Jehobah Ya Cancanci Mu Haɗa Kai Mu Yaba Masa
“Hallelujah.”—ZAB. 111:1.
1, 2. Menene ma’anar “Hallelujah,” kuma yaya aka yi amfani da shi a Nassosin Kirista na Helenanci?
“HALLELUJAH!” Ana yawan amfani da wannan kalmar a cocin Kiristendom. Mutane suna amfani da wannan kalmar don su nanata abin da suke faɗi. Mutane kaɗan ne daga cikinsu suka san ma’anar kalmar, kuma salon rayuwar mutane da yawa da suke amfani da kalmar ba ta girmama Allah. (Tit. 1:16) Wani ƙamus na Littafi Mai Tsarki ya bayyana ma’anar “Hallelujah,” ya ce “kalma ce da waɗanda suka rubuta zabura suke amfani da ita don su gayyaci dukan mutane su yabi Jehobah tare da su.” Hakika, wasu ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa “Hallelujah” yana nufin a “‘Yabi Jah,’ [wato] Jehobah.”
2 Littafi Mai Tsarki na New World Translation ya fassara kalmar nan da ke cikin Zabura 111:1 kamar haka, “Ku yabi Jah, ku mutane!” Kalmar Helenanci mai kama da wannan kalmar ta fito sau huɗu a Ru’ya ta Yohanna 19:1-6 a lokacin da za a yi murnar ƙarshen addinin ƙarya. Sa’ad da hakan ya faru, masu bauta ta gaskiya za su sami dalili na musamman na yin amfani da kalmar nan “Hallelujah” a hanyar da ta dace.
Ayyukansa Masu Girma
3. Menene ainihin dalilin da ya sa muke taruwa a kai a kai?
3 Marubucin Zabura sura 111 ya ba da dalilai da yawa da ya sa Jehobah ya cancanci dukanmu mu yaba masa. Aya ta 1 ta ce: “Zan yi godiya ga Ubangiji da dukan zuciyata, a cikin fadar masu-adilci, da cikin taron jama’a kuma.” Shaidun Jehobah a yau sun yarda da hakan. Ainihin dalilin da ya sa muke taruwa a kai a kai, a ikilisiyoyi da kuma manyan taro shi ne don mu yabi Jehobah.
4. Ta yaya mutane za su iya bincika ayyukan Jehobah?
4 “Ayukan Ubangiji da girma su ke, biɗaɗu ne ga dukan waɗanda su ke jin daɗinsu.” (Zab. 111:2) Ka lura da kalmar nan “biɗa.” In ji wani bincike, ayar tana nuni ga mutanen da suka mai da ayyukan Allah su zama “abin nazari da bimbini sosai.” Abubuwan da Jehobah ya halitta suna da manufa sosai. Ya kafa rana, duniya, da kuma wata, dukansu a inda ya kamata, saboda duniyarmu ta sami ɗumi, haske, dare da rana da kuma yanayi da malalawar teku.
5. Menene yadda ’yan adam suka ƙara fahimtar sararin samaniya ya nuna?
5 Masana kimiyya sun gano inda duniya take a tsarin rana da kuma girman wata. Yadda aka tsara waɗannan halittu na sama da yadda suke aiki tare sun sa yanayin duniya ya riƙa canjawa a kai a kai. Kuma, mun koyi game da yadda aka ƙera duniya da kyau. Da haka, a wani talifi mai jigo “Sararin Samaniya da ‘Aka Tsara da Kyau,’” wani masanin kimiyya ya ce: “Ba shi da wuya a fahimci dalilin da ya sa masana kimiyya da yawa suka canja ra’ayinsu a shekaru 30 da saka wuce, suka yarda cewa ana bukatar bangaskiya sosai don a gaskata cewa babu wanda ya ƙera sararin samaniya. Yayin da muke ƙara fahimtar yadda aka ƙera duniya da kyau za mu gaskata cewa akwai maƙeri mai basira.”
6. Yaya kake ji game da yadda Allah ya halicci mutum?
6 Wani aiki mai girma na halitta shi ne yadda Allah ya halicce mu. (Zab. 139:14) Sa’ad da ya halicci mutane, ya ba su zuciya, jiki da dukan gaɓoɓi da za su sa jiki ya yi aiki yadda ya kamata, da kuma ƙarfin yin aiki. Alal misali, abin mamaki ne baiwar da Allah ya ba mu na iya magana, saurarawa da kuma rubutu da karatu. Mutane da yawa suna da waɗannan baiwar. Jikinka kuma yana iya kasancewa a tsaye. Yadda aka ƙera jikinka, yadda yake aiki da kuma yadda yake amfani da abinci don ya ba ka kuzari, yana motsa mutum ya girmama Allah. Fiye da haka, yadda aka haɗa jijiyoyin da suke sa ƙwaƙwalwa da su ji da gani da taɓawa da ɗanɗanawa da sunsunawa su yi aiki sosai ya fi dukan abubuwan da ’yan kimiyya suka cim ma. Hakika, abin da ’yan adam suka cim ma ya yiwu ne saboda irin ƙwaƙwalwar da abubuwan da Allah ya sa a jikinsu. Injiniyar da ya fi ƙwarewa ba zai iya ƙera wani abu da ya yi kyau kuma masu amfani kamar yatsunmu goma ba. Ka tambayi kanka, ‘Za a iya yin zane-zane da gine-gine ba tare da amfani da yatsu da Allah ya ba mu ba?’
Ayyukan Jehobah Masu Girma da Kuma Halayensa
7. Me ya sa ya kamata mu ɗauki Littafi Mai Tsarki a matsayin ɗaya daga cikin ayyuka masu girma da Allah ya yi?
7 Ayyukan Jehobah masu girma sun ƙunshi wasu abubuwa masu al’ajabi da ya yi wa ’yan adam, kamar yadda aka kwatanta a cikin Littafi Mai Tsarki. Littattafan da ke cikin Littafi Mai Tsarki sun jitu da juna a hanya mai ban mamaki. Ba kamar sauran littattafai ba, wannan littafin “hurarre daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyarwa.” (2 Tim. 3:16) Alal misali, littafi na farko a cikin Littafi Mai Tsarki, wato, Farawa, ya bayyana yadda Allah ya kawar da mugunta a duniya a zamanin Nuhu. Littafi na biyu, wato, Fitowa, ya nuna yadda Jehobah ya ɗaukaka kansa sa’ad da ya ceci Isra’ila daga bauta a ƙasar Masar. Wataƙila mai Zabura yana tuna waɗannan abubuwan da suka faru shi ya sa ya ce: “Aikinsa [Jehobah] girma ne da [ɗaukaka]: adilcinsa kuma matabbaci ne har abada. Ya sa a yi tunani da al’ajibansa: Ubangiji mai-alheri ne, cike ya ke da juyayi.” (Zab. 111:3, 4) Ka yarda cewa ayyukan Jehobah a duka tarihi, har da abubuwan da ya yi a zamaninka, suna nuna ‘girmansa da ɗaukakarsa’?
8, 9. (a) A waɗanne hanyoyi ne ayyukan Allah suka bambanta da na ’yan adam? (b) Waɗanne halayen Allah ne kake so?
8 Ka lura cewa mai Zabura kuma ya nanata fitattun halayen Jehobah kamar adalci, alheri, da kuma juyayi. Ka san cewa yana da wuya mutane masu zunubi su yi abubuwa bisa adalci. Sau da yawa sukan yi abubuwa don haɗama, kishi da kuma girman kai. Hakan ya bayyana a mugayen makaman yaƙi da ’yan adam suke ƙerawa don yin yaƙe-yaƙen da suke jawowa da kuma samun kuɗi. Waɗannan abubuwan suna jawo bala’i ga waɗanda ba su san hawa da sauka ba. Kuma, ’yan adam sun cim ma ayyuka masu yawa ne ta wajen wahalar da talakawa. Misalin da yawanci za su iya tunawa shi ne yin amfani da bayi wajen gina dala. Waɗannan wuraren ne ake binne Fir’auna. Bugu da ƙari, yawancin ayyukan da mutane suke yi a yau na zaluntar mutane ne kuma suna “hallaka duniya.”—Karanta Ru’ya ta Yohanna 11:18.
9 Wannan ya bambanta da ayyukan Jehobah, waɗanda yake yi bisa adalci! Ayyukansa sun ƙunshi tanadin ceto da ya yi da tagomashi don ’yan adam masu zunubi. Ta wajen tanadin fansa, Allah yana “bayana adalcinsa.” (Rom. 3:25, 26) Hakika, “adalcinsa kuma matabbaci ne har abada”! Allah ya nuna alherinsa ta yadda yake bi da mutane masu zunubi da haƙuri. A wani lokaci, yana roƙonsu su guji muguwar hanyar da suke bi kuma su yi abin da ya dace.—Karanta Ezekiel 18:25.
Yana Cika Alkawuransa
10. Wane misali na amince ne Jehobah ya kafa game da alkawarin da ya yi wa Ibrahim?
10 “Ya bada abinci ga masu-tsoronsa: Har abada za ya riƙa tuna da alkawarinsa.” (Zab. 111:5) Wataƙila mai zabura yana nufin alkawarin da aka yi da Ibrahim ne. Jehobah ya yi alkawari cewa zai albarkaci zuriyar Ibrahim kuma ya ce za su gaji ƙofar magabtansu. (Far. 22:17, 18; Zab. 105:8, 9) A cikawa ta farko ta waɗannan alkawuran, zuriyar Ibrahim ta zama al’umma ta Isra’ila. Wannan al’umma ta daɗe tana bauta a ƙasar Masar, amma “Allah ya tuna da alkawarinsa da Ibrahim” kuma ya cece su. (Fit. 2:24) Yadda Jehobah ya bi da su ya nuna musu cewa shi mutum ne mai alheri. Ya yi musu tanadin abinci na zahiri don lafiyar jikinsu da kuma abinci na ruhaniya don su bi mizanansa. (K. Sha 6:1-3; 8:4; Neh. 9:21) A ƙarnuka da suka biyo baya, al’ummar ba ta yi biyayya ga Allah ba, duk da cewa ya aiki annabawa su aririce su su koma gare shi. Fiye da shekaru 1,500 bayan da ya ceci Isra’ilawa daga ƙasar Masar, Allah ya aiki Ɗansa makaɗaici zuwa duniya. Yawancin Yahudawa sun ƙi Yesu kuma suka sa aka kashe shi. Sai Jehobah ya kafa sabuwar al’umma ta ruhaniya, wato, “Isra’ila na Allah.” Tare da Kristi, al’ummar ta zama zuriyar Ibrahim ta ruhaniya, wadda Jehobah ya annabta cewa zai yi amfani da ita ya albarkaci ’yan adam.—Gal. 3:16, 29; 6:16.
11. Ta yaya Jehobah ya ci gaba da “tuna . . . alkawarinsa” ga Ibrahim?
11 Jehobah ya ci gaba da “tuna . . . alkawarinsa” da kuma albarkar da ya yi alkawarinta. A yau, yana yin tanadin abinci na ruhaniya da yawa a harsuna fiye da 400. Ya kuma ci gaba da amsa addu’o’i game da bukatunmu na zahiri, cikin jituwa da waɗannan kalmomin: “Ka ba mu yau da gobe abincin yini.”—Luk 11:3; Zab. 72:16, 17; Isha. 25:6-8.
Ikon Jehobah Mai Ban Mamaki
12. Ta wace hanya ce aka ba Isra’ila ta dā “gadon al’ummai”?
12 “Ya gwada ma jama’arsa ikon ayukansa, da ya ba su gadon al’ummai.” (Zab. 111:6) Wani fitaccen abu a tarihin Isra’ila da ke zuciyar mai zabura shi ne yadda Allah ya cece su daga ƙasar Masar ta hanyar mu’ujiza. Sa’ad da Jehobah ya ƙyale Isra’ilawa su shiga cikin Ƙasar Alkawari, sun ci nasara bisa al’ummai daga gabas da yamma da ke kusa da Kogin Urdun. (Karanta Nehemiah 9:22-25.) Hakika, Jehobah ya ba Isra’ila “gadon al’ummai.” Babu shakka, Allah ya nuna ikonsa!
13, 14. (a) Wane iko ne da Allah ya nuna wa Babila wataƙila mai zabura yake tunawa da shi? (b) Waɗanne ayyukan ceto masu ban al’ajabi ne Jehobah ya cim ma?
13 Mun san cewa, duk da abin da Jehobah ya yi musu, Isra’ilawa ba su daraja shi da kakanninsu Ibrahim, Ishaƙu, da kuma Yakubu ba. Sun ci gaba da yin rashin biyayya har Allah ya sa Babila ta cire su daga ƙasarsu ta kai su bauta. (2 Laba. 36:15-17; Neh. 9:28-30) Idan kamar yadda masana Littafi Mai Tsarki suka ce, wanda ya rubuta Zabura na 111 ya rayu ne bayan da Isra’ila ta dawo daga bauta a Babila, yana da ƙarin dalilai na yaba wa Jehobah don amincinsa da ikonsa. Allah ya nuna amincinsa da ikonsa sa’ad da ya ceci Yahudawa daga Babila, wato, ƙasar da sananna ce wajen riƙe bayinta.—Isha. 14:4, 17.
14 Bayan ƙarnuka biyar, Jehobah ya yi amfani da ikonsa a hanya mai girma ta wajen ceto mutanen da suka tuba daga zunubi da mutuwa. (Rom. 5:12) Sakamako na ɗaya shi ne mutane 144,000 sun sami zarafin zama mabiyan Kristi da aka shafa da ruhu. A shekara ta 1919, Jehobah ya yi amfani da ikonsa ya ceci mutane kaɗan daga cikin waɗannan shafaffu da suka rage daga bauta ta addinin ƙarya. Abubuwan da suka cim ma a wannan lokaci na ƙarshe ya yiwu ne kawai saboda ikon Allah. Idan suka kasance da aminci har mutuwa, za su yi sarauta da Yesu Kristi daga sama bisa duniya don amfanin mutanen da suka tuba. (R. Yoh. 2:26, 27; 5:9, 10) Za su gāji duniya a hanya mai girma fiye da Isra’ila ta dā.—Mat. 5:5.
Tabbatattun Ƙa’idodi na Har Abada
15, 16. (a) Menene ayyukan Allah suka ƙunsa? (b) Waɗanne dokoki ne Allah ya ba Isra’ila ta dā?
15 “Ayukan hannuwansa gaskiya ne da shari’a; dukan dokokinsa masu-aminci ne. Sun kafu har abada abadin, an gudana su cikin gaskiya da adilci.” (Zab. 111:7, 8) “Ayukan hannuwan [Jehobah]” sun ƙunshi alluna biyu na dutse da ke ɗauke da dokoki guda goma masu muhimmanci ga Isra’ila. (Fit. 31:18) Waɗannan dokokin, tare da sauran farillai da suke cikin Dokar Musa, suna bisa tabbatattun ƙa’idodin na dindindin.
16 Alal misali, wata ƙa’ida ko doka a waɗannan duwatsun ta ce: “Ni Ubangiji Allahnka Allah mai-kishi ne.” Ta kuma ce Jehobah yana ‘nuna jinƙai ga dubbai, daga masoyansa masu-kiyaye dokokinsa.’ Alluna na duwatsun suna ɗauke da ƙa’idodi da za a iya amfani da su a koyaushe kamar “ka bada girma ga ubanka da uwarka” kuma kada “ka yi sata,” da kuma doka da ta ce a guji yin kishin abin wasu.—Fit. 20:5, 6, 12, 15, 17.
Mai Cetonmu, da ke da Tsarki da Kwarjini
17. Waɗanne dalilai ne ya kamata su sa Isra’ilawa su tsarkake sunan Allah?
17 “Ya aiko ma jama’arsa da pansa; ya tsayadda alkawarinsa har abada: Sunansa da tsarki ya ke, mai-kwarjini ne kuma.” (Zab. 111:9) A wannan ayar kuma wataƙila mai zabura yana nufin amincin Jehobah ga alkawarin da ya yi wa Ibrahim. Saboda haka, Jehobah bai yi watsi da mutanensa ba da farko a ƙasar Masar ta dā da kuma sa’ad da suka je bauta a Babila. A waɗannan lokatai, Allah ya ceci mutanensa. Waɗannan abubuwan guda biyu kawai ban da sauran, sun isa sa Isra’ilawa su tsarkake sunan Allah.—Karanta Fitowa 20:7; Romawa 2:23, 24.
18. Me ya sa kake ganin cewa zama mai ɗauke da sunan Allah gata ne?
18 Haka yake ga Kiristoci a yau, waɗanda aka ceto daga zunubi da mutuwa. Ya kamata mu yi ƙoƙari mu yi rayuwar da ta jitu da roƙo na farko a cikin addu’ar misali: “A tsarkake sunanka.” (Mat. 6:9) Yin bimbini a kan wannan suna mai girma zai sa mu kasance da tsoron Allah. Marubucin Zabura sura 111 yana da ra’ayin da ya yi daidai na tsoron Allah, ya ce: “Tsoron Ubangiji mafarin hikima ne: dukan masu-aikata shi [bin dokokinsa] suna da kyakyawan fahimi.”—Zab. 111:10.
19. Menene za mu tattauna a talifi na gaba?
19 Tsoron Allah zai taimake mu mu ƙi abin da bai da kyau. Zai kuma taimake mu mu yi koyi da halayen Allah da aka ambata a Zabura sura 112, waɗanda za mu tattauna a talifi na gaba. Wannan zaburar ta nuna abin da zai sa mu kasance a cikin miliyoyin mutanen da za su mori yi wa Allah yabo na har abada. Ya cancanci a yabe shi. “Yabonsa matabbace ne har abada.”—Zab. 111:10.
Tambayoyi Don Bimbini
• Me ya sa Jehobah ya cancanci mu yaba masa mu duka?
• Waɗanne halayen Jehobah ne aka bayyana a ayyukansa?
• Yaya kake ɗaukan gatan zama mai ɗauke da sunan Allah?
[Hotunan da ke shafi na 20]
Ainihin dalilin da ya sa muke zuwa taro a kai a kai shi ne don mu yabi Jehobah
[Hotunan da ke shafi na 23]
Dukan dokokin Jehobah tabbatattun ƙa’idodi ne na dindindin