Ka Ci Gaba Da Aikata Abubuwa Da Ka Koya
“Abubuwan da kuka koya kuka karɓa kuma, kuka ji kuka gani a wurina, waɗannan sai ku aikata: Allah kuwa na salama za ya zauna tare da ku.”—FILIBBIYAWA 4:9.
1, 2. Galibi, Littafi Mai Tsarki yana da wani tasiri ne a rayukan mutane da suke ɗaukan kansu masu tsarin addini? Ka ba da bayani.
“ADDINI Yana Bunƙasa, amma Ɗabi’a Tana Lalacewa.” Wannan kan magana na jaridar Emerging Trends ya taƙaita bincike ne da aka yi a ƙasar Amirka. Hakika, mutane da suke zuwa coci a wannan ƙasar suna ƙaruwa kuma sun ce addini yana da muhimmanci ƙwarai a rayuwarsu. Amma, rahoton ya nuna cewa: “Duk da wannan adadi mai yawa, mutanen Amirka da yawa suna tambayar yadda imani ya shafi rayukan mutane da kuma al’ummar gabaki ɗaya.”
2 Wannan yanayi ba ƙasa ɗaya kawai ya shafa ba. A duniya baki ɗaya, mutane da yawa da suka ce sun gaskata da Littafi Mai Tsarki kuma suke da tsarin addini ba su ƙyale Nassosi sun yi wani tasirin gaske a rayuwarsu ba. (2 Timothawus 3:5) “Har yanzu mun ɗauki Littafi Mai Tsarki da daraja,” in ji shugaban masu binciken, “amma batun keɓe lokaci don karatunsa, da nazarinsa da kuma amfani da shi—wannan yayin dā ne.”
3. (a) Ta yaya Littafi Mai Tsarki yake shafan waɗanda suka zama Kiristoci na gaskiya? (b) Ta yaya mabiyan Yesu suke amfani da gargaɗin Bulus da ke rubuce a Filibbiyawa 4:9?
3 Amma, ga Kiristoci na gaskiya yanayin ya bambanta. Amfani da gargaɗin Kalmar Allah ya canja tunaninsu da kuma halayensu. Wasu kuma sun lura da sababbin halayensu. (Kolossiyawa 3:5-10) Ga mabiyan Yesu, Littafi Mai Tsarki ba littafi ba ne da ake bari ya tara ƙura. Akasin haka, manzo Bulus ya gaya wa Kiristoci a Filibbi: “Abubuwan da kuka koya kuka karɓa kuma, kuka ji kuka gani a wurina, waɗannan sai ku aikata: Allah kuwa na salama za ya zauna tare da ku.” (Tafiyar Tsutsa Tamu ce; Filibbiyawa 4:9) Kiristoci ba yarda da gaskiyar Kalmar Allah kawai suke yi ba. Suna aikata abubuwa da suka koya, suna ci gaba da amfani da gargaɗin Littafi Mai Tsarki—a cikin iyali, a wajen aiki, a cikin ikilisiya, da kuma a dukan wasu ɓangarorin rayuwa.
4. Me ya sa yake da wuya a bi dokokin Allah?
4 Bin dokoki da kuma mizanan Allah ba shi da sauƙi. Muna zama ne a cikin duniya da take ƙarƙashin ikon Shaiɗan Iblis, wanda Littafi Mai Tsarki ya kira shi “allah na wannan zamani.” (2 Korinthiyawa 4:4; 1 Yohanna 5:19) Saboda haka, yana da muhimmanci mu tsare kanmu daga dukan wani abu da zai hana mu bin tafarkin aminci ga Jehovah Allah. Ta yaya za mu zama masu aminci?
Ka Riƙe ‘Tafarkin Sahihan Kalmomi’
5. Menene furcin Yesu: “Kowacce rana shi biyo ni” yake nufi?
5 Wani ɓangare na aikata abin da muka koya ya ƙunshi riƙe bauta ta gaskiya cikin aminci, duk da hamayya daga marasa bi. Jimiri yana bukatar ƙoƙari. “Idan kowane mutum yana nufi shi bi ni,” in ji Yesu, “sai shi yi musun kansa, shi ɗauki [gungumensa na azaba] shi biyo ni.” (Luka 9:23) Yesu bai ce mu bi shi na mako guda, ko wata guda, ko kuma na shekara ba. Maimakon haka, ya ce: “Kowacce rana, shi biyo ni.” Waɗannan kalmomi sun nuna cewa almajirancinmu ba wani ɓangaren rayuwarmu ba ne ko kuma ibada mai shuɗewa, ta kasance yau, gobe ba ta. Ɗaukaka bauta ta gaskiya tana nufin jimre wa tafarkin da muka zaɓa cikin aminci, ko sama da ƙasa za ta haɗe. Ta yaya za mu yi haka?
6. Menene kwatancin sahihiyan kalmomi da Kiristoci na ƙarni na farko suka koya daga wurin Bulus?
6 Bulus ya aririci abokin aikinsa Timothawus: “Ka kiyaye kwatancin sahihiyan kalmomi waɗanda ka ji daga gareni, cikin bangaskiya da ƙauna wadda ke cikin Kristi Yesu.” (2 Timothawus 1:13) Menene Bulus yake nufi? Kalmar Helenanci da aka fassara a nan “kwatanci” a zahiri tana nufin zane. Ko da yake wannan ba cikakke ba ne, irin wannan zanen yana da tsari da mai kallo zai iya fahimtar zanen. Hakazalika, kwatancin gaskiya da Bulus ya koyar da Timothawus da wasu, ba a tsara shi ya amsa dukan wata tambaya da za a yi ba. Duk da haka, koyarwar ta ba da isashen kwatanci da masu zukatan kirki za su iya fahimtar abin da Jehovah yake bukata a gare su. Amma domin su faranta wa Allah rai, za su bukaci su ci gaba da riƙe wannan kwatancin gaskiya ta wajen aika abin da suka koya.
7. Ta yaya Kiristoci za su manne wa kwatancin sahihiyan kalmomi?
7 A ƙarni na farko, mutane kamar su Himinayus, Iskandari, da kuma Filitus sun yaɗa wani ra’ayi da bai dace da “kwatancin sahihiyan kalmomi” ba. (1 Timothawus 1:18-20; 2 Timothawus 2:16, 17) Ta yaya Kiristoci na farko za su guje kada ’yan ridda su bijirar da su? Ta mai da hankali wajen nazarin hurarrun rubutu da kuma amfani da su a rayuwarsu. Waɗanda suke aiki da misalin Bulus da wasu amintattu sun fahimci kuma sun ƙi dukan wani abin da bai jitu da kwatancin gaskiya da aka koya musu ba. (Filibbiyawa 3:17; Ibraniyawa 5:14) Maimako su kasance “maciwuci ne bisa ga tuhuma da muhawwara ta kalmomi.” (1 Timothawus 6:3-6) Mu ma muna yin haka sa’ad da muke aikata gaskiya da muka koya. Abin ban ƙarfafa ne mu ga bayin Jehovah miliyoyi a dukan duniya suna riƙe da kwatanci na gaskiyar Littafi Mai Tsarki da aka koya musu.—1 Tassalunikawa 1:2-5.
Ka Ƙi “Tatsuniyoyi”
8. (a) Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙari ya halaka bangaskiyarmu a yau? (b) Wane gargaɗi ne na Bulus aka samu a 2 Timothawus 4:3, 4?
8 Shaiɗan yana ƙoƙarin ya ɓata amincinmu ta wajen sa mu yi shakkar abin da aka koya mana. A yau, kamar a ƙarni na farko, ’yan ridda da kuma wasu suna ƙoƙarin su halaka bangaskiyar marasa laifi. (Galatiyawa 2:4; 5:7, 8) A wasu lokatai suna amfani da hanyar sadarwa su yaɗa algus ko kuma ma ƙarya kai tsaye game da tsarinmu da kuma muradin mutanen Jehovah. Bulus ya yi gargaɗi cewa za a kawar da wasu daga gaskiya. Ya rubuta cewa: “Kwanaki za su zo inda ba za su daure da koyarwa mai-lafiya ba; amma bisa ga ƙaiƙayin kunnuwa za su tattara wa kansu masu-koyarwa bisa ga sha’awoyinsu; za su kawarda kunnuwansu ga barin gaskiya, su karkata zuwa wajen tatsuniyoyi.”—2 Timothawus 4:3, 4.
9. Menene Bulus yake nufi sa’ad da ya yi maganar “tatsuniyoyi”?
9 Maimakon riƙe kwatancin sahihan kalmomi, wasu an ruɗe su da “tatsuniyoyi.” Menene waɗannan tatsuniyoyi? Wataƙila Bulus yana nufin ƙage-ƙage, kamar wanda yake cikin littafin afokirifa na Tobi.a Tatsuniyoyi wataƙila sun haɗa da jita-jita da ta bazu. Ga wasu kuma—“bisa ga ƙaiƙayin kunnuwansu”—wataƙila waɗanda suke yarda da ƙyaliya na mizanan Allah ko kuma waɗanda suke sukan waɗanda suke jagabanci a ikilisiya sun rinjaye su bisa basira. (3 Yohanna 9, 10; Yahuda 4) Ko waɗanne abubuwan sa sanyin jiki ne da akwai, wasu babu shakka sun gwammace ƙarya da gaskiyar Kalmar Allah. Ba da daɗewa ba suka daina aikata abin da suka koya, kuma wannan nasu ci baya ne na ruhaniya.—2 Bitrus 3:15, 16.
10. Waɗanne ne irin tatsuniyoyin ƙarya na zamani, kuma ta yaya Yohanna ya nanata bukatar mai da hankali?
10 Za mu guje juya wa ga tatsuniyoyi a yau idan muka yi bincike kuma muka yi zaɓe a dukan abin da muke sauraro da kuma abin da muke karantawa. Alal misali, hanyar sadarwa sau da yawa suna ƙarfafa lalata. Mutane da yawa suna ƙarfafa shakkar kasancewar Allah ko kuma rashin yarda da Allah. Gogaggun ’yan sūka suna yi wa Littafi Mai Tsarki ba’a domin da’awarsa na hurewa daga wurin Allah. Kuma ’yan ridda na zamani sun ci gaba da ƙoƙari su sa Kiristoci su yi shakka domin su yi wa bangaskiyarsu makarkashiya. Game da irin wannan haɗari da annabawan ƙarya suka kawo a ƙarni na farko, manzo Yohanna ya yi gargaɗi: “Masoya, kada ku bada gaskiya ga kowane ruhu, amma ku gwada ruhohi, ko na Allah ne: gama masu-ƙarya annabci dayawa sun fita zuwa cikin duniya.” (1 Yohanna 4:1) Saboda haka, muna bukatar mu mai da hankali.
11. Wace hanya ce ɗaya da za mu gwada mu gani ko muna cikin imani?
11 Domin wannan Bulus ya rubuta: “Ku gwada kanku ko kuna cikin imani.” (2 Korinthiyawa 13:5) Manzon ya aririce mu mu ci gaba da gwada kanmu mu gani ko muna riƙe da imani na Kirista. Idan kunnuwanmu suna son ji daga marasa wadatar zuci, muna bukatar mu bincika kanmu cikin addu’a. (Zabura 139:23, 24) Muna yawan neman laifi daga mutanen Jehovah? Idan haka ne, me ya sa? Abin da wani ya yi ko kuma ya faɗa ya ɓata mana rai ne? Idan haka ne, muna bi da abubuwa yadda suka dace? Wani tsanani da muka fuskanta a wannan zamani na ɗan lokaci ne. (2 Korinthiyawa 4:17) Ko ma mun fuskanci wasu gwaji a cikin ikilisiya, me ya sa za mu daina bauta wa Jehovah? Idan mun yi fushi domin wani abu, bai fi ba mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu warware matsalar sai kuma mu ƙyale batun a hannun Jehovah?—Zabura 4:4; Misalai 3:5, 6; Afisawa 4:26.
12. Ta yaya Biriyawa suka kafa mana misali mai kyau?
12 Maimakon mu kasance masu sūka, bari mu kasance da tunani mai kyau game da bayani da muka samu daga nazarinmu da kuma wanda muka samu daga taro na ikilisiya. (1 Korinthiyawa 2:14, 15) Maimakon tuhumar Kalmar Allah, hikima ce idan muka kasance da hali irin na Biriyawa na ƙarni na farko waɗanda suka bincika Nassosi ƙwarai! (Ayukan Manzanni 17:10, 11) Sai kuma mu yi abin da muka koya, mu guji tatsuniyoyi kuma mu riƙe gaskiya.
13. Ta yaya za mu yaɗa ƙarya ba da saninmu ba?
13 Da akwai wata irin tatsuniya kuma da muke bukatar mu yi hankali da ita. Ƙage da yawa suna yaɗuwa ta wajen E-mail. Yana da kyau mu mai da hankali domin irin waɗannan tatsuniyoyi, musamman ma idan ba mu san ainihin tushen bayanin ba. Ko mun samu wani labari daga wani Kirista mai martaba, wannan mutum ba zai kasance ya shaida wannan abin ba. Abin da ya sa ke nan yake da muhimmanci mu yi hankali da maimaita ko kuma aika labarin da ba mu tabbatar da gaskiyarsa ba. Hakika ba za mu so mu maimaita ‘ƙage na saɓon Allah’ ba, ko kuma ‘tatsuniyoyin saɓo.’ (1 Timothawus 4:7) Tun da dukanmu muna da hakkin mu faɗi gaskiya ga juna, muna nuna basira idan mun guje wa dukan wani abin da zai sa mu yaɗa ƙarya ko da ba da saninmu ba.—Afisawa 4:25.
Sakamako Mai Kyau na Aikata Gaskiya
14. Wane lada ake samu daga aikata abin da muka koya daga Kalmar Allah?
14 Aikata abin da muka koya daga nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma a taron Kirista zai kawo mana lada mai yawa. Alal misali, za mu ga cewa nasabarmu da waɗanda suka dangance mu a ruhaniya ta gyaru. (Galatiyawa 6:10) Rayuwarmu za ta gyaru idan muka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (Zabura 19:8) Bugu da ƙari, ta wajen aikata abin da muka koya, muna ‘kyawanta koyarwar Allah’ kuma wataƙila mu rinjayi wasu zuwa bauta ta gaskiya.—Titus 2:6-10.
15. (a) Ta yaya wata yarinya ta yi gaba gaɗi ta yi wa’azi a makaranta? (b) Menene ka koya daga wannan labarin?
15 A tsakanin Shaidun Jehovah da akwai matasa da yawa da suke aikata abin da suka koya daga nazarinsu na Littafi Mai Tsarki da kuma littattafai na Kirista da kuma abin da suka koya daga halartar taron ikilisiya a kai a kai. Halayensu masu kyau shaida ne mai ƙarfi ga malamai haɗe da ɗalibai a makaranta. (1 Bitrus 2:12) Ka yi la’akari da Leslie, ’yar shekara 13 a Amirka. Ta yarda cewa yana da wuya ta yi wa abokanta a makaranta wa’azi game da bangaskiyarta, amma wata rana yanayin ya sake. “Ajin suna tattaunawa game da yadda mutane suke talla. Wata yarinya ta ɗaga hannunta ta ambaci Shaidun Jehovah.” Tun da ita Mashaidiya ce, me Leslie ta yi? “Na kāre bangaskiyata,” in ji ta, “kuma hakan na tabbata ya ba kowa mamaki, tun da ba na magana a makaranta.” Menene sakamakon gaba gaɗin Leslie? “Na bai wa ɗalibar mujalla da warƙa, tun da tana da wasu tambayoyi,” in ji Leslie. Hakika Jehovah yana farin ciki idan matasa da suke aikata abin da suka koya, suka yi gaba gaɗi suka yi wa’azi a makaranta!—Misalai 27:11; Ibraniyawa 6:10.
16. Ta yaya Makarantar Hidima ta Allah ta amfani wata matashiya?
16 Wani misali na Elizabeth ne. Tun lokacin da take ’yar shekara bakwai har ta kare makarantar firamare, wannan yarinyar tana gayyatar malamanta zuwa Majami’ar Mulki duk lokacin da take da aiki a Makarantar Hidima ta Allah. Idan malamin ba zai iya zuwa ba, Elizabeth za ta tsaya bayan an tashi a makaranta ta gabatar da aikin ga malamin. Lokacin da take babban makaranta, Elizabeth ta rubuta shafi goma na rahoto game da amfanin Makarantar Hidima ta Allah kuma ta gabatar da shi a gaban malamai huɗu. Kuma an gayyace ta ta gwada jawabi na Makarantar Hidima ta Allah, sai ta zaɓi jigon nan “Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Mugunta?” Elizabeth ta amfana daga tsarin koyarwa na Shaidun Jehovah a Makarantar Hidima ta Allah. Tana ɗaya daga cikin matasa Kiristoci da suka kawo yabo ga Jehovah ta wurin aikata abin da suka koya daga Kalmarsa.
17, 18. (a) Wane gargaɗi Littafi Mai Tsarki ya yi game da yin gaskiya? (b) Ta yaya halin gaskiya na Shaidun Jehovah ya taɓa wani mutum?
17 Littafi Mai Tsarki ya gargaɗi Kiristoci su yi halin gaskiya a dukan abu. (Ibraniyawa 13:18) Rashin gaskiya zai ɓata dangantakarmu da wasu, kuma mafi muhimmanci da Jehovah kansa. (Misalai 12:22) Halayenmu abin dogara suna ba da tabbacin cewa muna aikata abin da muka koya, kuma ya sa wasu suna daraja Shaidun Jehovah ƙwarai.
18 Ka yi la’akari da labarin wani soja mai suna Phillip. Ya ɓatar da cek, da aka saka hannu amma ba a sa yawan kuɗin ba, bai sani ba har sai da aka mayar masa a cikin wasiƙa. Wani Mashaidin Jehovah ne ya tsinci cek ɗin, ya rubuta wata gajeriyar wasiƙa ya yi bayani cewa imaninsa ya motsa shi ya mayar da cek ɗin. Phillip sai ya yi kakabi. “Da sun raba ni da $9,000!” in ji shi. Ya taɓa baƙin ciki sa’ad da aka sace hularsa a cikin coci. Wataƙila, aboki ya saci hularsa, a nan kuma baƙo ya mayar masa da cek na dala dubbai! Hakika, Kiristoci masu gaskiya suna kawo wa Jehovah Allah yabo!
Ka Ci Gaba da Aikata Abin da Ka Koya
19, 20. Ta yaya za mu amfana daga aiki da abubuwa na Nassi da muka koya?
19 Waɗanda suka aikata abin da suka koya daga Kalmar Allah suna samun amfani mai yawa. Almajiri Yaƙub ya rubuta: “Wanda ya duba cikin cikakkiyar shari’a, shari’a ta ’yanci, ya lizima, shi kuwa ba mai-ji wanda ke mantuwa ba ne, amma mai-yi ne wanda ke aikatawa, wannan za ya zama mai-albarka a cikin aikinsa.” (Yaƙub 1:25) Hakika, idan muka aikata bisa ga abubuwa da suke ciki Nassi da muka koya, za mu yi farin ciki na gaske kuma za mu iya jimre wa matsi na rayuwa. Fiye ma da haka, za mu samu albarkar Allah da kuma begen rai madawwami!—Misalai 10:22; 1 Timothawus 6:6.
20 Ko yaya, ka ci gaba da yin nazarin Kalmar Allah. Ka riƙa taruwa da masu bauta wa Jehovah a kai a kai, kuma ka mai da hankali ga abin da ake gabatarwa a taron Kirista. Ka yi amfani da abin da ka koya, ka ci gaba da aiki da shi, ‘Allah kuwa na salama za ya zauna tare da kai.’—Filibbiyawa 4:9.
[Hasiya]
a Tobi, wanda wataƙila aka rubuta a ƙarni na uku K.Z., ya haɗa da tatsuniya na wani Bayahude mai suna Tobiya. Aka ce yana da hanyar samun iko na warkarwa da kuma na korar aljanu ta wajen yin amfani da zuciya, matsarmama, da kuma hantar wani babban kifi.
Ka Tuna?
• Menene “kwatanci na sahihiyan kalmomi,” kuma ta yaya za mu ci gaba da riƙe shi?
• Waɗanne “tatsuniyoyi” muke bukatar mu ƙi?
• Wane lada yake zuwa ga waɗanda suke aikata abin da suka koya daga Kalmar Allah?
[Hoto a shafi na 15]
Ta yaya Kiristoci na farko suka guje wa rinjaya daga ’yan ridda?
[Hotuna a shafi na 16]
Hanyar sadarwa, ta Intane, da kuma ’yan ridda na zamani za su iya su sa mu yi shakka
[Hoto a shafi na 17]
Ba daidai ba ne mu yaɗa rahoto da ba mu tabbatar da gaskiyarsa ba
[Hotuna a shafi na 18]
Shaidun Jehovah suna amfani da abin da suka karanta a Kalmar Allah, a makaranta, wajen aiki, da wasu wurare ma