa na zamani suna fahimta yadda za su bi da irin waɗannan yanayi. Hakika, dukan Kiristoci suna bukatar su saurari Ɗan Allah. (Markus 9:7) To, me za mu koya ta saurarar Kristi da yake wa ikilisiyoyin magana?

Zuwa ga Mala’ika a Afisus

5. Wane irin birni ne Afisus?

5 Yesu ya yaba kuma tsauta wa ikilisiya da ke Afisus. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 2:1-7.) Babban haikali na allahiya Artemis yana wannan wajen kasuwanci da kuma cibiyar addini ne a yammacin gaɓar tekun Asiya Ƙarama. Ko da Afisus ta cika da lalata, addinin ƙarya, da yin dabo, Allah ya albarkaci hidimar manzo Bulus da kuma wasu cikin birnin.—Ayukan Manzanni, sura ta 19.

6. Ta yaya Kiristoci masu aminci a yau suka yi kama da waɗanda suke Afisus ta dā?

6 Kristi ya yaba wa ikilisiya da ke Afisus, yana cewa: “Na san ayyukanka, da wahalarka da haƙurinka, na sani kuma ba ka iya jimrewa da miyagun mutane, ka kuma auna waɗanda ke ce da kansu manzanni, ba kuwa haka su ke ba, har ka iske su maƙaryata.” A yau, ikilisiyoyin mabiyan Yesu na gaske suna da irin wannan tarihin ayyuka masu kyau, aiki tuƙuru, da kuma jimiri. Ba sa ƙyale ’yan’uwa na ƙarya da suke son a ɗauka su manzanni. (2 Korinthiyawa 11:13, 26) Kamar Afisawa, Kiristoci masu aminci a yau ba sa “jimrewa da miyagun mutane.” Saboda haka, don a riƙe bautar Jehovah mai tsarki kuma a kāre ikilisiyar, ba sa zumunta da ’yan ridda da suka ƙi su tuba.—Galatiyawa 2:4, 5; 2 Yohanna 8-11.

7, 8. Wace matsala ce mai tsanani take ikilisiyar Afisus, kuma yaya za mu bi da irin wannan yanayi?

7 Duk da haka, Kiristoci a Afisus suna da matsala mai tsanani. “Ina da wannan game da kai,” in ji Yesu, “da ka bar ƙaunarka ta fari.” Waɗanda suke cikin ikilisiyar suna bukatar su sabonta ƙaunarsu ta fari ga Jehovah. (Markus 12:28-30; Afisawa 2:4; 5:1, 2) Dukanmu dole mu mai da hankali kada mu yi rashin ƙaunarmu ta fari ga Allah. (3 Yohanna 3) Amma idan abubuwa kamarsu sha’awar abin duniya ko biɗan annashuwa suka zama abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwarmu fa? (1 Timothawus 4:8; 6:9, 10) Sa’annan, ya kamata mu yi addu’a ƙwarai domin taimakon Allah mu sake irin waɗannan nufe-nufe da ƙauna mai zurfi ga Jehovah da godiya ga dukan abin da shi da Ɗansa suka yi mana.—1 Yohanna 4:10, 16.

8 Kristi ya aririci Afisawa: “Ka tuna fa daga inda ka fāɗi, ka tuba kuma, ka yi ayyuka na fari.” Idan ba su yi haka ba fa? Yesu ya ce: “In ba haka ba sai in zo wurinka, in kawarda fitilarka daga wurinta.” Idan dukan tumakin sun yi rashin ƙaunarsu na fari, “fitilar,” ko kuma ikilisiyar, ba za ta ƙara kasancewa ba. Da yake mu Kiristoci ne masu himma, bari mu yi aiki tuƙuru mu sa ikilisiyar ta ci gaba da haskakawa a ruhaniya.—Matta 5:14-16.

9. Yaya ya kamata a ɗauki bin ɗarika?

9 Abin yabo ne cewa, Afisawa sun ƙi “ayyukan Nikolawiyana.” Ban da abin da aka faɗa a Ru’ya ta Yohanna, ba a san ainihin asalin wannan ɗarikar, da koyarwarta, da ayyukanta ba. Amma, tun da Yesu ya haramta bin mutane, muna bukatar mu ci gaba da ƙin ɗarika, yadda Kiristoci a Afisus suka yi.—Matta 23:10.

10. Menene waɗanda suka yi biyayya da abin da ruhu ya faɗa za su samu?

10 “Wanda ya ke da kunne, bari shi ji abin da Ruhu ke faɗa ma ikilisiya,” in ji Kristi. Lokacin da yake duniya, Yesu ya yi magana ta ikon ruhun Allah. (Ishaya 61:1; Luka 4:16-21) Saboda haka, ya kamata yanzu mu saurari abin da Allah ya ce ta wurinsa ta ruhu mai tsarki. Ta wurin ja-gorar ruhun, Yesu ya yi alkawari: “Wanda ya yi nasara, a gareshi zan bayar da ci daga cikin itace na rai, wanda ke cikin [aljanna] na Allah.” Shafaffu, da suka yi biyayya da abin da ruhu ya ce, wannan yana nufin rai babu mutuwa a “[aljanna] na Allah” ta samaniya, ko kuma wajen Jehovah. “Taro mai-girma” waɗanda su ma suka saurari abin da ruhu ya ce, za su more aljanna a duniya inda za su sha daga “kogin ruwa na rai” kuma za su samu warkarwa daga “ganyayen itacen” kusa da shi.—Ru’ya ta Yohanna 7:9; 22:1, 2; Luka 23:43.

11. Ta yaya za mu iya ɗaukaka nuna ƙauna ga Jehovah?

11 Afisawa sun bar ƙaunarsu na farko, amma idan irin wannan yanayi yana tasowa cikin wata ikilisiya a yau fa? Bari dukanmu ɗaɗɗaya mu ɗaukaka ƙauna ga Jehovah ta yin magana game da hanyoyinsa masu kyau. Za mu iya nuna godiyarmu domin ƙauna da Allah ya nuna a yin tanadin fansa ta Ɗansa ƙaunatacce. (Yohanna 3:16; Romawa 5:8) Sa’ad da ya dace, muna iya ambata ƙaunar Allah a kalami da kuma cikin wasu sashe na taro. Za mu nuna tamu ƙauna ga Jehovah ta yabon sunansa a hidimar Kirista. (Zabura 145:10-13) Hakika, furcinmu da ayyuka za su iya mai da ko kuma ƙarfafa ƙaunar ikilisiya ta farko.

Zuwa ga Mala’ika a Samiruna

12. Menene tarihi ya bayyana game da Samiruna da ayyukan addini da ke wajen?

12 Kristi ya yaba wa ikilisiya da ke Samiruna, “na fari da na ƙarshe ya faɗi, shi wanda ya mutu, ya sake rayuwa” ta tashin matattu. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 2:8-11.) An kafa Samiruna (yanzu Izmir, Turkey) a gaɓar teku na yammacin Asiya Ƙarama. Helenawa suna da zama cikin birnin, amma Lidiyawa suka halaka ta a misalin 580 K.Z. Waɗanda suka ɗauki matsayin Iskandari Babba suka sake gina Samiruna a sabon wuri. Ya zama wata gunduma ta Roma na Asiya kuma cibiyar kasuwanci ne mai ci da aka san shi da gine-gine masu kyau. Haikalinta na Kaisar Tiberius ya sa ta zama cibiyar bautar daula. Masu bauta suna ƙone turare ɗis kuma su ce “Kaisar ne Ubangiji.” Kiristoci ba su bi su ba domin a gare su “Yesu ne Ubangiji.” Shi ya sa, suka sha tsanani.—Romawa 10:9.

13. Ko da ba su da abin duniya, a wane azanci ne Kiristoci a Samiruna suke mawadata?

13 Ban da tsanani, Kiristoci a Samiruna sun jimre da talauci, mai yiwuwa sun sha wahalar tattalin arziki domin ba su sa hannu cikin bautar daula ba. Ba a ware masu bauta wa Jehovah na zamani suke ba daga irin waɗannan gwaji. (Ru’ya ta Yohanna 13:16, 17) Ko da ba su da abin duniya, waɗanda suke Kiristoci a Samiruna mawadata ne a ruhaniya, kuma abin da yake da muhimmanci ke nan!—Misalai 10:22; 3 Yohanna 2.

14, 15. Wace ta’aziyya shafaffu suka samu daga Ru’ya ta Yohanna 2:10?

14 Yawancin Yahudawa a Samiruna “majami’ar Shaiɗan ne” domin sun manne wa al’adu da ba na nassi ba ne, sun ƙi da Ɗan Allah, kuma zargi mabiyansa haifaffu na ruhu. (Romawa 2:28, 29) Amma shafaffu za su samu ta’aziyya daga kalmomin Kristi na gaba! Ya ce: “Kada ka ji tsoron wahala da za ka sha: ga shi, Shaiɗan yana shiri ya jefa waɗansu daga cikinku a kurkuku, domin a gwada ku; kwana goma kuwa za ku sha ƙunci. Ka yi aminci har mutuwa, ni ma in ba ka rawanin rai.”—Ru’ya ta Yohanna 2:10.

15 Yesu bai ji tsoron ya mutu ba don ya ɗaukaka ikon mallakar Jehovah. (Filibbiyawa 2:5-8) Ko da yanzu Shaiɗan yana yaƙi da raguwar shafaffu, ba sa tsoron abubuwan da su rukunin dole su sha wahalarsa—tsanani, tsare a kurkuku, ko kuma mutuwa. (Ru’ya ta Yohanna 12:17) Za su ci nasara da duniya. Kuma maimakon kambin furanni da ake saka wa masu nasara a wasannin arna, Kristi ya yi wa shafaffu da aka tashe su daga matattu alkawarin “rawanin rai” su zama halittu marasa mutuwa a sama. Hakika wannan kyauta ce mai tamani!

16. Idan muna cikin ikilisiya kamar wadda take Samiruna ta dā, a kan wane batu ya kamata mu mai da hankalinmu?

16 Idan mu begenmu na sama ne ko na duniya, muna cikin ikilisiya da take kamar wadda take Samiruna ta dā ne? Sa’an nan bari mu taimake ’yan’uwa masu bi su mai da hankali a kan ainihin dalilin da ya sa Allah ya ƙyale tsanani—batun ikon mallakar dukan sararin samaniya. Kowanne Mashaidin Jehovah mai aminci yana sa Shaiɗan ya zama maƙaryaci kuma yana nuna cewa ko mutum da ake tsananta wa zai iya zama mai ɗaukaka ikon Allah shi Mamallakin Dukan Halitta ya yi sarauta. (Misalai 27:11) Bari mu ƙarfafa wasu Kiristoci su jimre wa tsanantawa kuma ta haka, su ci gaba da samun gatar “bauta ma [Jehovah] ba tare da tsoro ba, cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu”—har abada ma.—Luka 1:68, 69, 74, 75.

Zuwa ga Mala’ika da ke Birgamos

17, 18. Birgamos cibiyar wace irin bauta ce, me zai iya faruwa idan mutum ya ƙi sa hannu a irin wannan bautar gumaka?

17 An yabi kuma yi wa ikilisiya da ke Birgamos gyara. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 2:12-17.) Yana misalin mil 50 ne ta arewacin Samiruna, Birgamos birni ne cike da addinin arna. Masanan yanayin taurari na Chaldiyawa kamar sun gudu daga Babila zuwa wurin. Mutane masu rashin lafiya suna zuwa sanannen haikali na Asclepius a Birgamos, allahn ƙarya na warkarwa da kuma yin magani. Birgamos, da haikalinsa da ake bautar Kaisar Augustus ciki, an kira shi “babban cibiyar bauta a ƙarƙashin daula ta farko.”—Encyclopædia Britannica, 1959, Littafi na 17, shafi na 507.

18 A Birgamos akwai bagadi da aka keɓe wa Zafsa. Wannan birni cibiyar wurin da ake bauta wa mutane ne da Iblis ya motsa su. Ba abin mamaki ba ne da aka ce ikilisiya da ke wurin tana zama a inda mazaunin sarauta na “Shaiɗan ke zaune”! Ƙin bauta wa daular zai iya jawo mutuwa ga mai ɗaukaka ikon mallakar Jehovah. Duniya har ila tana hannun Iblis, kuma ana bauta wa alamu na ƙasashe. (1 Yohanna 5:19) Daga ƙarni na farko zuwa yanzu, Kiristoci da yawa masu aminci an kashe su, kamar wanda Kristi ya kira “Antibas mashaidina, mai-amincina, wanda aka kashe a cikinku.” Babu shakka, Jehovah Allah da Yesu Kristi suna tuna da irin bayin nan masu aminci.—1 Yohanna 5:21.

19. Menene Bal’amu ya yi, game da menene dole dukan Kiristoci su tsare kansu?

19 Kristi ya kuma yi maganar “koyarwa ta Bil’amu.” Domin haɗama ta abin duniya, Bil’amu annabin ƙarya ya yi ƙoƙarin ya la’anci Isra’ilawa. Sa’anda Allah ya juya la’anarsa zuwa albarka, Bal’amu ya yi aiki tare da Sarkin Mowab Balak ya jarabi Isra’ilawa da yawa cikin bautar gunki da lalata. Dattawa Kirista suna bukatar su yi tsayin daka don adalci yadda Phinehas ya yi, wanda ya yaƙe aikin Bal’amu. (Litafin Lissafi 22:1–25:15; 2 Bitrus 2:15, 16; Yahuda 11) Hakika, dukan Kiristoci dole su tsare kansu daga bautar gumaka kuma kada lalata ta cika ikilisiya.—Yahuda 3, 4.

20. Idan wani Kirista ya soma na’am da ra’ayin ’yan ridda, me ya kamata ya yi?

20 Ikilisiya da ke Birgamos tana cikin haɗari sosai domin ta ƙyale “waɗansu masu-kiyaye koyarwar Nikolawiyana.” Kristi ya gaya wa ikilisiyar: “Ka tuba fa; in ba haka ba na zo wurinka da sauri, in yi yaƙi da su da takobi na bakina.” Masu ɗaukaka ɗarika suna son su yi wa Kiristoci lahani a ruhaniya, kuma waɗanda suka dage su ɗaukaka rarrabuwa da ɗarika ba za su gāji Mulkin Allah ba. (Romawa 16:17, 18; 1 Korinthiyawa 1:10; Galatiyawa 5:19-21) Idan wani Kirista ya soma na’am da ra’ayin ’yan ridda kuma yana son ya yaɗa shi, ya kamata ya karɓi gargaɗi daga Kristi! Don ya guje wa masifa, ya kamata ya tuba kuma ya nemi taimako na ruhaniya na dattawa cikin ikilisiyar. (Yaƙub 5:13-18) Muhimmin abu ne a aikata nan da nan, domin Yesu yana zuwa da sauri ya zartar da hukunci.

21, 22. Su waye ke cin “ɓoyayyen manna,” kuma menene take wakiltawa?

21 Shafaffun Kiristoci masu aminci da abokansu ba sa bukatar su ji tsoron hukunci mai zuwa. Albarka na jiran dukan mutane da suka yi biyayya da gargaɗin da Yesu ya bayar ta wurin ja-gorar ruhu mai tsarki na Allah. Alal misali, shafaffu da suka ci nasara da duniya za a gayyace su su ci wasu “ɓoyayyen manna” kuma za a ba su “farin dutse” mai “sabon suna.”

22 Allah ya yi tanadin manna don ciyar da Isra’ilawa a lokacin gantalinsu na shekara 40 cikin jeji. An ajiye wasu “abincin” cikin ƙoƙo na zinariya cikin sunduƙi na alkawari kuma ta haka an ɓoye cikin wuri Mafi Tsarki na mazauni, inda wuta ta mu’ujiza ke wakiltar bayyanuwar Jehovah. (Fitowa 16:14, 15, 23, 26, 33; 26:34; Ibraniyawa 9:3, 4) Babu wanda aka yarda masa ya ci ɓoyayyen manna. A lokacin tashinsu daga matattu, shafaffun mabiyan Yesu sun yafa rashin mutuwa, da cin “ɓoyayyen manna” ke wakilta.—1 Korinthiyawa 15:53-57.

23. Menene ma’anar “farin dutse” da “sabon suna”?

23 Baƙin dutse hukunci ne a kotun Romawa, amma fari yana nufin ’yanci. Da Yesu ya ba da “farin dutse” wa Kiristoci shafaffu da suka ci nasara, ya nuna cewa ya ɗauka su marasa laifi ne, tsarkakku, masu tsabta. Tun da yake Romawa suna amfani da duwatsu su iya shigar wasu muhimman biki, “farin dutse” zai iya nuna cewa shafaffun sun samu shiga sama a auren Ɗan Ragon. (Ru’ya ta Yohanna 19:7-9) “Sabon suna” hakika na nuna gatar zama cikin haɗin kai da Yesu su abokan gādo a Mulki na samaniya. Babu shakka wannan yana ƙarfafa shafaffu da abokan tarayyarsu a hidimar Jehovah, da suke da begen zama cikin aljanna a duniya!

24. Wane mataki ya kamata mu kasance da shi game da ridda?

24 Yana da kyau mu tuna cewa ikilisiya da ke Birgamos suna cikin haɗarin ’yan ridda. Idan irin wannan yanayi ya yi wa ruhaniyar ikilisiyar da muke ciki barazana, bari mu ƙi da ’yan ridda gaba ɗaya mu ci gaba da tafiya cikin gaskiya. (Yohanna 8:32, 44; 3 Yohanna 4) Tun da yake malaman ƙarya ko mutane da suke tunanin riddawa za su iya ɓata ikilisiya gabaki ɗayanta, dole mu tsaya da ƙarfi gāba da ridda, kada mu ƙyale muguwar rinjaya ta hana mu yi wa gaskiya biyayya.—Galatiyawa 5:7-12; 2 Yohanna 8-11.

25. Saƙon Kristi ga waɗanne ikilisiyoyi za a tattauna a talifi na gaba?

25 Hakika kalmomi masu sa tunani na yabawa da gargaɗi ne Yesu Kristi da aka ɗaukaka ya yi wa ikilisiyoyi uku cikin bakwai da muka bincika a Asiya Ƙarama! Amma, yadda ruhu mai tsarki ya yi ja-gora, yana da abubuwa da yawa da zai gaya wa sauran ikilisiyoyi huɗun. Za a tattauna wannan saƙon da aka aika wa Tayatira, Sardisu, Filadalfiya, da Lawudikiya a talifi na gaba.

Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa za mu saurara ga abin da Kristi ya faɗa wa ikilisiyoyi?

• Ta yaya za mu taimaka mu mai da ƙauna ta fari a ikilisiya?

• Me ya sa za a ce Kiristoci matalauta a Samiruna ta dā masu arziki ne da gaske?

• Idan muka duba yanayin da ke ikilisiyar Birgamos, yaya ya kamata mu ɗauka ra’ayin ’yan ridda?

[Taswira a shafi na 8]

HELAS

ASIYA ƘARAMA

Afisus

Samiruna

Birgamos

Tayatira

Sardisu

Filadalfiya

Lawudikiya

[Hoto a shafi na 10]

“Taro mai-girma” za su more aljanna a duniya

[Hotuna a shafi na 11]

Kiristoci da aka tsananta musu sun ci nasara da duniya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba