DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | HOSIYA 1-7
Jehobah Yana Son Nuna Ƙauna da Aminci, Kai Fa?
Riƙon amana da nagarta da kuma aminci ne ke sa mu nuna irin wannan halin. Jehobah ya yi amfani da misalin Hosiya da matarsa marar aminci mai suna Gomer wajen koyar da darasi a nuna aminci, ƙauna da kuma gafartawa.—Ho 1:2; 2:7; 3:1-5.
Ta yaya Gomer ta nuna rashin aminci da ƙauna?
Ta yaya Isra’ilawa suka nuna rashin aminci da ƙauna?
Ta yaya Hosiya ya nuna aminci da ƙauna?
Ta yaya Jehobah ya nuna aminci da ƙauna?
DON BIMBINI: Ta yaya zan nuna aminci da ƙauna ga Jehobah?