Ka Tsare Kanka Daga Ruɗu
“Ku yi hankali kada kowa shi same ku ta wurin iliminsa da ruɗinsa na banza.”—KOLOSSIYAWA 2:8.
1-3. (a) Waɗanne misalai suka nuna cewa ruɗu yana shafan kusan kowanne fasalin rayuwar yau da kullum? (b) Me ya sa ba za mu yi mamakin ruɗu da ke duniya ba?
“KU NAWA ne masu neman hidima ba su taɓa yi wa ƙarya ba?” Wani shehun lauya ne ya yi wannan tambayar, da ya yi wani bincike shekarun baya. Mecece amsar? Ya bayyana: “A cikin dubban lauyoyi, ɗaya ne kawai masu neman hidima ba su yi wa ƙarya ba.” Me ya sa? “Saboda bai daɗe ba da lauyan ya soma aiki a babban ma’aikata kuma bai yi magana ba tukuna da masu neman hidimarsa.” Wannan labari na baƙin ciki—ƙarya da ruɗu ruwan dare gama gari ne a duniyar yau.
2 Ruɗu fasaloli dabam dabam suke kuma suna shafan kusan kowanne fannin rayuwan zamani. Waɗannan misalai sun cika labarai—’yan siyasa suna ƙarya game da abin da suke yi, ’yan akanta da lauyoyi suna ƙara kuɗinsu, masu talla suna ruɗin masu ciniki, masu kai kara suna cucin kamfanonin inshora, kaɗan kawai ke nan cikinsu. Sai kuma ruɗun addini. Limamai suna ruɗin jama’a ta wurin koya musu ƙarya, kamar su kurwa marar mutuwa, wutar jahannama, da kuma ra’ayin Allah-Uku-Cikin Ɗaya.—2 Timothawus 4:3, 4.
3 Za mu yi mamakin dukan waɗannan ruɗu ne? Ba sosai ba. Game da “kwanaki na ƙarshe,” Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi: “Miyagun mutane da masu-hila za su daɗa mugunta gaba gaba, suna ruɗi, ana ruɗinsu.” (2 Timothawus 3:1, 13) Mu Kiristoci, muna bukatar mu kasance a faɗake game da ra’ayin ruɗu da zai iya sa mu bijire daga gaskiya. A kan yi tambayoyin nan: Me ya sa ruɗu ke ko’ina a yau, kuma ta yaya za mu tsare kanmu daga ruɗu?
Me Ya Sa Akwai Ruɗu da Yawa Haka a Duniya?
4. Yaya Littafi Mai Tsarki ya bayyana dalilin da ya sa ruɗu yake ko’ina a duniya?
4 Littafi Mai Tsarki ya bayyana sarai dalilin da ya sa akwai ruɗu a ko’ina a wannan duniyar. Manzo Yohanna ya rubuta cewa “duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” (1 Yohanna 5:19) “Shaiɗan” shi ne mugun. Yesu ya faɗa game da shi haka: “Ba ya tsaya a kan gaskiya ba, domin babu gaskiya a cikinsa. Sa’anda ya ke yin ƙarya, don kansa ya ke yi: gama maƙaryaci ne shi, da uban ƙarya kuma.” Abin mamaki ne da wannan duniya take da halaye, daraja, da kuma ruɗu na mai sarautarta?—Yohanna 8:44; 14:30; Afisawa 2:1-3.
5. Ta yaya Shaiɗan yake daɗa ƙoƙarinsa na ruɗu a wannan lokaci na ƙarshe, kuma wa yake nema musamman?
5 A cikin wannan kwanaki na ƙarshe, Shaiɗan yana daɗa ƙoƙarinsa. An jefar da shi zuwa duniya. Ya sani cewa lokacinsa gajere ne, yana “hasala mai-girma.” Domin ya ƙudura ya janye mutane da yawa, ya sa ya zama “mai-ruɗin dukan duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9, 12) Shaiɗan ba ya ruɗinsa a wasu lokatai kawai ba. Ba ya gajiya a ƙoƙarinsa na ruɗin mutane.a Yana amfani da kowane fasalin ruɗu ya zama makaminsa—har da maguɗi da cin amana—don ya makantar da azantan marasa bi kuma ya hana su zuwa wajen Allah. (2 Korinthiyawa 4:4) Wannan shugaban ruɗu yana ƙoƙari musamman a son cinye waɗanda suke bauta wa Allah “cikin ruhu da cikin gaskiya.” (Yohanna 4:24; 1 Bitrus 5:8) Kada ka manta cewa Shaiɗan ya yi da’awar cewa: ‘Zan iya juyar da kowa daga Allah.’ (Ayuba 1:9-12) Bari mu yi la’akari da wasu “kissoshin” Shaiɗan da yadda za mu tsare kanmu game da su.—Afisawa 6:11, Littafi Mai Tsarki duk da Afokirifa.
Ka Tsare Kanka Daga Ruɗun ’Yan Ridda
6, 7. (a) Wace da’awa ’yan ridda suke yi? (b) Ta yaya Nassosi suka nuna sarai abin da ’yan ridda suke so?
6 Da daɗewa Shaiɗan yana amfani da ’yan ridda a ƙoƙarinsa ya rinjayi bayin Allah. (Matta 13:36-39) ’Yan ridda suna iya da’awar suna bauta wa Jehovah kuma cewa sun gaskata Littafi Mai Tsarki, amma suna ƙi da ƙungiyarsa ta duniya. Wasu ma suna koma son koyarwa ta “Babila Babba,” daular duniya na addinin ƙarya. (Ru’ya ta Yohanna 17:5; 2 Bitrus 2:19-22) Ta wurin hurewar Allah, marubutan Littafi Mai Tsarki sun yi amfani da kalmomi masu ƙuna su fallasa manufa da kuma hanyoyin ’yan ridda.
7 Menene ’yan ridda suke nema? Da yawansu ba sa son su bi imanin da suka yi a dā ba game da gaskiya. Sau da yawa, suna son wasu su bi su. Maimakon su su je su nemi nasu almajiran, ’yan ridda da yawa suna neman “janye masu-bi [wato, almajiran Kristi] bayansu.” (Ayukan Manzanni 20:29, 30) Game da masu koyarwan ƙarya, manzo Bulus ya ba da gargaɗi na gaggawa: “Ku yi hankali kada kowa shi same ku.” (Kolossiyawa 2:8) Wannan bai bayyana abin da ’yan ridda da yawa suke ƙoƙarin yi ba ne? Kamar wanda ya saci wani, ’yan ridda suna cin amanar waɗanda suke cikin ikilisiya da suke amince da su, suna neman su janye su daga garken.
8. Waɗanne hanyoyi ’yan ridda suke amfani da su su cim ma nufinsu?
8 Waɗanne hanyoyi ’yan ridda suke amfani da su don su cim ma abin da suke nema? Sau da yawa suna amfani da karkacewa, gaskiya rabi da rabi, da kuma ƙarya. Yesu ya sani cewa waɗanda suke “kowacce muguwar ƙarya” za su kama mabiyansa. (Matta 5:11, Today’s English Version) Irin waɗannan ’yan adawa za su yi ƙarya da niyyar su ruɗi wasu. Manzo Bitrus ya yi gargaɗi game da ’yan ridda da suke amfani da “maganganun rikici,” suna yaɗa ‘koyarwar ruɗu,’ kuma suna ‘daguladda Nassosi’ domin nasu riba. (2 Bitrus 2:3, 13; 3:16) Abin baƙin ciki kuwa, ’yan ridda suna nasara a “jirkitadda bangaskiyar waɗansu.”—2 Timothawus 2:18.
9, 10. (a) Ta yaya za mu tsare kanmu daga ruɗun ’yan ridda? (b) Me ya sa ba ma damuwa idan fahiminmu na ƙudurin Allah yana bukatar gyara?
9 Ta yaya za mu tsare kanmu kada ’yan ridda su ruɗe mu? Ta wurin bin shawarar Kalmar Allah, da ta ce: “Ku maida hankali ga waɗanda ke zama sanadin tsatsaguwa da dalilin tuntuɓe, saɓanin koyarwa da kuka samu: ku bijire musu.” (Romawa 16:17) Za mu “bijire musu” ta wurin ƙi da zancen—ko muna ganin mutumin ne, ko a rubuce, ko kuma cikin Intane. Me ya sa za mu ɗauki wannan matsayin? Da farko, domin Kalmar Allah ya ce mu yi hakan, kuma mun amince da Jehovah cewa yana son abu mafi kyau dominmu.—Ishaya 48:17, 18.
10 Na biyu, muna ƙaunar ƙungiyar da ta koyar da gaskiya mai tamani sarai da ta ware mu daga Babila Babba. Har ila kuma, mun tabbata cewa saninmu game da ƙudurin Allah ba cikakke ba ne; an yi gyara a fahiminmu na shekaru yanzu. Kiristoci masu aminci sun so su jira Jehovah domin irin gyaran nan. (Misalai 4:18) Har yanzu, ba za mu yi banza da ƙungiyar da Allah yake jin daɗin amfani da ita ba, domin mun ga tabbaci na sarai, albarkarsa a kanta.—Ayukan Manzanni 6:7; 1 Korinthiyawa 3:6.
Ka Tsare Kanka Daga Ruɗin Kanka
11. Me ya sa mutane ajizai suke da nufin su ruɗi kansu?
11 Mutane ajizai suna da wani nufi da Shaiɗan yake saurin zaluntawa—ruɗin kanmu. “Zuciya ta fi kome rikici, ciwuta gareta ƙwarai irin ta fidda zuciya: wa za ya san ta?” in ji Irmiya 17:9. Kuma Yaƙub ya rubuta: “Kowanne mutum ya jarabtu, sa’anda sha’awatasa ta janye shi, ta yi masa tarko.” (Yaƙub 1:14) Idan zuciyarmu ta jarabtu, zunubi na son ya jarabce mu ke nan, yana sa ya zama da kyau kuma marar lahani. Irin ra’ayin nan na ruɗu ne, domin fāɗa wa zunubi yana jawo halaka.—Romawa 8:6.
12. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya fāɗa wa tarkon ruɗin kanmu?
12 Yana da sauƙi mu fāɗa cikin tarkon ruɗin kanmu. Zuciya rikici gare ta da za ta iya ƙasƙanta wani lahani da muke da shi, ta neman hujja wa zunubi mai tsanani. (1 Samu’ila 15:13-15, 20, 21) Zuciyarmu mai rikici ma za ta nemi hujjar wasu halaye. Alal misali, batun nishaɗi. Wasu nishaɗi suna da kyau kuma da daɗin yi. Amma, yawancin abin da wannan duniyar take yi—tsarin siliman da telibijin da kuma a Intane—marasa tsarki ne kuma na lalata. Yana da sauƙi mu tabbatar da kanmu cewa za mu iya kallon nishaɗi marasa kyau ba tare da lahani ba. Wasu ma suna tunanin cewa, “ba ruwana idan bai dami lamirina ba?” Amma irin mutanen nan suna ‘ruɗin kansu ta wurin yaudara.’—Yaƙub 1:22.
13, 14. (a) Wane misali na Nassi ne ya nuna cewa lamirinmu ba kullum yake bishe mu daidai ba? (b) Ta yaya za mu tsare kanmu daga ruɗin kanmu?
13 Ta yaya za mu tsare kanmu daga ruɗin kanmu? Da farko, muna bukatar mu tuna cewa ba kullum ake iya tabbata da lamirin ’yan Adam ba. Ka bincika yanayin manzo Bulus. Kafin ya zama Kirista, ya tsananta wa mabiyan Kristi. (Ayukan Manzanni 9:1, 2) Ƙila lamirinsa ma bai dame shi ba a lokacin. Hakika, domin ba shi a kan hanya. “Da rashin sani na yi shi cikin rashin bangaskiya,” in ji Bulus. (1 Timothawus 1:13) Saboda haka, batun cewa wasu nishaɗi ba su dami lamirinmu ba ba ya nufin ba mu kuskura ba. Lamiri ne mai lafiya da Kalmar Allah ta koyar yake kāriya mai kyau.
14 Idan za mu guje wa ruɗin kanmu, da akwai wasu shawarwari masu taimakawa da muke bukatar mu tuna da su. Ka bincika kanka ta wurin addu’a. (Zabura 26:2; 2 Korinthiyawa 13:5) Idan muka bincika kanmu sarai za mu iya ganin bukatar mu yi wasu canji a ra’ayinmu ko hanyoyi. Ka saurari wasu. (Yaƙub 1:19) Tun da yake za mu iya bincika ra’ayinmu, zai yi kyau ma mu saurari kalmomin wasu ’yan’uwa Kiristoci da suka ƙware. Idan ka iske ka tsai da shawara ko kuma kana ayyuka da wasu ’yan’uwa masu bi da suka ƙware suke ganin bai dace ba, ka yi wa kanka tambaya, ‘Ban koyar da lamiri na da kyau ba ne ko kuma zuciya ta tana ruɗi na ne?’ Ka ciyar da kanka a kai a kai daga littattafai na Littafi Mai Tsarki. (Zabura 1:2) Yin haka zai taimake ka ka tsare tunaninka, halaye, da yadda kake ji su jitu da ƙa’idodin ibada.
Ka Tsare Kanka Daga Ƙaryace-Ƙaryacen Shaiɗan
15, 16. (a) A ƙoƙarinsa don ya ruɗe mu, waɗanne ƙaryace-ƙaryace Shaiɗan yake amfani da su? (b) Ta yaya za mu guje kada a ruɗe mu da waɗannan ƙaryace-ƙaryace?
15 Shaiɗan yana amfani da ƙaryace-ƙaryace a ƙoƙarce-ƙoƙarcensa ya ruɗe mu. Yana ƙoƙarin ya tabbatar da mu cewa abubuwan mallaka suna kawo farin ciki da kuma gamsarwa, amma ba haka yake da gaske ba. (Mai-Wa’azi 5:10-12) Yana son mu tabbata cewa wannan muguwar duniya za ta ci gaba har abada, ko da a bayyane yake cewa muna cikin “kwanaki na ƙarshe.” (2 Timothawus 3:1-5) Shaiɗan yana ƙarfafa ra’ayin cewa babu wani lahani a yin rayuwa ta lalata, ko da yake ma masu biɗan annashuwa suna shan mugun sakamako. (Galatiyawa 6:7) Ta yaya za mu guje kada a ruɗe mu da irin waɗannan ƙaryace-ƙaryacen?
16 Ka amfana daga misalan Littafi Mai Tsarki. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da misalan gargaɗi da yawa na mutane da ƙaryan Shaiɗan ya ruɗe su. Sun so abin duniya, suna kasa fahimtar yanayin da suke ciki a lokacin, ko kuma sun ba da kansu ga lalata—dukansu sun sha mugun sakamako. (Matta 19:16-22; 24:36-42; Luka 16:14; 1 Korinthiyawa 10:8-11) Ka koya daga misalai na zamani. Abin baƙin ciki kuwa, wasu lokaci Kiristoci sukan manta da yanayin gaggawa kuma su gaskata da cewa bauta wa Allah da suke yi suna hasarar wani abu. Suna iya barin gaskiya domin su biɗi rayuwa ta annashuwa. Amma, irin waɗannan mutane suna “wurare masu-santsi,” domin ba da daɗewa ba sukan sha mugun sakamakon halayensu na rashin ibada. (Zabura 73:18, 19) Abin hikima ne idan muka koya daga kuskuren da wasu suka yi.—Misalai 22:3.
17. Me ya sa Shaiɗan yake gabatar da ƙaryar cewa Jehovah ba ya sonmu kuma ba ya daraja mu?
17 Da akwai kuma wata ƙarya da Shaiɗan yake amfani da ita sosai—ƙaryar cewa Jehovah ba ya sonmu kuma ba ya daraja mu. Shekaru dubbai yanzu da Shaiɗan yake nazarin mutane ajizai. Ya sani sarai cewa sanyin gwiwa na iya raunana mu. (Misalai 24:10) Saboda haka, yana ƙarfafa ƙaryar cewa ba mu da daraja a gaban Allah. Idan aka ‘yasar’ da mu kuma muka tabbata cewa Jehovah ba ya damuwa da mu, za mu iya kasala. (2 Korinthiyawa 4:9) Abin da babban Mai Ruɗi yake so ke nan! To, ta yaya za mu tsare kanmu daga wannan ruɗun Shaiɗan?
18. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya tabbatar da mu game da ƙaunar Jehovah?
18 Ka yi bimbini a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da ƙaunar Allah gare mu. Kalmar Allah ta yi amfani da wasu kwatanci don ta tabbatar da mu cewa Jehovah yana ganinmu kuma yana ƙaunar kowannenmu. Yana sa hawayenka cikin ‘gorarsa,’ yana nufin cewa yana gani kuma yana tuna da hawayen da muke yi a ƙoƙarin mu kasance da aminci. (Zabura 56:8) Ya san lokacin da kake da ‘karyayyar zuciya,’ kuma yana zuwa kusa da kai a lokacin. (Zabura 34:18) Ya san kome game da kai, har da yawan ‘gasussuwan kanka.’ (Matta 10:29-31) Mafi muhimmanci ma, Allah ya “ba da Ɗansa, haifaffe shi kaɗai” dominka. (Yohanna 3:16; Galatiyawa 2:20) A wasu lokatai, zai zama da wuya ka yarda cewa kana iya amfani da waɗannan nassosi wa kanka. Hakika ya kamata mu amince da abin da Jehovah ya faɗi. Yana son mu gaskata cewa yana ƙaunarmu, ba a rukuni kawai ba amma kowannenmu.
19, 20. (a) Me ya sa yake da muhimmanci ka fahimci kuma ƙi ƙaryar Shaiɗan na cewa Jehovah ba ya ƙaunarka? (b) Ta yaya wani mai kula mai ziyara ya taimaki wasu da suka raunana?
19 Ka gano kuma ka ƙi ƙarya. Idan ka sani wani yana ƙarya za ka iya tsare kanka don kada ya ruɗe ka. Saboda haka, sanin cewa Shaiɗan dai yana son ka gaskata da ƙaryar nan cewa Jehovah ba ya ƙaunarka abin taimako ne ƙwarai. Wani Kirista da yake magana game da wani talifi na Hasumiyar Tsaro, game da dabarun Shaiɗan, ya ce: “Ban taɓa sanin cewa Shaiɗan yana amfani da jiye-jiye don ya raunana ni ba. Sanin wannan ya sa na iya sha kan jiye-jiyen nan.”
20 Ka yi la’akari da labarin wani mai kula mai ziyara a wata ƙasar Amirka ta Kudu. Sa’ad da yake ziyarar kiwo wajen ’yan’uwa masu bi da suka raunana, yakan tambaye su, ‘Ka gaskata da Allah-Uku-Cikin-Ɗaya?’ Raunanin yakan ce, ‘Sam,’ domin ya sani cewa wannan ɗaya ne cikin ƙaryan Shaiɗan. Sai dattijo mai ziyarar ya sake tambaya, ‘Ka gaskata da wutar jahannama?’ Sai mutumin ya ce, ‘A’a, sam!’ Sai dattijo mai ziyara ya ce musu, da akwai wata ƙaryar Shaiɗan da bai da sauƙi a gane ta. Sai ya jawo hankalinsu zuwa shafi 249, sakin layi na 21, na littafin nan Ka Kusaci Jehovah,b da ya fallasa ƙaryar cewa Jehovah ba ya ƙaunar kowannenmu ba. Mai kula mai ziyarar ya sami sakamako mai kyau ta wurin amfani da wannan a taimaka wa waɗanda suka raunana don su ƙi da ƙaryar Shaiɗan.
Ka Tsare Kanka Daga Yin Ƙarya
21, 22. Me ya sa ba ma rashin sanin dabarun ruɗu na Shaiɗan ba, kuma me ya kamata ya zama ƙudurinmu?
21 A ƙarshen wannan kwanaki na ƙarshe, da zaton cewa Shaiɗan zai ci gaba da ƙaryace-ƙaryace da kuma ruɗu. Abin godiya, Jehovah bai ƙyale mu cikin rashin sanin dabarun Shaiɗan ba. Littafi Mai Tsarki da littattafan “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” daga Littafi Mai Tsarki ya fallasa mugun hanyoyin Iblis. (Matta 24:45) Gargaɗin da ake mana domin mu kasance da shiri ne.—2 Korinthiyawa 2:11.
22 Bari mu tsare kanmu daga tunani da ’yan ridda suke yi. Bari mu ƙudura niyar mu guje wa tarkon ruɗun kai. Bari mu gane kuma mu ƙi dukan ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan. Ta yin haka, za mu tsare dangantakarmu da “Allah na gaskiya,” da ya ƙi ruɗu.—Zabura 31:5; Misalai 3:32.
[Hasiya]
a Game da siffar aikatau da aka fassara ‘ruɗi’ a Ru’ya ta Yohanna 12:9, wata majiya ta ce “yana nuna abin da ake ci gaba da yi ne ya zama halin mutum.”
b Shaidun Jehovah ne suka buga.
Ka Tuna?
• Me ya sa da akwai ruɗi a duniya a yau?
• Ta yaya za mu tsare kanmu kada ’yan ridda su ruɗe mu?
• Ta yaya za mu tsare kanmu daga nufin ruɗin kanmu?
• Ta yaya za mu guje fāɗa wa ƙaryar Shaiɗan?
[Hoto a shafi na 15]
Kada ka ruɗi kanka game da nishaɗi
[Hotuna a shafi na 16]
Don ka tsare kanka daga ruɗin kanka, ka bincika ta wurin addu’a, ka saurari wasu, kuma ka ciyar da kanka a kai a kai ta wurin Kalmar Allah