Masu Adalci Za Su Yabi Allah Har Abada
“Mai-adalci za ya zama abin tunawa . . . Adilcinsa ya tabbata har abada.”—ZAB. 112:6, 9.
1. (a) Menene waɗanda Allah ke ɗauka a matsayin adilai za su more a nan gaba? (b) Wace tambaya ce ta taso?
NAN gaba duk mutanen da Allah ke ɗauka adalai za su more rayuwa! Za su samu damar koyon halaye masu ban-sha’awa game da Jehobah har abada. Zukatan su tana cike da yabo yayin da suka koya abubuwa masu yawa game da abubuwan da Allah ya halitta. Mafi amfani cikin waɗannan abubuwan shi ne “adalci,” wanda aka ambata a Zabura 112. Amma ta yaya Jehobah Allah mai tsarki da kuma adalci, zai ɗauki ’yan adam masu zunubi a matsayin adilai? Duk da yadda muke ƙoƙari mu yi abin da yake da kyau, wani lokaci mukan yi kuskure mai tsanani.—Rom. 3:23; Yaƙ. 3:2.
2. Waɗanne mu’ujizoji guda biyu ne Jehobah ya yi don ƙauna?
2 Da yake Jehobah mai ƙauna ne ya yi tanadin yadda za a magance matsalar. Ta yaya? Na farko, ta wajen yin mu’ujiza na mai da ran Ɗansa ƙaunatacce zuwa cikin budurwa don a haife shi kamiltacce. (Luk 1:30-35) Bayan lokacin da maƙiyin Yesu suka kashe shi, Jehobah ya sake yin wata mu’ujiza mai ban mamaki. Allah ya ta da Yesu daga matattu sai ya maishe shi halitta na ruhu.—1 Bit. 3:18.
3. Menene ya sa Allah ya yi farin cikin ba wa ɗansa lada na yin rayuwa a sama?
3 Jehobah ya saka wa Yesu da abin da ba shi da shi kafin ya zo duniya, wato, rai marar mutuwa a sama. (Ibran. 7:15-17, 28) Jehobah ya ji daɗin yin hakan domin Yesu ya kasance da cikakken aminci a lokatan gwaji. Don hakan Yesu ya sa Ubansa ya sami amsa mai kyau da zai ba wa Shaiɗan wanda ya ce ’yan adam suna bauta wa Allah don son kai ba don suna ƙaunarsa sosai ba.—Mis. 27:11.
4. (a) Sa’ad da ya koma sama, menene Yesu ya yi domin mu, kuma menene Jehobah ya yi? (b) Yaya kake ji game da abin da Jehobah da Yesu suka yi domin ka?
4 A samaniya Yesu ya yi abubuwan da suka ɗara waɗanda ya yi a duniya. Ya ‘bayyana a gaban fuskar Allah da’ ‘jininsa’ sabili da mu. Ubanmu na sama mai ƙauna ya karɓi “hadayar sulhu [na Yesu] saboda gafarta zunubanmu.” Saboda haka, tare da ‘tsarkakar lamiri,’ za mu iya “mu bauta wa Allah Rayayye.” Lallai wannan zai sa mu furta kalaman farko na Zabura 112, “Hallelujah!”—Ibran. 9:12-14, 24; 1 Yoh. 2:2.
5. (a) Menene za mu yi don mu sami matsayi mai kyau a gaban Allah? (b) Ta yaya aka tsara Zabura 111 da 112?
5 Don mu kasance da matsayi mai kyau a gaban Allah, wajibi ne mu ci gaba da ba da gaskiya ga jinin da Yesu ya zubar. Kada mu bar rana ɗaya ta wuce ba tare da yi wa Jehobah godiya ba saboda ƙaunar da ya nuna mana. (Yoh. 3:16) Ya kamata mu ci gaba da yin nazarin Kalmar Allah da kuma yin iya ƙoƙarinmu mu yi rayuwa da ta jitu da saƙonsa. Zabura 112 yana cike da shawara masu kyau don duk waɗanda suke son su sami lamiri mai kyau a gaban Allah. Wannan zaburar ta yi dadai da Zabura 111. A yaren Ibrananci na asali, dukansu sun fara da kalaman nan “Ku yabi Jehobah” ko kuma “Hallelujah!” kuma suna da ayoyi 22, kowane layi ya soma da harufa na Ibrananci guda 22.a
Dalilin Farin Ciki
6. Ta yaya “mutum” da aka kwatanta a Zabura 112 yake da albarka?
6 “Mai-albarka ne mutum wanda ya ke tsoron Ubangiji, wanda ya ke faranta ransa cikin dokokinsa ƙwarai. Zuriyassa za ta zama mai-iko a duniya: Tsarar masu-adilci za ta zama mai-albarka.” (Zab. 112:1, 2) Ka lura cewa mai zabura ya fara ambata “mutum” amma daga baya ya yi amfani da “masu-adalci,” a aya ta biyu. Wannan ya nuna cewa Zabura 112 wataƙila tana magana ne game da rukuni na mutane ɗaɗɗaya. Abin farin ciki, an hure manzo Bulus ya bayyana yadda Zabura 112:9 ta shafi Kiristoci na ƙarni na farko. (Karanta 2 Korinthiyawa 9:8, 9.) Wannan zabura ta nuna yadda mabiyan Kristi a duniya za su iya samun farin ciki!
7. Me ya sa ya kamata bayin Allah su ji tsoronsa yadda ya dace, kuma yaya ya kamata mu ji game da umarninsa?
7 Yadda aka ambata a Zabura 112:1, waɗannan Kiristoci na gaskiya suna samun farin ciki yayin da suke tafiya cikin “tsoron Ubangiji.” Wannan tsoron ɓata masa rai tana sa su ƙi halin son kai na duniyar Shaiɗan. Suna ‘faranta ransu’ ta wajen yin nazarin Kalmar Allah da kuma bin dokokinsa. Hakan ya ƙunshi umurnin yin wa’azin bishara na Mulkin a dukan duniya. Suna ƙoƙarin almajirantar da dukan al’ummai yayin da suke yi wa miyagu gargaɗi game da ranar hukunci na Allah.—Ezek. 3:17, 18; Mat. 28:19, 20.
8. (a) Ta yaya aka albarkace mutanen Allah a yau domin ƙwazonsu? (b) Waɗanne albarkatai ne waɗanda za su zauna a duniya za su samu?
8 Don bin waɗannan umurnin, bayin Allah a duniya a yau sun kai miliyan bakwai. Wanene zai yi musu cewa mutanensa sun zama masu “iko a duniya”? (Yoh. 10:16; R. Yoh. 7:9, 14) Kuma za su sami “albarka” sosai yayin da Allah ya cika nufinsa! A rukuni, waɗanda suke da begen rayuwa a duniya za a cece su daga “babban tsanani” a shigar da su “sabuwar duniya” inda “adalci yake zaune.” Da shigewar lokaci, za a yi wa waɗanda suka tsira daga Armageddon “albarka” sosai. Za su kasance a shirye su yi maraba ga miliyoyin mutane waɗanda za a ta da su daga matattu. Wannan bege ne mai ban sha’awa! Daga bisani, waɗanda suke ‘faranta ransu’ cikin dokokin Allah ƙwarai za su zama kamiltattu su kuma more “’yanci na darajar ’ya’yan Allah” har abada.—2 Bit. 3:13; Rom. 8:21.
Yin Amfani da Arziki Yadda ya Dace
9, 10. Ta yaya Kiristoci na gaskiya suka yi amfani da arzikinsu na ruhaniya, kuma yaya adalcinsu zai tabbata har abada?
9 “Wadata da arziki suna cikin gidansa: Adilcinsa kuma ya tabbata har aɓada. Haske yana fitowa cikin duhu a kan masu-gaskiya: Mai-alheri ne shi, cike da juyayi, mai-adilci kuwa.” (Zab. 112:3, 4) A lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, an san cewa waɗansu cikin bayin Allah masu arziki ne. Kuma a wani azancin, waɗanda Allah ya amince da su sun zama masu arziki, ko da ba na abin duniya ba. Ainihin gaskiya shi ne, waɗanda suka zaɓi su ƙasƙantar da kansu a gaban Allah za su iya zama talakawa kuma a raina su, kamar yadda aka yi a zamanin Yesu. (Luk 4:18; 7:22; Yoh. 7:49) Amma ko mutum yana da wadata ko bai da ita, zai yiwu ya zama mai wadata a ruhaniya.—Mat. 6:20; 1 Tim. 6:18, 19; karanta Yaƙubu 2:5.
10 Kiristoci shafaffu, tare da abokansu, ba sa yin amfani da ruhaniyarsu su kaɗai. Maimakon haka, sun ‘yi haske’ a duniyar Shaiɗan mai duhu kamar haske ga “masu-gaskiya.” Suna yin hakan ta wajen taimaka wa waɗansu su amfana daga dukiya ta ruhaniya na hikima da sanin Allah. ’Yan hamayya sun yi ƙoƙari su daina aikin wa’azin Mulki amma sun kasa. Maimakon hakan, ɗiyar wannan aiki na adalci za ta ‘tabbata har abada.’ Ta wajen kasancewa da adalci a lokacin gwaji, bayin Allah suna da tabbacin yin rayuwa na dindindin, wato “har abada.”
11, 12. A waɗanne hanyoyi ne mutanen Allah suke yin amfani da wadatar da suke da shi?
11 Mutanen Allah, wato, rukunin shafaffu da “taro mai-girma” suna karimci da dukiyarsu. Zabura 112:9 ta ce: “Ya watsa, ya babbayas ga masu-mayata.” Kiristoci na gaskiya a yau sukan taimaka wa ’yan’uwansu Kirista da maƙwabtansu waɗanda suke da bukatu. Sukan yi amfani da wadatarsu wajen ba da agaji ga mutanen da bala’i ya shafe su. Kamar yadda Yesu ya nuna zai zama hakan, wannan ma abin farin ciki ne.—Karanta A. M. 20:35; 2 Korinthiyawa 9:7.
12 Ƙari ga haka, ka yi tunanin kuɗin da ake kashewa wajen buga wannan mujallar a harsuna 172, kuma yawancin harsunan nan talakawa ne ke yin su. Ka yi la’akari, kuma cewa ana buga wannan mujallar a yaren kurame dabam dabam, da kuma na makafi.
Mai Alheri da Marar Son Zuciya
13. Wanene ya kafa misali mafi kyau na nuna alheri, kuma yaya za mu iya yin koyi da misalinsu?
13 “Salama tana ga wannan mutum wanda ya ke aikin alheri, yana bada rance.” (Zab. 112:5) Wataƙila ka lura cewa mutanen da suke taimaka wa waɗansu ba masu alheri ba ne. Wasu sukan bayar don a san cewa suna da wadata ko don ya zama dole. Ba abin farin ciki ba ne a karɓi taimako daga wanda zai sa ka ji kamar kana damunsa. Maimakon hakan, abin farin ciki ne ƙwarai mu samu taimako daga mai alfarma. Jehobah ne fitacce wajen nuna alheri, da mai bayarwa da daɗin rai. (1 Tim. 1:11; Yaƙ. 1:5, 17) Yesu Kristi ya yi koyi da misalin Ubansa na nuna alheri sarai. (Mar. 1:40-42) Da haka, idan muna son Allah ya ɗauke mu masu adalci, sai mu riƙa bayarwa da daɗin rai da alfarma, musamman sa’ad da muke taimakon mutane su san Allah.
14. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya ‘tsaya a wurin shari’a’?
14 “Da’awatasa za ta tsaya a wurin shari’a.” (Zab. 112:5) Kamar yadda aka annabta, rukunin wakili mai aminci yana kula da mallakar Ubangijinsa cikin jituwa da shari’ar Jehobah. (Karanta Luka 12:42-44.) Mun san hakan ta ja-gorar da aka ba dattawa a cikin Nassi, waɗanda wani lokaci sukan yi shari’a da waɗanda suke yin zunubi mai tsanani a cikin ikilisiya. Ana ganin hanya mai kyau na yin abubuwa ta wajen bin shawarwarin Littafi Mai Tsarki da bawan nan mai aminci yake bayarwa game da yadda za a gudanar da ikilisiyoyi, masaukin masu wa’azi a ƙasashen waje, da Bethel. Ba dattawa kaɗai ba ne ya kamata su riƙa nuna halin yin gaskiya amma ya kamata duk Kiristoci su riƙa yin hakan da juna da kuma marasa bi, har da sha’anin kasuwanci.—Karanta Mikah 6:8, 11.
Masu Adalci Za Su Sami Albarka
15, 16. (a) Menene sakamakon mummunan labarai ga masu adalci? (b) Menene bayin Allah suka ƙudurta za su ci gaba da yi?
15 “Gama ba za a jijjige shi da daɗai; mai-adalci za ya zama abin tunawa har abada. Ba za ya ji tsoron mugun labari ba: zuciyatasa a kafe ta ke, yana dogara ga Ubangiji. Zuciyatasa ta kafu, ba za ya ji tsoro ba, Har shi ga muradinsa ya biya a bisa kan magabtansa.” (Zab. 112:6-8) Babu lokaci a tarihi da aka taɓa samun mugun labarai, kamar su yaƙe-yaƙe, ta’addanci, sababbin cututtuka da tsofaffi da ke sake dawowa, aika laifi, talauci, da gurɓata duniya. Waɗanda Allah ke ɗaukan masu adalci ba za su iya guje wa sakamakon wannan mugun labarai ba, amma hakan ba ya sa su tsoro. Maimakon hakan, zukatansu “a kafe ta ke” ko kuma ta “kafu” yayin da suke duba gaba da gaba gaɗi, da sanin cewa duniyar Allah ta adalci ta yi kusa. Idan bala’i ya faɗa musu, sukan iya jurewa domin sun dogara ga Jehobah. Bai taɓa barin a “jijjige” bayinsa masu adalci ba, yana taimaka musu kuma yana ba su ƙarfin jurewa.—Filib. 4:13.
16 Bayin Allah sun jure ƙiyayya da ƙarya da ’yan hamayya suke yaɗawa, amma hakan ba zai taɓa sa Kiristoci na gaskiya su daina yin wa’azi ba. Maimakon hakan, bayin Allah sun ci gaba da aminci ba tare da jijjiga ba a aikin da Jehobah ya ba su; wato yin wa’azin bishara ta Mulki da almajirantar da duk waɗanda suka saurara. Babu shakka, masu adalci za su fuskanci hamayya fiye da dā yayin da ƙarshe yake kusatowa. Wannan ƙiyayya za ta zo ƙarshenta sa’ad da Shaiɗan Iblis zai yi faɗa da mutanen Allah a matsayinsa na Gog na Magog. Sa’an nan, za mu dubi ‘magabtanmu’ yayin da za su sha hallaka. Zai zama abin farin ciki mu ga yadda za a tsarkake sunan Jehobah!—Ezek. 38:18, 22, 23.
“Ɗaukaka da Girma”
17. Ta yaya za a “ɗaukaka” mai adalci “da girma”?
17 Zai zama abin farin ciki a yaba wa Jehobah tare, ba tare da hamayyar Iblis da duniyarsa ba! Wannan farin cikin zai zama lada ta har abada na waɗanda suka kasance da matsayi mai kyau a gaban Allah. Ba za su ji kunya ba kuma ba za a halaka su ba, domin Jehobah ya yi alkawarin cewa “ƙahon” masu adalci za a “ɗaukaka da girma.” (Zab. 112:9) Bayin Jehobah masu adalci za su yi murna sosai sa’ad da suka ga faɗuwar dukan magabtan ikon mallakar Jehobah.
18. Yaya kalaman Zabura 112 za ta samu cikawa?
18 “Mugun za ya gani, ya ji haushi; Za ya ciji baki, shi narke: Gurin mugu za ya lalace.” (Zab. 112:10) Dukan waɗanda suka ci gaba da yin hamayya da mutanen Allah za su “narke” a kishinsu da ƙiyayya. Son ganin ƙarshen aikinmu zai hallaka tare da su a lokacin “ƙunci mai-girma” da ke zuwa nan gaba.—Mat. 24:21.
19. Wane tabbaci Za mu kasance da shi?
19 Za ka kasance cikin waɗanda suka tsira a wannan lokacin cin nasara mai girma? Ko kuwa idan ka rasu saboda ciwo ko tsufa kafin ƙarshen wannan zamani na Shaiɗan, za ka kasance cikin masu-adalci da za a ta da daga matattu? (A. M. 24:15) Amsar ka za ta zama e idan ka ci gaba da ba da gaskiya ga hadayar fansa ta Yesu da kuma yin koyi da Jehobah, kamar waɗanda “mutum” mai adalci da aka kwatanta a Zabura 112 ke wakilta. (Karanta Afisawa 5:1, 2.) Jehobah zai tabbata cewa za su zama “abin tunawa,” kuma ba za a manta da ayyukansu na adalci ba. Jehobah zai tuna da su ya kuma ƙaunace su har abada abadin.—Zab. 112:3, 6, 9.
[Hasiya]
a Za mu ga kamanin waɗannan zabura guda biyu daga tsarinsu da kuma abin da ke ciki. Marubucin Zabura 112 wanda ‘mutumi’ ne mai tsoron Allah ya yi koyi da yadda aka ɗaukaka halayen Allah a Zabura 111, za mu ga hakan ta wajen gwada 111:3, 4 da Zabura 112:3, 4.
Tambayoyi Don Bimbini
• Don waɗanne dalilai ne za mu furta “Hallelujah”?
• Wane aukuwa ne na zamani ya sa Kiristoci na gaskiya farin ciki?
• Wane irin mai bayarwa ne Jehobah yake ƙauna?
[Hotunan da ke shafi na 25]
Don mu kasance da matsayi mai kyau a gaban Allah, wajibi ne mu ba da gaskiya ga hadayar fansa na Yesu
[Hotunan da ke shafi na 26]
Gudummawar da aka ba da da son rai tana taimaka wa don aikin agaji da kuma buga mujallu