“Muryarsu Ta Fita Cikin Dukan Ƙ asa”
“Ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki.”—MATTA 28:19.
1, 2. (a) Wane umurni Yesu ya ba almajiransa? (b) Me ya sa Kiristoci na ƙarni na farko suka iya cim ma abu da yawa?
JIM kaɗan kafin ya hau sama, Yesu ya ba almajiransa umurni. Ya gaya musu: “Ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki.” (Matta 28:19) Wannan aiki ne mai girma!
2 Ka yi tunani! A Fentakos na shekara ta 33 A.Z., an zuba ruhu mai tsarki wa almajirai 120 kuma suka soma idar da wannan umurnin ta gaya wa mutane cewa Yesu ne Almasihu da aka yi alkawarinsa da daɗewa wanda za a samu ceto ta wurinsa. (Ayukan Manzanni 2:1-36) Yaya wannan ƙaramin rukuni za su kai wurin “dukan al’ummai”? Ga mutane kam ba mai yiwuwa ba, amma “ga Allah dukan abu ya yiwu.” (Matta 19:26) Kiristoci na farko sun samu taimakon ruhu mai tsarki na Jehovah, kuma suna da azancin gaggawa. (Zechariah 4:6; 2 Timothawus 4:2) Shi ya sa, cikin ’yan shekaru, manzo Bulus ya ce an yi shelar bishara “cikin dukan halitta da ke ƙarƙashin sama.”—Kolossiyawa 1:23.
3. Menene ya sha kan “alkama” Kirista na gaskiya?
3 A dukan ƙarni na farko, bauta ta gaskiya ta ci gaba da yaɗawa. Amma, Yesu ya yi annabci cewa lokaci yana zuwa da Shaiɗan zai shuka “zawa” kuma ya sha kan “alkama” Kirista na gaskiya na ƙarnuka da yawa har sai lokacin girbi. Bayan mutuwar manzannin, wannan annabci ya faru da gaske.—Matta 13:24-39.
Ƙaruwa da Hanzari a Yau
4, 5. Somawa da shekara ta 1919, wane aiki Kiristoci shafaffu suka soma yi, kuma me ya sa wannan aiki ne mai wuya?
4 Shekara ta 1919, lokaci ne da za a ware alkama ta Kirista na gaskiya daga zawan. Kiristoci shafaffu sun sani cewa har ila za su bi umurni mai girma na Yesu. Sun gaskata sarai cewa suna zama a “kwanaki na ƙarshe” kuma suna sane da annabcin Yesu: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.” (2 Timothawus 3:1; Matta 24:14) Hakika, sun sani cewa akwai aiki da yawa da za a yi.
5 Amma, kamar almajirai a shekara ta 33 A.Z., waɗannan Kiristoci shafaffu suna da aiki mai girma. Dubbai kalilan ne kawai a cikinsu suke ƙasashe kalilan. Ta yaya za su yi wa’azin bishara “cikin iyakar duniya”? Ka tuna, jama’ar duniya ta ƙaru daga kusan miliyan 300 a lokacin Kaisar zuwa kusan biliyan 2 bayan yaƙin duniya na farko. Kuma a dukan ƙarni na 20, zai ci gaba da ƙaruwa.
6. Har yaya aka yaɗa bishara a shekarun 1930?
6 Duk da haka, bayin Jehovah shafaffu, kamar ’yan’uwansu na ƙarni na farko, suka soma aikin da aka ba su da cikakkiyar bangaskiya ga Jehovah, kuma ruhunsa yana tare da su. A tsakiyar shekarun 1930, wasu masu wa’azin bishara 56,000 sun yi shelar gaskiyar Littafi Mai Tsarki a ƙasashe 115. An riga an yi aiki sosai amma har ila akwai aiki da yawa da za a yi.
7. (a) Wane sabon ƙalubale Kiristoci shafaffu suka fuskanta? (b) Ta taimakon “waɗansu tumaki” ta yaya aikin tara mutane ya ci gaba har wa yau?
7 Sai kuma fahimta “taro mai-girma” da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna 7:9 ta zama ƙalubale amma wannan zai taimaki waɗannan Kiristoci masu aiki tuƙuru nan gaba. Za a tattara taro na “waɗansu tumaki,” da ba a san adadinsu ba, da suke da begen zama a duniya, daga “cikin kowane iri, da dukan ƙabilai da al’ummai da harsuna.” (Yohanna 10:16) Waɗannan za su ‘yi ma Jehovah bauta dare da rana.’ (Ru’ya ta Yohanna 7:15) Wannan yana nufin cewa za su taimaka a aikin wa’azi da koyarwa. (Ishaya 61:5) Saboda haka, Kiristoci shafaffu sun yi farin cikin ganin adadin masu wa’azin bishara ya ƙaru da dubbai har kuma miliyoyi. A shekara ta 2003, sabon ƙoli na 6,429,351 sun sa hannu cikin aikin wa’azi—yawancinsu suna cikin taro mai girma.a Kiristoci shafaffu suna godiya don wannan taimako, kuma taro mai girma suna godiya don gatar tallafa wa ’yan’uwansu shafaffu.—Matta 25:34-40.
8. Menene Shaidun Jehovah suka yi game da matsi mai tsanani da suka fuskanta a yaƙin duniya na biyu?
8 Sa’ad da ajin alkama ya sake bayyana, Shaiɗan ya yi yaƙi mai tsanani da su. (Ru’ya ta Yohanna 12:17) Me ya yi sa’ad da taro mai girma suka soma bayyana? Ya yi faɗā sosai! Za mu yi shakka ne cewa shi ya zuga farmaki na dukan duniya game da bauta ta gaskiya da ya faru lokacin yaƙin duniya na biyu? A duk fannin yaƙin, an tsananta wa Kiristoci sosai. ’Yan’uwa ƙaunatattu da yawa sun sha gwaji ƙwarai, wasu sun mutu don bangaskiyarsu. Duk da haka, ta halayensu sun nuna suna da ra’ayin mai Zabura: “Cikin Allah zan yabi maganatasa: cikin Allah na dogara, ba zan ji tsoro ba; ina abin da jiki za ya yi mini?” (Zabura 56:4; Matta 10:28) Da yake ruhun Jehovah ne ya ƙarfafa su, Kiristoci shafaffu da waɗansu tumaki, sun yi tsayin daka. (2 Korinthiyawa 4:7) Saboda haka, “maganar Allah kuwa ta yawaita.” (Ayukan Manzanni 6:7) Sa’ad da aka soma yaƙi a shekara ta 1939, Kiristoci masu aminci 72,475 suka ba da rahoton aikinsu na wa’azi. Amma, rahoto na shekara ta 1945, shekarar da aka gama yaƙin ya nuna cewa Shaidu 156,299 masu ƙwazo sun yaɗa bisharar ko da rahoton ba cikakke ba ne. Cin nasara ne bisa Shaiɗan!
9. Waɗanne sababbin makarantu aka sanar sa’ad da ake Yaƙin Duniya na ll?
9 A bayyane yake cewa ɗimaucewa da yaƙin duniya na biyu ya kawo bai sa bayin Jehovah su yi shakkar cewa za a yi aikin wa’azi ba. Hakika, a shekara ta 1943, sa’ad da yaƙin yake da tsanani, an sanar da sababbin makarantu biyu. Ɗaya da yanzu ake kira Makarantar Hidima ta Allah, za a gudanar da shi a dukan ikilisiyoyi don a koyar da Shaidu su yi wa’azi kuma su samu almajirai. Ɗayan kuma, Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead ce, don a koya wa masu wa’azi na ƙasashen waje da za su yi aikin wa’azi a wata ƙasa. Hakika, sa’ad da aka gama yaƙin, Kiristoci na gaskiya suna shirye don ƙarin ayyuka.
10. Ta yaya mutanen Jehovah suka yi himma a shekara ta 2003?
10 Makarantun sun yi taimako sosai! Da yake an koyar da su a Makarantar Hidima ta Allah, duka—manya da ƙanana, iyaye da yara, har da naƙasassu—sun sa hannu kuma sun ci gaba da yin aiki mai girma da Yesu ya ba mu. (Zabura 148:12, 13; Joel 2:28, 29) A shekara ta 2003, kowanne wata averijin masu shela 825,185 sun nuna suna da azancin gaggawa ta sa hannu na ɗan lokaci ko kuma a kai a kai cikin hidima ta majagaba. A wannan shekarar, Shaidun Jehovah sun yi sa’o’i 1,234,796,477 suna gaya wa mutane game da bisharar Mulki. Babu shakka Jehovah yana farin ciki da himmar mutanensa!
A Yankunan Ƙasashen Waje
11, 12. Waɗanne misalai ne suka nuna rahoto mai kyau na masu wa’azi a ƙasashen waje?
11 Cikin shekaru da yawa, waɗanda suka sauke karatu na Gilead da kuma na Makarantar Koyar da Masu Hidima kwanan bayan nan suna da rahoto mafi kyau. Alal misali, a Brazil masu shela sun ɗan fi 400 sa’ad da masu wa’azi a ƙasashen waje na farko suka kai wajen a shekara ta 1945. Waɗannan masu wa’azin da waɗanda suka bi bayansu sun yi aiki tuƙuru tare da ’yan’uwansu na Brazil masu himma, kuma Jehovah ya albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcensu sosai. Abin farin ciki ne ga waɗanda suka tuna da waɗancan lokaci na farko su ga Brazil ta ba da rahoton sabon ƙoli na 607,362 a shekara ta 2003!
12 Ka yi la’akari da Japan. Kafin yaƙin duniya na biyu, suna da misalin masu shelar Mulki ɗari a ƙasar. A lokacin yaƙin, tsanantawa ta zalunci ya rage adadin masu shela, kuma a ƙarshen yaƙin, Shaidu kalilan ne kawai suke da rai a ruhaniya kuma a zahiri. (Misalai 10:9) Waɗannan kalilan da suke da aminci sun yi farin ciki ƙwarai a shekara ta 1949 su marabci masu wa’azi na ƙasashen waje 13 na Gilead na farko da aka koyar da su, kuma masu wa’azi na ƙasashen wajen sun so ’yan’uwansu Japanisawa masu halin karɓan baƙi, masu ƙwazo kuma. Bayan shekara 50, a shekara ta 2003, Japan ta ba da rahoton ƙolin adadin masu shela 217,508! Jehovah ya albarkaci mutanensa sosai a wannan ƙasar. Da akwai irin wannan rahoto daga ƙasashe da yawa. Waɗanda suka yi wa’azi a yankunan ƙasashen waje sun sa hannu sosai a yaɗa bishara, shi ya sa a shekarar 2003 an ji bishara a ƙasashe, tsibirai, da kuma yankuna 235 kewaye da duniya. Hakika, taro mai girma suna fitowa daga “dukan al’ummai.”
“Daga . . . Dukan Ƙabilai da Al’ummai da Harsuna”
13, 14. A wace hanya ce Jehovah ya nuna amfanin wa’azin bishara cikin ‘dukan harsuna’?
13 Mu’ujiza ta farko da aka ba da rahotonta bayan an shafa almajiran da ruhu mai tsarki a Fentakos na shekara ta 33 A.Z., ita ce cewa suna magana a harsuna dabam dabam ga taro da suka taru. Waɗanda suka saurare su mai yiwuwa suna yare da ake amfani da shi a ƙasashe da yawa, wataƙila Helenanci. Da yake “masu tsoron Allah” ne, mai yiwuwa suna iya fahimta hidima da ake yi a Ibrananci a haikalin. Sun motsa su saurara sa’ad da suka ji ana bishara a yaren da suka koya suna yara.—Ayukan Manzanni 2:5, 7-12.
14 A yau ma, ana amfani da harsuna da yawa a aikin wa’azi. An yi annabci cewa taro mai girma za su fito ba kawai daga al’ummai ba amma daga “ƙabilai . . . da harsuna.” Cikin jituwa da wannan, Jehovah ya yi annabci ta Zechariah: ‘Mutum goma daga cikin dukan harsunan al’ummai za su kama ƙafar wanda shi ke Ba-yahudi, su ce, Za mu tafi tare da ku, gama mun ji labari Allah yana tare da ku.’ (Zechariah 8:23) Ko da Shaidun Jehovah ba su da baiwar magana da waɗansu harsuna ba, sun san amfanin koyarwa a harsuna da mutane suke ji.
15, 16. Ta yaya masu wa’azi na ƙasashen waje da kuma wasu suka fuskanci ƙalubale na wa’azi cikin harsunan yankunansu?
15 Hakika, a yau harsuna kalilan ne ake amfani da su a dukan duniya, kamar Turanci, Faransa, da Spanisanci. Amma, waɗanda suka bar ƙasarsu su yi hidima a wasu ƙasashe sun yi ƙoƙarin koya harsunan yankin da suke hidima don “waɗanda aka ƙaddara su ga rai na har abada” su ji bisharar. (Ayukan Manzanni 13:48) Wannan yana da wuya. Sa’ad da ’yan’uwa a ƙasar South Pacific na Tuvalu suka bukaci littattafai a nasu yare, wani mai wa’azi na ƙasan waje ya ɗauki aikin. Tun da yake babu ƙamus na yaren, ya soma rubuta wasu fassarar jerin kalmomin Tuvalu da ma’anarsu. Da shigewar lokaci, aka buga littafin nan Kana iya Rayuwa Har Abada Cikin Aljanna a Duniya a yaren Tuvalu.b Sa’ad da masu wa’azi na ƙasashen waje suka kai Curaçao, babu Littafi Mai Tsarki kuma babu ƙamus a yarensu da ake kira Papiamento. An yi jayayya sosai a yadda za a rubuta yaren. Duk da haka, bayan shekara biyu da masu wa’azi na ƙasashen waje na farko suka kai wurin, aka buga warƙa ta farko na Kirista daga Littafi Mai Tsarki a wannan yaren. A yau, yaren Papiamento yana cikin harsuna 133 da ake buga Hasumiyar Tsaro a lokaci ɗaya da Turanci.
16 A Namibia masu wa’azi na ƙasashen waje na farko ba su iya samun Mashaidi na wurin da zai taimake su fassara ba. Ban da haka, wani yaren Nama, ba shi da furcin da ake amfani da su a littattafanmu, kamar “kamiltacce.” Wani mai wa’azi na ƙasan waje ya ce: “Ina amfani da malaman makaranta da suke nazarin Littafi Mai Tsarki su yi fassarar. Da yake suna da ɗan ilimin gaskiya, ina kasancewa tare da su don na tabbata cewa kowacce jimla daidai ne.” Duk da haka, daga baya aka fassara warƙar nan Rai Cikin Sabuwar Duniya Mai-Salama cikin harsunan huɗu na Namibia. A yau, ana buga Hasumiyar Tsaro a kai a kai a yaren Kwanyama da yaren Ndonga.
17, 18. Waɗanne matsala na aka bi da su a Mexico da kuma wasu ƙasashe?
17 A Mexico, yarensu na musamman Spanisanci ne. Amma, kafin mutanen Spain su kai wurin, ana harsuna da yawa a wajen, kuma har ila da yawa cikinsu ana amfani da su. Saboda haka, ana buga littattafan Shaidun Jehovah yanzu a harsunan Mexico guda bakwai da kuma Bebenci na Mexico. Kingdom Ministry na yaren Maya ne takarda ta farko mai kwanan wata da aka buga a Yaren American Indian. Hakika, mutane dubbai masu yaren Maya, Aztecs, da kuma wasu suna cikin 572,530 na masu shelar Mulki a Mexico.
18 Kwanan bayan nan, mutane da yawa sun yi gudun hijira zuwa wasu ƙasashe, ko kuma sun ƙaura don neman aiki. Saboda haka, ƙasashe da yawa yanzu a lokaci na farko suna da yankunan wasu harsuna da suke da ɗan girma. Shaidun Jehovah sun ɗauki aikin. Alal misali, a Italiya akwai ikilisiyoyi a harsuna 22 ban da yaren Italiya. Domin a taimaki ’yan’uwa su yi wa mutane da suke wasu harsuna wa’azi, kwanan bayan nan an shirya azuzuwa don a koyar da harsuna 16 har da Bebenci na Italiya. A ƙasashe da yawa, Shaidun Jehovah suna irin wannan ƙoƙarce-ƙoƙarce don su yi wa mutane da suke shigowa wa’azi. Hakika, da taimakon Jehovah, taro mai girma suna fitowa daga harsuna da yawa.
“Cikin Dukan Ƙasa”
19, 20. Waɗanne kalmomin Bulus suke cika a hanya ta musamma a yau? Ka ba da bayani.
19 A ƙarni na farko, manzo Bulus ya rubuta: “Ba su ji ba? I, hakika, muryarsu ta fita cikin dukan ƙasa, kalmominsu kuma har iyakan duniya.” (Romawa 10:18) Idan haka ya kasance a ƙarni na farko, zai fi ma a zamaninmu! Miliyoyi—wataƙila fiye da kowane lokaci a tarihi—suna cewa: “Zan albarkaci Ubangiji a kowane loto: yabonsa kuwa za ya zauna a bakina tuttur.”—Zabura 34:1.
20 Ƙari ga haka, aikin ba ragewa yake yi ba. Adadin masu shelar Mulki ya ci gaba da ƙaruwa. Ana ƙara ba da lokaci ga aikin wa’azi. Ana koma ziyara dubbai kuma ana gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da yawa. Sababbi sun ci gaba da son saƙon. Bara, sabon ƙolin 16,097,622 sun halarci bikin Tuna da mutuwar Yesu. Hakika, da akwai ƙarin aiki da za a yi. Bari mu ci gaba da yin koyi da amincin ’yan’uwanmu da suka jimre tsanantawa. Kuma mu yi koyi da himmar ’yan’uwanmu da tun shekara ta 1919 sun ba da kansu a hidimar Jehovah. Bari dukanmu mu ci gaba da bin waƙar mai Zabura: “Abin da yake da numfashi duka shi yi yabon Ubangiji. Hallelujah!”—Zabura 150:6.
[Hasiya]
a Ka duba rahoto na shekara a shafofi 28 zuwa 31 na wannan jarida.
b Shaidun Jehovah ne suka buga.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Wane aiki ’yan’uwa suka soma yi a shekara ta 1919, kuma me ya sa kaluɓale ne?
• Su waye aka tattara don su tallafa wa aikin wa’azi?
• Wane rahoto masu wa’azi na ƙasashen waje da wasu da suke hidima a wani waje suka ba da?
• Wane misali za ka nuna cewa Jehovah yana yi wa aikin mutanensa a yau albarka?
[Taswira a shafi na 28-31]
2003 SERVICE YEAR REPORT OF JEHOVAH’S WITNESSES WORLDWIDE
(See bound volume)
[Hotuna a shafuffuka na 24, 25]
Ɗimaucewa na yaƙin duniya na biyu bai sa Kiristoci su yi shakka cewa za a yi wa’azin bishara ba
[Inda aka Dauko]
Nakiya: hoton sojojin teku na Amirka; wasu: Hoton Coast Guard na Amirka
[Hotuna a shafuffuka na 26, 27]
Taro mai girma za su fito daga dukan ƙabilai da harsuna