Kana Jin Daɗin “Shari’ar Allah”?
“Albarka ta tabbata ga mutumin da . . . [ke] jin daɗin karanta shari’ar Allah.”— ZABURA 1:1, 2.
1. Me ya sa mu bayin Jehovah muke farin ciki?
JEHOVAH yana taimakonmu bayinsa masu aminci kuma yana yi mana albarka. Hakika, muna fuskantar gwaji da yawa. Amma kuma muna morar farin ciki na gaske. Wannan ba abin mamaki ba ne domin muna bauta wa “Allah [mai farin ciki],” kuma ruhunsa mai tsarki yana sa mu farin ciki. (1 Timoti 1:11; Galatiyawa 5:22) Ana samun farin ciki na gaske daga wani abu da ake tsammaninsa ko kuma wani nagarin abu da aka samu. Ubanmu na samaniya babu shakka yana ba mu kyakkyawar baiwa. (Yakubu 1:17) Shi ya sa muke farin ciki!
2. Wace zabura za mu tattauna?
2 An nanata albarka a littafin Zabura. Alal misali, an nanata ta a Zabura ta 1 da ta 2. Mabiyan Yesu Kristi na farko sun ce sarkin Isra’ila, Dauda ne ya rera zabura ta biyu. (Ayyukan Manzanni 4:25, 26) Wanda ya rubuta zabura ta farko da ba a ambata sunansa ba ya soma waƙarsa da aka hure da waɗannan kalmomin: “Albarka ta tabbata ga mutumin da ba ya karɓar shawarar mugaye.” (Zabura 1:1) A wannan talifin da na gaba, za mu ga yadda Zabura ta 1 da ta 2 ta ba mu dalilin murna.
Asirin Samun Albarka
3. In ji Zabura 1:1, waɗanne dalilai ya sa albarka ta tabbata ga mai ibada?
3 Zabura ta 1 ta nuna abin da ya sa albarka ta tabbata ga mutum mai ibada. Da yake ba da wasu dalilan irin wannan albarka, mai Zabura ya rera: “Albarka ta tabbata ga mutumin da ba ya karɓar shawarar mugaye, wanda ba ya bin al’amuran masu zunubi, ko ya haɗa kai da masu wasa da Allah.”—Zabura 1:1.
4. Wane tafarki da abin koyi ne Zakariya da Alisabatu suka biɗa?
4 Don mu samu albarka ta gaske, dole ne mu yi biyayya da farillai masu adalci na Jehovah. Zakariya da Alisabatu da suke da gatar zama iyayen Yahaya mai Baftisma, “masu adalci ne a gaban Allah, suna bin umarnin Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi.” (Luka 1:5, 6) Za mu zama masu albarka idan mun bi irin wannan tafarki kuma muka ƙi “karɓar shawarar mugaye” ko kuma shawararsu ta mugunta ta yi mana ja-gora.
5. Menene zai taimake mu mu ƙi da “al’amuran masu zunubi”?
5 Idan mun ƙi ra’ayin mugaye, ba za mu ‘bi al’amuran masu zunubi’ ba. Wannan yana nufin cewa ba za mu je wuraren da suke ba—wuraren nishaɗi na lalata ko kuma mummunar wurare. Idan aka jarabe mu mu bi masu zunubi a ayyukansu da ba na Nassi ba fa? Sai mu yi addu’a mu nemi taimakon Allah don mu aikata daidai da kalmomin manzo Bulus: “Kada ku yi cuɗanya marar dacewa da marasa ba da gaskiya. To, me ya haɗa aikin adalci da na mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu?” (2 Korantiyawa 6:14) Idan mun dogara ga Allah kuma muka kasance masu “tsarkakakkiyar zuciya,” za mu ƙi da hali da salon rayuwa na masu zunubi kuma za mu kasance da ra’ayi da sha’awoyi masu tsabta, tare da “sahihiyar bangaskiya.”—Matiyu 5:8; 1 Timoti 1:5.
6. Me ya sa za mu mai da hankali game da masu ba’a?
6 Don mu faranta wa Jehovah rai, ba za mu ‘haɗa kai da masu wasa da Allah ba.’ Wasu suna wasa da kiyaye dokokin Allah, amma a wannan “zamanin ƙarshe,” waɗanda dā Kiristoci ne da suka zama ’yan ridda sukan kasance da reni sosai a ba’ar da suke yi. Manzo Bitrus ya yi wa ’yan’uwa masu bi gargaɗi: “Ya ƙaunatattuna . . . da farko dai lalle ne ku fahimci wannan, cewa can zamanin ƙarshe masu ba’a za su zo suna ba’a, suna biye wa muguwar sha’awa tasu, suna cewa, ‘To, ina alkawarin dawowa tāsa? ai, tun lokacin da kakannin-kakanninmu suka ƙaura, dukan abubuwa suna tafe ne kamar dā, tun farkon halitta.’ ” (2 Bitrus 3:1-4) Idan ba ma ‘haɗa kai da masu ba’a’ za mu kauce wa masifa da hakika zai same su.—Karin Magana 1:22-27.
7. Me ya sa za mu yi biyayya da kalmomin Zabura 1:1?
7 Idan ba mu yi biyayya da kalmomin da suka soma Zabura ta 1 ba, muna iya rashin ruhaniya da muka samu ta nazarin Nassosi. Hakika, rayuwarmu tana iya daɗa muni. Rashin ruhaniyarmu zai iya soma idan mun bi shawarar mugaye. Sai mu soma tarayya da su kullum. A kwana a tashi, muna iya zama ’yan ridda marasa aminci masu ba’a. Babu shakka, abokantaka da mugaye zai iya sa mu kasance da ruhun rashin ibada kuma zai halaka dagantakarmu da Jehovah Allah. (1 Korantiyawa 15:33; Yakubu 4:4) Kada mu ƙyale wannan ya faru mana!
8. Menene zai taimake mu mu sa zuciyarmu a kan abubuwa na ruhaniya?
8 Addu’a za ta taimake mu mu sa zuciyarmu a abubuwa na ruhaniya kuma mu kauce wa tarayya da mugaye. Bulus ya rubuta: “Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta yin addu’a da roƙo, tare da gode wa Allah. Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.” Manzon ya ƙarfafa a yi tunanin abubuwa na gaskiya, na girmamawa, da ke daidai, na tsattsarka, ƙauna, daddaɗar magana, mafifici, da abin da ya cancanci yabo. (Filibiyawa 4:6-8) Bari mu aikata cikin jituwa da gargaɗin Bulus, kuma kada mu ƙasƙantar da kanmu zuwa yanayin mugaye.
9. Ko da muna kauce wa ayyukan mugunta, ta yaya muke ƙoƙarin mu taimaki dukan iri-irin mutane?
9 Ko da muna ƙi da ayyuka na mugunta, muna yi wa mutane wa’azi da hikima yadda manzo Bulus ya yi wa Filikus Gwamnar Roma magana “a kan adalci, da kamunkai, da kuma hukuncin nan mai zuwa.” (Ayyukan Manzanni 24:24, 25; Kolosiyawa 4:6) Muna wa dukan iri-irin mutane wa’azin bisharar Mulki, kuma muna bi da su a hankali. Muna da tabbaci cewa waɗanda “aka ƙaddara wa samun rai madawwami” za su zama masu bi da suke son shari’ar Allah.—Ayyukan Manzanni 13:48.
Yana Jin Daɗin Shari’ar Jehovah
10. Menene zai sa mu riƙa tuna da abin da muka karanta a lokacin nazari na kanmu?
10 Game da mutum mai albarka, mai Zabura ya daɗa cewa: “Yana jin daɗin karanta shari’ar Allah, [ya kan riƙa tunani] dare da rana.” (Zabura 1:2; Litafi Mai-Tsarki) Da yake mu bayin Allah ne muna ‘jin daɗin shari’ar Jehovah.’ Idan ya yiwu, lokacin nazari da bimbini na kanmu, muna iya “tunani” a kan abin da muke karantawa. Yin hakan sa’ad da muke karanta kowane wuri a cikin Nassosi zai sa mu riƙa tunawa.
11. Me ya sa za mu karanta Littafi Mai Tsarki “dare da rana”?
11 “Amintaccen bawan nan mai hikima,” yana ƙarfafa mu mu karanta Littafi Mai Tsarki kullum. (Matiyu 24:45) Domin muna son mu sarƙu da saƙon Jehovah ga ’yan Adam, yana da kyau mu karanta Littafi Mai Tsarki “dare da rana”—hakika, har sa’ad da ba mu iya barci don wasu dalilai ba. Bitrus ya aririce mu: “Kamar jariri sabon haihuwa, ku yi marmarin shan madara marar gami mai ruhu, domin ku girma da shi, har ya kai ku ga samun ceto.” (1 Bitrus 2:1, 2) Kana jin daɗin karanta Littafi Mai Tsarki kullum da kuma yin bimbini a kan Kalmar Allah da nufe-nufensa daddare? Mai Zabura ya yi hakan.—Zabura 63:6.
12. Menene za mu yi idan muna jin daɗin shari’ar Jehovah?
12 Za mu sami madawwamin farin ciki idan muna jin daɗin shari’ar Allah. Cikakkiya ce da kuma adalci, ana samun lada mai yawa a yin biyayya da ita. (Zabura 19:7-11) Almajiri Yakubu ya rubuta: “Mai duba cikakkiyar ƙa’idan nan ta ’yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai ya mance ba, sai dai mai aikatawa ne ya zartar, to, wannan shi za a yi wa albarka cikin abin da yake aikatawa.” (Yakubu 1:25) Idan muna jin daɗin shari’ar Jehovah da gaske, kowace rana za mu bincika batutuwa na ruhaniya. Hakika, za mu motsa mu ‘nemi zurfafan al’amuran Allah’ kuma mu fara ƙwallafa rai ga al’amuran Mulki.—1 Korantiyawa 2:10-13; Matiyu 6:33.
Yana Kama da Itace
13-15. A wane azanci ne za mu zama kamar itace da aka shuka kusa da tushen ruwa mai yawa?
13 Mai Zabura ya ci gaba da kwatanta adali, ya ce: “Yana kama da itacen da ke a gefen ƙorama, yakan ba da ’ya’ya a kan kari, ganyayensa ba sa yin yaushi, yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.” (Zabura 1:3) Kamar dukan mutane ajizai, mu da muke bauta wa Jehovah muna fuskantar matsaloli a rayuwa. (Ayuba 14:1) Muna iya shan wahalar tsanantawa da wasu gwaje-gwaje domin bangaskiyarmu. (Matiyu 5:10-12) Amma da taimakon Allah, za mu yi nasara a jimre wa waɗannan gwaje-gwaje, yadda lafiyayyen itace yake jimre wa iska mai ƙarfi.
14 Itace da aka shuka wurin da yake samun ruwa koyaushe ba ya bushewa a lokacin zafi ko fari. Idan mu masu jin tsoron Allah ne, ƙarfinmu na zuwa daga Tushe da ba ya kasawa—Jehovah Allah. Bulus ya nemi taimako wurin Allah shi ya sa ya ce: “Zan iya yin kome albarkacin wannan [Jehovah] da yake ƙarfafata.” (Filibiyawa 4:13) Yayin da ruhu mai tsarki na Jehovah yana yi mana ja-gora kuma kiyaye mu a ruhaniya, ba za mu shanye ba, mu zama marasa ba da ’ya’ya ko kuma mu mutu a ruhaniya. Muna ba da ’ya’ya a hidimar Allah da kuma nuna albarkar ruhunsa.—Irmiya 17:7, 8; Galatiyawa 5:22, 23.
15 Ta yin amfani da kalmar Helenanci da aka fassara “kama,” mai Zabura ya yi amfani da tamka. Yana kwatanta abubuwa biyu da suke kama da juna amma sun bambanta. Mutane dabam suke da itatuwa, amma kyaun itace da aka shuka kusa da tushen ruwa, babu shakka ya tuna wa mai Zabura ni’ima ta ruhaniya na waɗanda suke “jin daɗin karanta shari’ar Allah.” Idan muna jin daɗin shari’ar Allah, kwanakinmu za su iya zama kamar na itace. Hakika, za mu iya rayuwa har abada.—Yahaya 17:3.
16. Me ya sa kuma ta yaya muke ‘nasara a dukan abin da muke yi’?
16 Yayin da muka biɗi tafarkin adalci, Jehovah zai taimake mu mu jimre wa gwaje-gwaje da wahala. Za mu yi farin ciki kuma mu ba da ’ya’ya a hidimar Allah. (Matiyu 13:23; Luka 8:15) ‘Mukan yi nasara a dukan abin da muke yi’ domin manufarmu ta musamman ita ce mu yi nufin Jehovah. Tun da yake nufe-nufensa koyaushe na nasara kuma muna jin daɗin umurninsa, za mu yi nasara a ruhaniya. (Farawa 39:23; Joshuwa 1:7, 8; Ishaya 55:11) Hakan yake har lokacin da muke fuskantar wahala.—Zabura 112:1-3; 3 Yahaya 2.
Mugaye Kamar Suna Nasara
17, 18. (a) Da menene mai Zabura ya kamanta mugaye? (b) Idan ma mugaye suna nasara a samun abin duniya, me ya sa ba su da kwanciyar rai na dindindin?
17 Yanayin mugu dabam yake da na adali! Mugaye kamar suna samun nasarar abin duniya na ɗan lokaci, amma ba sa nasara a ruhaniya. Mai Zabura ya nuna haka ta kalmominsa na gaba: “Amma mugaye ba haka suke ba, su kamar yayi suke wanda iska take kwashewa. Allah kuwa zai hukunta mugaye, masu zunubi kuwa za a ware su daga adalai.” (Zabura 1:4, 5) Ka lura cewa mai Zabura ya ce, “mugaye ba haka suke ba.” Yana nufin cewa ba su yi kama da masu ibada ba, da aka kwatanta su da itatuwa masu ba da ’ya’ya na dogon lokaci.
18 Idan ma mugaye suna nasara a samun abin duniya, ba su da kwanciyar rai na dindindin. (Zabura 37:16; 73:3, 12) Sun yi kama da mutum mai arziki marar azanci da Yesu ya ambata a wani kwatanci sa’ad da aka gaya masa ya tsai da shawara a kan batun samun gadō. Yesu ya gaya wa waɗanda suke wajen: “Ku kula fa, ku yi nesa da kowane irin kwaɗayi, don yawan kaya ba shi ne rai ba.” Yesu ya ba da wannan misalin cewa gonar wani mai arziki ta yi albarka ƙwarai da ya yi shawara zai rushe rumbunsa ya gina waɗansu manya da zai zuba amfanin gonarsa. Sai mutumin ya yi shiri ya yi ta ci, ya sha, yana shagali. Amma Allah ya ce: “Kai marar azanci! A daren nan za a karɓi ranka. To, kayan da ka tanada, na wa za su zama?” Don ya nanata darasin, Yesu ya daɗa: “Haka wanda ya tanadar wa kansa dukiya yake, ba shi kuwa da wani tanadi a gun Allah.”—Luka 12:13-21.
19, 20. (a) Ka kwatanta yadda ake sussuke da kuma sheƙa hatsi a Isra’ila ta dā. (b) Me ya sa aka kwatanta mugaye da ƙaiƙayi?
19 Mugaye ba su da “wani tanadi a gun Allah.” Shi ya sa ba su fi ƙaiƙayi kwanciyar hankali da ƙarfi ba. Bayan an girbe hatsi a Isra’ila ta dā, sai a kai masussuka, babban fili a kan tudu. A wajen, dabbobi suna jan ƙatuwar guduma mai dutse mai ƙaifi ko kuma mai haƙorin ƙarfe bisa hatsin don su murtsuke ƙwayoyin daga ƙaiƙayin. Bayan haka, sai a yi amfani da tebur na sheƙa don a rairaye duka, iska kuma ta kwashe ƙaiƙayin. (Ishaya 30:24) Ƙwayoyin hatsin za su riƙa faɗiwa a ƙasa, sai kuma iska ta kwashe kuma ta hura ƙaiƙayin. (Rut 3:2) Bayan an rairaye don a cire ƙananan duwatsu da sauransu, sai a ajiye ko kuma a niƙa. (Luka 22:31) Amma babu ƙaiƙayin kuma.
20 Yadda ƙwayoyin hatsi suke faɗiwa a ƙasa kuma ake tattara su, yayin nan kuma iska ta kwashe ƙaiƙayin, haka adali zai kasance amma za a kawar da mugaye. Hakika, muna farin ciki cewa ba da daɗewa ba za a kawar da masu aika laifi har abada. Idan an kawar da su, za a albarkaci mutane da suke jin daɗin shari’ar Jehovah sosai. Hakika, mutane masu biyayya bayan haka za su sami kyautar Allah na rai madawwami.—Matiyu 25:34-46; Romawa 6:23.
An Albarkaci “Al’amuran Adalai”
21. Ta yaya Jehovah ‘yake lura da al’amuran adalai’?
21 Zabura ta farko ta kammala da waɗannan kalmomi: “Ubangiji yana lura da al’amuran adalai, amma al’amuran mugaye za su watse.” (Zabura 1:6) Ta yaya Allah ‘yake lura da al’amuran adalai’? To, idan muna biɗan tafarki na adalci, za mu tabbata cewa Ubanmu na samaniya yana lura da rayuwarmu ta ibada kuma yana ɗaukanmu bayinsa da ya amince da su. Za mu iya mu jibga masa dukan alhininmu da tabbacin cewa yana kula da mu, kuma ya kamata mu yi hakan.—Ezekiyel 34:11; 1 Bitrus 5:6, 7.
22, 23. Menene zai faru wa mugaye da kuma adalai?
22 “Al’amuran adalai” za su kasance har abada, mugaye da suka ƙi gyara halayensu za su halaka domin hukuncin Jehovah mai tsanani. Kuma ‘al’amuransu’ ko kuma tafarkin rayuwa zai ƙare tare da su. Za mu kasance da tabbacin a cikar kalmomin Dauda: “A ɗan ƙanƙanen lokaci mugaye za su shuɗe, za ka neme su, amma ba za a same su ba, amma masu ladabi za su zauna lafiya a ƙasar, su ji daɗin cikakkiyar salama. Adalai za su yi zamansu lafiya a ƙasar, su gāje ta har abada.”—Zabura 37:10, 11, 29.
23 Za mu yi farin ciki sosai idan muna da gatar zama cikin aljanna a duniya sa’ad da mugaye ba za su ƙara kasancewa ba! Masu tawali’u da adalai za su more salama ta gaske domin koyaushe za su riƙa jin daɗin “shari’ar Allah.” Amma kafin lokacin, dole a yi “abin da Ubangiji ya hurta.” (Zabura 2:7a) Talifi na gaba zai taimake mu mu san abin da aka hurta da abin da yake nufi a gare mu da kuma dukan iyalin ’yan Adam.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa albarka za ta tabbata ga mai ibada?
• Menene yake nufi cewa muna jin daɗin shari’ar Jehovah?
• Yaya mutum zai zama kamar itace da ke samun ruwa sosai?
• Ta yaya al’amuran adali ya bambanta da na mugu?
[Hoto a shafi na 7]
Addu’a za ta taimaka mana mu kauce wa shawarar mugaye
[Hoto a shafi na 8]
Me ya sa adali yake kama da itace?