Bishara Don Mutanen Dukan Al’ummai
“Za ku kuma zama shaiduna . . . har ya zuwa iyakar duniya.”—Ayyukan Manzanni 1:8.
1. Da yake mu masu koyar da Littafi Mai Tsarki ne, ga menene muke mai da hankali, kuma don me?
ƘWARARRUN malamai suna mai da hankali ga abubuwa da suke gaya wa ɗalibansu da kuma yadda suke gaya musu. Mu masu koyar da Littafi Mai Tsarki, mu ma muna yin haka. Muna mai da hankali ga saƙon da muke wa’azinsa da kuma hanyoyin da muke yin sa. Saƙonmu, bisharar Mulkin Allah, ba ta canjawa, amma muna canja hanyoyinmu. Me ya sa? Domin mu kai ga mutane masu yawa.
2. Idan muka daidaita hanyoyinmu na wa’azi, waye ne muke koyi da shi?
2 Idan muka daidaita hanyoyinmu na yin wa’azi, muna bin misalin bayin Allah na dā. Alal misali, yi la’akari da manzo Bulus. Ya ce: “Ga Yahudawa, sai na zama kamar Bayahude. . . . Ga marasa Shari’a kuwa, sai na zama kamar marar Shari’a. . . . Ga raunana, sai na zama kamar rarrauna, domin in rinjayi raunana. Na zama kowane irin abu ga kowaɗanne irin mutane, domin ta ko ƙaƙa in ceci waɗansu.” (1 Korantiyawa 9:19-23) Daidaituwa da Bulus ya yi ta ba da albarka. Mu ma za mu sami sakamako mai kyau idan muka daidaita bayaninmu da mutanen da muke tattaunawa da su.
Zuwa “Ko’ina a Duniya”
3. (a) Wane ƙalubale ne muke fuskanta a aikinmu na wa’azi? (b) Ta yaya ne kalaman Ishaya 45:22 suke cika a yau?
3 Ainihin ƙalubalen da masu wa’azin bishara suke fuskanta shi ne girman yankinsu wato “ko’ina a duniya.” (Matiyu 24:14) A ƙarni na ƙarshe, yawancin bayin Jehobah sun yi aiki tuƙuru domin su yaɗa bishara zuwa ƙasashe masu yawa. Menene sakamakon haka? An sami faɗaɗa mai ban mamaki a dukan duniya. A somawar ƙarni na 20, ana wa’azi ne kawai a ƙasashe kalilan, amma a yau Shaidun Jehobah suna ƙwazo a ƙasashe 235! Hakika, ana shelar bisharar Mulki “ko’ina a duniya!”—Ishaya 45:22.
4, 5. (a) Su waye ne suka saka hannu musamman a yaɗa bishara? (b) Menene wasu ofisoshin reshe suka ce game da waɗanda suka zo daga ƙasashen waje da suke hidima a yankin reshensu?
4 Menene dalilin samun wannan ci gaba? Dalilan suna da yawa. Masu wa’azi na ƙasashen waje da aka koyar a Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gileyad, da kuma mutane 20,000 da suka sauke karatu a Makarantar Koyar da Masu Hidima sun taimaka ƙwarai. Haka kuma Shaidu masu yawa da suka koma da kansu zuwa ƙasashen da ake bukatar masu shelar Mulki da yawa. Irin waɗannan Kiristoci maza da mata, yara da manya, ma’aurata da marasa aure, da suka ba da kansu sun saka hannu musamman a wa’azin saƙon Mulki a dukan duniya. (Zabura 110:3; Romawa 10:18) Ana ƙaunarsu sosai. Ka lura da abin da wasu ofisoshin reshe suka rubuta game da ’yan ƙasan waje da suke hidima a inda ake bukata sosai a yankin reshensu.
5 “Waɗannan ƙaunatattun Shaidu, suke ja-gora a yin wa’azi a wararrun yankuna, sun taimaka a kafa sababbin ikilisiyoyi, kuma sun taimaka wajen motsa ’yan’uwa su manyanta a ruhaniya.” (Ecuador) “Idan ɗarurruwan ’yan ƙasashen waje da suke hidima a nan suka tashi, hakan zai shafi ikilisiyoyin. Albarka ne zamansu tare da mu.” (Jamhuriyar Dominikan) A yawancin ikilisiyoyinmu, ’yan’uwa mata sun fi yawa, a wani lokacin har kashi 70. (Zabura 68:11) Yawancinsu sababbi ne a cikin gaskiya, amma ’yan’uwa mata majagaba da ba su da aure, da suka zo daga wasu ƙasashe suna taimakawa sosai wajen koyar da waɗannan sababbin. Waɗannan ’yan’uwa mata da suka zo daga ƙasashen waje baiwa ce mai tamani a gare mu!” (Gabashin Turai) Ka taɓa tunanin yin hidima a wata ƙasa kuwa?a—Ayyukan Manzanni 16:9, 10.
‘Mutum Goma Daga Kowane Harshe’
6. Ta yaya ne Zakariya 8:23 ta yi bayani game da ƙalubale na yare a aikin wa’azinmu?
6 Wani muhimman ƙalubale shi ne bambancin yaren da ake yi a duniya. Kalmar Allah ta ce: “A waɗannan kwanaki mutum goma daga kowace al’umma da kowane harshe za su kama kafa wurin Bayahude, su ce, ‘Ka yardar mana mu tafi tare da kai, gama mun ji Allah yana tare da ku.’ ” (Zakariya 8:23) A cikar wannan annabci na zamani, mutum goma na wakiltan ƙasaitaccen taro da aka annabta a Wahayin Yahaya 7:9. Ka lura cewa “mutum goma” in ji annabcin Zakariya, za su fito ba kawai daga dukan al’ummai ba amma kuma ‘daga kowace al’umma da kowane harshe.’ Mun ga cikar wannan muhimmin annabcin kuwa? Hakika.
7. Wane adadi ne ya nuna cewa mutane “daga kowane harshe” suna samun bishara?
7 Ka yi la’akari da wannan. Shekaru hamsin da suka shige ana wallafa littattafanmu a harsuna 90. Amma, a yau, adadin harsunan ya fi 400. “Amintaccen bawan nan mai hikima” ya ci gaba da yin ƙoƙari wajen wallafa littattafai har ga wasu harsunan da mutane ƙalilan ne suke yin su. (Matiyu 24:45) Alal misali, akwai littafi na Littafi Mai Tsarki a Greenlandic wadda (mutane 47,000 ne kawai ke yaren), Palauan wadda (mutane 15,000 ke yaren), da kuma Yapese wadda (mutane kusan 7,000 ne ke yaren).
“Hanya Mai Faɗi” Tana Kawo Wasu Zarafi
8, 9. Wane ci gaba ne ya buɗe mana “hanya mai faɗi,” kuma ta yaya ne dubban Shaidu suka saka hannu?
8 A zamanin nan, ba ma bukatar mu je ƙasar waje domin mu yi wa mutane na kowane harshe bishara. A shekaru na baya bayan nan, miliyoyin mutanen da suka ƙaura zuwa wata ƙasa da kuma ’yan gudun hijira zuwa ƙasashe masu tattalin arziki, sun sa an sami yankuna na mutanen da suka ƙaura da suke yare dabam dabam. Alal misali, a Faransa, Paris, ana harsuna dabam dabam har kusan 100. A Toronto, Kanada, adadin 125 ne; a Landan, Ingila, ana harsuna fiye da 300! Waɗannan mutanen daga wasu ƙasashe a yankunan yawancin ikilisiyoyi sun buɗe “hanya mai faɗi” da ta kai ga samun zarafi na yi wa mutane na dukan al’ummai bishara.—1 Korantiyawa 16:9.
9 Dubban Shaidu suna fuskantar wannan ƙalubalen ta wajen koyon wani yare. Ga yawancinsu, abu ne mai wuya, duk da haka, sun sami lada domin ƙoƙarinsu, domin farin cikin da suka samu na taimaka wa mutanen da suka ƙaura da kuma ’yan gudun hijira su koyi gaskiyar da ke cikin Kalmar Allah. A cikin wata shekarar da ta shige, kusan kashi 40 na dukan waɗanda suka yi baftisma a wani taron gunduma a Yammancin Turai, sun zo ne daga wata ƙasa.
10. Ta yaya ne ka yi amfani da ƙasidar nan Good News for People of All Nations? (Duba akwati “Abubuwan da ke cikin Ƙasidar nan Good News for People of All Nations,” da ke shafi na 32.)
10 Hakika, ba dukanmu ba ne ke da damar koyon wani yare. Duk da haka, muna iya saka hannu wajen taimaka wa waɗanda suka ƙaura ta wajen yin amfani da sabuwar ƙasidar nan da aka fito da ita Good News for People of All Nations,b wadda take ɗauke da saƙon Littafi Mai Tsarki mai gamsarwa a harsuna dabam dabam. (Yahaya 4:37) Kana amfani da wannan ƙasidar a hidimarka kuwa?
Sa’ad da Mutane Suka Ƙi Saurara
11. Wane ƙalubale ne ake fuskanta a wasu yankuna?
11 Yayin da tasirin Shaiɗan ke ƙara yaɗuwa a duniya, ana sake fuskantar wani ƙalubale—yankunan da ba a saurara sosai. Hakika, wannan yanayin ba abin mamaki ba ne a gare mu, domin Yesu ya annabta cewa hakan zai faru. Sa’ad da yake magana game da zamaninmu, ya ce: “Sai ƙaunar yawancin mutane ta yi sanyi.” (Matiyu 24:12) Hakika, yawancin mutane imaninsu ga Allah da kuma daraja Littafi Mai Tsarki ya ragu. (2 Bitrus 3:3, 4) Domin haka, a wasu ɓangarorin duniya, mutane kaɗan ne kawai suka zama sababbin almajiran Kristi. Hakan ba ya nufin cewa, wahalar da ’yan’uwanmu Kiristoci da suke da aminci suka yi a waɗannan yankunan da ba a sauraro sosai na banza ne ba. (Ibraniyawa 6:10) Me ya sa? Yi la’akari da abin da ke gaba.
12. Menene manufa biyu na aikin wa’azinmu?
12 Linjilar Matiyu ta taƙaita ainihin manufa biyu na ayyukan wa’azinmu. Guda shi ne muna “almajirtar da dukkan al’ummai.” (Matiyu 28:19) Ɗayan kuma shi ne, saƙon Mulki “shaida” ne. (Matiyu 24:14) Dukan manufan suna da muhimmanci, amma na biyun ya fi. Me ya sa?
13, 14. (a) Menene abu mafi muhimmanci na alamar dawowar Kristi? (b) Menene ya kamata mu sa a zuciya, musamman ma sa’ad da muke wa’azi a yankunan da ba a saurara sosai?
13 Marubucin Littafi Mai Tsarki Matiyu ya rubuta cewa manzannin sun tambayi Yesu: “Mecece kuma alamar dawowarka, da ta ƙarewar zamani?” (Matiyu 24:3) Yesu ya ce, mafificin alamar nan ita ce aikin wa’azi a dukan duniya. Yana magana ne game da almajirantarwa? A’a. Ya ce: ‘Za a kuma yi bisharan nan ta Mulkin Sama ko’ina a duniya domin shaida ga dukkan al’ummai.’ (Matiyu 24:14) Da haka, Yesu ya nuna cewa aikin wa’azi na Mulki zai zama abu mafi muhimmanci ta alamar.
14 Saboda haka, sa’ad da muke wa’azin bisharar Mulki, mu riƙa tuna cewa idan ba mu yi nasara a almajirantarwa ba, muna yin nasara a wajen ba da “shaida.” Ko da yaya mutane suka aikata, sun san abin da muke yi, da haka muna saka hannu wajen cika annabcin Yesu. (Ishaya 52:7; Wahayin Yahaya 14:6, 7) Jordy, wani Mashaidi matashi a Yammacin Turai, ya ce: “Sanin cewa Jehobah yana amfani da ni wajen cika Matiyu 24:14, yana ba ni farin ciki.” (2 Korantiyawa 2:15-17) Babu shakka, kai ma kana jin haka.
Sa’ad da Ake wa Saƙonmu Hamayya
15. (a) Game da menene Yesu ya yi wa mabiyansa gargaɗi? (b) Me ya sa muke wa’azi duk da hamayya?
15 Yanayi mai tsanani na jawo ƙalubale ga wa’azin bishara ta Mulki. Yesu ya yi wa mabiyansa gargaɗi: “Duk al’ummai za su ƙi ku saboda sunana.” (Matiyu 24:9) Kamar Kiristoci na fari, a yau an ƙi mabiyan Yesu, ana yi musu hamayya, ana kuma tsananta musu. (Ayyukan Manzanni 5:17, 18, 40; 2 Timoti 3:12; Wahayin Yahaya 12:12, 17) A wasu ƙasashe, a yanzu gwamnati ta hana aikinsu. Duk da haka, domin yin biyayya ga Allah, Kiristoci na gaskiya a waɗannan ƙasashe sun ci gaba da wa’azin bisharar Mulki. (Amos 3:8; Ayyukan Manzanni 5:29; 1 Bitrus 2:21) Menene ya taimaka musu, da kuma sauran Shaidu a dukan duniya su yi haka? Jehobah ya ƙarfafa su ta wajen ruhunsa mai tsarki.—Zakariya 4:6; Afisawa 3:16; 2 Timoti 4:17.
16. Ta yaya ne Yesu ya nuna jituwar da ke tsakanin aikin wa’azi da kuma ruhun Allah?
16 Yesu ya nanata jituwar da ke tsakanin ruhun Allah da kuma aikin wa’azi sa’ad da ya gaya wa mabiyansa: ‘Amma za ku sami iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna . . . har ya zuwa iyakar duniya.’ (Ayyukan Manzanni 1:8; Wahayin Yahaya 22:17) Yadda aka jera aukuwar a wannan nassin na da muhimmanci. Na farko, manzannin sun sami ruhu mai tsarki, kuma suka soma aikin wa’azi na dukan duniya. Ta wajen taimakon ruhun Allah ne kawai za su sami ƙarfin jimrewa a yin “shaida ga dukkan al’ummai.” (Matiyu 24:13, 14; Ishaya 61:1, 2) Hakan ya dace sa’ad da Yesu ya yi nuni ga ruhu mai tsarki cewa “mai taimako” ne. (Yahaya 15:26) Ya ce ruhun Allah zai koya wa almajiransa kuma ya yi musu ja-goranci.—Yahaya 14:16, 26; 16:13.
17. Sa’ad da muka fuskanci mugun hamayya, ta yaya ne ruhu mai tsarki ke taimaka mana?
17 A waɗanne hanyoyi ne ruhun Allah ke taimaka mana a yau, sa’ad da muka fuskanci mugun tsanantawa game da wa’azin bishara? Ruhun Allah na ƙarfafa mu, kuma yana hamayya da waɗanda suke tsananta mana. Alal misali, yi la’akari da rayuwar Sarki Saul.
Hamayya Daga Ruhun Allah
18. (a) Wane irin canji marar kyau ne Saul ya yi? (b) Waɗanne hanyoyi ne Saul ya yi amfani da su ya tsananta wa Dauda?
18 Saul ya soma da kyau a matsayin sarkin Isra’ila na farko, amma daga baya, ya yi wa Jehobah rashin biyayya. (1 Sama’ila 10:1, 24; 11:14, 15; 15:17-23) A sakamakon haka, ruhun Allah ya daina taimaka wa sarkin. Saul ya yi mugun fushi da Dauda, wanda an riga an naɗa shi ya zama sarki na gaba kuma yana samun taimakon ruhun Allah. (1 Sama’ila 16:1, 13, 14) Kamar Dauda zai shiga hannun Saul cikin sauƙi. Tun da ma, Dauda yana riƙe ne kawai da molo, amma Saul na riƙe da māshi. Wata rana sa’ad da Dauda ke kaɗa molonsa, “Saul kuwa yana riƙe da māshi. Yana cewa a ransa, ‘Zan nashe shi, in kafe shi da bango.’ Sau biyu yana cakar Dawuda da māshi, amma Dawuda ya goce.” (1 Sama’ila 18:10, 11) Bayan haka, Saul ya saurari ɗansa Jonatan, abokin Dauda, kuma ya rantse: “Hakika, ba za a kashe [Dauda] ba.” Bayan haka kuma, Saul “kuwa ya yi shiri ya nashi Dawuda, ya kafe shi ga bango. Da ya nashe shi, sai ya goce, māshin ya sami bangon.” Dauda ya gudu, amma Saul ya bi shi. A wannan lokaci mai tsanani, ruhun Allah ya zama mai hamayya ga Saul. A wace hanya?—1 Sama’ila 19:6, 10.
19. Ta yaya ne ruhun Allah ya kāre Dauda?
19 Dauda ya tsere zuwa wajen annabi Sama’ila, amma Saul ya aika mutane su tafi su kamo Dauda. Sa’ad da suka isa inda Dauda ya ɓuya, sai “ruhun Allah ya sauko a kan manzannin Saul, su kuma suka yi annabci.” Ruhun Allah ya sha kansu gabaki ɗaya har suka mance dalilin zuwansu. Saul ya ƙara aika mutanensa sau biyu domin su kamo Dauda, su ma suka soma annabci. A ƙarshe, Sarki Saul da kansa ya tafi wurin Dauda, amma Saul da kansa ya kasa tsayayya wa ruhun Allah. Hakika, ruhu mai tsarki ya sa gwiwarsa ta yi sanyi “dukan yini da dukan dare”—hakan ya ba Dauda isashen lokaci na tserewa.—1 Sama’ila 19:20-24.
20. Wane darassi ne za mu iya koya daga labarin tsananta wa Dauda da Saul ya yi?
20 Wannan labarin Saul da Dauda na ɗauke da darassi mai ƙarfafawa: Masu tsananta wa bayin Allah ba za su yi nasara ba sa’ad da ruhun Allah ke hamayya da su. (Zabura 46:11; 125:2) Jehobah ya riga ya ƙudurta cewa Dauda zai zama sarki bisa Isra’ila. Babu wanda zai iya canza hakan. Ga zamaninmu, Jehobah ya riga ya ƙudurta cewa za a ‘yi bisharan nan ta Mulkin Sama ko’ina a duniya.’ Babu wanda zai iya hana hakan faruwa.—Ayyukan Manzanni 5:40, 42.
21. (a) Ta yaya ne wasu masu hamayya suke aikatawa? (b) Wane tabbaci muke da shi?
21 Wasu addinai da shugabannin ’yan siyasa suna iya amfani da ƙarairai da kuma mugunta domin su hana mu. Amma, kamar yadda Jehobah ya kāre Dauda a ruhaniya, haka zai kāre mutanensa a yau. (Malakai 3:6) Saboda haka, kamar Dauda, mun ce da gaba gaɗi: “A gare shi [Allah] nake dogara, ba zan ji tsoro ba. Me mutum kawai zai yi mini?” (Zabura 56:11; 121:1-8; Romawa 8:31) Da taimakon Jehobah, bari mu ci gaba da jimre wa dukan ƙalubale yayin da muke ci gaba da yin aikin da Allah ya ba mu, na yin wa’azin bishara na Mulki ga dukan al’ummai.
[Hasiya]
a Ka duba akwati “Gamsuwa ta Ƙwarai,” da ke shafi na 28.
b Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
Za Ka Iya Tunawa?
• Me ya sa muke canja hanyoyin da muke yin wa’azi?
• “Hanya mai faɗi” da ke kai wa ga waɗanne zarafi ke a buɗe?
• Menene muke cim ma wa ta wajen aikin wa’azinmu, har ma a inda ba a saurara sosai?
• Me ya sa babu wani mai hamayya da zai iya hana wa’azin bisharar Mulki?
[Akwati a shafi na 28]
Gamsuwa ta Ƙwarai
“Suna farinciki kuma suna jin daɗin hidimarsu ta haɗin kai ga Jehobah.” Waɗannan kalaman sun kwatanta wani iyalin da suka ƙaura daga Spain zuwa Bolivia. Wani cikin yaran ne ya tafi can don ya taimaka wa wani rukunin da ke a ware. Farincikinsa ya burge iyayensa wanda hakan ya motsa duka iyalin, har da ’ya’yansu maza su huɗu masu shekaru 14 zuwa 25 suka tafi yin hidima a can. Uku cikin yaran sun zama majagaba, kuma wanda ya soma zuwa wajen ya halarci Makarantar Koyar da Masu Hidima.
“Ƙalubalen suna da yawa,” in ji Angelica, mai shekara 30 daga Kanada, wadda take hidima a Yammacin Turai, “amma ina samun gamsuwa daga taimaka wa mutane a hidima. Kuma kalamai na godiya da nake samu daga Shaidu na yankin, don zuwana taimaka musu, yana motsa ni.”
“Akwai al’adu masu yawa da za mu koya,” in ji wasu ’yan’uwa mata waɗanda uwarsu ɗaya ubansu ɗaya da suke ƙarshen shekarunsu na 20, waɗanda suka zo daga Amirka, kuma suna hidima a Jamhuriyar Dominican. “Amma, mun ci gaba a aikinmu, kuma ɗalibanmu na Littafi Mai Tsarki guda bakwai yanzu suna halartar taro.” An yi amfani da waɗannan ’yan’uwa mata biyu wajen ƙafa rukunin masu shelar Mulki a wani gari inda babu ikilisiya.
Laura, wata ’yar’uwa da take ƙarshen shekarunta na 20, wadda take hidima a ƙasar waje fiye da shekara huɗu. Ta ce: “Na sauƙaƙa rayuwata da son rai. Hakan ya taimaka wa masu shelar su fahimci cewa yin rayuwa mai sauƙi batu ne na zaɓi da kuma natsuwa, ba talauci ba. Taimaka wa wasu, musamman matasa, ya ba ni farin ciki ƙwarai har ya kawar da ƙalubalen yin hidima a ƙasar waje. Ba zan sauya hidima ta a nan domin wata rayuwa ba, kuma zan ci gaba har sai Jehobah ya ce, ya isa.”
[Box/Hoto a shafi na 32]
Abubuwa da ke Cikin Ƙasidar nan Good News for People of All Nations
Ƙasidar nan Good News for People of All Nations na ɗauke da saƙo na shafi ɗaya har harsuna 92. An rubuta saƙon kamar ana yi wa mutum ɗaya ne magana. Saboda haka, sa’ad da mai gidan ke karanta saƙon, zai zama kamar kana masa magana ne.
Shafi na ciki na ɗauke da taswira na duniya. Ka yi amfani da wannan taswirar ka yi abuta da mai gidan. Wataƙila za ka nuna ƙasar da kake da zama kuma ka nuna cewa za ka so ka san inda ya fito. Ta haka, za ka sa ya faɗi ra’ayinsa kuma hankalinsa ya kwanta.
Gabatarwa ta ƙasidar ta jera hanyoyi masu yawa da za mu iya amfani da su mu taimaka wa waɗanda suke wata yare da ba mu fahimta ba. Don Allah ka karanta waɗannan matakai a hankali kuma ka yi amfani da su da kyau.
Sashen abin da ke ciki ya tsara harsuna da kuma alamun harsunan. Wannan tsarin zai taimaka maka ka gane alamun yare da aka wallafa a warƙoƙinmu da sauran littattafanmu da suke a wasu harsuna.
[Picture]
Kana amfani da wannan ƙasida a hidima kuwa?
[Hotuna a shafi na 29]
Yanzu akwai littattafanmu na Littafi Mai Tsarki a fiye da harsuna 400
GĀNA
PHILIPPINES
LAPLAND (SWEDEN)
[Hotuna a shafuffuka na 30, 31]
Kana iya yin hidima a inda ake da bukata mai yawa na masu shelar Mulki kuwa?
ECUADOR
JAMHURIYAR DOMINICAN