Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 1/1 pp. 11-16
  • Ka Kasance A Shirye Domin Ranar Jehovah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kasance A Shirye Domin Ranar Jehovah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Guje wa Halin Ba Ruwana
  • Ka Tsayayya wa Gyangyaɗi na Ruhaniya
  • Ka Guje wa Yayin Rayuwa da ke Haɗari ga Ruhaniya
  • Ka Yi Iyakacin Ƙoƙari Ka Kasance a Shirye
  • “Ku Zauna A Faɗake”—Lokacin Hukunci Ya Yi!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • “Ku Yi Tsaro”!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Kasancewarmu A Faɗake Ya Fi Gaggawa Yanzu Da Dā
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ka Kasance Da Shiri!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 1/1 pp. 11-16

Ka Kasance A Shirye Domin Ranar Jehovah

“Ku fa ku zama da shiri: gama cikin sa’an da ba ku sa tsammani ba Ɗan mutum yana zuwa.”—MATTA 24:44.

1. Me ya sa ya kamata mu damu game da ranar Jehovah?

ZA TA zama ranar yaƙi da hasala, na baƙin ciki da damuwa, na duhu da halaka. “Babban rana ta ban razana” ta Jehovah lallai za ta zo a kan mugun zamanin nan, kamar yadda Rigyawan ta shanye muguwar duniya ta zamanin Nuhu. Hakika za ta zo. Amma, “iyakar wanda ya kira bisa sunan Ubangiji za ya tsira.” (Joel 2:30-32; Amos 5:18-20) Allah zai halaka magabtansa kuma ya ceci mutanensa. Cikin gaggawa, annabi Zafaniya ya ce: “Babbar ranar Ubangiji ta kusa, kurkusa ce, tana kuwa gaggabta ƙwarai.” (Zephaniah 1:14) To, har sai yaushe za a zartar da wannan hukunci na Allah?

2, 3. Me ya sa ya kamata mu shirya domin ranar Jehovah?

2 “Amma zancen ranan nan da sa’an nan ba wanda ya sani ba, ko mala’iku na sama, ko Ɗa, sai Uba kaɗai,” in ji Yesu. (Matta 24:36) Tun da yake ba mu san ainihin lokacin ba, ya kamata mu tuna da kalmomin jigonmu na shekara ta 2004: “Ku yi tsaro fa . . . Ku zama da shiri.”—Matta 24:42, 44.

3 Da yake nuna yadda za a ceci waɗanda suke a shirye kuma a ƙyale wasu, Yesu ya ce: “Mutum biyu za su kasance a gona; za a ɗauki ɗaya, za a bar ɗaya: mata biyu za su kasance suna niƙa wurin maniƙa; za a ɗauki ɗaya, za a bar ɗaya.” (Matta 24:40, 41) A lokacin, wane yanayi za mu kasance ciki? Za mu kasance ne a shirye, ko ranar za ta same mu babu shiri ne? Ya dangana sosai ga abin da muke yi ne yanzu. Domin mu kasance a shirye don ranar Jehovah, muna bukatar mu guje wa wasu halaye da ke ko’ina a yau, yana nufin mu ƙi yarda mu fāɗa cikin wani irin yanayi na ruhaniya, kuma yana nufin mu ƙi wasu yayin rayuwa.

Ka Guje wa Halin Ba Ruwana

4. Wane irin hali mutanen zamanin Nuhu suke da shi?

4 Ka yi la’akari da zamanin Nuhu. “Ta wurin bangaskiya Nuhu, da aka faɗakarda shi a kan al’amuran da ba a gani ba tukuna, domin tsoro mai-ibada, sai ya shirya jirgi domin ceton gidansa,” in ji Littafi Mai Tsarki. (Ibraniyawa 11:7) Jirgin na zahiri ne kuma babba. Ban da haka ma, Nuhu “mai-shelan adalci” ne. (2 Bitrus 2:5) Ginin da Nuhu yake yi da kuma wa’azin da yake yi ba su motsa mutanen zamaninsa ba. Me ya sa? Domin suna “ci suna sha, suna aure, suna aurarwa.” Waɗanda Nuhu ya yi musu wa’azi sun shaƙu cikin harkokinsu da annashuwa “ba su sani ba har rigyawa ta zo ta kwashe su duka.”—Matta 24:38, 39.

5. Menene ra’ayin mazaunan Saduma a zamanin Lutu?

5 Haka yake ma a zamanin Lutu. Nassosi sun gaya mana: “Suna ci, suna sha, suna saye, suna sayarwa, suna dashe, suna gini; amma randa Lutu ya fita Saduma aka zuba wuta da ƙibiritu daga sama, aka halaka su duka.” (Luka 17:28, 29) Bayan da mala’iku suka gargaɗi Lutu game da halakar da ke zuwa, ya gaya wa surukansa abin da zai faru. Amma, a ganinsu “ya zama kamar mai-ba’a.”—Farawa 19:14.

6. Wane hali ne dole mu guje wa?

6 Kamar yadda yake a zamanin Nuhu da Lutu, “hakanan kuma bayyanuwar Ɗan mutum za ta zama” in ji Yesu. (Matta 24:39; Luka 17:30) Hakika, halin mutane da yawa a yau na ba ruwana ne. Dole mu lura kada irin halin nan ya shafe mu. Babu laifi a more abinci mai daɗi da abin sha daidai wa daida. Haka nan kuma, aure tsarin Allah ne. Amma, idan al’amuran nan suka zama mafi muhimmanci a rayuwarmu kuma aka tura na ruhaniya gefe guda, a shirye muke kuwa domin rana mai ban razana ta Jehovah?

7. Wace muhimmiyar tambaya ya kamata mu yi kafin mu fara wani abu, kuma me ya sa?

7 “An gajertadda kwanaki,” in ji manzo Bulus. “Domin nan gaba waɗanda su ke da mata su yi kamar ba su da su.” (1 Korinthiyawa 7:29-31) Lokaci kaɗan ne ya rage mana mu gama aikin wa’azin Mulki da Allah ya ba mu. (Matta 24:14) Bulus ya gargaɗi har waɗanda suka yi aure cewa ba dukan lokacinsu za su ba wa juna ba da ba za su sa batun Mulki farko a rayuwarsu ba. A bayyane yake, irin halin da Bulus a nan yake yaba wa ba na ba ruwana ba ne. Yesu ya ce: “Amma ku fara biɗan mulkinsa, da adalcin [Allah].” (Matta 6:33) Sa’ad da kake tsai da wata shawara ko kuma kafin ka fara wani abu, muhimmin abu ne ka yi tambayar nan, ‘Yaya wannan zai shafi biɗan Mulki farko a rayuwata?’

8. Idan harkokin yau da kullum sun sha kanmu, me za mu yi?

8 Idan muka ga cewa mun riga mun shaƙu cikin harkokin yau da kullum har da sun soma shaƙe al’amura na ruhaniya fa? Da akwai bambanci kuwa tsakanin yayin rayuwarmu da na maƙwabtanmu da ba su da sanin Nassosi kuma da su ba masu shelar Mulki ba? Idan haka ne, to, mu sa shi cikin addu’a. Jehovah zai iya taimakonmu mu kasance da halin da ya dace. (Romawa 15:5; Filibbiyawa 3:15) Zai iya taimake mu mu sa batun Mulki farko, mu yi abin da ke daidai, kuma mu cika hakkinmu gare shi.—Romawa 12:2; 2 Korinthiyawa 13:7.

Ka Tsayayya wa Gyangyaɗi na Ruhaniya

9. Bisa Ru’ya ta Yohanna 16:14-16, me ya sa yake da muhimmanci mu tsayayya wa gyangyaɗi na ruhaniya?

9 Annabcin da ya yi zancen zuwan “yaƙi na babban rana na Allah mai-iko Duka” a Armageddon ya ce wasu ba za su kasance a faɗake ba. “Duba, kamar ɓarawo ni ke zuwa,” in ji Ubangiji Yesu Kristi. “Mai-albarka ne shi wanda ya ke tsaro, yana lura da tufafinsa, kada ya yi tafiya a tsiraice, a ga kunyarsa.” (Ru’ya ta Yohanna 16:14-16) Tufafi da aka ambata a nan yana nufin abin da yake nuna mu Kiristoci ne Shaidun Jehovah. Wannan ya shafi aikinmu na masu shelar Mulki da kuma halinmu na Kirista. Idan muka ja baya domin rashin ƙwazo, za a tsiraice mu daga zama Kirista. Wannan abin kunya ne kuma na haɗari. Dole ne mu tsayayya wa yanayi na gyangyaɗi na ruhaniya ko kuma na rashin ƙwazo. Ta yaya za mu guje wa irin wannan nufin?

10. Me ya sa karatun Littafi Mai Tsarki ke taimakonmu mu kasance a faɗake a ruhaniya?

10 Sau da sau Littafi Mai Tsarki ya nanata bukatar mu kasance a faɗake kuma mu mai da hankali. Alal misali, labarin Lingila ya tunasar da mu: “Ku yi tsaro fa” (Matta 24:42; 25:13; Markus 13:35, 37); “ku zama da shiri” (Matta 24:44); “ku yi lura, ku yi tsaro” (Markus 13:33); “ku yi shiri” (Luka 12:40). Bayan ya ambata cewa ranar Jehovah za ta zo ba zato a kan wannan duniyar, manzo Bulus ya aririce ’yan’uwa masu bi: “Kada fa mu yi barci, kamar sauran mutane, amma mu yi zamanmu ba barci ba maye.” (1 Tassalunikawa 5:6) A cikin littafi na ƙarshe cikin Littafi Mai Tsarki, Kristi Yesu da aka ɗaukaka ya nanata yadda zai zo farat ɗaya, yana cewa: “Ina zuwa da sauri.” (Ru’ya ta Yohanna 3:11; 22:7, 12, 20) Annabawa Ibraniyawa da yawa ma sun kwatanta kuma yi gargaɗi game da babban rana ta hukuncin Jehovah. (Ishaya 2:12, 17; Irmiya 30:7; Joel 2:11; Zephaniah 3:8) Karatun Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki kowacce rana, da kuma yin bimbini a kan abin da muka karanta taimako ne domin mu kasance a faɗake a ruhaniya.

11. Me ya sa nazarin Littafi Mai Tsarki da kanmu yake da muhimmanci domin kasancewa a faɗake a ruhaniya?

11 Hakika, nazarin Nassosi da kanmu abin motsa mu ne ƙwarai mu kasance a faɗake muna amfani da littattafai masu tushe cikin Littafi Mai Tsarki da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” yake tanadinsu! (Matta 24:45-47) Amma domin mu sami amfanin nazari da kanmu, dole ne mu ci gaba da yinsa a kai a kai. (Ibraniyawa 5:14–6:3) Dole ne mu ci abinci na ruhaniya a kai a kai. Samun lokaci domin haka a kwanakin nan ƙalubale ne. (Afisawa 5:15, 16) Amma, karanta Littafi Mai Tsarki tare da littattafai na Nassosi sai sa’ad da muka sami lokaci ne kawai bai isa ba. Nazari da kanmu a kai a kai yana da muhimmanci domin mu kasance “sahihai cikin imani” kuma mu kasance a faɗake.—Titus 1:13.

12. Ta yaya taron Kirista, manyan taro da kuma na gunduma suke taimakonmu mu yaƙi gyangyaɗi na ruhaniya?

12 Taron Kirista, manyan taro, da kuma na gunduma, suna taimakonmu mu yaƙi gyangyaɗi na ruhaniya. Ta yaya? Ta wurin koyarwa da ake yi mana. A wurin waɗannan taron, ba ana tunasar da mu game da cewa ranar Jehovah ta kusa ba? Taron Kirista na mako mako ma zarafi ne ‘mu tsokani juna zuwa ƙauna da nagargarun ayyuka.’ Irin tsokanar nan ana bukatarta domin kasance a faɗake a ruhaniya. Ba abin mamaki ba da aka umurce mu mu taru a kai a kai da yake muna “ganin ranan nan tana gusowa.”—Ibraniyawa 10:24, 25.

13. Ta yaya hidimar Kirista ke taimakonmu mu kasance a faɗake a ruhaniya?

13 Muna samun taimako kuma mu kasance a faɗake sa’ad da muke sa hannu cikin hidimar Kirista da zuciya ɗaya. Akwai wani abin da ke tunasar da mutum alamun zamani da ma’anarsu fiye da ka gaya wa wasu game da hakan? Kuma sa’ad da muka ga waɗanda muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su suna ci gaba kuma sun soma bin abin da suke koya, za mu daɗa gaggawarmu. “Ku natsu, kuna ɗamaracen gindin hankalinku,” in ji manzo Bitrus, “ku kafa begenku sarai.” (1 Bitrus 1:13) “Kuna yawaita cikin aikin Ubangiji,” taimako ne mai kyau don kasance a faɗake a ruhaniya.—1 Korinthiyawa 15:58.

Ka Guje wa Yayin Rayuwa da ke Haɗari ga Ruhaniya

14. Yadda aka kwatanta a Luka 21:34-36, wane yayin rayuwa Yesu ya yi gargaɗi a kai?

14 A cikin annabcinsa game da alama ta bayyanuwarsa, Yesu har ila ya ba da wani gargaɗi. Ya ce: “Ku yi hankali da kanku, kada ya zama zukatanku su yi nauyi da zarin ci da maye da shagulgula na wannan rai, har ranan nan ta hume ku, ba labari, kamar tarko: gama hakanan za ta humi dukan mazaunan fuskar duniya duk. Amma a kowane loto sai ku yi tsaro, kuna yin roƙo ku sami ikon da za ku tsere ma dukan waɗannan al’amuran da za su faru, ku tsaya kuma a gaban Ɗan mutum.” (Luka 21:34-36) Yesu ya kwatanta daidai irin yayin rayuwa da mutane galiba suke yi: zarin ci, maye, da rayuwa da take da alhini da yawa.

15. Me ya sa ya kamata mu guje wa zarin ci da sha?

15 Zarin ci da maye ba su jitu da ƙa’idodi na Littafi Mai Tsarki ba kuma ya kamata a ƙi su. “Kada ka kasance kana cikin masu-shayeshaye: Ko wurin masu-zarin cin nama,” in ji Littafi Mai Tsarki. (Misalai 23:20) Ba sai ci da sha ɗin ya yi yawa ainun kafin ya zama da muni ba. Zai sa mutum gyangyaɗi kuma sa shi ƙyuya da daɗewa. “Ran rāgo yana fata” in ji karin magana ta Littafi Mai Tsarki, “ba ya kuwa sami kome ba.” (Misalai 13:4) Irin mutumin nan zai so ya yi nufin Allah, amma burin ba zai cika ba domin rāgoncinsa.

16. Ta yaya za mu guje sa alhinin iyali ya nauyaya mu?

16 Menene alhinin rai da Yesu ya yi gargaɗi a kansu? Sun haɗa da damuwar mutum, yi wa iyali tanadi, da sauransu. Ba zai zama hikima ba mu yarda su nawaita mu! Yesu ya yi tambaya: “Wanene fa daga cikinku, bisa ga alhininsa, yana da iko da ya ƙara ko kamu ɗaya ga tsawonsa?” Ya gargaɗi masu sauraronsa: “Kada ku yi alhini fa, kuna cewa, Me za mu ci? ko kuwa, Me za mu sha? ko kuwa, Da menene za mu yi sutura? Gama waɗannan abu duka Al’ummai suna ta biɗa; gama Ubanku na sama ya sani kuna bukatar waɗannan abu duka.” Sa harkokin Mulki da farko a rayuwarmu kuma kasance da gaba gaɗin cewa Jehovah za ya yi mana tanadin bukatu zai rage mana alhini kuma sa mu kasance a faɗake.—Matta 6:25-34.

17. Ta yaya biɗan abin duniya ke kawo alhini?

17 Za mu iya jawo alhini ma ta wurin biɗan abin duniya. Alal misali, wasu suna yin rayuwa da ba sa iya adanawa. Wasu sun kamu cikin son yin arziki na dare ɗaya da zuba jarin da ke da haɗari. Ga wasu, ilimin duniya don samun ribar kuɗi ya zama musu tarko. Hakika, don a iya samun aiki ana bukatar a yi wani babban makaranta. Amma, gaskiyar cewa biɗe-biɗe da ke cin lokaci a samun ƙarin ilimi ya zama haɗari ga wasu a ruhaniya. Lallai yanayi ne na haɗari da mutum ya kasance ciki, da ranar Jehovah ke jawo kusa! Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi: “Waɗanda suna so su zama mawadata su kan fāɗa cikin jaraba da tarko da sha’awoyi dayawa na wauta da ɓarna, irin da kan dulmaya mutane cikin halaka da lalacewa.”—1 Timothawus 6:9.

18. Don kada mu fāɗa cikin hanyar rayuwa ta biɗan abin duniya, dole wace iyawa za mu kasance da ita?

18 Domin kada mu fāɗi cikin hanyar biɗan abin duniya yana bukatar mu iya bambanta tsakanin abin da ke daidai da abin da ba daidai ba kuma a tsai da shawara. Ana iya samun iyawar nan ta wurin cin ‘abinci mai-ƙarfi da ke domin isassun mutane,’ a kai a kai kuma ta yin amfani da ‘hankali da ya horu bisa ga aikaceya.’ (Ibraniyawa 5:13, 14) Tabbatawa game da “mafifitan al’amura” sa’ad da kake jera abubuwa mafi muhimmanci za su tsare mu daga tsai da muguwar shawara.—Filibbiyawa 1:10.

19. Idan muka lura cewa muna da ɗan lokaci ne kawai don biɗan abubuwa na ruhaniya, me za mu yi?

19 Yayin rayuwa na son abin duniya zai makantar da mu, da ba za mu sami lokaci ba don biɗan abubuwa na ruhaniya. Ta yaya za mu bincika kanmu kuma mu guje wa shigan tarkon irin yayin rayuwar nan? Muna bukatar mu sa yadda za mu sauƙaƙa rayuwarmu cikin addu’a da kuma yawan yadda za mu yi hakan. Sarki Sulemanu na Isra’ila ta dā ya ce: “Barcin mutum ma’aikaci da daɗi ne, ko ya ci kaɗan, ko dayawa; amma ƙoshin mai-arziki ba za ya bar shi ya yi barci ba.” (Mai-Wa’azi 5:12) Yawan kula da mallakarmu suna ci mana lokaci da kuma ƙarfi ne? Idan muna da abin mallaka da yawa, muna da abin da za mu adana da yawa ke nan, mu lura da su kuma mu kāre su. Za mu amfana ne idan muka rage wasu abin mallaka daga rayuwarmu?

Ka Yi Iyakacin Ƙoƙari Ka Kasance a Shirye

20, 21. (a) Wane tabbaci ne manzo Bitrus ya bayar game da ranar Jehovah? (b) Waɗanne ayyuka da halaye dole mu yi mu tabbatar da cewa muna a shirye domin ranar Jehovah?

20 Lokaci ya kure wa duniyar zamanin Nuhu kuma haka zai kure wa wannan zamani. Manzo Bitrus ya tabbatar mana: “Ranar Ubangiji kamar ɓarawo za ta zo; a cikinta fa sammai za su shuɗe tare da ƙara mai-girma, rundunan kuma za su narke da ƙuna mai-zafi, duniya kuwa da ayyukan da ke cikinta za su ƙone.” Sammai na alama—muguwar gwamnati—ko kuma duniya ta alama—mutane da suke bare daga Allah—ba za mu iya tsira wa zafin fushin Allah ba. Da yake nuna yadda za mu kasance a shirye domin ranar, Bitrus ya ce: “Waɗanne irin mutane ya kamata ku zama cikin tasarrufi mai-tsarki da ibada kuma? kuna sauraron ranar Allah, kuna kuwa marmarin zuwanta ƙwarai.”—2 Bitrus 3:10-12.

21 Halartan taronmu na Kirista a kai a kai da kuma sa hannu a wa’azin bishara yana cikin ayyukan tasarrufi mai tsarki. Bari mu yi su da cikakkiyar ibada ga Allah sa’ad da muke sauraron babbar ranar Jehovah da haƙuri. Bari mu “bada aniyya a tararda [mu] cikin salama, marasa-aibi marasa-laifi a gaban [Allah].”—2 Bitrus 3:14.

Ka Tuna?

• Me ya sa za mu tabbatar muna a shirye domin ranar Jehovah?

• Idan biɗan yau da kullum ya zama muhimmi a rayuwarmu, me za mu yi?

• Me zai taimake mu mu tsayayya wa gyangyaɗi na ruhaniya?

• Waɗanne yayin rayuwa dole mu ƙi, kuma ta yaya?

[Hotuna a shafuffuka na 12, 13]

Mutane na zamanin Nuhu ba su lura ba game da hukuncin da ke zuwa—kai fa?

[Hoto a shafi na 15]

Za ka iya sauƙaƙa rayuwarka ka samu isashen lokaci domin biɗe-biɗe na ruhaniya?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba