Ku Tsaya Da Ƙarfi Bisa Koyarwa Da Ke Ta Ibada
“Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.”—MISALAI 3:5, 6.
1. Ta yaya ilimin mutane yake bayane a garemu fiye da dā?
YANZU, akwai jaridu kusan 9,000 da suke zagaya dukan duniya. Kowace shekara ana buga sababbin littattafai 200,000 a United States kawai. Bisa wani kimantawa da aka yi, a Maris 1998, da akwai kusan shafi miliyan 275 a hanyar wasa labarai na Internet. An ce wannan adadi yana ƙaruwa da shafi miliyan 20 kowane wata. Fiye da dā, mutane suna samun labari a kan kowane batu. Yayin da wannan yanayi yana da ɓangare mai kyau, irin waɗannan labarai da suka yi yawa sosai ya jawo matsaloli.
2. Wace matsala ce za ta iya ɓullowa daga samun labarai da yawa?
2 Wasu mutane suna son jin labarai sosai, koyaushe suna son su san abin da yake faruwa, ya sa sun yi banza da abubuwa da suka fi muhimmanci. Wasu sun samo labari game da abubuwa masu wuyan ganewa na ilimi kuma sun ɗauki kansu gwanaye. Bisa ga fahimi kaɗan da suke da shi, suna iya ɗaukan mataki da za ta yi masu lahani ko kuwa wasu. Kuma da akwai haɗarin jin labarin ƙarya ko kuma waɗanda ba cikakku ba. Sau da yawa babu tabbatacciyar hanyar sani ko waɗannan labarai da sun yi yawa cikakku ne ko kuma gaskiya.
3. Waɗanne gargaɗi ne game da neman hikima ta mutane aka samu a cikin Littafi Mai-Tsarki?
3 ’Yan Adam suna da halin son su sani. An gano haɗarin ɓad da lokaci mai yawa wajen neman labari da ba shi da amfani ko kuma mai lahani can kwanakin Sarki Sulemanu. Ya ce: “Karɓi gargaɗi: gama yin littattafai ba shi da iyaka; yawan karatu kuma gajiyadda kai ne.” (Mai-Wa’azi 12:12) Ƙarnuka bayan haka manzo Bulus ya rubuta wa Timothawus: “Ka tsare abin da aka damƙa maka, kana bijire ma maganganu na saɓo da kuma tsayayyar ilimin da ana ce da shi hakanan a ƙaryace; abin da waɗansu cikin shaidarsa sun kuskure wajen imani.” (1 Timothawus 6:20, 21) I, Kiristoci a yau suna bukatar su guje wa ra’ayoyi masu lahani.
4. Wace hanya ɗaya za mu iya nuna mun dogara ga Jehovah da kuma koyarwansa?
4 Yana da kyau mutanen Jehovah su yi biyayya ga kalmomin Misalai 3:5, 6: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.” Dogara ga Jehovah ya haɗa da ƙin kowane ra’ayi da ya saɓa da Kalmar Allah, ko ya fito ne daga namu tunani ko kuma na wani. Don mu tsare ruhaniyarmu, yana da muhimmanci mu koyar da hankalinmu don mu gane labari mai lahani kuma mu ƙi shi. (Ibraniyawa 5:14) Bari mu tattauna wasu tushe na irin waɗannan labaran.
Duniya da Shaiɗan Ya Fi Ƙarfinta
5. Menene tushe ɗaya na ra’ayoyi masu lahani, kuma waye ne ke goyon bayansa?
5 Mutanen duniya su ne tushen ra’ayoyi masu lahani. (1 Korinthiyawa 3:19) Yesu Kristi ya yi addu’a ga Allah game da almajiransa: “Ba na yin addu’a ka ɗauke su daga cikin duniya ba, amma domin ka tsare su daga mugun.” (Yohanna 17:15) Roƙon Yesu a tsare almajiransa daga “mugun” ya nuna tasiri da Shaiɗan yake da shi a duniya. Don mu Kiristoci ne ba zai tsare mu daga mummunan tasiri na wannan duniya ba. Yohanna ya rubuta: “Mun sani mu na Allah ne, duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” (1 Yohanna 5:19) Musamman ma wannan sashen kwanaki na ƙarshe, ya kamata a sani cewa Shaiɗan da aljanunsa za su yaɗa labarai masu lahani a duniya.
6. Ta yaya duniya ta nishaɗi za ta ɓata ɗabi’a mai kyau?
6 Ya kamata mu sani cewa wasu cikin labaran nan masu lahani za su iya zama kamar mara lahani ne. (2 Korinthiyawa 11:14) Alal misali, yi la’akari da nishaɗi na duniya, da wasanninta na telibijin, silima, kaɗe-kaɗe, da kuma littattafai. Mutane da yawa sun yarda cewa a lokutta da yawa wasu nishaɗi suna ɗaukaka ayyukan ƙazanta, irinsu lalata, mugunta, da shan miyagun ƙwayoyi. Idan jama’a suka ga nishaɗi da yake da mummunar ɗabi’a da farko yakan ba su mamaki. Amma idan suna gani a kai a kai sai ya zama masu a jiki. Bai kamata ba mu amince da nishaɗi da yake ɗaukaka ra’ayoyi masu lahani ko kuma mu ce ba shi da lahani.—Zabura 119:37.
7. Wace irin hikima ce ta mutane takan iya rusar da amincinmu cikin Littafi Mai-Tsarki?
7 Yi la’akari da wani tushen labari da zai iya yin ɓarna—ra’ayoyi masu yawa da wasu masana kimiyya da ɗalibai waɗanda suka musanta gaskiyar Littafi Mai-Tsarki suke bugawa. (Gwada da Yaƙub 3:15.) Irin waɗannan sau da yawa suna bayyana a cikin jaridu na kullum da sanannun littattafai, kuma sukan iya ɓata aminci cikin Littafi Mai-Tsarki. Wasu mutane suna jin daɗin raunana ikon Kalmar Allah da zace-zace da ba su da iyaka. Irin wannan haɗari ya wanzu a kwanakin manzanni, yadda yake a bayane cikin kalmomin manzo Bulus: “Ku yi hankali kada kowa shi same ku ta wurin iliminsa da ruɗinsa na banza, bisa ga tadar mutane, bisa ga rukunai na duniya, ba bisa ga Kristi ba.”—Kolossiyawa 2:8.
Magabtan Gaskiya
8, 9. Ta yaya ridda take nuna kanta a yau?
8 ’Yan ridda suna iya yin barazana ga ruhaniyarmu. Manzo Bulus ya annabta cewa ridda za ta taso tsakanin waɗanda suke da’awa su Kiristoci ne. (Ayukan Manzanni 20:29, 30; 2 Tassalunikawa 2:3) A cikar kalmominsa, bayan mutuwar manzanni, ridda mai girma ta sa Kiristendam ya bayyana. A yau, babu ridda mai girma tsakanin mutanen Allah. Duk da haka, mutane kalilan sun bar mu, kuma wasu cikinsu sun ƙuduri aniyar su ɓata sunan Shaidun Jehovah ta wajen yaɗa ƙarya da bayanai da ba daidai ba. Kalilan suna aiki da wasu rukuni don shirya hamayya ga bauta ta gaskiya. Ta yin haka, suna goyon bayan ɗan ridda na farko, Shaiɗan.
9 Wasu ’yan ridda suna ƙara yin amfani da hanyar wasa labarai dabam dabam, haɗe da Internet, don su yaɗa labarin ƙarya game da Shaidun Jehovah. A sakamakon haka, yayin da mutane suke bincika imaninmu da gaskiya, suna iya ganin ra’ayi da ’yan ridda suke yaɗawa. Wasu Shaidu ma ba tare da saninsu ba sun sa kansu a irin waɗannan abubuwa masu lahani. Ƙari ga haka, wasu lokutta ’yan ridda suna magana a telibijin ko kuma a rediyo. Wane tafarkin hikima ya kamata a bi game da wannan?
10. Menene abu na hikima da ya kamata mu yi ga ra’ayoyi na ridda?
10 Manzo Yohanna ya gaya wa Kiristoci kada su marabci ’yan ridda a gidajensu. Ya rubuta: “Idan kowa ya zo wurinku, ba ya kuwa kawo wannan koyarwa ba, kada ku karɓe shi cikin gidanku, kada ku yi masa gaisuwa kuma: gama wanda ya yi masa gaisuwa yana tarayya cikin miyagun ayyukansa.” (2 Yohanna 10, 11) Guje wa yin tarayya da waɗannan abokan gaba zai tsare mu daga tunanin lalata. Ba da kanmu ga koyarwa ta ridda ta hanyoyin wasa labarai dabam dabam na zamani yana da lahani yadda karɓan wanda ya ridda a gidajenmu yake da lahani. Bai kamata son mu sani ya ja mu cikin tafarki na bala’i ba!—Misalai 22:3.
A Cikin Ikklisiya
11, 12. (a)Wane tushe na ra’ayoyi masu lahani ya kasance a ikklisiya na ƙarni na farko? (b) Ta yaya wasu Kiristoci suka kasa tsayawa da ƙarfi bisa koyarwa da ke ta ibada?
11 Har ila, ka yi la’akari da wani tushe na ra’ayoyi masu lahani. Ko da yake ba da niyyar ya koyar da ƙarya ba, Kirista da ya keɓe kai zai iya ɗaukan halin yin magana da garaje. (Misalai 12:18) Domin mu ajizai ne, dukanmu a wasu lokutta muna zunubi da harshenmu. (Misalai 10:19; Yaƙub 3:8) Hakika, a lokacin Bulus, akwai wasu cikin ikklisiya da suka kasa riƙe harshensu kuma sun shiga yin jayayya game da kalmomi. (1 Timothawus 2:8) Akwai wasu da suke yawan tunani game da nasu ra’ayoyi har ma sun zargi matsayin Bulus. (2 Korinthiyawa 10:10-12) Irin wannan hali yana kawo jayayya da bai kamata ba.
12 Wasu lokutta wannan jayayya tana kai wa ga “gardama,” tana ɓata salama ta ikklisiya. (1 Timothawus 6:5; Galatiyawa 5:15) Game da waɗanda suke haddasa wannan jayayyar, Bulus ya rubuta: “Idan kowa yana yin koyarwa dabam, ba ya kuwa yi jayayya da sahihan kalmomi, watau kalmomin Ubangijinmu Yesu Kristi, da koyarwa wadda ke bisa ga ibada; ya kumbura, ba ya gane komi ba, amma maciwuci ne bisa ga tuhuma da muhawwara ta kalmomi, inda kishi ya ke fitowa, da husuma, da zage-zage, da miyagun zace-zace.”—1 Timothawus 6:3, 4.
13. Wane halaye ne yawancin Kiristoci suke da shi a ƙarni na farko?
13 Abin farin ciki, a lokuttan manzanni yawanci Kiristoci suna da aminci kuma sun nace a aikin shelar bishara na Mulkin Allah. Sun shagala wajen kula da “marayu da gwamraye cikin ƙuncinsu” kuma sun tsare kansu “mara-aibi daga duniya,” ba sa ɓata lokacinsu a jayayyar wofi game da kalmomi. (Yaƙub 1:27) Suna guje wa “zama da miyagu” har ma a cikin ikklisiyar Kirista don su ƙare ruhaniyarsu.—1 Korinthiyawa 15:33; 2 Timothawus 2:20, 21.
14. Idan ba mu mai da hankali ba, yaya taɗin ra’ayoyi da yake daidai zai kawo jayayya mai lahani?
14 Hakanan ma, yanayi da aka kwatanta a izifi na 11 ba irin na ikklisiyoyin Shaidun Jehovah ba ne a yau. Duk da haka, yana da kyau mu gane wofincin irin wannan jayayya. Hakika, daidai ne a tattauna darasi na Littafi Mai-Tsarki ko kuma a yi tunani game da fasaloli na sabuwar duniya da aka yi alkawarinta da ba ta bayana ba tukuna. Kuma yana da kyau a yi taɗin ra’ayoyi game da al’amura na kai, irinsu sa tufafi da yin ado ko kuma nishaɗi da ake zaɓa. Amma, idan mun zama marasa la’akari game da ra’ayoyinmu kuma ɓata rai yayin da wasu ba su yarda da namu ba, ikklisiyar za ta rabu domin ƙananan al’amura. Abin da ya soma kamar ɗan magana mara lahani, sai ya zama mai lahani ƙwarai.
Tsare Amanarmu
15. Har yaya “koyarwar aljanu” za ta iya yi mana lahani a ruhaniya, kuma wane gargaɗi aka bayar cikin Nassosi?
15 Manzo Bulus ya yi kashedi: “Amma Ruhu yana faɗi a sarari, cikin kwanaki na ƙarshe waɗansu za su ridda daga imani, suna maida hankali ga ruhohi na ruɗami da koyarwar aljanu.” (1 Timothawus 4:1) I, ra’ayoyi masu lahani suna yin kurari ƙwarai. Saboda haka, Bulus ya roƙi abokinsa da yake ƙauna Timothawus: “Ya Timothawus, ka tsare abin da aka damƙa maka, kana bijire ma maganganu na saɓo da kuma tsayayyar ilimin da ana ce da shi hakanan a ƙaryace; abin da waɗansu cikin shaidarsa sun kuskure wajen imani.”—1 Timothawus 6:20, 21.
16, 17. Menene Allah ya ba mu amana, kuma ta yaya za mu tsare shi?
16 Ta yaya mu a yau za mu amfana daga wannan kashedi na ƙauna? An ba Timothawus amana—abu mai kyau da zai kula da shi kuma ya tsare shi. Menene wannan? Bulus ya bayyana: “Ka kiyaye kwatancin sahihiyan kalmomi waɗanda ka ji daga gareni, cikin bangaskiya da ƙauna wadda ke cikin Kristi Yesu. Wannan abin kirki fa da aka damƙa maka, ka tsare shi ta wurin Ruhu Mai-tsarki wanda ke zaune cikinmu.” (2 Timothawus 1:13, 14) I, amanar da ke wajen Timothawus ya ƙunshi “sahihiyan kalmomi,” “koyarwa wadda ke bisa ga ibada.” (1 Timothawus 6:3) Cikin jituwa da waɗannan kalmomi, Kiristoci a yau sun ƙudiri aniya su tsare bangaskiyarsu da gaskiya da aka ba su amana.
17 Tsare wannan amana ya ƙunshi gina abubuwa masu kyau irinsu hali mai kyau na nazarin Littafi Mai-Tsarki da nacewa cikin addu’a, yayin da kuma suna aika “nagarta zuwa ga dukan mutane, tun ba waɗanda su ke cikin iyalin imani” ba. (Galatiyawa 6:10; Romawa 12:11-17) Bulus ya ƙara ba da gargaɗi: “Ka bi adalci, ibada, bangaskiya, ƙauna, haƙuri, tawali’u. Ka yi yaƙin kirki na imani, ka ribce rai na har abada, wanda aka kira ka zuwa gareshi, har kuwa ka furta kyakkyawan furci a gaban shaidu masu-yawa.” (1 Timothawus 6:11, 12) Yadda Bulus ya yi amfani da irinsu furci nan “yaƙin kirki na imani” da kuma “ka ribce” ya nuna sarai cewa dole ne mu ƙi da tasiri mai lahani a ruhaniya da ƙwazo da kuma aniyya.
Bukatar Fahimi
18. Ta yaya za mu nuna daidaitawa na Kirista a al’amarin labarai na mutane?
18 Hakika, a yin yaƙin kirki na imani ana bukatar fahimi. (Misalai 2:11; Filibbiyawa 1:9) Alal misali, ba zai yi kyau ba idan mun ƙi dukan labarai na mutane. (Filibbiyawa 4:5; Yaƙub 3:17) Ba dukan ra’ayoyin mutane ba ne suka saɓa da Kalmar Allah. Yesu ya yi nuni cewa ya kamata masu ciwo su je wurin likita—mutum mai ilimi sosai. (Luka 5:31) Duk da hanyar magani na kwanakin Yesu a dā, ya gane cewa za a samu amfani ta zuwa wurin likita. Kiristoci a yau suna nuna daidaitawa a al’amarin labarai na mutane, amma suna ƙin kowane abu da zai kawo masu lahani a ruhaniya.
19, 20. (a) Yaya dattiɓai suke amfani da fahimi sa’anda suke taimakon waɗanda suke magana mara hikima? (b) Ta yaya ikklisiya za su bi da waɗanda suka nace wajen ɗaukaka koyarwan ƙarya?
19 Dattiɓai ma suna bukatar fahimi sa’anda aka kira su su taimaka ma waɗanda suke yin magana mara hikima. (2 Timothawus 2:7) A wasu lokutta, waɗanda suke cikin ikklisiya sai su kaure da jayayya game da ƙananan al’amari da kuma yin musu. Don a tsare haɗin kan ikklisiya, ya kamata dattiɓai su yi sauri su daidaita irin matsalolin nan. Duk da haka, suna guje shuka mummunar muraɗi ga ’yan’uwansu kuma ba sa hanzarin ɗaukansu ’yan ridda.
20 Bulus ya kwatanta halin da za a iya ba da taimako. Ya ce: “ ’Yan’uwa, ko an iske mutum a cikin kowane laifi, ku da ku ke masu-ruhaniya, cikin ruhun tawali’u ku komo da irin wannan.” (Galatiyawa 6:1) Yin magana musamman game da Kiristoci masu fama da shakka, Yahuda ya rubuta: “Sai a yi jinƙai, lokacinda suna muhawara da ku; waɗansu kuma sai a yi cetonsu, ana fizge su daga cikin wuta.” (Yahuda 22, 23) Hakika, idan bayan gargaɗi sau da yawa wani ya nace wajen ɗaukaka koyarwar ƙarya, ya kamata dattiɓai su tsai da shawara don su tsare ikklisiyar.—1 Timothawus 1:20; Titus 3:10, 11.
Cika Zukatanmu da Abubuwa da Suka Isa Yabo
21, 22. Game da menene ya kamata mu yi zaɓe, kuma ya kamata muna cika azantanmu da menene?
21 Ikklisiyar Kirista tana ƙyamar kalmomi masu lahani da ke “ci kamar zuganye.” (2 Timothawus 2:16, 17; Titus 3:9) Wannan gaskiya ne idan irin kalmomin nan yana nuna “hikima,” yaudara ta duniya, ra’ayi na ’yan ridda, ko kuma magana da garaje cikin ikklisiya. Yayin da lafiyayyen sha’awa na koyon sabbabin abubuwa yana da amfani, halin son sani da ba shi da linzami zai iya kai mu ga ra’ayoyi masu lahani. Ba ma cikin jahilci game da makiɗan Shaiɗan. (2 Korinthiyawa 2:11) Mun san cewa yana ƙoƙari sosai ya janye hankalinmu don ya rage hidimarmu ga Allah.
22 Yadda muke masu hidima da kyau, bari mu tsaya da ƙarfi bisa koyarwa da ke ta ibada. (1 Timothawus 4:6) Bari mu yi amfani da lokacinmu da kyau ta wurin zaɓan labarai da za mu ji. Sa’annan ra’ayi da Shaiɗan ya hura ba zai jijjiga mu da sauri ba. I, bari mu ci gaba da yin la’akari da “iyakar abin da ke mai-gaskiya, iyakar abin da ya isa bangirma, iyakar abin da ke mai-adalci, iyakar abin da ke mai-tsabta, iyakar abin da ke jawo ƙauna, iyakar abin da ke da kyakkyawan ambato; idan akwai kirki, idan akwai yabo.” Idan mun cika azancinmu da zukatanmu da irin waɗannan abubuwan, Allah kuwa na salama zai zauna tare da mu.—Filibbiyawa 4:8, 9.
Me Muka Koya?
• Ta yaya hikima ta duniya za ta iya yi wa ruhaniyarmu kurari?
• Menene za mu iya yi don mu tsare kanmu daga labarai na lahani na ’yan ridda?
• Ya kamata mu guje wa waɗanne irin maganganu cikin ikklisiya?
• Ta yaya ake nuna daidaitawa ta Kirista a bi da labarai masu yawa a yau?
[Hoto a shafi na 21]
Sanannun jaridu da yawa da littattafai sun saɓa da abubuwan daraja ta Kirista
[Hoto a shafi na 22]
Kiristoci za su iya yin taɗin ra’ayoyi ba tare da zama marasa la’akari ba