Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 11/1 pp. 9-13
  • Ka Ƙara Wa Saninka Kamewa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Ƙara Wa Saninka Kamewa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Kamewa, Abin da Za a Koya
  • Kamewa Tana wa Wasu Wuya Ainu
  • Kamewa Cikin Aure
  • Ku Ci Gaba da Taimakon Juna
  • Ka Nuna Kamewa Domin Ka Sami Lada!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ka Rika Kame Kanka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Kamewa​—Halin da Ke Faranta Ran Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Mu Rika Kame Kanmu
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 11/1 pp. 9-13

Ka Ƙara Wa Saninka Kamewa

“Ku ƙara . . . [wa] ilimi . . . kamewa.”—2 BITRUS 1:5-8.

1. Matsaloli da yawa na ’yan Adam don wace kasawa ce?

A LOKACIN kamfen mai muhimmanci na kada a sha ƙwaya, an yi wa matasa a Amirka gargaɗi: “Ku ce a’a kawai.” Lallai yanayi zai fi kyau idan kowa zai ƙi ba shan ƙwaya kawai ba amma har da yawan shan giya, yayin rayuwa marar kyau ko kuma na lalata, ha’inci a kasuwanci da kuma bin ‘sha’awoyi na jiki’! (Romawa 13:14) Amma, waye zai ce faɗan a’a, kullum yake da sauƙi?

2. (a) Waɗanne misalan Littafi Mai Tsarki suka nuna cewa ba sabon abu ba ne a ce faɗan a’a na da wuya? (b) Me ya kamata waɗannan misalai su ƙarfafa mu mu yi?

2 Tun da yake yana wa dukan ’yan Adam ajizai wuya su kame kansu, ya kamata mu so mu koya yadda za mu ci nasara da kasawarmu. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da mutane na dā da suka ƙoƙarta su bauta wa Allah da a wasu lokatai ya yi musu wuya su ce a’a. Ka tuna da Dauda da ya yi zina da Bath-sheba. Ya jawo mutuwar marasa laifi, mijin Bath-sheba da kuma ɗan da aka haifa ta wurin zina. (2 Samu’ila 11:1-27; 12:15-18) Ko kuma ka yi tunanin manzo Bulus da ya faɗa a fili: “Gama nagarta da ni ke so in yi, ba na aikawa ba: amma mugunta da ba na so ba, ita ni ke aikawa.” (Romawa 7:19) Kai ma wasu lokatai kana irin baƙin cikin nan? Bulus ya ci gaba: “Ina murna da shari’ar Allah bisa ga mutum na ciki: amma ina ganin wata shari’a dabam a cikin gaɓaɓuwana, tana yaƙi da shari’ar hankalina, tana saka ni bauta ƙarƙashin shari’ar zunubin nan da ke cikin gaɓaɓuwana. Kaitona, ga ni mutum, abin tausayi! wanene za ya tsamo ni daga cikin jikin nan na mutuwa?” (Romawa 7:22-24) Misalan Littafi Mai Tsarki ya kamata su ƙarfafa ƙudurinmu na cewa ba za mu taɓa kasala ba a kokawarmu mu ƙara kamewa.

Kamewa, Abin da Za a Koya

3. Ka bayyana abin da ya sa ba zai yi sauƙi a nuna kamewa ba.

3 An ambata kamewa da ta ƙunshi iya ce a’a cikin 2 Bitrus 1:5-7 tare da bangaskiya, halin kirki, ilimi, haƙuri, ibada, son ’yan’uwa da kuma ƙauna. Babu wani cikin waɗannan halaye masu kyau da aka haife mu da su. Dole ne a koye su. Yana bukatar ƙuduri da ƙoƙari mu nuna ta. Saboda haka, za mu yi tunanin koyan kamewa za ta yi sauƙi ne?

4. Me ya sa mutane da yawa suke jin ba su da damuwa game da kamewa, wannan tabbacin menene?

4 Hakika, mutane da yawa za su ji ba su da damuwa game da kamewa. Da saninsu ko ba da saninsu ba, suna rayuwa yadda suka ga dama, suna bin sha’awar jikinsu ajizi kuma ba sa damuwa da abin da zai zama sakamakon—gare su ko ga wasu. (Yahuda 10) Ana ganin rashin iya faɗan a’a da rashin son faɗansa yanzu fiye da dā. Tabbaci ne cewa muna cikin “kwanaki na ƙarshe” da Bulus ya faɗi sa’ad da ya annabta: “Miyagun zamanu za su zo. Gama mutane za su zama masu-son kansu, masu-son kuɗi, masu-ruba, masu-girman kai, masu-zagi, . . . marasa-kamewa.”—2 Timothawus 3:1-3.

5. Me ya sa Shaidun Jehovah suke son zancen kamewa, kuma wane gargaɗi har ila yake da muhimmanci?

5 Shaidun Jehovah suna sane da ƙalubale da bukatar kamewa take da ita. Kamar Bulus, sun san kokawa da ke cikin sha’awar faranta wa Allah rai ta yin rayuwa daidai da mizanansa da tafarkin da jikinsu ajizi ke sa su bi. Domin wannan dalili, da daɗewa suna son su san yadda za su yi nasara da wannan yaƙi. Can baya a shekara ta 1916, wata fita ta wannan jarida da kake karatunta yanzu ta faɗi “mataki da ya dace mu ɗauka domin mu kame kanmu, tunaninmu, kalmominmu da kuma halayenmu.” Ta ba da shawara a tuna da Filibbiyawa 4:8. Har ila, gargaɗin Allah cikin ayar tana da muhimmanci ko da yake shekaru 2,000 da suka shige aka ba da kuma wataƙila ya fi wuya a bi ta yanzu fiye da dā ko a shekara ta 1916. Duk da haka, Kiristoci suna ƙoƙari su ƙi da sha’awoyi ta duniya, da sanin cewa ta yin haka suna jituwa da Mahaliccinsu.

6. Me ya sa ba mu da dalilin fid da rai sa’ad da muke koyon kamewa?

6 An ambata kamewa a Galatiyawa 5:22, 23 cikin ‘ ’yar Ruhu [mai tsarki].’ Idan muka nuna wannan halin tare da “ƙauna, farin ciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, [da] tawali’u,” za mu amfana ƙwarai. Yadda Bitrus ya yi bayani, yin haka zai hana mu “zama raggaye ko kuma marasa-amfani” a hidimarmu ga Allah. (2 Bitrus 1:8) Amma bai kamata mu fid da rai ko kuma hukunta kanmu ba idan muka kasa nuna waɗannan halaye yadda za mu so. Wataƙila ka lura cewa a makaranta wani ɗalibi ya fi saurin koyan abu fiye da wani. Ko kuma wani ya fi saurin koyan sabon aiki da abokan aikinsa. Haka nan ma, wasu sun fi wasu saurin koyon halayen Kirista. Muhimmin abu shi ne mu ci gaba da koyon halaye na ibada yadda za mu iya. Za mu iya hakan ta wurin amfani da taimakon da Jehovah yake bayar ta Kalmarsa da ƙungiya. Muhimmin abu ba saurin koyon ba ne amma mu ci gaba da gyara.

7. Me ya nuna cewa kamewa tana da muhimmanci?

7 Ko da yake an lissafa ta a ƙarshe cikin halaye na ruhu, kamewa tana da muhimmanci kamar sauran. Hakika kuwa. Ya kamata mu tuna cewa za mu iya guje wa dukan “ayyukan jiki” idan muna da cikakkiyar kamewa. Amma ’yan Adam ajizai suna da halin faɗa wa wasu “ayyukan jiki . . . fasikanci ke nan, ƙazanta, lalata, bautar gumaka, sihiri, magabtaka, husuma, kishe-kishe, hasala, tsatsaguwa, rabuwa, hamiya.” (Galatiyawa 5:19, 20) Saboda haka, dole mu ci gaba da kokawa, mu ƙudura niyya mu kawar da munanan halaye daga zuciya da azanci.

Kamewa Tana wa Wasu Wuya Ainu

8. Waɗanne abubuwa suke sa kamewa ta yi wa wasu wuya?

8 Ya fi wa wasu Kiristoci wuya su kame kai. Me ya sa? Reno ko kuma abin da ya faru musu dā zai iya sa ya yi musu wuya. Idan ba mu da damuwar koyo da kuma nuna kamewa, to, abin farin ciki ne. Amma ya kamata mu ji tausayi kuma mu nuna fahimi sa’ad da muke bi da waɗanda yake musu wuya su koye ta, ko idan ma ba ma jin daɗin rashin kamewarsu. Domin ajizancinmu, wanene cikinmu yake da dalilin nuna adalcin kai?—Romawa 3:23; Afisawa 4:2.

9. Waɗanne kasawa wasu suke da shi, kuma yaushe za a sha kan waɗannan dindindin?

9 Ga misali: Ƙila mun san wasu ’yan’uwa Kiristoci da suka daina shan sigari ko kuma shan ƙwaya, da a wasu lokatai suna sha’awar sake shan ta. Wasu kuma suna iske shi da wuya su rage cin abinci da shan giya. Wasu kuma yana musu wuya su kame harshensu, a ta haka suna sa wasu tuntuɓe da maganarsu. Domin a bi da irin wannan kasawa ana bukatar ƙoƙari a koyon kamewa. Me ya sa? Yaƙub 3:2 ta yarda haka: “A cikin abu dayawa dukanmu mu kan yi tuntuɓe. Idan wani ba ya yi tuntuɓe ga wajen magana ba, wannan cikakken mutum ne, mai-ikon sarrafa dukan jiki kuma.” Har ila wasu suna sha’awar yin caca sosai. Ko kuma yana musu wuya su kame fushinsu. Yana bukatar lokaci su koya yadda za su daina waɗannan ko kuma irin wannan kumamancin. Ko da za mu iya nasara yanzu, sai mun kamalta za mu iya kawar da waɗannan munanan sha’awoyi dindindin. A yanzu kokawa a nuna kamewa za ta taimake mu mu guje wa faɗawa cikin tafarkin rayuwa ta zunubi. Yayin da muke kokawa, bari mu taimaki juna kada mu kasala.—Ayukan Manzanni 14:21, 22.

10. (a) Me ya sa kamewa a batun jima’i musamman yake wa wasu wuya? (b) Wane canji na musamman wani ɗan’uwa ya yi? (Duba akwati a shafi na 12.)

10 Wani wuri da kamewa take wa wasu wuya shi ne a zancen jima’i. Jehovah Allah ya yi mu da sha’awar yin jima’i. Duk da haka, wasu suna iske shi da wuya su sa jima’i wurin da ya dace, daidai da mizanan Allah. Kaluɓalen zai fi muni domin sha’awarsu ta yin jima’i tana da ƙarfi sosai. Muna cikin duniya ta haukan lalata da take sha’awoyinta a hanyoyi dabam dabam. Wannan takan zama matsala ga Kiristoci da ba sa son su yi aure—aƙalla na ɗan lokaci—don su bauta wa Allah ba tare da raba hankali da aure ke kawo wa ba. (1 Korinthiyawa 7:32, 33, 37, 38) Daidai da umurni na Nassi ‘gwamma a yi aure, da sha’awa ta ci rai’ suna iya shawara su yi aure, wadda hakika yana da daraja. Amma sun ƙudura niyya su yi “sai dai cikin Ubangiji,” yadda Nassi ya faɗa. (1 Korinthiyawa 7:9, 39) Mun tabbata cewa Jehovah yana farin ciki da yake suna son su ɗaukaka ƙa’idodinsa na adalci. ’Yan’uwansu Kiristoci suna farin ciki su yi tarayya da masu bauta ta gaskiya da suke da irin wannan mizanan ɗabi’a masu girma da kuma aminci.

11. Yaya za mu taimake ɗan’uwa ko ’yar’uwa da suke son su yi aure amma ba su iya yin haka ba?

11 Idan ba a samu abokiyar aure da ta dace ba fa? Ka yi tunanin baƙin cikin wanda yake son ya yi aure amma bai iya yin haka ba! Yana iya ganin abokansa suna aure kuma suna farin ciki, sa’an nan kuma har ila yana neman abokiyar aure da ta dace. Wasu da suke cikin irin yanayin nan, suna iya shiga matsalar mummunar halin tsarance. Ko yaya dai, babu wani Kirista da yake son ya ɓata rai wa wani da yake kokawa ya kasance da tsabtar rai. Muna iya sa wani sanyin gwiwa ba da saninmu ba idan muka yi furci da bai dace ba kamar “Yaushe za ka yi aure?” Ƙila mun faɗi haka ba da wani mugun nufi ba ne, amma zai fi kyau mu nuna kamewa a zancen riƙe harshenmu! (Zabura 39:1) Waɗanda suke tsakaninmu da ba su yi aure ba da suke da hali mai kyau suna bukatar a yaba musu sosai. Maimakon mu faɗi abin da zai sa su sanyin gwiwa, mu yi ƙoƙari mu ƙarfafa su. Alal misali, za mu iya mu gayyaci waɗanda ba su yi aure ba zuwa cin abinci ko kuma tarayya ta Kirista da waɗanda suka ƙware.

Kamewa Cikin Aure

12. Me ya sa masu aure ma suke bukatar kamewa?

12 Yin aure ba ya kawar da bukatar kamewa game da jima’i. Alal misali, sha’awar jima’i na mata da miji ta bambanta ƙwarai. Ko kuma yanayin jiki na abokiyar aure wani lokaci na iya sa jima’i ya yi wuya ko kuma ba zai yiwu ba ma. Wataƙila domin abin da ya faru dā, abokiyar aure za ta iske shi da wuya ta yi biyayya da umurnin: “Mijin shi ba matatasa abin da ya wajabce ta: matan kuma hakanan ga mijinta.” A irin wannan yanayin, abokin aure zai bukaci ƙarin kamewa. Amma su biyu za su iya tuna gargaɗin Bulus mai kyau ga Kiristoci masu aure: “Kada ku hana ma juna, sai dai da yardan juna domin kwanaki, da za ku maida kanku ga addu’a, ku sake gamuwa, domin kada Shaiɗan ya jarabce ku ta wurin rashin daurewarku.”—1 Korinthiyawa 7:3, 5.

13. Me za mu iya yi wa waɗanda suke kokawa su kame kansu?

13 Ma’aurata za su yi murna idan su biyun sun koyi kamewa da ta dace a wannan dangantaka ta kud da kud. Har ila, ya kamata su nuna fahimi ga ’yan’uwa masu bauta da suke kokawa su nuna kamewa a batun. Kada mu manta mu roƙi Jehovah ya ba wa ’yan’uwanmu na ruhaniya fahimi, gaba gaɗi, da kuma ƙuduri su ci gaba da kokawa su nuna kamewa kuma su ɗauki mataki su sha kan mummunar sha’awoyi.—Filibbiyawa 4:6, 7.

Ku Ci Gaba da Taimakon Juna

14. Me ya sa za mu bi da ’yan’uwa Kiristoci da tausayi da fahimi?

14 A wasu lokatai, yana iya yi mana wuya mu nuna fahimi game da ’yan’uwa Kiristoci da suke fama su nuna kamewa a batun da ba matsala ba ce gare mu. Amma mutane sun bambanta. Wasu yana da sauƙi tsotsuwar zuciya ta sha kansu; wasu kuma ba haka ba. Wasu kuma suna iske shi da sauƙi su kame kansu ba tare da wata matsala ba. Wasu suna iske shi da wuya ƙwarai. Ka tuna, wanda yake fama ba mugu ba ne. ’Yan’uwa Kiristoci suna bukata mu fahimce su kuma mu ji tausayinsu. Mu ma za mu yi farin ciki sa’ad da muka ci gaba da nuna jinƙai ga waɗanda har ila suke fama su daɗa nuna kamewa. Muna iya ganin wannan cikin kalmomin Yesu da ke Matta 5:7.

15. Me ya sa kalmomin Zabura 130:3 ke da ban ƙarfafa a batun kamewa?

15 Kada mu sūki ɗan’uwa Kirista da a wani lokaci zai kasa nuna hali na Kirista. Yana da ban ƙarfafa mu sani cewa ban da wani lokaci da muke kasawa, Jehovah yana ganin lokatai da yawa da ba ma kasawa, ko idan ’yan’uwa Kiristoci ba su lura ba. Ya fi ban ƙarfafa mu tuna da kalmomin Zabura 130:3: “Idan kai, ya Ubangiji, za ka ƙididdiga laifofi, wa za ya tsaya, ya Ubangiji?”

16, 17. (a) Ta yaya za mu yi amfani da Galatiyawa 6:2, 5 game da kamewa? (b) Menene za mu sake bincika game da kamewa?

16 Dole kowannenmu mu koyi kamewa don mu faranta wa Jehovah rai, amma za mu tabbata ’yan’uwanmu Kiristoci za su ba da taimako. Ko da dole ne kowannenmu zai ɗauki nasa hakki, an aririce mu mu taimaki juna mu jimre da kumammanci. (Galatiyawa 6:2, 5) Za mu gode wa iyaye, abokiyar aure, ko kuma aboki da ya hana mu daga zuwan wurare da bai kamata mu je ba, daga kallon abubuwa da bai kamata mu kalla ba, ko yin abubuwa da ba su kamata ba. Suna taimakonmu mu nuna kamewa, mu iya ce a’a kuma mu dage!

17 Kiristoci da yawa suna bin abin da muka bincika daga farko zuwa nan game da kamewa, amma suna iya jin za su daɗa gyara. Za su so su nuna kamewa yadda za a yi tsammani daga ’yan Adam ajizai. Haka kake ji? To, me za ka iya yi ka koyi wannan fasali na ’yar ruhun Allah? Amma yaya yin haka zai taimake ka ka cim ma burinka na Kirista na dogon lokaci? Bari mu ga a talifi na gaba.

Ka Tuna?

Me Ya Sa Kamewa . . .

• take da muhimmanci Kiristoci su koya?

• take wa wasu wuya?

• wajibi ne cikin aure?

• hali ne da za mu taimaki juna su koya?

[Box/Hoto a shafi na 12]

Ya Koya Ya Ce A’a

Wani Mashaidin Jehovah da yake zama a Jamus yana aikin akawu a tashan telibijin. Aikinsa ya haɗa da lura da tsarin ayyuka 30 dabam dabam na telibijin da na rediyo. Sa’ad da iska ta birkice, sai ya mai da hankali ga tsarin ayyuka domin ya gano matsalar. Ya ce: “Birkicewar tana faruwa lokacin da bai dace ba, lokacin tsarin nuna ƙarfi ko kuma na jima’i. Waɗannan munanan ayyuka suna daɗewa a zuciyata na kwanaki har makonni ma, kamar an shuka cikin ƙwaƙwalwata.” Ya ce wannan ya shafi ruhaniyarsa: “Na kasance mai zafin rai, saboda tsarin ayyuka na nuna ƙarfi ya sa ya yi mini wuya na kame kai. Tsarin ayyuka na jima’i yana kawo wa ni da matata faɗa. Kullum ina kokawa da wannan tasiri. Domin in sha kan wannan tasiri na shawarta na nemi sabon aiki, ko idan albashin zai kasa. Bai daɗe ba da na samu wani aiki. Bukatata ta biya.”

[Hotuna a shafi na 11]

Sani daga nazarin Littafi Mai Tsarki na taimakonmu mu kame kai

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba