Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 6/1 pp. 13-18
  • Ka Saurara Abin Da Ruhu Ya Faɗa!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Saurara Abin Da Ruhu Ya Faɗa!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Zuwa ga Mala’ika a Tayatira
  • Zuwa ga Mala’ika a Sardisu
  • Zuwa ga Mala’ika a Filadalfiya
  • Zuwa ga Mala’ika a Lawudikiya
  • Darasi Domin Dukanmu
  • Kristi Ya Yi Wa Ikilisiyoyi Magana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ka Koyi Biyayya Yayin Da Ƙarshe Ya Matso Kusa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 6/1 pp. 13-18

Ka Saurara Abin Da Ruhu Ya Faɗa!

“Wanda ya ke da kunne, bari shi ji abin da Ruhu ya faɗa ma ikilisiyai.”—RU’YA TA YOHANNA 3:22.

1, 2. Waɗanne gargaɗi aka maimaita game da saƙonnin Yesu ga ikilisiyoyi bakwai da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna?

BAYIN Jehovah dole su mai da hankali ga hurarrun kalmomin Yesu Kristi ga ikilisiyoyi bakwai da aka ambata a littafin Ru’ya ta Yohanna cikin Littafi Mai Tsarki. Hakika, kowanne cikin waɗannan saƙonni yana ɗauke da wannan gargaɗin: “Wanda ya ke da kunne, bari shi ji abin da Ruhu ke faɗa ma ikilisiyai.”—Ru’ya ta Yohanna 2:7, 11, 17, 29; 3:6, 13, 22.

2 Mun riga mun bincika saƙonnin Yesu ga mala’iku, ko dattawan Afisus, Samiruna, da Bargimos. Ta yaya za mu amfana daga abin da ya faɗa wa sauran ikilisiyoyi huɗu ta ruhu mai tsarki?

Zuwa ga Mala’ika a Tayatira

3. Ina Tayatira take, da wane kayayyaki aka san ta da su?

3 “Ɗan Allah” ya yaba wa ikilisiyar Tayatira kuma tsauta musu. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 2:18-29.) An gina Tayatira (yanzu Akhisar) kusa da tabkin Kogin Gediz (Hermus ta dā) a yammacin Asiya Ƙarama. An san birnin da kayayyakin fasaha. Masu yin shuni suna amfani da saiwa na yin sanannen launi jar zur, ko kuma shunayya. Lidiya wadda ta zama Kirista lokacin ziyarar Bulus zuwa Filibbi a Helas, “mai-sayarda turin shunayya, ta birnin Tayatira” ne.—Ayukan Manzanni 16:12-15.

4. Domin me aka yaba wa ikilisiya da ke Tayatira?

4 Yesu ya yaba wa ikilisiyar da ke Tayatira domin nagargarun ayyukanta, ƙauna, bangaskiya, jimiri, da aiki a hidima. Hakika, ‘ayyukansu na ƙarshe sun ɗara na farin.’ Ko idan ma muna da tarihi na nagarin hali, ya kamata mu mai da hankali ga ɗabi’armu.

5-7. (a) Wacce ce “macen nan Izabil,” menene za a yi game da rinjayarta? (b) Saƙon Kristi zuwa ikilisiyar Tayatira na taimaka wa mata masu ibada su yi menene?

5 Ikilisiya da ke Tayatira ta ƙyale bautar gumaka, koyarwar ƙarya, da lalatar jima’i. A tsakaninsu akwai “macen nan Izabil”—wataƙila rukunin mata ne masu halaye kamar na muguwar Sarauniya Izabil na ƙabila goma ta Mulkin Isra’ila. Wasu manazarta sun ce ‘annabawa mata’ na Tayatira sun yi ƙoƙari su jarabi Kiristoci su bauta wa alloli da allaniya ta tarayyar kasuwanci kuma su shagala a bukukuwa da ya ƙunshi yi wa gumaka hadayar abinci. Kada macen da take ce da kanta annabiya ta nemi ta rinjayi wasu cikin ikilisiyar Kirista na zamani!

6 Kristi yana son ya ‘jefa macen nan Izabil cikin gado, da waɗanda ke yin zina tare da ita cikin ƙunci mai tsanani, in ba ta tuba ba ga barin ayyukanta.’ Kada dattawa su amince da irin wannan muguwar koyarwa da tasiri, kuma ba Kirista da yake bukata ya yi fasikanci na ruhaniya da na zahiri ko kuma sa hannu cikin bautar gumaka domin ya fahimta cewa “zurfafan al’amura na Shaiɗan” gabaki ɗaya na mugunta ne. Idan mun yi biyayya da kashedin Yesu, ‘za mu riƙe abin da muke da shi,’ zunubi ba zai sha kanmu ba. Domin sun ƙi da ayyuka da ba na ibada ba, sha’awace-sha’awace, da kuma buri, shafaffu da aka ta da daga matattu sun sami “iko bisa al’ummai” kuma za su bi Kristi wajen karkarya su. Ikilisiyoyi na zamani suna da taurari na alama, kuma za a ba shafaffu, “tauraro na asuba, mai-haske,” Angon, Yesu Kristi, bayan da an ta da su daga matattu zuwa sama.—Ru’ya ta Yohanna 22:16.

7 An yi wa ikilisiya da ke Tayatira kashedi kada ta ƙyale mugun tasiri na mata masu ridda. Hurarren saƙon Kristi ga ikilisiya na taimaka wa mata masu ibada su riƙe matsayin da Allah ya ba su a yau. Ba sa ƙoƙari su nuna iko bisa maza kuma ba sa rinjayar ’yan’uwa maza cikin fasikanci na ruhaniya ko na zahiri ba. (1 Timothawus 2:12) Maimako, irin waɗannan mata suna kafa misalin nagargarun ayyuka da hidima ga yabon Allah. (Zabura 68:11; 1 Bitrus 3:1-6) Idan ikilisiya tana tsare abin da take da shi—koyarwa da hali mai tsarki kuma da daraja hidimar Mulki—Kristi zai zo da lada mai girma, ba hukunci ba.

Zuwa ga Mala’ika a Sardisu

8. (a) Ina Sardisu take, waɗanne abubuwa aka faɗa game da ita? (b) Me ya sa ikilisiya da ke Sardisu ke bukatar taimako?

8 Ikilisiya da ke Sardisu na bukatar taimako na gaggawa domin a mace take a ruhaniya. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 3:1-6.) Sardisu tana misalin mil 30 ta kudancin Tayatira, birni ne mai ni’ima. Kasuwanci, amfanin gonar ƙasar, yin kayan ulu da kapet sun sa ya zama birni mai arziki da dā take da mazauna 50,000. In ji ɗan tarihi Josephus, Sardisu tana da Yahudawa da yawa a ƙarni na farko K.Z. Majalisa da haikali na allaniya Artemis na Afisus suna cikin kangon birnin.

9. Me ya kamata mu yi idan hidimarmu muna yi ne kawai?

9 Kristi ya gaya wa mala’ika da ke ikilisiyar Sardisu: “Na san ayyukanka, kana da suna mai-rai ne, amma matacce ne.” Idan ana ganin muna faɗake a ruhaniya amma ba ma son gata ta Kirista, hidimarmu kamar ana yi ne kawai, kuma a ruhaniya muna “bakin mutuwa” fa? Sa’an nan muna bukatar ‘mu tuna yadda muka karɓa kuma muka ji’ saƙon Mulkin, ya kamata mu sabonta ƙoƙarinmu a hidimar fage. Hakika ya kamata mu fara yin furci a taron Kirista da zuciya ɗaya. (Ibraniyawa 10:24, 25) Kristi ya yi wa ikilisiya da ke Sardisu kashedi: “Idan fa ba ka yi tsoro ba, ina zuwa da kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san sa’an da zan auko maka ba.” Zamaninmu fa? Ba da daɗewa ba za mu ba da lissafi.

10. Har ma a yanayi kamar wanda yake Sardisu, menene zai kasance gaskiya game da wasu Kiristoci?

10 Har a yanayi kamar na Sardisu, za a samu kalilan da ‘ba su ƙazantar da tufafinsu ba, waɗannan za su yi tafiya tare da Kristi yafe da fari; gama sun isa.’ Sun adana sunansu na Kirista, sun kasance marar aibi, ba tare da tabo na ɗabi’a da na addini ba daga wannan duniya. (Yaƙub 1:27) Saboda haka, Yesu ‘ba zai kuwa shafe sunansu daga cikin littafin rai ba daɗai, zai kuma shaida su a gaban Ubansa, da gaban mala’iku.’ Da yake sun cancanta su yi tafiya da Kristi, za a yafa wa shafaffu ajin amaryarsa tufafi mai haske, da tsabta da ke wakiltar ayyukan adalci na masu tsarki na Allah. (Ru’ya ta Yohanna 19:8) Gatar hidima mai ban al’ajabi da ke jiransu a sama ya motsa su su yi nasara da wannan duniya. Albarka na jiran waɗanda suke layin samun rai madawwami a duniya. An rubuta sunansu ma a littafin rai.

11. Me ya kamata mu yi idan muna ja da baya a ruhaniya?

11 Babu wani cikinmu da zai so ya shiga cikin yanayin ruhaniya na baƙin ciki na ikilisiyar Sardisu. Amma idan mun fahimta cewa muna barci a ruhaniya fa? Ya kamata mu aikata da sauri domin amfaninmu. A ce an rinjaye mu cikin hanyoyin rashin ibada ko kuma mun ja da baya a halartar taro ko kuma a hidimarmu. Bari mu nemi taimakon Jehovah cikin addu’a. (Filibbiyawa 4:6, 7, 13) Karatun Littafi Mai Tsarki kullum da nazarin Nassosi da littattafan “wakili mai-aminci” zai daɗa sa mu kasance a farke a ruhaniya. (Luka 12:42-44) Sa’an nan za mu zama kamar waɗanda suke Sardisu da suke da amincewar Kristi, kuma za mu zama abin ƙarfafa ga ’yan’uwa masu bi.

Zuwa ga Mala’ika a Filadalfiya

12. Yaya za ka kwatanta yanayin addini na Filadalfiya na dā?

12 Yesu ya yaba wa ikilisiyar Filadalfiya. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 3:7-13.) Filadalfiya (yanzu Alasehir) cibiyar inda ake yin barasa ne a yamman Asiya Ƙarama. Hakika, allahnta na musamman Dionysus ne, allahn barasa. Babu shakka, Yahudawa a Filadalfiya ba su yi nasara a nace wa Kiristoci Yahudawa da suke wajen su ci gaba da yin wasu ayyuka na Dokar Musa ko su koma yinsu ba.

13. Yaya Kristi ya yi amfani da “maƙulin Dauda”?

13 Kristi yana da “maƙulin Dauda,” kuma an ɗanka masa dukan abubuwan Mulki da shugabancin iyalin imani. (Ishaya 22:22; Luka 1:32) Yesu ya yi amfani da wannan maƙulin ya buɗe zarafi da gata na Mulkin ga Kiristoci a Filadalfiya ta dā da kuma wani waje. Tun shekara ta 1919 ya buɗe wa “wakili mai-aminci” “ƙofa mai-faɗi” da ke kai ga wa’azin Mulki da ba mai hamayya da zai iya rufewa. (1 Korinthiyawa 16:9; Kolossiyawa 4:2-4) Hakika, an rufe wa waɗanda suke na “majami’ar Shaiɗan,” ƙofa zuwa gatar Mulki domin su ba Isra’ila na ruhaniya ba.

14. (a) Wane alkawari Yesu ya yi wa ikilisiya a Filadalfiya? (b) Ta yaya ba za mu faɗi ba a “sa’ar jaraba”?

14 Yesu ya yi wa Kiristoci a Filadalfiya ta dā wannan alkawari: “Tun da ka kiyaye maganar haƙurina, ni ma zan kiyaye ka daga sa’ar jaraba, wannan da ke zuwa bisa ga dukan duniya.” Wa’azi na bukatar irin jimiri da Yesu ya nuna. Bai taɓa fāɗa wa abokin gāba ba amma ya ci gaba da yin nufin Ubansa. Shi ya sa aka ta da Kristi zuwa rai marar matuƙa a samaniya. Idan mun manne wa shawararmu mu bauta wa Jehovah kuma mu tallafa wa Mulkin ta yin wa’azin bishara, ba za mu fāɗi ba lokacin gwaji na zamani, “sa’ar jaraba.” Za mu ci gaba da ‘riƙe abin da muke da shi’ daga Kristi ta yin ƙoƙari mu ƙara waɗannan abubuwa na Mulki. Yin haka zai kawo kambi na samaniya mai tamani ga shafaffu da rai madawammi a duniya ga abokansu masu aminci.

15. Menene ake bukata daga waɗanda za su zama ‘jigo a haikalin Allah’?

15 Kristi ya daɗa: “Wanda ya yi nasara, zan maishe shi jigo cikin haikalin Allahna, . . . zan rubuta bisansa sunan Allahna, da sunan birnin Allahna, sabuwar Urushalima, wadda ta ke saukowa daga cikin sama daga wurin Allahna, da nawa sabon suna kuma.” Dattawa shafaffu dole su ɗaukaka bauta ta gaskiya. Dole su cancanta zama waɗanda suke na “sabuwar Urushalima” ta wa’azi game da Mulkin Allah kuma kasance da tsabta a ruhaniya. Wannan wajibi ne idan suna son su zama jigo a haikalin samaniya mai ɗaukaka da kuma idan za su ɗauki sunan birnin Allah su mazauna na samaniya kuma su yi amfani da sunan Kristi su amaryarsa. Kuma za su kasance da kunne su “ji abin da Ruhu ya faɗa ma ikilisiyoyi.”

Zuwa ga Mala’ika a Lawudikiya

16. Waɗanne abubuwa ne aka sani game da Lawudikiya?

16 Kristi ya tsauta wa ikilisiya a Lawudikiya da suke da halin ba ruwansu. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 3:14-22.) Yana mil 90 a gabashin Afisus kuma a mararrabar hanyoyin kasuwanci a ƙwari mai ni’ima na Kogin Lycus, Lawudikiya birni ne inda ake kayayyaki da cibiyar neman arziki. An san da tufafi da aka ɗinka daga baƙin ulu na wajen. Da yake wajen sanannen makarantar magani ne, wataƙila a Lawudikiya ne aka yi maganin ido da ake kiran hodan Firijiya. Asclepius, allahn magani, yana ɗaya cikin manyan allolin birnin. Kamar dai Lawudikiya tana da Yahudawa da yawa, wasu cikinsu mawadata ne.

17. Me ya sa aka tsauta wa Lawudikiyawa?

17 Da yake yi wa ikilisiya da ke Lawudikiya magana ta wurin “mala’ika,” Yesu ya yi magana da iko shi “amintaccen mashaidi mai-gaskiya, farkon halittar Allah.” (Kolossiyawa 1:13-16) An tsauta wa Lawudikiyawa domin ba su da “sanyi ko zafi” a ruhaniya. Domin suna tsaka-tsaka, Kristi zai fitar da su daga cikin bakinsa. Bai kamata ya yi musu wuya su fahimta wannan kwatancin ba. Hiyarabolis da ke kusa suna da rafi mai zafi, kuma Kolossi suna da ruwan sanyi. Tun da ruwa ta bututu yake zuwa Lawudikiya da ke da nisa, kamar dai kafin ya kai birnin yana da ɗumi. A rabin hanya, ta wurin kwangirin ruwa suke samun ruwa. Kusa da Lawudikiya, ruwan yana tafiya ta duwatsu da aka huje da aka yi wa shafe.

18, 19. Ta yaya za a taimaka wa Kiristoci na zamani kamar waɗanda suke Lawudikiya?

18 Mutane irin na Lawudikiya a yau ba su da zafi sosai ko kuwa sanyi mai wartsakarwa ba. Kamar ruwa mai tsaka-tsaka, za a zubar da su daga cikin baki! Yesu ba ya son su zama kakakinsa, shafaffu “manzanni . . . madadin Kristi.” (2 Korinthiyawa 5:20) In ba su tuba ba, za su yi hasarar gatarsu na masu shelar Mulki. Lawudikiyawa sun nemi dukiya na duniya kuma ‘ba su sani ba cewa su malalata ne, abin tausayi, matalauta, makafi, tsiraru.’ Domin su cire talaucinsu, makanta, da tsirararsu ta ruhaniya, duk wanda yake kamar su a yau yana bukatar ya sayi daga Kristi “zinariya gyartaciya” na bangaskiya da aka gwada, “fararen tufafi” na adalci, da “maganin ido” da ke warkar da ganin gari na ruhaniya. Dattawa Kirista na farin ciki su taimake su su mai da hankali ga bukatarsu na ruhaniya domin su kasance “mawadata cikin bangaskiya.” (Yaƙub 2:5; Matta 5:3) Bugu da ƙari, dattawa suna bukatar su taimaka musu su yi amfani da “maganin ido” na ruhaniya—su yi na’am kuma bi koyarwar Yesu, gargaɗi, misali, da halinsa. Wannan magani ne na “kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu, da darajar rai ta wofi.”—1 Yohanna 2:15-17.

19 Yesu yana tsauta wa kuma yi wa waɗanda yake ƙauna horo. Dattawa da suke ƙarƙashinsa dole su yi haka cikin juyayi. (Ayukan Manzanni 20:28, 29) Lawudikiyawa suna bukata su ‘yi himma fa, su tuba,’ su yi canji a yadda suke tunani da hanyar rayuwa. To, wasunmu sun saba da yayin rayuwa da ke sa hidimarmu ga Allah marar muhimmanci ne a rayuwa? To, bari mu ‘sayi maganin ido daga wurin Yesu’ domin mu ga muhimmancin biɗan Mulkin da farko da himma.—Matta 6:33.

20, 21. Su wa suke buɗe ƙofa ga “ƙwanƙwasar” Yesu a yau, wane bege suke da shi?

20 “Duba” in ji Kristi, “ina tsayawa a bakin ƙofa ina ƙwanƙwasawa: idan kowane mutum ya ji muryata ya buɗe ƙofa, sai in shiga wurinsa, in ci tare da shi, shi kuma tare da ni.” Yesu sau da yawa ya yi koyarwa na ruhaniya sa’ad da yake cin abinci. (Luka 5:29-39; 7:36-50; 14:1-24) Yanzu yana ƙwanƙwasan ƙofar irin ikilisiya da ke Lawudikiya. Waɗanda suke ciki za su buɗe kofa ne, su sabonta ƙaunarsu gare shi, su marabce shi cikinsu, kuma ya koyar da su? Idan haka ne, Kristi zai ci tare da su su sami amfani na ruhaniya mai yawa.

21 “Taro mai girma” a yau suna buɗe wa Yesu ƙofa a alamance, kuma irin wannan ayyuka na kai wa ga rai madawwami. (Yohanna 10:16; Matta 25:34-40, 46) Ga kowane shafaffe da ya yi nasara, Kristi zai ba shi gatar ‘zama tare da shi cikin kursiyinsa, kamar yadda shi kuma ya yi nasara, ya zauna kuma tare da Ubansa cikin Nasa kursiyi.’ Hakika, ga shafaffu da suka yi nasara, Yesu ya yi musu alkawarin lada mai girma na kursiyi tare da shi a hannun dama na Ubansa a sama. Kuma waɗansu tumaki da suka yi nasara suna sauraran wuri mai ban al’ajabi a duniya a ƙarƙashin sarautar Mulki.

Darasi Domin Dukanmu

22, 23. (a) Ta yaya dukan Kiristoci za su amfana daga kalmomin Yesu zuwa ga ikilisiyoyi bakwai? (b) Me ya kamata mu ƙudura aniyar yi?

22 Babu shakka cewa dukan Kiristoci za su amfana sosai daga kalmomin Yesu ga ikilisiyoyi bakwai a Asiya Ƙarama. Alal misali, da sun lura cewa Kristi ya ba da yabo da ya dace, dattawa Kirista sun motsa su yaba wa mutane da kuma ikilisiyoyi da suke ƙoƙari a ruhaniya. Inda akwai kumamanci, dattawa suna taimakon ’yan’uwa masu bi su yi amfani da taimakon Nassosi. Dukanmu za mu iya ci gaba da amfana daga gargaɗi dabam dabam da Kristi ya ba wa ikilisiyoyi bakwai, muddin mun yi amfani da shi tare da addu’a kuma babu ɓata lokaci.a

23 Waɗannan kwanaki na ƙarshe ba lokacin ƙoshin kai ba ne, son abin duniya, ko kuma wani abu da zai sa mu rage hidimarmu ga Allah. Saboda haka, bari dukan ikilisiyoyi su ci gaba da haskaka kamar fitilu da Yesu ya ajiye a tsayawarsu. Da yake mu Kiristoci masu aminci ne, bari koyaushe mu ƙuduri aniyar mai da hankali sa’ad da Kristi ya yi magana kuma mu saurara abin da ruhu ke faɗa. Sa’an nan za mu samu farin ciki na dindindin na masu ɗauke da haske ga ɗaukakar Jehovah.

[Hasiya]

a An tattauna Ru’ya ta Yohanna 2:1–3:22 a babi 7 zuwa 13 na littafin nan Revelation—Its Grand Climax At Hand!, Shaidun Jehovah ne suka buga.

Ta Yaya Za Ka Amsa?

• Wacce ce “macen nan Izabil” kuma me ya sa mata masu ibada ba za su yi koyi da ita ba?

• Wane yanayi ne yake cikin ikilisiya da ke Sardisu, me za mu yi mu guje zama kamar Kiristoci da yawa da suke zama wajen?

• Waɗanne alkawura Yesu ya yi wa ikilisiyar Filadalfiya, yaya za a yi amfani da su yau?

• Me ya sa aka tsauta wa Lawudikiyawa, wane bege Kiristoci masu himma suke da shi?

[Hoto a shafi na 14]

Dole a guje wa mugun hanyoyin “macen nan Izabil”

[Hotuna a shafi na 16]

Yesu ya buɗe wa mabiyansa “ƙofa mai-faɗi” zuwa ga gatar Mulki

[Hoto a shafi na 18]

Kana yi wa Yesu maraba kana kuma saurare shi?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba