Za Ka Saurari Gargaɗin Jehobah Kuwa?
“Wannan ita ce hanya, ku bi ta.”—ISHA. 30:21.
1, 2. Mene ne Shaiɗan ya ƙuduri aniyar yi, kuma yaya Kalmar Allah ta taimaka mana?
SA’AD DA kake tafiya a kan hanya, alamar da ke nuna hanyar da ba ta dace ba za ta iya ɓatar da kai kuma hakan zai iya kasance da haɗari. A ce wani aboki ya yi maka gargaɗi cewa wani mugu ya canja alamar hanyar domin yana son mutane su ɓace. Babu shakka za ka saurari gargaɗin abokinka.
2 Babu shakka, Shaiɗan mugun maƙiyi ne da ya ƙuduri aniyar ɓatar da mu. (R. Yoh. 12:9) Shaiɗan yana amfani da dukan haɗarurruka da muka tattauna a talifin da ya gabata don ya sa mu yi wa Jehobah rashin biyayya kuma mu bijire daga hanyar rai madawwami. (Mat. 7:13, 14) Amma mun kuma koya cewa abokinmu Jehobah Allah ya gargaɗe mu game da dabarun Shaiɗan. Yanzu bari mu tattauna ƙarin abubuwa uku da Shaiɗan yake amfani da su don ya yaudare mu. Sa’ad da muka karanta Littafi Mai Tsarki, za mu iya zana hoton zuci cewa Jehobah yana tafiya a bayanmu kuma yana cewa: “Wannan ita ce hanya, ku bi ta.” (Isha. 30:21) Yayin da muke nazarin waɗannan gargaɗin da ke a bayane, za mu fi ƙudurta mu yi abin da Jehobah ya faɗa.
Kada Ka Bi “Masu-Ƙaryan Malanta”
3, 4. (a) Ta yaya malaman ƙarya suke kama da rijiyoyi da babu ruwa a ciki? (b) Daga ina ne malaman ƙarya suka fito, kuma mene ne suke so?
3 A ce kana tafiya kuma ka bi ta hamada, sai ka soma ƙishirwa. Sai ka hangi rijiya daga nesa, kana ganin za ka sami ruwa a ciki. Amma sa’ad da ka isa rijiyar sai ka ga babu ruwa a ciki. Sai ka yi baƙin ciki! Malaman ƙarya suna kama da rijiyoyi da babu ruwa a ciki. Mutanen da suke ganin cewa malaman ƙarya suna da gaskiya za su fid da rai. Ta wurin manzo Bulus da Bitrus Jehobah ya yi mana gargaɗi game da malaman ƙarya. (Karanta Ayyukan Manzanni 20:29, 30; 2 Bitrus 2:1-3.) Su waye ne waɗannan malaman ƙaryan? Kalaman Bulus da Bitrus sun gaya mana inda waɗannan malaman ƙaryan suka fito da kuma yadda suke rinjayar mutane.
4 Bulus ya gaya wa dattawan da ke ikilisiyar Afisa cewa: “Daga cikin tsakiyarku kuma mutane za su tashi, suna faɗin karkatattun zantattuka.” Da yake magana da ’yan’uwansa Kiristoci Bitrus ya rubuta: “Masu-ƙaryan malanta za su kasance kuma a cikinku.” Malaman ƙarya suna iya fitowa daga cikin ikilisiya. Waɗannan malaman ’yan ridda ne.a Mene ne suke so? Bulus ya bayyana cewa sa’ad da suka bar ƙungiyar Jehobah, suna son “su janye masu-bi bayansu.” Almajiran da Bulus yake maganarsu sune almajiran Yesu Kristi. Waɗannan malaman ƙarya ba sa neman nasu almajirai a wani wuri sai a cikin ikilisiya. Suna ƙoƙari su ɗauki, ko kuma su saci almajirai daga cikin ikilisiya. Yesu ya ce ’yan ridda suna kama da kerketai masu cin tumaki. ’Yan ridda suna neman su halaka bangaskiyar ’yan’uwa da suke cikin ikilisiya kuma suna son ’yan’uwa su bar bin gaskiya.—Mat. 7:15; 2 Tim. 2:18.
5. Ta yaya malaman ƙarya suke ruɗin mutane?
5 Ta yaya malaman ƙarya suke rinjayar mutane? Suna yin hakan da wayo. ’Yan ridda suna shigo da nasu ra’ayoyi cikin ikilisiya da “wayo,” kamar masu aikata laifofi da suke shigo da abubuwa cikin ƙasa a ɓoye. ’Yan ridda suna yin amfani da “maganganun rikici.” Hakan yana nufin cewa suna faɗin abubuwa da suke sa ra’ayoyinsu na ƙarya su zama kamar gaskiya ne, yadda jebun takardun masu aikata laifofi suke kama da na gaske. Suna ƙoƙari su sa mutane da yawa su gaskata da koyarwarsu na ruɗu. Bitrus ya kuma ce suna son “juya” Nassosi. Suna bayyana ayoyin Littafi Mai Tsarki a hanyar da ba ta dace ba don mutane su gaskata da nasu ra’ayoyi. (2 Bit. 2:1, 3, 13; 3:16) ’Yan ridda ba sa kula da mu. Idan mun bi su, za mu bijire daga hanyar rai madawwami.
6. Wane gargaɗi ne Littafi Mai Tsarki ya ba mu dalla-dalla game da malaman ƙarya?
6 Ta yaya za mu kāre kanmu daga malaman ƙarya? Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abin da za mu yi. (Karanta Romawa 16:17; 2 Yohanna 9-11.) Kalmar Allah ta ce: “Ku bijire masu.” Hakan yana nufin mu guje musu. Gargaɗin Littafi Mai Tsarki yana kama da gargaɗi daga wani likita wanda ya gaya maka ka guji wanda yake da cuta da wasu za su iya kamuwa da ita kuma su mutu sanadiyyar cutar. Gargaɗinsa a bayane yake, kuma za ka yi abin da ya ce. Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa ’yan ridda ba sa “gane kome” kuma suna amfani da koyarwarsu don su sa mutane su riƙa tunani kamar su. (1 Tim. 6:3, 4) Jehobah yana kama da wannan nagarin likita. Ya gaya mana sarai mu guji malaman ƙarya. Dole ne mu ƙuduri aniya mu bi gargaɗinsa a koyaushe.
7, 8. (a) Mene ne ya wajaba mu yi don mu guji malaman ƙarya? (b) Me ya sa ka ƙuduri aniya ka guji malaman ƙarya?
7 Mene ne ya wajaba mu yi don mu guji malaman ƙarya? Ba ma musu magana ko kuma mu gayyace su cikin gidajenmu. Ba ma karanta littattafansu, ba ma kallonsu a talabijin, ba ma karanta abin da suka rubuta a Intane ko kuma mu ba da kalamanmu game da abin da suka rubuta a Intane. Me ya sa muka ƙuduri aniya mu guje su? Na farko, domin muna ƙaunar “Allah na gaskiya.” Saboda haka, ba ma son mu saurari koyarwar ƙarya da ta saɓa wa gaskiya da ke cikin Kalmar Allah. (Zab. 31:5; Yoh. 17:17) Muna kuma ƙaunar ƙungiyar da Jehobah yake amfani da ita don ya koya mana gaskiya mai ban al’ajabi haɗe da sunan Jehobah da abin da take nufi da nufin Allah ga duniya da abin da yake faruwa da mu sa’ad da muka mutu da kuma begen tashin matattu. Ka tuna yadda kake farin ciki sa’ad da ka fara koyan waɗannan koyarwa masu yawa? Saboda haka, kada ka ƙyale ƙaryace-ƙaryace na malaman ƙarya su sa ka juya baya ga ƙungiyar da ta koya maka waɗannan abubuwan.—Yoh. 6:66-69.
8 Ko da mene ne malaman ƙarya za su faɗa, ba za mu bi su ba! Bai kamata mu saurari mutanen da suke kama da rijiyoyi da babu ruwa a ciki don kada mu yi da na sani. Mun ƙuduri aniya mu kasance da aminci ga Jehobah da ƙungiyarsa wadda ba ta taɓa sa mu yi da na sani ba kuma a koyaushe tana ba mu ruwaye masu tsarki na gaskiya daga Kalmar Allah a yalwace.—Isha. 55:1-3; Mat. 24:45-47.
Kada Ka Saurari “Tatsuniyoyi”
9, 10. Wane gargaɗi ne Bulus ya ba Timotawus game da tatsuniyoyi? Waɗanne labaran ƙarya ne Bulus yake tunaninsu? (Duba hasiya.)
9 Idan wani ya juya alamar da ke kan hanya, hakan zai iya yaudararmu. A wasu lokatai yana da sauƙi a ga cewa alamar tana nuni ga wurin da ba daidai ba, amma a wasu lokatai ba shi da sauƙi. Hakan yake da ƙaryar da Shaiɗan yake yi. Manzo Bulus ya yi mana gargaɗi game da waɗannan ƙaryace-ƙaryace. Ya kira su “tatsuniyoyi.” (Karanta 1 Timotawus 1:3, 4.) Mene ne waɗannan tatsuniyoyin, kuma yaya za mu guji sauraron su? Muna bukatar amsoshi ga waɗannan tambayoyi don mu kasance a hanyar rai madawwami.
10 Bulus ya yi gargaɗi game da labarun ƙarya a cikin wasiƙarsa ta fari ga Timotawus, dattijo Kirista cewa ya sa ikilisiyar ta kasance da tsabta kuma ya taimaka wa ’yan’uwa su kasance da aminci ga Jehobah. (1 Tim. 1:18, 19) Kalmar nan na Helenawa da Bulus ya yi amfani da ita tana nufin ƙarya ko kuma labarin da aka ƙaga. Littafin nan The International Standard Bible Encyclopaedia ya ce tatsuniya “labarin addini ce da ba shi da alaƙa da labarin gaskiya.” Wataƙila Bulus yana magana ne game ƙaryace-ƙaryacen addinai da suka fito daga tatsuniyoyi na dā da mutane suka ƙage da yake sa mutane son sanin abubuwa.b Waɗannan labaran “su kan jawo muhawwara” wato, sai a soma tambayoyi game da abubuwa da ba gaskiya ba ne kuma a riƙa neman amsoshin. Shaiɗan yana amfani da waɗannan labaran da aka ƙaga da ƙaryace-ƙaryacen addinai don ya sa mutane su manta da abubuwa mafi muhimmanci. Kalaman Bulus a bayane suke cewa: Kada mu saurari tatsuniyoyi!
11. Ta yaya Shaiɗan yake yin amfani da addinin ƙarya don yaudarar mutane? Wane gargaɗi ne ya kamata mu saurara?
11 Waɗanne labaran ƙarya ne za su iya yaudararmu idan ba mu mai da hankali ba? Muna iya cewa “tatsuniyoyi” sune kowacce koyarwa na addini da ke sa mu “barin gaskiya,” wato, da ke sa mu daina sauraron gaskiya. (2 Tim. 4:3, 4) Shaiɗan da ke mai da kansa “mala’ika na haske,” yana yin amfani da addinin ƙarya don ya yaudari mutane. (2 Kor. 11:14) Alal misali, addinan Kiristendam sun ce suna bin Kristi, amma suna koyar da abubuwa kamar su Allah-Uku-Cikin Ɗaya da kuma wutar jahannama. Suna kuma koyar cewa wasu sashen jikin ’yan Adam suna rayuwa bayan mutuwa. Mutane da yawa suna tunanin cewa bukukuwan Kirismati da Ista suna faranta wa Allah rai, amma abubuwan da mutane suke yi a lokacin waɗannan bukukuwa ainihi daga bauta ta ƙarya ce. Labaran ƙarya ba za su yaudare mu ba idan mun saurari gargaɗin Allah cewa mu ware kanmu daga addinin ƙarya kuma “kada mu taɓa kowane abu marar-tsarki.”—2 Kor. 6:14-17.
12, 13. (a) Waɗanne ƙaryace-ƙaryace uku ne Shaiɗan yake yi? Mene ne gaskiya game da waɗannan ƙaryace-ƙaryacen? (b) Mene ne ya wajaba mu yi idan ba ma son Shaiɗan ya yaudare mu da tatsuniya?
12 Akwai wasu ƙaryace-ƙaryace na Shaiɗan da za su iya yaudararmu idan ba mu mai da hankali ba. Ga wasu misalai. Kana iya yin abin da ka ga dama; ka tsai da shawara a kan abin da ke daidai da abin da ba daidai ba. Sau da yawa muna jin waɗannan a talabijin da fina-finai da jaridu da kuma a Intane. Idan muna jin wannan ƙaryar a koyaushe, yana da sauƙi mu soma tunani hakan kuma mu bi ra’ayoyin lalata na duniya. Amma gaskiyar ita ce muna bukatar Allah ya gaya mana abin da ke daidai da abin da ba daidai ba. (Irm. 10:23) Allah ba zai taɓa canja kome a duniya ba. Kasancewa da irin wannan ra’ayin na yin rayuwa don yau kawai zai iya sa mu zama “raggaye ko kuwa marasa-amfani.” (2 Bit. 1:8) Gaskiyar ita ce ba da daɗewa ba Jehobah zai canja abubuwa a duniya, kuma dole ne mu nuna cewa mun gaskata hakan ta hanyar da muke yin rayuwa. (Mat. 24:44) Allah ba ya kula da kai. Gaskatawa da wannan ƙarya da Shaiɗan yake yi zai iya sa mu daina bauta wa Jehobah muna tunani cewa Allah ba zai taɓa ƙaunarmu ba. Gaskiyar ita ce Jehobah yana ƙaunar kowane cikin bayinsa kuma kowane mutum yana da muhimmanci a gare shi.—Mat. 10:29-31.
13 Dole ne mu mai da hankali don kada mu yi tunani kamar mutane a duniyar Shaiɗan. A wasu lokatai abin da suka ce da kuma suke tunani kamar gaskiya ce. Amma ku tuna cewa Shaiɗan yana son ya yaudare mu, kuma ba wanda ya fi shi iya yaudarar mutane. Dole ne mu saurari gargaɗi da ke cikin Littafi Mai Tsarki idan ba ma son Shaiɗan ya yaudare mu da “tatsuniyoyi da aka ƙaga da wayo.”—2 Bit. 1:16.
Kada Ka Bi “Shaiɗan”
14. Wane gargaɗi ne Bulus ya ba wasu ƙananan gwauraye? Me ya sa dukanmu muke bukatar bin wannan gargaɗin?
14 A ce ka ga wata alama a kan hanya da ta ce: “Ka Bi Wannan Hanyar don Ka Bi Shaiɗan.” Hakika, babu kowanne Kirista da zai so ya bi wannan alamar. Amma, Kiristoci na gaskiya suna iya soma “bin Shaiɗan.” Bulus ya yi mana gargaɗi game da yadda hakan zai iya faruwa. (Karanta 1 Timotawus 5:11-15.) Ya rubuta game da wasu “gwauraye ƙanƙanana” da suke cikin ikilisiya a lokacin, amma dukanmu za mu iya koya daga abin da ya ce. Waɗannan gwaurayen ba sa ganin cewa suna bin Shaiɗan, amma abin da suka yi ya nuna cewa suna yin hakan. Ta yaya za mu iya guji bin Shaiɗan ba tare da sanin mu ba? Yanzu za mu yi magana game da gargaɗin Bulus a kan mugun gulma, wato, faɗin abin da bai dace ba game da wasu mutane.
15. Mene ne Shaiɗan yake so? Kamar yadda Bulus ya bayyana, waɗanne abubuwa ne Shaiɗan yake amfani da su don ya sa mu yi abin da yake so?
15 Shaiɗan ba ya son mu yi magana game da abin da muka gaskata. Yana son mu daina wa’azin bishara. (R. Yoh. 12:17) Yana son mu yi abubuwan da ba su dace ba ko da za su ɓata lokacinmu ko kuma su jawo faɗa tsakanin mutanen Jehobah. Bulus ya ambata wasu abubuwa da Shaiɗan yake amfani da su. ‘Ragwaye ne masu yawo.’ Alal misali muna iya yin amfani da yawan lokacinmu da na wasu mutane don karanta da kuma aika da saƙon i-mel game da abubuwa da ba su da muhimmanci kuma wani lokaci ba gaskiya ba ne. “Masu-tsegumi.” A wasu lokatai masu-tsegumi suna faɗan abin da ba gaskiya ba game da wasu mutane. Wannan yana da haɗari sosai domin tsegumi ƙaryace-ƙaryace ne game da mutane. Sau da yawa waɗannan ƙaryace-ƙaryace suna sa mutane faɗa. (Mis. 26:20) Waɗanda suke yin ƙarya game da wasu mutane suna kama da Shaiɗan Iblis, ko idan ba su san da hakan ba.c Sai Bulus ya ce waɗannan gwaurayen “masu-shishigi” ne. Suna ƙoƙari su gaya wa mutane yadda za su yi rayuwarsu. Babu wanda yake da izinin yin hakan. Dukan waɗannnan suna iya sa mu daina tunani game da aiki mai muhimmanci da Jehobah ya ba mu mu yi. Ya kamata mu yi amfani da lokacinmu don yin wa’azi game da Mulkin Allah. Idan muka daina wa’azi za mu soma bin Shaiɗan. Kuma idan muna gefen Shaiɗan, muna gāba da Jehobah ke nan. Dukanmu muna bukatar mu zaɓa gefen da za mu kasance.—Matt. 12:30.
16. Yin biyayya ga wace shawara ce za ta taimaka mana mu guji bin Shaiɗan?
16 Yin biyayya ga shawarar Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana kada mu bi Shaiɗan. Bulus ya ambata wasu abubuwa da za su taimaka mana. Ya ce mu riƙa “yawaita cikin aikin Ubangiji.” (1 Kor. 15:58) Shagalawa a ayyukan Mulki zai kāre mu daga haɗarurruka na ragwanci da biɗe-biɗe masu ɓata lokaci. (Mat. 6:33) Bulus ya kuma gaya mana mu yi magana “da ke mai-kyau garin ginawa.” (Afis. 4:29) Kada ka yi gulma, kuma kada ka saurari gulma.d Ka dogara da kuma daraja ’yan’uwanka masu bi. Da hakan za mu riƙa faɗan abubuwa masu kyau game da su. Bulus ya kuma faɗa mana abin da ya kamata ya zama ƙudurinmu. Ya ce: ‘Ku ƙallafa ranku ga yin naku sha’ani.’ (1 Tas. 4:11) Ka nuna ka damu da mutane amma ka yi hakan da daraja. Ka tuna cewa da akwai abubuwa da ba sa son su yi magana a kai kuma ba sa son mutane su sani. Kuma ka tuna cewa bai kamata mu tsai da wa mutane shawarwari da suke bukatar su tsai da da kansu ba.—Gal. 6:5.
17. (a) Me ya sa Jehobah ya yi mana gargaɗi a kan abin da muke tattaunawa? (b) Mene ne ya wajaba mu ƙuduri aniyar yi?
17 Muna godiya ga Jehobah don yana gaya mana abin da bai kamata mu bi ba! Ya kamata a koyaushe mu riƙa tuna cewa Jehobah ya ba mu gargaɗi da muka tattauna domin yana ƙaunarmu sosai. Ba ya son Shaiɗan ya yaudare mu kuma ya sa mu sha wahala. Hanyar da Jehobah yake son mu zaɓa matsatsiya ce, amma hanya ce kaɗai da za ta sa mu samu rai madawwami. (Mat. 7:14) Dole ne a koyaushe mu ƙuduri aniya mu saurari Jehobah sa’ad da ya gaya mana: “Wannan ita ce hanya, ku bi ta.”—Isha. 30:21.
[Hasiya]
a “Ridda” yin tawaye ne ga bauta ta gaskiya da kuma barin ta.
b Littafin nan Tobi da wasu mutane suke gani cewa yana cikin sashen Littafi Mai Tsarki, misali ne na labaran ƙarya da ake yi a zamanin Bulus. An rubuta littafin a misalin ƙarni na uku kafin Kristi. Wannan littafin yana cike da imanin ƙarya da labaran sihiri. Ya ba da labaran ƙarya kuma ya ce gaskiya ce.—Duba littafin nan Insight on the Scriptures, Littafi na 1, shafi na 122.
c A Helenanci “Iblis” yana nufin “wanda yake ƙarya game da mutane don ya yi musu lahani.” Wannan kalmar wani laƙabi ne na Shaiɗan, wanda shi ne maƙaryaci na farko.—Yoh. 8:44; R. Yoh. 12:9, 10.
d Ka duba akwati nan “Watsa Gasu a Iska.”
Mece ce Amsarka?
Ta yaya za ka nuna cewa kana sauraron gargaɗin da ke cikin waɗannan nassosin?
• 2 Bitrus 2:1-3
• 1 Timotawus 1:3, 4
• 1 Timotawus 5:11-15
[Akwati/Hotona a shafi na 19]
Watsa Gasu a Iska
Akwai wani labarin Yahudawa na zamanin dā da ya nuna sakamakon yaɗa mugun gulma.
Wani mutum ya yi tsegumi game da wani mafi hikima da ke ƙauyensu. Bayan wani lokaci, mutumin da ya yi tsegumin ya fahimci kuskurensa sai ya nemi mutum mafi hikiman ya gafarta masa. Sai ya ce zai yi dukan abin da ake bukata don a gafarta masa. Mutum mafi hikiman ya gaya masa: “Akwai abu ɗaya da za ka iya yi. Ka ɗauki jaka cike da gasu. Ka juye jakar don gasun su tashi sama.” Mutumin bai san dalilin yin hakan ba, amma ya yi abin da mutum mafi hikiman ya ce ya yi. Daga baya ya koma wurin mutum mafi hikiman, sai ya tambaye shi: “Ka gafarta mini yanzu?” Sai mutum mafi hikiman ya gaya masa: “Da farko, ka koma ka tattara dukan gasun.” Sai mutumin ya ce masa: “Amma, ai hakan yana da wuya. Iska ta riga ta watsar da gasun ko’ina. Ba zan iya ganinsu kuma ba. Sai mutum mafi hikiman ya ce: “Kamar yadda gasun suka watsu ko’ina, hakan ma ƙaryace-ƙaryace da ka yi ta shiga kunnuwan mutane da yawa. Kuma kamar yadda ba za ka iya neman gasun ba, ba za ka iya sa mutane su mance da abin da ka faɗa ba.”
Darasin a bayane yake. Ba za mu iya canja abin da muka faɗa ba bayan mun faɗe ta. Kuma wani lokaci ba za mu iya canja mugun sakamakon abin da muka faɗa ba. Saboda haka, kafin mu faɗa wani abu marar kyau game da mutane, yana da kyau mu tuna cewa kalamanmu suna kama da gasu da iska ta watsar.
[Hoto a shafi na 16]
Ta yaya wasu za su iya gayyatar ’yan ridda cikin gidajensu?