Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 7/1 pp. 15-20
  • Ka Nemi Abu Mai Kyau Cikin Dukan Mutane

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Nemi Abu Mai Kyau Cikin Dukan Mutane
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • A ta Wa’azi da Almajirantarwa
  • Cikin Iyali
  • Cikin Ikilisiyar Kirista
  • Neman Abu Mai Kyau Cikin Dukan Mutane
  • Nagarta​—Ta Yaya Za Mu Koyi Nuna Wannan Halin?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Ka Ci Gaba Da Yin Nagarta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • “Allah Mai Nagarta Ne da Babu Kamarsa!”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Kana Ɗaukan Mutane Yadda Jehobah Ya Ɗauke su?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 7/1 pp. 15-20

Ka Nemi Abu Mai Kyau Cikin Dukan Mutane

“Ka tuna da ni, ya Allahna, tare da alheri.”—NEHEMIAH 13:31.

1. Ta yaya Jehovah yake aika nagarta ga dukan mutane?

BAYAN kwanakin gajimare da duhu, hasken rana ya kawo canji. Mutane sun fi hali, suna farin ciki. Haka nan ma, bayan tsawon lokatai na ƙunan rana a rani ƙwarai, ko yayyafi—ko tarin girgizai ma—yana kawo wartsakewa da sauƙaƙawa. Jehovah, Mahaliccinmu mai ƙauna, ya shirya duniya ta kasance da wannan kyautar yanayi na ban al’ajabi. Yesu ya jawo hankali ga karimcin Allah sa’ad da ya koyar da cewa: “Ku yi ƙaunar magabtanku, kuma waɗanda su kan tsananta muku, ku yi musu addu’a; domin ku zama ’ya’yan Ubanku wanda ke cikin sama: gama ya kan sa ranatasa ta fito ma miyagu da nagargaru, ya kan aiko da ruwa bisa masu-adalci da marasa-adalci.” (Matta 5:43-45) Hakika, Jehovah yana aika nagarta ga dukan mutane. Ya kamata bayinsa su yi ƙoƙari su yi koyi da shi ta neman abu mai kyau cikin wasu.

2. (a) Domin menene Jehovah yake aikatawa da nagarta? (b) Menene Jehovah yake lura da shi game da yadda muke aikatawa ga nagartansa?

2 Domin menene Jehovah yake aikatawa da nagarta? Tun lokacin da Adamu ya yi zunubi, Jehovah ya ci gaba da neman abu mai kyau cikin mutane. (Zabura 130:3, 4) Nufinsa ya mai da mutane masu biyayya ne zuwa rai cikin Aljanna. (Afisawa 1:9, 10) Alherinsa ya ba mu begen ceto daga zunubi da ajizanci ta Zuriya da aka yi alkawarinsa. (Farawa 3:15; Romawa 5:12, 15) Yin na’am da tsarin fansa ya sa ya yiwu a iya koma kamilcewa. Jehovah yanzu yana lura da kowannenmu ya ga yadda za mu aikata ga karimcinsa. (1 Yohanna 3:16) Yana ganin dukan abin da muke yi mu nuna muna godiya ga nagartansa. Manzo Bulus ya rubuta: “Allah ba marar-adalci ba ne da za shi manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa.”—Ibraniyawa 6:10.

3. Wace tambaya ya kamata mu bincika?

3 To, ta yaya za mu yi koyi da Jehovah a neman abu mai kyau cikin wasu? Bari mu bincika amsoshi ga wannan tambayar a ɓangarori huɗu na rayuwa: (1) hidimar Kirista, (2) iyali, (3) ikilisiya, da kuma (4) dangantakarmu da wasu.

A ta Wa’azi da Almajirantarwa

4. Ta yaya sa hannu cikin hidimar Kirista nuni ne na neman abu mai kyau cikin wasu?

4 “Gona duniya ce,” Yesu ya yi wa almajiransa bayani da suke tambaya game da ma’anar almarar alkama da zawa. Da yake mu almajiran Kristi ne na zamani, muna fahimta wannan gaskiya sa’ad da muke sa hannu cikin hidima. (Matta 13:36-38; 28:19, 20) Hidimarmu ta ƙunshi shelar bangaskiyarmu a fili. Gaskiya cewa an san Shaidun Jehovah sosai yanzu don hidimarsu ta ƙofa ƙofa da kuma ta kan titi ya ba da tabbaci cewa muna ƙwazo a neman duka da suka cancanta don saƙon Mulki. Hakika, Yesu ya ba da umurni: “Kowane birni ko ƙauye inda kuka shiga, a cikinsa ku nemi wanda ya cancanta.”—Matta 10:11; Ayukan Manzanni 17:17; 20:20.

5, 6. Me ya sa muke ci gaba da sake ziyarar mutane a gidajensu?

5 Sa’ad da muke yi wa mutane ziyara da ba a gayyace mu ba, muna lura da yadda suke aikata ga saƙonmu. Wani lokaci mukan iske wani cikin iyali zai saurare mu, amma wani, daga cikin iyalin har ila ya ce “Ba ma so,” sai ziyarar ta ƙare. Abin baƙin ciki ne cewa hamayya ko rashin so na mutum guda yakan shafi wasu! To, me za mu iya yi don mu nace a neman abu mai kyau cikin dukan mutane?

6 Ziyararmu ta gaba a gidan sa’ad da muke wa’azi a wajen zai iya ba mu zarafi mu yi magana kai tsaye da wanda ya hana ziyarar dā. Tuna abin da ya faru a lokacin zai taimake mu mu shirya. Mai yiwuwa mai hamayyar ya aikata da nufin kirki, ya gaskata cewa ya kamata ya sa wanda yake son sauraro ya daina saurarar saƙon Mulki. Labarin ƙarya game da ra’ayinmu wataƙila ya shafi ra’ayinsa. Amma wannan ba zai hana mu daga ci gaba da wa’azin Mulkin bishara a gidan ba, cikin basira mu daidaita al’amura. Muna son mu taimake dukan mutane su samu cikakken sani na Allah. Wataƙila Jehovah zai jawo wannan mutumin ga kansa.—Yohanna 6:44; 1 Timothawus 2:4.

7. Menene zai taimake mu mu kasance da hali mai kyau sa’ad da muka dumfari mutane?

7 Umurnin Yesu ga almajiransa ya haɗa da hamayya daga iyali. Ya faɗa cewa: “Na zo domin in haɗa mutum da ubansa, ’ya kuma da uwarta, surukuwa kuma da surukuwatata.” Yesu ya daɗa: “Maƙiyan mutum za su kasance daga iyalin gidansa.” (Matta 10:35, 36) Duk da haka, yanayi da halaye sukan canja. Ciwo, mutuwar dangi, bala’i, damuwa ta jiye-jiye, da wasu abubuwa da yawa na shafan yadda mutane suke aikata ga wa’azinmu. Kasancewa da baƙin ido—cewa mutane da muke musu wa’azi ba za su taɓa saurara ba—muna neman abu mai kyau ne cikinsu ke nan? Me ya sa ba za ka sake ziyarar gidajensu wani lokaci da farin ciki ba? Muna iya iske cewa za su aikata dabam. Wasu lokatai ba kawai abin da muka faɗa ba amma yadda muka faɗe shi ne zai sa su aikata da kyau. Sahihiyar addu’a ga Jehovah kafin mu soma wa’azi za ta taimake mu mu kasance da hali mai kyau kuma mu ba da saƙon Mulki a hanyar da za ta gamsar da dukan mutane.—Kolossiyawa 4:6; 1 Tassalunikawa 5:17.

8. Menene zai iya zama sakamakonsa sa’ad da Kiristoci suka ga abu mai kyau wajen danginsu marasa bi?

8 A wasu ikilisiyoyi mutane da yawa da suke cikin iyali ɗaya suna bauta wa Jehovah. Sau da yawa abin da ke sa matasa su yaba wa kuma daraja tsofaffi dangi da suke da dangantakarsu mai kyau cikin iyali da kuma cikin gamin aure, na sa matasa su canja ra’ayinsu. Yin biyayya da gargaɗin manzo Bitrus ta taimaki mata Kirista da yawa su rinjaye maigidantansu “banda magana.”—1 Bitrus 3:1, 2.

Cikin Iyali

9, 10. Ta yaya Yakubu da Yusufu suka nemi abu mai kyau cikin iyalinsu?

9 Gami da ke haɗa waɗanda suke cikin iyali wani ɓangare ne da za mu nemi abu mai kyau cikin wasu. Yi la’akari da yadda Yakubu ya bi da ’ya’yansa. A Farawa sura 37, ayoyi 3 da 4, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yakubu ya fi ƙaunar Yusufu. ’Yan’uwan Yusufu sun yi kishi, har suka ƙulla su kashe ƙanensu. Duk da haka, ka lura da halayen Yakubu da Yusufu a rayuwarsu ta gaba. Dukansu biyu sun nemi abu mai kyau cikin iyalinsu.

10 Sa’ad da Yusufu yake hidimar shugaban masu ba da abinci a Masar a lokacin fari, ya yi wa ’yan’uwansa maraba. Ko da bai bayyana kansa nan take ba, ya lura da abubuwa, ya tabbata cewa an kula da su sosai kuma sun kai wa babansu da ya tsufa abinci. Hakika, ko da sun tsane shi, Yusufu ya aikata domin zaman lafiyarsu. (Farawa 41:53–42:8; 45:23) Haka nan ma, a gadon mutuwarsa Yakubu ya sanar da albarka na annabci a kan dukan ’ya’yansa. Ko da mummunar ayyukansu ya sa aka rage wasu gata, an ba dukansu gadō a ƙasar. (Farawa 49:3-28) Lallai Yakubu ya nuna ƙauna mai jimrewa!

11, 12. (a) Wane misali na annabci ne ya nanata muhimmancin neman abu mai kyau cikin iyali? (b) Wane darasi muka koya daga misalin uba cikin kwatancin Yesu na ɗa mubazzari?

11 Tsawon jimrewa na Jehovah a sha’ani da al’ummar Isra’ila marasa aminci ya ƙara ba da fahimi a yadda yake neman abu mai kyau cikin mutanensa. Ta yin amfani da yanayin iyali na annabi Hosea, Jehovah ya kwatanta ƙaunarsa mai jimrewa. Gomer, matar Hosea, ta yi zina sau da sau. Duk da haka, Jehovah ya ba Hosea umurni: “Je ka, har wa yau, ka ƙaunaci mace ƙaunataciyar mijinta amma mazinaciya, kamar yadda Ubangiji ya ke ƙaunar ’ya’yan Isra’ila, ko da sun juya ga bin waɗansu alloli, suna kuwa son waina na zabibi.” (Hosea 3:1) Me ya sa ya ba da irin wannan umurni? Jehovah ya san cewa cikin al’umma da suka bijire daga hanyoyinsa, wasu mutane za su aikata abin da yake da kyau domin haƙurinsa. Hosea ya sanar: “Daga baya kuma ’ya’yan Isra’ila za su komo, su biɗi Ubangiji Allahnsu, da Dauda sarkinsu; da tsoro kuma za su zo wurin Ubangiji da wurin alherinsa kuma cikin kwanakin ƙarshe.” (Hosea 3:5) Hakika wannan misali ne mai kyau da za a yi tunani a kai sa’ad da muke fuskantar wahalar iyali. Idan ka ci gaba da neman abu mai kyau cikin waɗanda suke cikin iyali za ka kafa aƙalla misalin haƙuri.

12 Almarar Yesu na ɗa mubazzari ya ba mu ƙarin fahimi a yadda za mu nemi abu mai kyau game da waɗanda suke cikin iyalinmu. Ɗan ƙarami ya koma gida bayan rayuwarsa ta lalata. Uban ya yi masa jinƙai. Yaya uban ya aikata sa’ad da ɗansa na fari da bai taɓa barin gida ba yake gunaguni? Da yake yi wa ɗansa na fari magana, uban ya ce: “Ɗana, tuttur kana tare da ni, dukan nawa kuwa naka ne.” Wannan ba bala’in ƙi ba ne amma tabbaci ne na ƙaunar uba. Ya ci gaba: “Daidai ne a yi farinciki da murna,” in ji shi, “gama wannan ɗan’uwanka ya mutu, ya sāke rayawa; ya ɓace, ya samu kuma.” Mu ma haka nan za mu iya ci gaba da neman abu mai kyau cikin wasu.—Luka 15:11-32.

Cikin Ikilisiyar Kirista

13, 14. Wace hanya ɗaya ce muke nuna muhimmin umurni na ƙauna tsakanin ikilisiyar Kirista?

13 Da yake mu Kiristoci ne, muna son mu cika muhimmin umurni na ƙauna. (Yaƙub 2:1-9) Hakika, mai yiwuwa za mu amince da waɗanda yanayinsu a zahiri ya bambanta da namu cikin ikilisiya. Amma muna yin “tara” ta ƙabila, al’ada, ko kuma addini ne? Idan haka ne, ta yaya za mu yi biyayya da gargaɗin Yaƙub?

14 Yi wa duka da suke halartar taron Kirista maraba yana ba da tabbaci cewa muna da halin karɓan baƙi. Sa’ad da muka ɗauki mataki na soma wa sababbi da suka zo Majami’ar Mulki magana, duk kunya da rashin sakewa da suke ji zai ɓace. Hakika, wasu da suka halarci taron Kirista na farko, sun ce: “Kowa yana da halin abokantaka. Kamar dai kowa ya san ni dama. Na saki jiki.”

15. Ta yaya za a taimaki matasa cikin ikilisiya su nuna suna damuwa da tsofaffi?

15 A wasu ikilisiyoyi, matasa kalilan sukan taru a ciki ko waje da Majami’ar Mulki a ƙarshen taro, suna guje tarayya da tsofaffi. Wane nagarin abu za a yi don a sha kan wannan halin? Mataki na farko shi ne iyaye su koyar da yaransu a gida, su shirya su don taro. (Misalai 22:6) Za a iya ba su aikin shirya littattafai dabam dabam don duka su samu abubuwa da ake bukata a tafi taron da su. Iyaye suna matsayi mafi kyau su ƙarfafa yaransu su yi taɗi da tsofaffi da naƙasassu a Majami’ar Mulki. Gaya wa irin waɗannan mutane abu mai ma’ana na gamsar da yara.

16, 17. Ta yaya manya za su nemi abu mai kyau cikin matasa a ikilisiya?

16 ’Yan’uwa tsofaffi ya kamata su nuna suna damuwa da matasa cikin ikilisiya. (Filibbiyawa 2:4) Suna iya ɗaukan mataki su soma yi wa matasa magana a hanya mai ƙarfafa. Ana samun darussa na musamman lokacin taron. Ana iya tambayar matasa ko sun ji daɗin taron ko kuma akwai darussa da musamman suke so kuma za su iya amfani da su. Da yake sune sashe na musamman na ikilisiya, ya kamata a amince da mai da hankalinsu kuma yaba musu don kowanne kalami da suka yi a taro ko kuma sashen taro da suka sa hannu. Yadda matasa suke taɗi da tsofaffi cikin ikilisiya da yadda suke aikin gida zai nuna cewa za su iya kula da hakki mai girma da kyau a rayuwa ta gaba.—Luka 16:10.

17 Ta karɓan hakki, wasu matasa sun ci gaba har ingancinsu na ruhaniya ya taimake su su samu ayyuka da suka fi muhimmanci. Samun abin yi zai taimaka wajen hana halin wauta. (2 Timothawus 2:22) Irin wannan aiki zai “gwada” ’yan’uwa maza da suke burin aikin bayi masu hidima ko sun dace. (1 Timothawus 3:10) Kalaminsu a taro da himmarsu a hidima, da halin kulawa da kowa cikin ikilisiya, na taimakon dattawa su yi niyyar bincika su don ƙarin ayyuka.

Neman Abu Mai Kyau Cikin Dukan Mutane

18. Wane tarko game da shari’a za a guje wa, kuma me ya sa?

18 “Tara wurin shari’a ba ta da kyau,” in ji Misalai 24:23. Hikima daga bisa tana bukatar dattawa su guje yin tara sa’ad da suke shari’a cikin ikilisiya. Yaƙub ya sanar: “Hikima mai-fitowa daga bisa tsatsarka ce dafari, bayan wannan mai-salama ce, mai-sauƙin hali, mai-siyasa, cike da jinƙai da kyawawan ’ya’ya, marar-kokanto, marar-riya ce.” (Yaƙub 3:17) Hakika, yayin da suke neman abu mai kyau cikin wasu, dattawa suna bukatar su tabbata cewa dangantaka ko tsotsuwar zuciya ba ta shafi shari’arsu ba. Mai Zabura Asaph ya rubuta: “Allah yana tsaye cikin taron jama’ar Allah.” “Yana hukunci a tsakiyar alloli [“masu kama da allah,” hasiyar tana nuni ga mahukuntan mutane]. Har yaushe za ku hukunta da rashin gaskiya, kuna ganin girman miyagu?” (Zabura 82:1, 2) Daidai, dattawa Kirista suna ƙi da kowanne halin son kai a al’amura da ya shafi aboki ko kuma dangi. A wannan hanyar suna adana haɗin kai na ikilisiya kuma ƙyale ruhun Jehovah ya kasance wurin.—1 Tassalunikawa 5:23.

19. A waɗanne hanyoyi ne za mu nemi abu mai kyau cikin wasu?

19 A neman abu mai kyau cikin ’yan’uwanmu, muna nuna halin Bulus sa’ad da yake wa ikilisiyar Tassalunika magana. Ya ce: “Muna kuwa amincewa ga Ubangiji a kanku, kuna yin abin da mu ke umurtanku, za ku yi kuma.” (2 Tassalunikawa 3:4) Za mu fi ƙyale laifin wasu sa’ad da muka nemi abu mai kyau cikinsu. Za mu nemi wurare da za mu yaba wa ’yan’uwanmu, muna guje wa halin kushe musu. Bulus ya rubuta: “Abin da a ke nema ga wakilai, a iske mutum da aminci.” (1 Korinthiyawa 4:2) Aminci ba kawai na waɗanda suke da hakki a cikin ikilisiya ba amma na dukan ’yan’uwa Kirista da yake sa su zama ƙaunatattu gare mu. Ta haka, muna matsa kusa da su, muna ƙarfafa gami na abokantaka ta Kirista. Muna ɗaukan ra’ayi kamar na Bulus game da ’yan’uwa a zamaninsa. Su “abokan aiki . . . zuwa mulkin Allah” da “waɗanda suka yi m[ana] ta’aziyya.” (Kolossiyawa 4:11) Ta haka muna nuna halin Jehovah.

20. Waɗanne albarka waɗanda suke neman abu mai kyau cikin wasu za su samu?

20 Hakika muna sake maimaita addu’ar Nehemiah: “Ka tuna da ni, ya Allahna, tare da alheri.” (Nehemiah 13:31) Muna farin ciki cewa Jehovah yana neman abu mai kyau cikin mutane! (1 Sarakuna 14:13) Bari mu yi haka a sha’aninmu da wasu. Yin haka yana ba mu begen fansa da rai madawwami a sabuwar duniya da ta yi kusa.—Zabura 130:3-8.

Yaya Za Ka Amsa?

• Bisa menene Jehovah yake aikata da nagarta ga dukan mutane?

• Ta yaya za mu nemi abu mai kyau cikin wasu

• a hidimarmu?

• a cikin iyalinmu?

• a cikin ikilisiyarmu?

• a dukan dangantaka da muke yi?

[Hoto a shafi na 16]

Duk da cewa da farko ’yan’uwansa sun tsane shi, Yusufu ya nemi zaman lafiyarsu

[Hoto a shafi na 17]

Hamayya ba ta hana mu daga taimakon dukan mutane

[Hoto a shafi na 18]

Duk da halinsu dā, babu wani cikin ’ya’yan Yakubu da ba a yi masa albarka ba

[Hoto a shafi na 19]

Ka yi wa dukan mutane maraba a taron Kirista

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba