Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 12/15 pp. 11-15
  • Ka Sa Ci Gabanka Ya Bayyanu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Sa Ci Gabanka Ya Bayyanu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Muke Sa Ci Gabanmu Na Ruhaniya Ya Bayyanu
  • Ka Zama Gurbi Wajen Yin Magana
  • Nuna Misali Mai Kyau a Halinmu da kuma Ɗabi’armu
  • Ƙauna da Bangaskiya Suna da Muhimmanci
  • Ka Yi Ƙoƙari Ka Sa Ci Gabanka Ya Bayyanu
  • Matasa, Ku Sa Ci Gabanku Ya Bayyanu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • “Dana Cikin Ubangiji, Kaunatacce, Mai-Aminci.”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Ka Sa Ci Gabanka Ya Bayyana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Dattawa da Bayi Masu Hidima​—Ku Bi Misalin Timoti
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 12/15 pp. 11-15

Ka Sa Ci Gabanka Ya Bayyanu

“Ka yi ƙwazo cikin waɗannan al’amura; ka bada kanka gare su sosai; domin cingabanka ya bayanu ga kowa.”—1 TIM. 4:15.

1, 2. Menene muka sani game da Timotawus sa’ad da yake yaro da kuma canjin da ya auku sa’ad da ya kusan shekara ashirin?

SA’AD da yake yaro, Timotawus yana zaune ne a lardin Roma da ke Galatiya, a ƙasar Turkiya ta yanzu. Shekaru da yawa bayan mutuwar Yesu, an kafa ikilisiyoyin Kirista da yawa a wajen. A wani lokaci, Timotawus matashi, mamarsa, da kakarsa suka soma bin Kiristanci kuma suka zama masu ƙwazo a ɗaya daga cikin ikilisiyoyin. (2 Tim. 1:5; 3:14, 15) Babu shakka, Timotawus ya ji daɗin rayuwarsa na matashi Kirista a cikin waɗannan sanannun yankunan. Kwatsam, sai abubuwa suka soma canjawa.

2 Ya soma ne da ziyara ta biyu da manzo Bulus ya kai wajen. A lokacin, mai yiwuwa Timotawus yana gab da shekara ashirin ko kuma farkon shekarunsa na ashirin. A lokacin ziyararsa, mai yiwuwa a Listra, Bulus ya lura cewa ’yan’uwa da suke cikin ikilisiyoyi da ke wajen ‘suna shaidar’ Timotawus. (A. M. 16:2) Babu shakka, Timotawus matashi ya nuna ya manyanta sosai. Da ja-gorar ruhu mai tsarki, Bulus da rukunin dattawa suka ɗora hannunsu a kan Timotawus, suka ware shi don aiki na musamman a cikin ikilisiya.—1 Tim. 4:14; 2 Tim. 1:6.

3. Wane gatan hidima na musamman Timotawus ya samu?

3 Timotawus ya samu gayyata da bai taɓa samu ba, wato, ya zama abokin tafiyar manzo Bulus! (A. M. 16:3) Ka yi tunanin irin mamaki da kuma farin ciki da Timotawus ya yi. A cikin shekaru masu yawa, Timotawus zai riƙa tafiya da Bulus kuma a wani lokaci da wasu, yana hidimomi dabam-dabam a madadin manzanni da kuma dattawa. Bulus da Timotawus sun yi aikin tafiye-tafiye da ya ƙarfafa ’yan’uwa a ruhaniya. (Karanta A. M. 16:4, 5.) Saboda haka, Timotawus ya zama sananne ga Kiristoci da yawa don ci gabansa na ruhaniya. Bayan shekara goma na yin aiki da Timotawus, manzo Bulus ya rubuta zuwa ga Filibiyawa: “Ba ni da kowa wanda hankalinsa ya yi daidai da nasa [Timotawus] ba, wanda zai yi tattalin zamanku da gaskiya. . . . Kun san shaidarsa, kamar yadda ɗa ya ke bauta ma uba, haka ya yi bauta tare da ni zuwa yaɗuwar bishara.”—Filib. 2:20-22.

4. (a) Wane hakki mai girma aka ɗanka wa Timotawus? (b) Waɗanne tambayoyi ne za a iya yi game da kalaman Bulus da ke 1 Timotawus 4:15?

4 Kusan lokacin da Bulus ya rubuta wasiƙa zuwa ga Filibiyawa, ya ɗanka wa Timotawus hakki mai girma, wato, naɗa dattawa da bayi masu hidima. (1 Tim. 3:1; 5:22) A bayane yake cewa Timotawus ya zama amintaccen Kirista mai kula. Duk da haka, a cikin wasiƙar, Bulus ya ƙarfafa Timotawus ya sa ‘ci gabansa ya bayyanu ga kowa.’ (1 Tim. 4:15) Ba Timotawus ya riga ya sa ci gabansa ya bayyanu sosai ba? To, menene Bulus yake nufi da waɗannan kalmomi, kuma yaya za mu amfana daga shawararsa?

Yadda Muke Sa Ci Gabanmu Na Ruhaniya Ya Bayyanu

5, 6. Yaya aka yi wa tsabtar ruhaniya na ikilisiyar Afisa barazana, yaya Timotawus zai kāre ikilisiyar?

5 Bari mu bincika yanayin da suka shafi kalaman da ke 1 Timotawus 4:15. (Karanta 1 Timotawus 4:11-16.) Kafin ya rubuta waɗannan kalaman, Bulus ya yi tafiya zuwa Makidoniya amma ya gaya wa Timotawus ya zauna a Afisa. Me ya sa? Wasu a cikin wannan birnin suna kawo rarrabuwa a cikin ikilisiya ta wajen gabatar da koyarwar ƙarya. Hakkin Timotawus ne ya kāre tsabtar ruhaniya ta ikilisiyar. Yaya zai cim ma wannan? Ta wajen kafa misali mai kyau don wasu su yi koyi da shi.

6 Bulus ya rubuta zuwa ga Timotawus: “Zama gurbi ga masu-bada gaskiya, cikin magana, tasarrufi, ƙauna, bangaskiya, da tsabtar rai.” Bulus ya daɗa: “Ka yi ƙwazo cikin waɗannan al’amura; ka bada kanka gare su sosai; domin cingabanka ya bayanu ga kowa.” (1 Tim. 4:12, 15) Wannan ci gaban ya shafi halaye na ruhaniya na Timotawus ne maimakon wani matsayi nasa. Irin wannan ci gaba ne ya kamata kowane Kirista ya nuna.

7. Menene ake bukata daga dukan waɗanda suke cikin ikilisiya?

7 A yau kamar yadda yake a zamanin Timotawus, da akwai hakkoki dabam-dabam a cikin ikilisiya. Wasu dattawa ne ko bayi masu hidima. Wasu suna hidimar majagaba. Har ila wasu suna more hidimar masu kula masu ziyara, hidima a Bethel, ko kuma hidima a ƙasar waje. Dattawa suna sa hannu a koyarwa dabam-dabam, kamar a manyan taro da taron gunduma. Amma, dukan Kiristoci—maza, mata, da kuma yara suna iya sa ci gabansu ya bayyanu. (Mat. 5:16) Yadda yake a batun Timotawus, ana bukatar Kiristoci da suke da matsayi na musamman su sa halayensu na ruhaniya su bayyanu ga dukan mutane.

Ka Zama Gurbi Wajen Yin Magana

8. Yaya furcinmu yake shafan bautarmu?

8 Hanya ɗaya da Timotawus zai kafa misali mai kyau ita ce a maganarsa. Ta yaya za mu bayyana ci gabanmu a wannan sashen? Furcinmu yana bayyana ko waɗanne irin mutane ne mu. Yesu ya ce: “Daga cikin yalwar zuciya baki ya kan yi magana.” (Mat. 12:34) Yaƙub, ɗan’uwan Yesu ya fahimci yadda furcinmu zai iya shafan bautarmu. Ya rubuta: “Idan kowane mutum yana aza kansa mai-addini ne, shi kuwa ba ya kame harshensa ba amma yana yaudara zuciyatasa, addinin wannan banza ne.”—Yaƙ. 1:26.

9. A waɗanne hanyoyi ne ya kamata mu nuna misali mai kyau a furcinmu?

9 Furcinmu zai iya bayyana wa mutane a cikin ikilisiya yawan ci gaba da muka samu a ruhaniya. Saboda haka, maimakon su yi furcin da bai dace ba, maganganun banza, baƙar magana, ko magana ta ɓacin rai, Kiristoci da suka manyanta suna ƙoƙarin su ƙarfafa, da kuma yin ta’aziyya. (Mis. 12:18; Afis. 4:29; 1 Tim. 6:3-5, 20) Kasancewa a shirye mu yi magana don mu kāre mizanai mai girma na Allah da kuma game da sha’awarmu na yin rayuwa daidai da mizanan suna iya nuna ibadarmu ga Allah. (Rom. 1:15, 16) Babu shakka mutane masu zuciyar kirki za su lura da yadda muke yin amfani da kyautar iya magana kuma su bi misalinmu.—Filib. 4:8, 9.

Nuna Misali Mai Kyau a Halinmu da kuma Ɗabi’armu

10. Me ya sa bangaskiya marar riya take da muhimmanci ga ci gabanmu a ruhaniya?

10 Kirista yana bukatar fiye da furci mai ƙarfafawa don ya nuna misali mai kyau. Faɗin abubuwan da suka dace ba tare da yin su ba zai sa mutum ya zama munafuki. Bulus ya san munafuncin Farisawa da ɓarna da tafarkinsu ya yi. Fiye da sau ɗaya, ya gargaɗi Timotawus game da irin wannan rashin gaskiyar da kuma munafunci. (1 Tim. 1:5; 4:1, 2) Amma Timotawus ba mai riya ba ne. A wasiƙarsa ta biyu zuwa ga Timotawus, Bulus ya rubuta: “An tuna mani da bangaskiya marar-riya wanda ke cikinka.” (2 Tim. 1:5) Duk da haka, Timotawus yana bukatan ya sa mutane su ga cewa shi mai yin gaskiya ne a matsayin Kirista. Yana bukatan ya kafa misali mai kyau ta halinsa.

11. Menene Bulus ya rubuta wa Timotawus game da arziki?

11 A cikin wasiƙunsa biyu da ya rubuta wa Timotawus, Bulus ya ba da shawarwari game da wurare da yawa na ɗabi’a. Alal misali, Timotawus zai guji biɗar arziki. Bulus ya rubuta: “Son kuɗi asalin tushen kowace irin mugunta ne: waɗansu kuwa garin begen samu sun ratse daga imani, sun huda kansu da baƙinciki mai-yawa.” (1 Tim. 6:10) Son arziki alama ce ta rashin ruhaniya. Akasin haka, Kiristoci da suke samun gamsuwa wajen yin rayuwa mai sauƙi, “da abinci da sutura” suna nuna ci gaba a ruhaniya.—1 Tim. 6:6-8; Filib. 4:11-12; Zab. 121:1, 2.

12. Yaya za mu sa mutane su ga ci gabanmu a rayuwarmu?

12 Bulus ya ambata wa Timotawus yadda yake da muhimmanci mata Kirista su “yafa tufafi na ladabi tare da tsantseni da hankali.” (1 Tim. 2:9) Mata masu filako da hankali wajen zaɓan tufafi da yin ado, da kuma wasu wurare na rayuwarsu, suna kafa misalai masu kyau. (1 Tim. 3:11) Wannan mizanin ya shafi Kiristoci maza ma. Bulus ya ƙarfafa masu kula su zama masu ‘kāmewa, masu shimfiɗaɗen hankali, natsattsu.’ (1 Tim. 3:2) Idan muka nuna waɗannan halaye a ayyukanmu na yau da kullum, kowa zai ga ci gabanmu.

13. Kamar Timotawus, yaya za mu kafa misalai masu kyau a ɗabi’a mai kyau?

13 Timotawus yana bukatan ya kafa misali mai kyau a batun ɗabi’a mai kyau. Ta wajen yin amfani da wannan furcin, Bulus yana maganar wani bangare ne na musamman na ɗabi’a, wato, jima’i. Halin Timotawus zai kasance babu zargi musamman a sha’aninsa da mata. Zai bi da “dattijai mata kuma kamar uwaye; ƙanƙanana kamar ’yan’uwa mata, cikin dukan tsabtar rai.” (1 Tim. 4:12; 5:2) Allah ya san da ayyukan lalata da kamar asiri ne kuma babu shakka daga baya ’yan adam za su san da hakan. Hakika, ba za a iya ɓoye nagargarun ayyuka na Kirista ba. (1 Tim. 5:24, 25) Dukan mutanen da ke cikin ikilisiya suna da zarafin bayyana ci gabansu a halinsu da kuma ɗabi’arsu mai kyau.

Ƙauna da Bangaskiya Suna da Muhimmanci

14. Ta yaya Nassosi suka nanata bukatar kasancewa da ƙauna a tsakaninmu?

14 Ƙauna ce fanni na musamman na Kiristanci na gaskiya. Yesu ya gaya wa almajiransa: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yoh. 13:35) Ta yaya za mu nuna irin wannan ƙaunar? Kalmar Allah ta roƙe mu mu riƙa ‘haƙuri da juna cikin ƙauna,’ mu ‘kasance da nasiha zuwa ga junanmu, masu-tabshin zuciya, muna yi ma junanmu gafara,’ da kuma karimci. (Afis. 4:2, 32; Ibran. 13:1, 2) Manzo Bulus ya rubuta: “Ku yi zaman daɗin soyayya da junanku cikin ƙaunar ’yan’uwa.”—Rom. 12:10.

15. Me ya sa ƙauna take da muhimmanci ga dukan mutane, musamman dattawa Kirista?

15 Da a ce Timotawus bai bi da Kiristoci masu bi cikin halin kirki ba, da hakan zai rage abin da zai cim ma a matsayinsa na malami da kuma mai kula. (Karanta 1 Korantiyawa 13:1-3.) A wani sassa, da yake Timotawus ya nuna tabbatacciyar ƙauna ga ’yan’uwansa, tare da nagargarun ayyuka da karimci a madadinsu, hakan ya nuna cewa ya samu ci gaba a ruhaniya. Saboda haka, ya dace a cikin wasiƙarsa zuwa ga Timotawus, manzo Bulus ainihi ya ambata ƙauna a cikin halayen da Timotawus zai kafa misali mai kyau a kai.

16. Me ya sa Timotawus yake bukatan ya kasance da bangaskiya mai ƙarfi?

16 Sa’ad da yake Afisa, an gwada bangaskiyar Timotawus. Wasu mutane suna gabatar da koyarwa da ba ta jitu da gaskiya ta Kirista ba. Wasu kuma suna yaɗa “tatsuniyoyi” ko kuma ra’ayoyin da suka binciko da ba su da amfani ga ruhaniya na ikilisiyar ba. (Karanta 1 Timotawus 1:3, 4) Bulus ya kwatanta irin waɗannan mutane a matsayin masu ‘kumbura, ba sa gane kome ba, amma macuci ne bisa ga tuhuma da muhawara ta kalmomi.’ (1 Tim. 6:3, 4) Timotawus zai yi watsi ne da ra’ayoyi masu lahani da ke shiga cikin ikilisiya? A’a, gama Bulus ya aririci Timotawus ya “yi yaƙin kirki na imani” kuma ya guji “maganganu na saɓo da kuma surutai na banza irin ilimin da ake fadinsu haka nan kawai a ƙaryace.” (1 Tim. 6:12, 20, 21) Babu shakka cewa Timotawus ya bi shawara mai kyau ta Bulus.—1 Kor. 10:12.

17. Ta yaya za a iya gwada bangaskiyarmu a yau?

17 Yana da kyau da aka gaya wa Timotawus cewa “cikin kwanaki na ƙarshe waɗansu za su ridda daga imani, suna maida hankali ga ruhohi na ruɗani da koyarwar aljanu.” (1 Tim. 4:1) Dukan waɗanda suke cikin ikilisiya har da waɗanda suke da hakki suna bukatan su zama kamar Timotawus wajen kasancewa da bangaskiya mai ƙarfi. Ta wajen ƙudurta aniya ɗaukan mataki nan da nan na guje wa ra’ayin ridda, za mu sa a ga ci gabanmu kuma za mu kafa misali mai kyau na bangaskiya.

Ka Yi Ƙoƙari Ka Sa Ci Gabanka Ya Bayyanu

18, 19. (a) Yaya za ka sa ci gabanka ya bayyanu ga kowa? (b) Menene za a bincika a gaba?

18 Hakika, ba a ganin ci gaba na ruhaniya na Kirista na gaskiya a kamaninsa na zahiri, iyawarsa, ko kuma matsayi. Kuma wataƙila ba za a ga hakan ba a shekarun da mutumin ya yi yana hidima a cikin ikilisiya ba. Maimakon hakan, ana ganin ci gaba ta ruhaniya a yadda muke biyayya ga Jehobah a tunaninmu, furcinmu, da kuma halinmu. (Rom. 16:19) Ya kamata mu yi biyayya da umurni mu yi ƙaunar juna kuma mu kasance da bangaskiya mai ƙarfi. Hakika, bari mu yi bimbini bisa kalaman Bulus ga Timotawus kuma mu ba da kanmu a gare su domin ci gabanmu ya bayyanu ga kowa.

19 Wani hali da ke nuna cewa muna ci gaba a ruhaniya kuma mun manyanta shi ne farin ciki, sashe ne na ’yar ruhu mai tsarki na Allah. (Gal. 5:22, 23) Talifi na gaba zai tattauna yadda za mu kasance da farin ciki kuma mu ci gaba da yin hakan a lokacin wahala.

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene mutane za su koya game da mu daga furcinmu?

• Ta yaya ake ganin ci gabanmu a halinmu da kuma ɗabi’a mai kyau?

• Me ya sa ya kamata Kiristoci su nuna misali mai kyau game da ƙauna da bangaskiya?

[Hotunan da ke shafi na 11]

Timotawus matashi ya nuna ya manyanta fiye da shekarunsa

[Hotunan da ke shafi na 13]

Mutane suna ganin ci gabanka?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba