“Ka Faranta Zuciyarka Cikin Ubangiji”
“Ka faranta zuciyarka cikin Ubangiji kuma; za ya kuwa biya maka muradin zuciyarka.”—ZABURA 37:4.
1, 2. Wanene Tushen farin ciki na gaske, kuma ta yaya Sarki Dauda ya jawo hankali ga wannan gaskiyar?
“MASU albarka ne masu-ladabi a ruhu . . . masu albarka ne masu jinƙai . . . masu albarka ne masu-sada zumunta.” Waɗannan ne muhimman gabatarwa na Huɗuba Bisa Dutse na Yesu tare da wasu kwatanci shida na waɗanda suke farin ciki, yadda marubucin Lingila, Matta ya rubuta. (Matta 5:3-11) Kalmomin Yesu sun tabbatar da mu cewa za mu iya samun farin ciki.
2 Wata waƙar bauta da Sarki Dauda na Isra’ila ta dā ya rubuta ya jawo hankali ga Tushen farin ciki na gaske, Jehovah. “Ka faranta zuciyarka cikin Ubangiji,” in ji Dauda, “za ya kuwa biya maka muradin zuciyarka.” (Zabura 37:4) Amma menene zai sa sanin Jehovah da kuma fasaloli na mutuntakarsa ya zama abin ‘faranta zuciya’? Ta yaya bincika abin da ya yi da wanda zai yi a cika ƙudurinsa za su sa ka yi tsammanin samun “muradin zuciyarka”? Idan muka bincika Zabura 37, ayoyi 1 zuwa 11 sosai, za ta ba da amsoshin.
‘Kada Ka Ji Kishi’
3, 4. Kamar yadda aka rubuta a Zabura 37:1, wace shawara ce Dauda ya bayar, kuma me ya sa binta ta dace a yau?
3 Muna zama cikin “miyagun zamanu,” kuma mugunta tana yawaitawa. Mun riga mun ga gaskiyar kalmomin manzo Bulus: “Miyagun mutane da masu-hila za su daɗa mugunta gaba gaba, suna ruɗi, ana ruɗinsu.” (2 Timothawus 3:1, 13) Yana da sauƙi mu ƙyale cin nasara da miyagu suke yi da kuma ni’imarsu su shafe mu! Dukan wannan na iya raba mana hankali kuma ya sa fahiminmu na ruhaniya ya birkice. Ka lura da yadda kalmomi na farko na Zabura 37 suke faɗakar da mu ga haɗarin da ke cikin wannan: “Kada ka dami ranka saboda masu-aika mugunta, kada kuwa ka ji kishin masu-aika rashin adalci.”
4 Hanyoyin wasa labarai na duniya kowacce rana suna damunmu da labarai na yawan rashin gaskiya. ’Yan kasuwa masu zamba suna samun nasara. Masu aika laifi suna zambaci marasa taimako. Waɗanda suke kisan kai ba a kama su ko kuma ba a yi musu horo. Irin waɗannan misalai duka na kangara wa gaskiya suna iya fusata mu kuma su dami salamarmu. Yadda miyagu suke samun nasara zai iya sa mu yi kishinsu. Amma fushi ne zai gyara yanayin? Kishin nasarar da miyagu suke samu ne zai hana sakamakon da zai same su? Sam, ba haka ba! Hakika, ba mu da dalilin mu ‘dami ranmu.’ Me ya sa?
5. Me ya sa aka kamanci miyagu da ciyayi?
5 Mai Zabura ya amsa: “Gama da wuri za a shibce su kamar ciyawa, su yi yaushi kamar ɗanyen ganye.” (Zabura 37:2) Sababbin ciyayi suna da kyaun gani, amma ba da daɗewa ba sukan yi yaushi su mutu. Haka zai faru wa miyagu. Ni’imarsu ba za ta daɗe ba. Idan suka mutu, dukan ribarsu na ha’inci ba zai iya taimakonsu ba. Daga bisani kowa zai shaida gaskiya. “Hakkin zunubi mutuwa ne,” in ji Bulus. (Romawa 6:23) Miyagu da kuma dukan marasa adalci a ƙarshe za su sami ‘hakkinsu’ ba za su ƙara kasancewa. Hakika hanyar rayuwa ce marar amfani!—Zabura 37:35, 36; 49:16, 17.
6. Wane darasi za mu koya daga Zabura 37:1, 2?
6 To, ya kamata ne mu yarda wa ni’ima ta miyagu da ba ta daɗewa ta dame mu? Darasi daga ayoyi biyu na farko na Zabura 37 shi ne: Kada ka yarda cin nasararsu ta sa ka kauce daga tafarkin da ka zaɓa na bauta wa Jehovah. Maimako, ka sa zuciyarka ga albarka ta ruhaniya da kuma makasudanka.—Misalai 23:17.
“Ka Dogara ga Ubangiji, Ka Yi Aikin Nagarta”
7. Me ya sa ya kamata mu dogara ga Jehovah?
7 Mai Zabura ya aririce mu: “Ka dogara ga Ubangiji, ka yi aikin nagarta.” (Zabura 37:3a) Idan muna alhini ko kuma shakka, muna bukatar mu dogara sosai ga Jehovah. Shi ne Wanda yake ba da kwanciyar rai ta ruhaniya. “Mai-zama cikin sitirar Maɗaukaki,” in ji Musa, “za ya dawwama a ƙarƙashin inuwar mai-iko duka.” (Zabura 91:1) Sa’ad da muke damuwa saboda ƙaruwar taka doka ta wannan zamani, muna bukatar mu dogara ga Jehovah sosai. Idan idon ƙafanmu ya tangarɗe, za mu so mu sami taimakon wani aboki mu dafā masa. Haka kuma, idan muka yi ƙoƙarin yin tafiya cikin aminci, muna bukatar goyon bayan Jehovah.—Ishaya 50:10.
8. Ta yaya sa hannu cikin hidimar Kirista ke taimakonmu mu guje wa damuwa ainun da ni’imar miyagu?
8 Hanya ɗaya da ba za mu damu da ni’imar miyagu ba ita ce ta taƙurewa a neman kuma a taimakon masu kama da tumaki su samu cikakken sani na ƙudurin Jehovah. Domin ƙaruwar mugunta, muna bukatar mu taƙure a taimakon wasu. “Kada ku manta da yin alheri da zumuntar tarayya,” in ji manzo Bulus, “gama da irin waɗannan hadayu Allah yana jin daɗi.” “Alheri” mai girma da za mu iya yi wa wasu shi ne, mu yi musu bishara mai ɗaukaka ta Mulkin Allah. Hakika, wa’azin da muke yi a fili “hadayu” ne.—Ibraniyawa 13:15, 16; Galatiyawa 6:10.
9. Ka bayyana kashedin Dauda na a “zauna a cikin ƙasan.”
9 Dauda ya ci gaba da cewa: “Ka zauna a cikin ƙasan, ka lizimci aminci.” (Zabura 37:3b) “Ƙasan” ta zamanin Dauda ita ce yankin da Jehovah ya ba wa Isra’ila, Ƙasar Alkawari. A lokacin sarautar Sulemanu yankunan sun kai daga Dan a ta arewa zuwa Beer-sheba a ta kudu. Inda Isra’ila ke zama ke nan. (1 Sarakuna 4:25) A yau, duk inda muke zama a duniya, muna sauraron lokacin da dukan duniya za ta zama aljanna a sabuwar duniya ta adalci. Kafin lokacin, muna da kwanciyar rai ta ruhaniya.—Ishaya 65:13, 14.
10. Me zai zama sakamakon idan muka “lizimci adalci”?
10 Me zai zama sakamakon idan muka “lizimci adalci”? Wannan huraren karin magana ta tunasar da mu: “Amintaccen mutum za ya cika da albarka.” (Misalai 28:20) Idan muka ci gaba cikin yin wa’azin bishara duk inda muke kuma ga dukan wanda za mu iya kai wa, za ta kawo albarka daga Jehovah. Alal misali, Frank da matarsa, Rose, suka shiga aikin majagaba shekaru 40 da suka shiga a wani gari a arewacin Scotland. Kalilan da suka so gaskiya lokacin sun bijire yanzu. Ba su yi sanyin gwiwa ba, aurarrun nan majagaba suka ci gaba da aikin wa’azinsu kuma suna almajirantarwa. Yanzu da akwai ikilisiyar da take ci gaba a wannan garin. Lallai amincin aurarrun nan ya sami albarkar Jehovah. “Babban albarkar,” in ji Frank, “ita ce cewa muna cikin gaskiya kuma muna da amfani wajen Jehovah.” Hakika, idan muka “lizimci adalci,” za mu samu kuma mu yi godiya ga albarka mai yawa.
“Ka Faranta Zuciyarka Cikin Ubangiji”
11, 12. (a) Ta yaya za mu ‘faranta zuciya cikin Ubangiji’? (b) Wane makasudi za ka iya ka kafa domin nazarinka, kuma ƙila wane sakamako za ka samu?
11 Dole ne mu ‘faranta zuciyarmu cikin Ubangiji’ idan za mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehovah kuma adana dogararmu gare shi. (Zabura 37:4a) Ta yaya za mu yi wannan? Maimakon mu dulmaya domin damuwa da yanayinmu, ko da yana da wuya ma, za mu biɗi Jehovah. Hanya ɗaya ta yin haka ita ce mu keɓe lokaci don mu karanta Kalmarsa. (Zabura 1:1, 2) Kana farin ciki a karatun Littafi Mai Tsarki naka? Haka zai zama idan ka karanta shi da nufin ƙara koyo game da Jehovah. Me ya sa ba za ka ɗan dakanta ba bayan ka yi karatun, kuma ka tambayi kanka, ‘Menene wannan wurin yake koya mini game da Jehovah?’ Ƙila zai yi kyau kana da wani littafin rubutu ko kuma takarda sa’ad da kake karatun Littafi Mai Tsarki. Duk lokacin da ka dakanta ka yi tunani a kan abin da ka karanta, ka ɗan rubuta wani abin da zai tuna maka wani halin Allah da kake so. A cikin wata Zabura kuma Dauda ya rera: “Bari batutuwan bakina, da tunanin zuciyata, su zama abin karɓa a gareka, Ya Ubangiji, dutsena da mai-fansana.” (Zabura 19:14) Idan muka mai da hankali a yin tunanin Kalmar Allah zai zama “abin karɓa” ne ga Jehovah—kuma abin farin ciki ne gare mu.
12 Ta yaya za mu sami farin ciki daga nazarinmu da kuma yin bimbini? Za mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu koya game da Jehovah da kuma hanyoyinsa. Irin waɗannan littattafai na The Greatest Man Who Ever Lived da kuma Ka Kusaci Jehovaha za su taimake mu don mu yi tunani da zai amfane mu. Da haka, Dauda ya tabbatar da masu adalci, Jehovah “za ya kuwa biya maka muradin zuciyarka.” (Zabura 37:4b) Irin wannan tabbaci ne lallai ya sa manzo Yohanna ya rubuta waɗannan kalmomi: “Gaba gaɗi ke nan da mu ke yi a gabansa, idan mun roƙi kome daidai da nufinsa, yana jinmu: kuma idan mun sani yana jinmu, kome mu ke roƙo, mun sani muna samun abin da mun roƙa a gareshi.”—1 Yohanna 5:14, 15.
13. A cikin shekarun bayan nan wace faɗaɗawa na aikin wa’azin Mulki aka gani a ƙasashe da yawa?
13 Mu masu riƙe aminci, farin cikinmu shi ne mu ga an kunita ikon mallaka na Jehovah. (Misalai 27:11) Ba ma farin ciki ne idan muka ji game da aikin wa’azi mai girma da ’yan’uwanmu suke yi a ƙasashe da a dā suke ƙarƙashin mulkin kama karya ko kuma na zalunci? Muna ɗokin sauraron ƙarin ’yanci da za a iya samu kafin ƙarshen wannan zamani. Bayin Jehovah da yawa da suke a ƙasashen Gabas suna sa hannu sosai a yin wa’azi ga ɗalibai, ’yan gudun hijira, da wasu kuma da suke zama a wurin na ɗan lokaci da suke moran ’yanci. Muradinmu ne cewa sa’ad da mutanen nan suka koma gida, za su ci gaba da haskaka hasken gaskiya a wuraren da kamar yana da wuya a kai su.—Matta 5:14-16.
“Ka Danƙa ma Ubangiji Tafarkinka”
14. Wane tabbaci ne akwai cewa za mu iya dogara ga Jehovah?
14 Abin murna ne mu sani cewa damuwanmu da kuma abubuwan da kamar suna nauyaya mana sosai za a sami sauƙinsu! Ta yaya? “Ka danƙa ma Ubangiji tafarkinka,” in ji Dauda sai kuma ya daɗa, “shi kuma za ya tabbatadda shi.” (Zabura 37:5) A ikilisiyoyinmu muna da tabbaci isashe cewa Jehovah ne yake toƙara mana sarai. (Zabura 55:22) Waɗanda suke hidima ta cikakken lokaci, ko majagaba, masu kula masu ziyara, masu wa’azi na ƙasashen waje, ko kuma waɗanda suke ba da kansu su yi hidima a Bethel ne, duka suna iya yarda da tabbacin kulawar Jehovah gare su. Me ya sa ba za ka yi magana da waɗanda ka sani ka tambaye su yadda Jehovah ya taimake su ba? Babu shakka za ka ji labarai da yawa na nuna cewa ko a lokatai masu wuya ma, Jehovah ba ya kasa taimakawa. Kowane lokaci yana tanadin bukatun rayuwa.—Zabura 37:25; Matta 6:25-34.
15. Ta yaya adalcin mutanen Allah yake haskakawa?
15 Sa’ad da muka dogara ga Jehovah mun tabbata da shi sarai, za mu iya shaida kalmomin mai Zabura na gaba: “Za ya sa adalcinka ya bayyana kamar haske, hukuncinka kuma kamar tsakar rana.” (Zabura 37:6) Sau da yawa, mu Shaidun Jehovah mukan iske ana ɓata sunanmu. Amma Jehovah yana buɗe idanun masu zuciyar kirki ya taimake su su fahimta cewa hidimarmu ta fili ƙaunarmu ga Jehovah ne da kuma maƙwabta ke motsa mu. Har ila kuma, ba ma iya ɓoye nagarin halinmu, ko da mutane da yawa suna ɓata mana suna. Jehovah yana kiyaye mu duk cikin kowacce irin hamayya da tsanani. Domin haka, adalcin mutanen Allah yana haskakawa kamar rana da tsakar rana.—1 Bitrus 2:12.
‘Ka Natsu . . . Kana Sauraro’
16, 17. A jituwa da Zabura 37:7, yanzu lokacin menene ne, kuma me ya sa?
16 Kalmomin mai Zabura na gaba sune: ‘Ka natsu a gaban Ubangiji, ka yi haƙuri kana sauraronsa: Kada ka dami ranka saboda wanda ya ke albarka a cikin tafarkinsa, saboda mutumin da ke tsira munanan dabaru, suna kuwa ci.’ (Zabura 37:7) A nan Dauda ya nanata bukatar mu jira cikin haƙuri ga Jehovah don ya aikata. Ko da ma ƙarshen zamani bai zo ba tukuna, ba dalilin yin gunaguni ba ne. Ba ma gani ne cewa jinƙan Jehovah da kuma haƙurinsa yana da girma fiye da yadda dā muke tsammani? Mu ma za mu iya nuna ta wurin taƙurewa cikin wa’azin bishara kafin ƙarshen zamanin ya zo? (Markus 13:10) Yanzu ne lokaci da za mu guje wa shawara ta garaje da za ta hana mu farin ciki da kuma kwanciyar rai ta ruhaniya. Yanzu ne lokaci da za mu tsayayya wa ɓatanci masu ƙarfi na duniyar Shaiɗan. Yanzu ne kuma lokaci na riƙe ɗabi’ar tsabta kuma mu ƙi ɓata tsayawarmu ta adalci wurin Jehovah. Bari mu ci gaba da ƙi da tunanin lalata kuma mu guje wa halaye da ba su dace ba wajen kishiyar jinsi ko kuma waɗanda ba kishiyar jinsi ba.—Kolossiyawa 3:5.
17 Dauda ya yi mana gargaɗi: “Ka daina yin fushi, ka rabu da hasala: Kada ka dami ranka, wannan ba ya kawo kome ba sai mugunta. Gama za a datse masu-aika mugunta: amma waɗanda ke sauraro ga Ubangiji, su ne za su gāji duniya.” (Zabura 37:8, 9) Hakika, za mu kasance da tabbaci a sauraron lokaci—da yanzu ya yi kusa—da Jehovah zai kawar da dukan ɓatanci da waɗanda suke yinsa daga duniya.
“In An Jima Kaɗan”
18, 19. Wace ƙarfafa ka samu daga Zabura 37:10?
18 “Gama in an jima kaɗan, sa’annan mai-mugunta ba shi: hakika, da anniya za ka duba wurin zamansa, ba kuwa za ya kasance ba.” (Zabura 37:10) Dubi yadda waɗannan kalmomi suke ƙarfafa mu da muke kusa da ƙarshen wannan zamani da kuma ƙarshen mugun ’yanci daga Jehovah! Ko wace irin gwamnati ce ko iko mutum ya tsara, lallai ta kasa sarai. Yanzu kuma muna kusa da lokaci da za mu koma sarauta ta Allah, Mulkin Jehovah a hannun Yesu Kristi. Za ya sarrafa dukan harkokin duniya kuma cire dukan ’yan hamayya da Mulkin Allah.—Daniel 2:44.
19 A cikin sabuwar duniya ta Mulkin Allah, kana iya bincike yadda ka iya, ba za ka ga “mai-mugunta” ba. Hakika, duk wanda a lokacin ya yi tawaye ga Jehovah, da sauri za a cire shi. Babu wanda yake fāɗa da ikonsa na mallaka ko kuma ke ƙin yin biyayya ga ikon Allah da zai kasance a wurin. Dukan maƙwabtanka za su zama waɗanda suke son su faranta wa Jehovah rai ne. Lallai wannan zai kawo kwanciyar rai—babu maƙullai, ko matsari, babu abin da zai ɓata dogara ta sarai da farin ciki ba!—Ishaya 65:20; Mikah 4:4; 2 Bitrus 3:13.
20, 21. (a) Su waye ne “masu-tawali’u” na Zabura 37:11, kuma a ina suke samun “yalwar salama”? (b) Wace albarka za mu samu idan muka yi koyi da Dauda Babba?
20 Sai kuma, “masu-tawali’u za su gaji ƙasan.” (Zabura 37:11a) Amma su waye “masu-tawali’u”? Kalmar da aka fassara “tawali’u” ta fito ne daga kalmar nan da take nufin “wanda aka wahal, mai sauƙin kai, da aka kunyatar.” Hakika, “masu tawali’u” waɗanda suke jiran Jehovah cikin sauƙin kai don ya kawar da mugunta da ake yi musu. “Za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.” (Zabura 37:11b) Ko a yanzu ma muna samun yalwar salama a aljanna ta ruhaniya ta wurin yin tarayya da ikilisiyar Kirista ta gaskiya.
21 Ko da yake har ila muna cikin wahala, muna goyon bayan juna kuma muna ta’azantar da waɗanda suke baƙin ciki. A ta haka, ana gabatar da gamsuwa tsakanin mutanen Jehovah. ’Yan’uwa da aka naɗa makiyaya suna hidima ta ruhaniya da kyau—kuma a wasu lokatai suna taimakawa a biyan bukatu na jiki—da ke taimaka a jimre wa wahala domin adalci. (1 Tassalunikawa 2:7, 11; 1 Bitrus 5:2, 3) Lallai wannan salamar dukiya ce mai tamani! Kuma muna da begen rai na har abada cikin Aljanna ta salama da ke zuwa. Bari mu yi koyi da Dauda Babba, Kristi Yesu, wanda himmarsa ga Jehovah ke motsa shi ya yi hidima da aminci zuwa ƙarshe. (1 Bitrus 2:21) Ta yin haka, za mu ci gaba da farin ciki, muna yabon wanda muke faranta zuciyarmu gare shi, Allahnmu Jehovah.
[Hasiya]
a Shaidun Jehovah ne suka buga.
Za Ka Iya Amsawa?
• Waɗanne darussa ka koya daga Zabura 37:1, 2?
• Ta yaya za ka iya “faranta zuciyarka cikin Ubangiji”?
• Wane tabbaci muke da shi cewa za mu dogara ga Jehovah?
[Hoto a shafi na 21]
Kiristoci ba sa ‘kishin waɗanda suke rashin adalci’
[Hoto a shafi na 22]
“Ka dogara ga Ubangiji, ka yi aikin nagarta”
[Hoto a shafi na 23]
Ka faranta zuciyarka cikin Jehovah ta yin iyakacin ƙoƙarinka ka koya game da shi
[Hoto a shafi na 24]
“Masu-tawali’u za su gāji ƙasan”