Jehovah Mai Yawan Ƙaunar Aminci Ne
“Ubangiji . . . mai-yawan [ƙaunar alheri].”—ZABURA 145:8.
1. Yaya yawan ƙaunar Allah take?
“ALLAH ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Wannan furci mai kyau yana tabbatar da cewa hanyar sarautar Jehovah tushenta daga ƙauna ce. Hakika, mutane da ba sa biyayya gare shi ma suna amfana daga rana da ruwan sama da yake tanadinsu da kyau! (Matta 5:44, 45) Saboda ƙaunar da Allah yake wa duniya, magabtansa ma suna iya tuba, su juya gare shi, su sami rai. (Yohanna 3:16) Amma, ba da daɗewa ba, Jehovah za ya kawar da miyagu domin mutane da suke ƙaunarsa su iya morar rai na har abada cikin sabuwar duniya ta adalci.—Zabura 37:9-11, 29; 2 Bitrus 3:13.
2. Wane fasali ne na ƙauna Jehovah ya nuna wa waɗanda suka keɓe kansu gare shi?
2 Jehovah yana ƙaunar waɗanda suke bauta masa a hanya mai kyau da daɗewa. Kalmar Ibrananci na “ƙaunar alheri,” ko kuma “ƙaunar aminci” ce take nunin irin wannan ƙaunar. Sarki Dauda na Isra’ila ta dā ya nuna godiya ƙwarai ga ƙaunar alheri na Allah. Saboda abin da ya faru masa da kuma bimbini da yake yi a kan yadda Allah yake bi da mutane, da gaba gaɗi Dauda ya rera: “Ubangiji . . . mai-yawan jinƙai [“ƙaunar alheri,” ko kuma “ƙaunar aminci”].”—Zabura 145:8.
Yadda Za a San Amintattu na Allah
3, 4. (a) Ta yaya Zabura ta 145 ta taimake mu mu san masu aminci na Jehovah? (b) Ta yaya ne masu aminci na Allah suke “albarkace” shi?
3 Uwar annabi Sama’ila, Hannatu, ta faɗi haka game da Jehovah Allah: “Za ya kiyaye sawayen tsarkakansa [“masu amincinsa,” NW ].” (1 Samu’ila 2:9) Su wanene waɗannan “masu aminci”? Sarki Dauda ya ba da amsar. Bayan da ya ɗaukaka kyawawan halayen Jehovah, ya ce: “Tsarkakanka kuma za su albarkace ka.” (Zabura 145:10) Kana iya tunanin ta yaya zai yiwu mutane su yi wa Allah albarka. Yana yiwuwa musamman ta yi masa yabo ko kuma ta yin magana mai kyau game da shi.
4 Ana iya sanin amintattu na Jehovah a yadda suke amfani da bakunansu su yi zancen kirki game da shi. A lokacin liyafa da kuma taron Kirista, menene suke yawan taɗinsa? Hakika, Mulkin Jehovah ne! Amintattun bayin Allah sun yarda da abin da Dauda ya faɗa, da ya rera: “Za su yi zancen ɗaukakar mulkinka [Jehovah], su kama maganar ikonka.”—Zabura 145:11.
5. Ta yaya muka sani cewa Jehovah yana lura sa’ad da amintattunsa suka yi maganar kirki game da shi?
5 Jehovah yana lura kuwa sa’ad da amintattunsa suke yabonsa? E, yana lura da abin da suke faɗa. A cikin wani annabci game da bauta ta gaskiya a zamaninmu, Malachi ya rubuta: “Sa’annan su waɗanda suka ji tsoron Ubangiji suka yi zance da junansu; Ubangiji kuma ya kasa kunne, ya ji, aka rubuta littafin tunawa a gabansa, domin waɗanda su ke jin tsoron Ubangiji, masu-tunawa da sunansa.” (Malachi 3:16) Abin farin ciki ne ƙwarai ga Jehovah sa’ad da amintattunsa suka yi maganar kirki game da shi, yana tuna da su.
6. Waɗanne ayyuka ke taimakawa a san amintattu na Allah?
6 Ana kuma sanin amintattun bayin Jehovah ta wurin gaba gaɗinsu da ɗaukan mataki su yi wa mutane da ba masu bi ba magana game da Allah na gaskiya. Hakika, amintattun Allah “suna sanar ma ’yan Adam ayyukansa masu-iko, da darajar ɗaukaka ta mulkinsa.” (Zabura 145:12) Kana nema kuma kana amfani da zarafi na yin magana da baƙi game da mulkin Jehovah? Mulkinsa madawwami ne ba kamar na ’yan Adam da ba da daɗewa ba zai shuɗe. (1 Timothawus 1:17) Abin gaggawa ne mutane su koya game da mulki mai dawwama na Jehovah kuma suna ɗaukan matsayinsu na goyon bayansa. “Mulkinka madawwamin mulki ne,” in ji Dauda, “sarautarka ta tabbata kuma ta cikin dukan tsararaki.”—Zabura 145:13.
7, 8. Me ya faru a shekara ta 1914, kuma wane tabbaci ne muke da shi cewa yanzu Allah yana sarauta ta wurin Mulkin Ɗansa?
7 Tun shekara ta 1914 an daɗa samun dalili na yin magana game da mulkin Jehovah. A shekarar ce Allah ya kafa Mulkin Almasihu a samaniya da Yesu Kristi, Ɗan Dauda ne, Sarkinsa. Ta haka Jehovah ya cika alkawarinsa na cewa mulkin Dauda zai kahu sosai har abada.—2 Samu’ila 7:12, 13; Luka 1:32, 33.
8 Ana ganin tabbacin cewa Jehovah yanzu yana sarauta ta Mulkin Ɗansa, Yesu Kristi ta wurin cikar alamar bayyanuwarsa. Alama ta musamman ita ce game da aikin da Yesu ya annabta ga dukan amintattun Allah sa’ad da ya ce: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.” (Matta 24:3-14) Domin amintattun Allah suna ƙwazo a cika wannan annabci, mutane fiye da miliyan shida maza, mata, da kuma yara yanzu suna sa hannu a wannan aiki mai girma da ba za a sake yi ba. Ba da daɗewa ba dukan masu hamayya da Mulkin Jehovah za su kai ƙarshensu.—Ru’ya ta Yohanna 11:15, 18.
Amfana Daga Ikon Mallaka na Jehovah
9, 10. Menene ya bambanta Jehovah da ’yan Adam masu mulki?
9 Idan mu Kiristoci da suka keɓe kai ne, dangantakarmu da Ubangiji Jehovah Mai Ikon Mallaka na kawo mana fa’idodi da yawa. (Zabura 71:5; 116:12) Alal misali, domin muna tsoron Allah kuma muna aikata adalci, yana amince da mu kuma muna matso kusa da shi a ruhaniya. (Ayukan Manzanni 10:34, 35; Yaƙub 4:8) Akasin haka, mutane masu sarauta sau da yawa suna tarayya ne da shahararrun mutane, irinsu shugabannin sojoji, masu arziki, ko kuma ’yan liyafa da su shahararru ne. A cikin wata jaridar Afirka ta Sowetan, wani ma’aikacin gwamnati ya faɗi haka game da wuraren da suke talauci a ƙasarsa: “Na gane abin da ya sa yawancinmu ba ma so mu je wuraren nan. Kawai domin ba ma son mu tuna da irin yanayin da ke wuraren ne. Yana damun lamirinmu kuma muna kunyar manyan [motoci] da muke da su.”
10 Hakika, wasu masu mulki suna damuwa da gaske game da lafiyar talakawansu. Amma har sanannu cikinsu ba su san talakawansu sosai ba. Muna iya yin tambaya: Da akwai wani mai mulki ne da yake kula da dukan talakawansa sosai kuma ba ya ɓata lokaci sa’ad da suke bukatar taimako a lokacin wahala? E, akwai. Dauda ya rubuta: “Ubangiji yana talafan dukan waɗanda su ke faɗuwa, yana tada dukan tanƙwararru.”—Zabura 145:14.
11. Wane gwaji amintattun Allah suke fuskanta, kuma wane taimako suke samu?
11 Amintattu na Jehovah Allah suna fuskantar gwaji da kuma masifu da yawa saboda ajizancinsu domin suna cikin duniya da take kwanciya cikin ikon mugun, “Shaiɗan.” (1 Yohanna 5:19; Zabura 34:19) Kiristoci suna shan tsanani. Wasu suna shan wahalar ciwo ko kuma baƙin cikin rasuwa. A wasu lokatai, kuskuren da amintattun Jehovah suke yi yana sa su ‘tanƙwara’ domin sanyin gwiwa. Amma, ko da wane irin gwaji ne ya same su Jehovah a shirye yake ya yi musu ta’aziyya kuma ya ba kowannensu ƙarfi a ruhaniya. Haka ma, Sarki Yesu Kristi yake damuwa da talakawansa amintattu.—Zabura 72:12-14.
Abinci Mai Gamsarwa a Lokacinsa
12, 13. Ta yaya Jehovah yake tanadin bukatun “kowanne mai-rai”?
12 Saboda yawan ƙaunarsa ta alheri, Jehovah ya yi tanadin dukan bukatun bayinsa. Wannan ya haɗa da ba su abinci na gina jiki. Sarki Dauda ya ce: “Idanun dukan mutane suna sauraro a gareka [Jehovah]; Kana kuwa ba su abincinsu a kan kari. Kana buɗe hannunka, kana biya ma kowane mai-rai muradinsa.” (Zabura 145:15, 16) Har a lokacin bala’i ma, Jehovah yakan sarrafa al’amura domin amintattunsa su samu “abincin yini.”—Luka 11:3; 12:29, 30.
13 Dauda ya ambata cewa “kowane mai-rai” za a gamsar da shi. Wannan ya haɗa da dabbobi. Da ba domin yawan ire-iren tsiron ƙasa da tsiron teku ba, rayukan cikin ruwa, tsuntsaye, da kuma dabbobi ba za su sami iskar sheƙa ko abin ci ba. (Zabura 104:14) Amma Jehovah yana musu tanadin dukan bukatunsu.
14, 15. Ta yaya ake tanadin abinci na ruhaniya a yau?
14 ’Yan Adam suna da bukata ta ruhaniya ba kamar dabbobi ba. (Matta 5:3) Dubi yadda Jehovah yake tanadin bukata ta ruhaniya ga amintattunsa! Kafin mutuwarsa, Yesu ya yi wa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” alkawari cewa zai yi wa mabiyan Yesu tanadin “abincinsu a lotonsa.” (Matta 24:45) Wannan raguwar shafaffu 144,000 sune ajin bawan a yau. Ta wurinsu, Jehovah ya yi tanadin abinci na ruhaniya a yalwace.
15 Alal misali, yawancin mutanen Jehovah yanzu suna moran fassara mai kyau na Littafi Mai Tsarki a yarensu. New World Translation of the Holy Scriptures ta zama albarka ta ƙwarai! Ban da haka ma, ana ci gaba da buga abubuwan taimako na yin nazarin Littafi Mai Tsarki da yawa a harsuna sama da 300. Dukan wannan abinci na ruhaniya albarka ce ga masu bauta ta gaskiya a duniya kewaye. Wa za a yaba wa domin dukan wannan? Jehovah Allah ne. Ta wurin ƙaunarsa ta alheri, ya zama da sauƙi wa ajin bawan ya yi tanadin “abinci a lotonsa.” Ta wurin tanadin nan, ana iya “biya ma kowane mai-rai muradinsa” a wannan aljanna ta ruhaniya na zamani. Lallai kuwa bayin Jehovah suna farin ciki a begen ganin cewa ba da daɗewa ba duniya za ta zama aljanna ta zahiri!—Luka 23:42, 43.
16, 17. (a) Waɗanne misalai ne na abinci na ruhaniya da ke zuwa a lotonsa? (b) Ta yaya Zabura ta 145 ta furta yadda amintattu na Allah suke ji game da batu na musamman da Shaiɗan ya tayar?
16 Ka yi la’akari da misalin abinci na ruhaniya da ake samu a lotonsa. A shekara ta 1939, aka soma Yaƙin Duniya na II a Turai. A shekarar ce talifi a kan “Tsaka-Tsaki” ya fito cikin fitar Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba. Saboda bayani sarai da aka yi, Shaidun Jehovah a duniya kewaye sun ga bukatar su yi tsaka-tsaki a harkokin al’ummai da suke yaƙi. Wannan ya sa gwamnati su yi fushi da ya jawo fāɗa na shekaru shida ɗin. Duk da cewa an yi musu hani kuma an tsananta musu, amintattu na Allah sun ci gaba da yin wa’azin bisharar Mulkin. An albarkace su da ƙaruwa kashi 157 daga shekara ta 1939 zuwa 1946. Ban da haka, labarin kasancewa da aminci a lokacin yaƙin ya ci gaba da taimakon mutane su san addini na gaskiya.—Ishaya 2:2-4.
17 Abinci na ruhaniya da Jehovah yake tanadinsa ba kawai yana zuwa a kan lokaci ba, amma kuma mai gamsarwa ne. Ko da yake al’ummai suna cikin yaƙi sosai a Yaƙin Duniya na II, an taimaki mutanen Jehovah su mai da hankali ga wani abin da ya fi muhimmanci da nasu ceto. Jehovah ya taimake su su fahimci batu na musamman, da ya shafi dukan sararin halitta game da ikon mallaka ta Jehovah. Abin gamsarwa ne mu sani cewa ta wurin amincin kowanne Mashaidin Jehovah, ya ɗan sa hannu a kunita ikon mallaka na Jehovah da kuma mai da Iblis maƙaryaci! (Misalai 27:11) Ba kamar Shaiɗan ba ne da ya tsegunta Jehovah da hanyar sarautarsa, amintattu na Jehovah suna ci gaba da sanarwa a fili: “Ubangiji mai-adalci ne cikin dukan tasarrufinsa.”—Zabura 145:17.
18. Wane misali ne na kwanan bayan nan na abinci na ruhaniya da ke zuwa a lotonsa kuma mai gamsarwa?
18 Wani misalin abinci a lotonsa mai gamsarwa shi ne littafin nan Ka Kusaci Jehovah, da aka fito da shi a ɗarurruwan Taron Gunduma na “Masu Shelar Mulki da Himma” da aka yi a shekara ta 2002-2003. Wannan littafin da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” suka fito da shi da Shaidun Jehovah suka buga, littafin game da halayen Jehovah Allah ne na ban sha’awa, har da waɗanda aka ambata a Zabura ta 145. Wannan littafi mai kyau lallai yana da muhimmanci a taimaka wa amintattu na Allah su matsa kusa wurinsa.
Lokaci da Za a Fi Kusa da Jehovah
19. Wane lokaci ne na musamman da ke matso kusa, kuma ta yaya za mu bi da shi?
19 Mataki na musamman da za a bi na warware batun ikon mallaka na Jehovah shi ne a matsa kusa da shi. Kamar yadda aka annabta a Ezekiel sura ta 38, ba da daɗewa ba Shaiɗan zai gama aikinsa na “Gog na ƙasar Magog.” Wannan zai haɗa da farmaki a kan mutanen Jehovah a dukan duniya. Shaiɗan ne zai yi ƙoƙarin ya ɓata amincin amintattu na Allah a dukan duniya. Fiye da dā, masu bauta wa Jehovah suna bukatar su biɗe shi da dukan zuciya, har ma su nemi taimako. Tsoron Allah da suke yi da kuma ƙaunarsa na banza ne? A’a, Zabura ta 145 ta ce: “Ubangiji yana kusa da dukan waɗanda su ke kira bisa gareshi, ga dukan waɗanda su ke kira gareshi da gaskiya. Za ya biya muradin waɗanda ke tsoronsa; Za ya kuma ji kukarsu, ya cece su. Ubangiji yana kiyayadda dukan waɗanda ke ƙaunarsa; Amma za ya halaka dukan miyagu.”—Zabura 145:18-20.
20. Ta yaya kalmomin Zabura 145:18-20 za su cika a nan gaba kusa?
20 Abin farin ciki ne mu shaida yadda Jehovah yake kusa da mu da ikonsa na ceto sa’ad da zai halaka miyagu! Wannan lokaci na musamman da ya yi kusa yanzu, Jehovah zai saurari “waɗanda su ke kira gareshi da gaskiya.” Babu shakka ba zai saurari masu riya ba. Kalmar Allah ta nuna sarai cewa duk wani kiran sunansa da miyagu za su yi da gaggawa zai zama banza.—Misalai 1:28, 29; Mikah 3:4; Luka 13:24, 25.
21. Ta yaya amintattu na Jehovah suke nuna cewa suna farin cikin yin amfani da sunan Allah?
21 Yanzu fiye da dā shi ne lokaci domin waɗanda suke jin tsoron Jehovah su “kira gareshi da gaskiya.” Amintattunsa suna farin ciki a yin amfani da sunansa cikin addu’o’insu kuma cikin kalamin da suke yi a taro. Suna yin amfani da sunan Allah ma a taɗinsu. Kuma suna sanar da sunan Jehovah da gaba gaɗi a hidimarsu ta fage.—Romawa 10:10, 13-15.
22. Me ya sa yake da muhimmanci mu ci gaba da tsayayya wa halayen duniya da kuma sha’awoyi?
22 Don mu ci gaba da amfana daga dangantaka ta kusa da Jehovah Allah, yana da muhimmanci mu ci gaba da yin tsayayya da abubuwan da suke na suƙuƙucewa ne a ruhaniya, irin su son abin duniya, mugun nishaɗi, halin ƙin gafartawa, ko kuma rashin damuwa da mabukata. (1 Yohanna 2:15-17; 3:15-17) Idan ba a lura ba, irin halayen nan da biɗe-biɗe za su sa mutum zunubi kuma ya yi rashin amincewar Jehovah. (1 Yohanna 2:1, 2; 3:6) Matakin hikima ce a tuna cewa Jehovah zai ci gaba da nuna ƙaunarsa ta alheri, ko ƙauna ta aminci, gare mu idan muka kasance da aminci gare shi.—2 Samu’ila 22:26.
23. Wane zato mai girma dukan amintattun Allah suke jira a nan gaba?
23 To, bari mu riƙa zaton abin da dukan amintattu na Jehovah suke jira a nan gaba. Ta yin haka, muna da zato mai girma na kasance cikin waɗanda za su ɗaukaka Jehovah, su yi masa albarka, su kuma yabe shi “kowacce rana” kuma “har abada abadin.” (Zabura 145:1, 2) Saboda haka, bari mu ‘tsare kanmu cikin ƙaunar Allah, muna sauraron rai na har abada.’ (Yahuda 20, 21) Da muke ci gaba da amfana daga halaye masu girma na Ubanmu na samaniya, haɗe da yawan ƙauna ta alheri da yake nuna wa waɗanda suke ƙaunarsa, bari furcinmu na kullum ya zama kamar wanda Dauda ya faɗi a Zabura ta 145: “Bakina za ya faɗi yabon Ubangiji; Bari dukan abu mai-rai kuma shi albarkaci sunansa mai-tsarki har abada abadin.”
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya Zabura ta 145 ta taimaka a yadda za a san amintattun Allah?
• Ta yaya Jehovah yake ‘gamsar da muradin kowane abu mai-rai’?
• Me ya sa muke bukatar mu matsa kusa da Jehovah?
[Hoto a shafi na 9]
Amintattun Allah suna farin ciki a yin taɗin manyan ayyukansa
[Hoto a shafi na 10]
Bayin Jehovah da gaba gaɗi suna taimakon baƙi su koya game da ɗaukakar mulkinsa
[Hotuna a shafi na 11]
Jehovah yana tanadin abinci ga “kowane mai-rai”
[Inda aka Dauko]
Dabbobi: Parque de la Naturaleza de Cabárceno
[Hoto a shafi na 12]
Jehovah yana ba da ƙarfi da kāriya ga amintattunsa da suke neman taimakonsa ta wurin addu’a