Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 7/1 pp. 14-19
  • “Ku Je Ku Almajirtar”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ku Je Ku Almajirtar”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “An Mallaka Mini Dukkan Iko”
  • Tabbaci na Ƙwarai da Ra’ayi da Ya Dace
  • “Almajirtar da Dukkan Al’ummai”
  • ‘Daga Kowane Harshe’
  • Za Ka Iya Sa Hannu a Hidima da Take da Albarka?
  • Ka Yi Amfani da Fasaloli Dabam Dabam
  • ‘Ku Koya Musu Su Kiyaye Duk Iyakar Abin Da Na Umarce Ku’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • An Koyar Da Su Domin Su Yi Wa’azi Da Kyau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Mutane Daga “Kowane Harshe” Sun Ji Bishara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 7/1 pp. 14-19

“Ku Je Ku Almajirtar”

“An mallaka mini dukkan iko a Sama da ƙasa. Don haka sai ku je ku almajirtar.”—MATIYU 28:18, 19.

1, 2. (a) Wane aiki Yesu ya ba wa mabiyansa? (b) Waɗanne tambayoyi game da umurnin Yesu za a bincika?

BAZARA ce a Isra’ila a shekara ta 33 A.Z., da almajiran Yesu suka taru a kan dutse a Galili. Lokaci ne da Ubangijinsu da aka ta da daga matattu zai haura sama, amma yana da wani muhimmin abin da zai gaya musu. Akwai aikin da Yesu yake son ya ba su. Wane aiki ne? Me almajiransa suka yi game da aikin? Kuma yaya aikin nan ya shafe mu a yau?

2 An rubuta abin da Yesu ya ce a Matiyu 28:18–20: “An mallaka mini dukkan iko a Sama da ƙasa. Don haka sai ku je ku almajirtar da dukkan al’ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki, kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har matuƙar zamani.” Yesu ya yi maganar “dukkan iko,” da “dukkan al’ummai,” da “iyakar abin da,” da kuma “kullum.” Umurninsa da ya ƙunshi waɗannan abubuwa huɗu sun ta da muhimman tambayoyi da za a iya taƙaita haka, me ya sa? a ina? menene? da kuma yaushe? Bari mu yi la’akari da waɗannan tambayoyi ɗaɗɗaya.a

“An Mallaka Mini Dukkan Iko”

3. Me ya sa ya kamata mu yi biyayya da umurnin nan mu almajirtar?

3 Da farko, me ya sa ya kamata mu yi biyayya da umurnin nan mu almajirtar? Yesu ya ce: “An mallaka mini dukkan iko a sama da ƙasa. Don haka sai ku je ku almajirtar.” Kalmar nan “don haka” tana nuna wani muhimmin dalili da ya sa za mu yi biyayya da wannan umurnin. Dalilin shi ne cewa Yesu da ya bayar da umurnin yana da “dukkan iko.” Yaya girman ikonsa yake?

4. (a) Yaya girman ikon Yesu yake? (b) Yaya ya kamata sanin ikon da Yesu yake da shi zai shafe yadda za mu ɗauki umurnin mu almajirtar?

4 Yesu yana da iko a kan ikilisiyarsa, kuma tun shekara ta 1914 yana da iko a kan sabon Mulki na Allah da aka kafa. (Kolosiyawa 1:13; Wahayin Yahaya 11:15) Shi ne babban mala’ika kuma yana da iko a kan miliyoyin mala’iku a sama. (1 Tasalonikawa 4:16; 1 Bitrus 3:22; Wahayin Yahaya 19:14–16) Ubansa ne ya ba shi iko ya halaka “dukkan sarauta da mulki da iko” da suke hamayya da ƙa’idodin adalci. (1 Korantiyawa 15:24–26; Afisawa 1:20–23) Iyakar ikon Yesu ba a kan masu rai kawai ba ne. Shi ne kuma “mai hukunta rayayyu da matattu” yana da ikon da Allah ya ba shi domin ya ta da waɗanda suka mutu. (Ayyukan Manzanni 10:42; Yahaya 5:26–28) Lalle, ya kamata a ɗauki umurnin Wanda yake da iko haka da muhimmanci ƙwarai. Saboda haka, da son ranmu muna ladabi muna kuma biyayya da umurnin Kristi mu ‘je mu almajirtar.’

5. (a) Ta yaya Bitrus ya yi biyayya da kalmomin Yesu? (b) Wace albarka Bitrus ya samu domin biyayyarsa ga umurnin Yesu?

5 Da farko a hidimarsa a duniya, Yesu ya koya wa almajiransa sarai cewa idan sun fahimci ikonsa kuma sun yi biyayya da umurninsa za su sami albarka. A wani lokaci ya gaya wa Bitrus da shi masunci ne: “Zakuɗa da jirgin zuwa wuri mai zurfi, ku saki tarunanku, ku janyo kifi.” Bitrus kuwa ya tabbata cewa babu kifi wajen, saboda haka ya ce wa Yesu: “Maigida, dare farai muna wahala, ba mu kama kome ba.” Amma da sauƙin kai Bitrus ya daɗa cewa: “Amma tun da ka yi magana zan saki tarunan.” Da Bitrus ya yi biyayya da umurnin Kristi, ya kama “kifi jingim.” Bitrus ya yi mamaki ƙwarai, ya “fāɗi a gaban Yesu ya ce, “Ya Ubangiji, wane ni da za ka tsaya kusa da ni, domin ni mutum ne mai zunubi.” Amma Yesu ya ce: “Kada ka ji tsoro. Nan gaba mutane za ka riƙa kamowa.” (Luka 5:1–10; Matiyu 4:18) Me muka koya daga wannan labarin?

6. (a) Menene labarin kamun kifi na mu’ujiza ya nuna game da irin biyayya da Yesu yake bukata? (b) Ta yaya za mu iya yin koyi da Yesu?

6 Ba kafin lokacin da suka yi kamun kifi na ban mamaki ne Yesu ya ba wa Bitrus, Andarawas, da wasu manzanni aiki su zama “masuntan mutane” ba, amma daga baya ne. (Markus 1:16, 17) A bayyane yake cewa Yesu bai so a yi masa biyayya domin an tsorata ba. Ya ba da tabbaci mai kyau da zai sa mutanen su yi masa biyayya. Yadda suka yi biyayya da umurnin Yesu su jefa tarunansu, ya kawo musu albarka mai yawa, haka ma yin biyayya da umurnin Yesu a zama ‘masuntan mutane’ zai kawo albarka mai yawa. Domin bangaskiyarsu manzannin suka yi biyayya. Labarin ya kammala da cewa: “Da suka kawo jiragensu gaci, suka bar kome duka suka bi shi.” (Luka 5:11) Sa’ad da muke ƙarfafa mutane su sa hannu cikin aikin almajirantarwa a yau, muna yin koyi ne da Yesu. Ba kawai muna cewa mutane su yi yadda muka gaya musu ba, amma za mu nuna musu tabbaci da zai sa su yi biyayya da umurnin Kristi.

Tabbaci na Ƙwarai da Ra’ayi da Ya Dace

7, 8. (a) Waɗanne dalilai na Nassi muke da su game da wa’azin Mulki da kuma almajirantarwa? (b) Wane nassi musamman ya motsa ka don ka ci gaba da aikin wa’azi? (Duba hasiya kuma.)

7 Saboda mun fahimci ikon Kristi muna sa hannu a aikin wa’azi na Mulki da kuma na almajirantarwa. Waɗanne dalilai na Nassi muke da su na sa hannu cikin wannan aiki da za mu so ya motsa mutane su ma su yi? Ka yi la’akari da abubuwan da wasu Shaidu masu aminci a ƙasashe da yawa suka yi kuma ka lura da yadda nassosi da suka nuna suke goyon bayan abin da suka ce.

8 Roy ya yi baftisma a shekara ta 1951: “Sa’ad da na keɓe kaina ga Jehovah na yi alkawarin cewa shi zan bauta wa kullum. Ina son na cika alkawarina.” (Zabura 50:14; Matiyu 5:37) Heather ta yi baftisma a shekara ta 1962: “Sa’ad da na tuna da dukan abin da Jehovah ya yi mini, nakan so na nuna masa godiyata ta wurin bauta masa da aminci.” (Zabura 9:1, 9–11; Kolosiyawa 3:15) Hannelore ta yi baftisma a shekara ta 1954: “Duk lokacin da muke hidima, mala’iku suna goya mana baya—babbar gata kuwa! (Ayyukan Manzanni 10:30–33; Wahayin Yahaya 14:6, 7) Honor ta yi baftisma a shekara ta 1969: “Sa’ad da lokacin hukuncin Jehovah ya kai, ba na son wani cikin maƙwabtana ya ce Jehovah da Shaidunsa ba su kula ba, cewa ‘ba a yi masa gargaɗi ba!’ ” (Ezekiyel 2:5; 3:17–19; Romawa 10:16, 18) Claudio ya yi baftisma a shekara ta 1974: “Sa’ad da muke wa’azi ‘Allah yana kallonmu’ har da ‘Kristi’ ma. Ji fa! Sa’ad da muke hidimar fage muna jin daɗin tarayyar nagargarun Abokanmu.”—2 Korantiyawa 2:17.b

9. (a) Menene labarin kamun kifi na Bitrus da sauran manzanni ya nuna game da dalilin da ya dace a yi wa Kristi biyayya? (b) Menene dalilin da ya dace na yi wa Allah da kuma Kristi biyayya a yau, kuma me ya sa?

9 Labarin kamun kifi na ban mamakin ma ya nuna dalilin da ya dace na yin biyayya ga Kristi—wato ƙauna. Sa’ad da Bitrus ya ce, “Wane ni da za ka tsaya kusa da ni, domin ni mutum ne mai zunubi,” Yesu bai ƙyale Bitrus ko kuwa hukunta shi don wani zunubi ba. (Luka 5:8) Yesu bai soki Bitrus domin ya ce masa kada ya tsaya kusa da shi ba. Maimako, Yesu ya ce: “Kada ka ji tsoro.” Razana ba dalili mai kyau ba ne da zai sa a yi wa Kristi biyayya. Maimakon haka, Yesu ya gaya wa Bitrus da abokansa cewa za su zama masuntan mutane. Haka ma a yau ba ma razanar da mutane, ba ma sa su ji sun yi laifi, ba ma sa su ji kunya, kuma mu tilasta musu su yi wa Kristi biyayya ba. Biyayya ta zuci saboda ƙaunar Allah da Kristi ne ke faranta wa Jehovah rai.—Matiyu 22:37.

“Almajirtar da Dukkan Al’ummai”

10. (a) Wane daki ne game da umurnin Yesu na a almajirtar ya kawo wa almajiransa ƙalubale mai girma? (b) Menene almajiran suka yi game da umurnin Yesu?

10 Tambaya ta biyu da aka yi game da umurnin Kristi ita ce, A ina za a yi aikin almajirantarwan? Yesu ya gaya wa mabiyansa: “Ku almajirtar da dukkan al’ummai.” Kafin lokacin hidimar Yesu, ana marabtar mutanen al’umma sa’ad da suka zo Isra’ila su bauta wa Jehovah. (1 Sarakuna 8:41–43) Yawancin waɗanda Yesu ya yi musu wa’azi ma Yahudawa ne, amma yanzu ya gaya wa mabiyansa su je wajen al’ummai. Yana nufi ke nan cewa wajen kamun kifi na almajiransa dā daga cikin ‘ɗan ruwa’ ne—wato, Yahudawa kawai—yanzu zai haɗa da dukan “tekun” mutane. Ko da yake wannan canjin ya kawo wa almajiran ƙalubale, nan da nan suka yi biyayya ga Yesu. Bai kai shekaru 30 bayan da Yesu ya mutu, manzo Bulus ya rubuta cewa an yi wa’azin bishara ba ga Yahudawa kawai ba amma ga “dukkan talikan da ke duniya.”—Kolosiyawa 1:23.

11. Wace faɗaɗawar ‘wuraren kamun kifi’ aka samu tun farkon ƙarni na 20?

11 A kwanan baya bayan nan an ga faɗaɗawar yankin wa’azi mai kama da wannan. A farkon ƙarni na 20 ‘wuraren kamun kifi’ a ƙasashe kalilan ne kawai. Duk da haka, mabiyan Kristi sun yi koyi da misalin Kiristoci na ƙarni na farko kuma suna ɗokin faɗaɗa yankin da suke wa’azi. (Romawa 15:20) A farkon shekarun 1930, suna almajirantarwa a ƙasashe ɗari. A yau, ‘wuraren kamun kifi’ sun kai ƙasashe 235.—Markus 13:10.

‘Daga Kowane Harshe’

12. Wane ƙalubale annabcin da ke a Zakariya 8:23 ya nanata?

12 Almajirantarwa a dukan al’ummai ƙalubale ne ba domin ƙasar kawai ba amma kuma saboda yaren. Jehovah ya annabta ta bakin annabi Zakariya: ‘A waɗannan kwanaki mutum goma daga kowace al’umma da kowane harshe za su kama kafa wurin Bayahude, su ce, ‘Ka yardar mana mu tafi tare da kai, gama mun ji Allah yana tare da ku.’ (Zakariya 8:23) A cika mai girma ta wannan annabcin, “Bayahude” yana wakiltar raguwar shafaffun Kiristoci, sa’in nan kuma “mutum goma” na wakiltar “ƙasaitaccen taro.”c (Wahayin Yahaya 7:9, 10; Galatiyawa 6:16) Ana iya samun wannan ƙasaitaccen taro na almajiran Kristi a al’ummai da yawa, yadda Zakariya ya nuna, suna yare dabam dabam. Mutanen Allah na zamani suna yin wannan fasali na almajirantarwa kuwa? Hakika kuwa.

13. (a) Waɗanne abubuwa suka faru game da harsuna a tsakanin mutanen Allah na zamani? (b) Menene rukunin amintaccen bawan nan suka yi game da ƙarin bukata ta abinci na ruhaniya a harsuna dabam dabam? (Haɗa da akwatin nan “Littattafai Domin Makafi.”)

13 A shekarun 1950, a duk duniya tsakanin Shaidun Jehovah guda 3 cikin 5, Turanci suke yi. Da aka kai shekarun 1980, wannan ya canja ya zama 2 ne cikin 5, a yau kuma 1 ne tak cikin Shaidu 5 ya iya Turanci. Menene rukunin amintaccen bawan nan mai hikima suka yi game da canji a yare haka? Sun yi tanadin abinci na ruhaniya a harsuna da yawa. (Matiyu 24:45) A shekara ta 1950 ana buga littattafanmu cikin harsuna 90, amma a yau sun kai 400. Ana samun albarka a wannan mai da wa mutane na harsuna dabam dabam hankali da aka yi kuwa? Hakika! Kowanne mako a shekara ana samun mutane 5,000 ‘daga kowane harshe’ suna zama almajiran Kristi! (Wahayin Yahaya 7:9) Ƙaruwar tana ci gaba. A wasu ƙasashe “tarunan” suna kamu mai kyau!—Luka 5:6; Yahaya 21:6.

Za Ka Iya Sa Hannu a Hidima da Take da Albarka?

14. Ta yaya za mu taimaki waɗanda suke yankinmu da yarensu dabam ne? (Haɗa da akwatin nan “Bebenci da Almajirantarwa.”)

14 Saboda yawan baƙi da suke shigar wata ƙasa, ana iske matsala a almajirtar da mutane na ‘kowane harshe’ a ƙasar. (Wahayin Yahaya 14:6) Ta yaya za mu taimaki mutane a yankinmu da suke wani yare ba namu ba? (1 Timoti 2:4) A fannin alama, za mu iya yin amfani da abin kamun kifi da ya dace. Ka ba waɗannan mutane littattafai cikin nasu harsuna. Idan zai yiwu ka shirya wani Mashaidi da yake yaren ya ziyarce su. (Ayyukan Manzanni 22:2) Yanzu yana da sauƙi a shirya wannan domin Shaidu da yawa sun koyi yare da ba nasu ba don su taimaki baƙi su zama almajiran Kristi. Rahotanni sun nuna cewa taimakawa a wannan hanyar tana gamsarwa.

15, 16. (a) Waɗanne misalai suka nuna cewa albarka ce a taimaki waɗanda suke wani yare dabam? (b) Waɗanne tambayoyi game da hidima a wani waje da ake wani yare za mu iya tunaninsa?

15 Ka yi la’akari da misalai biyu daga Nedalan inda ake wa’azin Mulki a cikin harsuna 34. Wasu Shaidu aurarru suka ba da kai su je su almajirtar da baƙi waɗanda suke yaren ƙasar Poland. Mutanen suna son saƙon sosai da ya sa maigidan ya rage lokacin aikinsa don ya ƙara kwana ɗaya a mako don tafiyar da nazarin Littafi Mai Tsarki da waɗanda suke son saƙon. Ba da daɗewa ba, aurarrun suna tafiyar da nazari guda 20 na Littafi Mai Tsarki kowane mako. Suka ce: “Hidimarmu ta sa mu farin ciki ƙwarai.” Waɗanda suke almajirantarwa suna farin ciki ƙwarai sa’ad da waɗanda suka ji gaskiyar Littafi Mai Tsarki a nasu yare sun motsa su su nuna godiyarsu. Alal misali, a lokacin wani taro a yarenVietnam, wani tsoho ya tashi tsaye yana neman izinin ya yi magana. Da hawaye a ido ya gaya wa Shaidun: “Na gode ƙoƙarinku a koyon wannan yare mai wuya. Na yi murna ƙwarai da na koyi abubuwa da yawa duk da tsufata daga Littafi Mai Tsarki.”

16 Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa waɗanda suke hidima a ikilisiyoyi na yare suna samun albarka mai yawa. Wasu aurarru daga Britaniya suka ce: “Yin hidima a wani yare abin farin ciki ne da muka samu cikin shekaru 40 na hidimarmu na Mulki.” Za ka iya gyara yanayinka don ka iya sa hannu a irin wannan hidima mai motsawa? Idan kai ɗan makaranta ne, za ka iya koyon sabon yare don shirin sa hannu cikin wannan hidima? Yin haka zai ba da zarafin samun gamsuwa a rayuwa mai kyau. (Karin Magana 10:22) Me ya sa ba za ka tattauna wannan da iyayenka ba?

Ka Yi Amfani da Fasaloli Dabam Dabam

17. Ta yaya za mu iya daɗa kai wurin mutane da yawa a yankinmu na ikilisiya?

17 Gaskiya kam, yanayinmu ba sa yarda mana mu jefa “tarunan” mu a yankuna na wani yare ba. Amma za mu iya kai wajen mutane da yawa fiye da yadda muke yanzu a yankinmu na ikilisiya. Ta yaya? Ta wurin bambanta hanyoyi da muke wa’azi ba a saƙonmu kawai ba. A wurare da yawa mutane suna zama a gidaje da ake tsaronsu. Mutane da yawa kuma ba sa gida lokacin da muka isa gidajensu a hidimarmu ta gida gida. Saboda haka, za mu sa “tarunan” mu a wasu lokatai a wurare dabam dabam. A ta haka, muna yin koyi ne da Yesu. Ya nemi hanyoyi dabam dabam ya yi magana da mutane a wurare dabam dabam.—Matiyu 9:9; Luka 19:1–10; Yahaya 4:6–15.

18. Ta yaya yin wa’azi a yanayi dabam dabam ya zama da amfani? (Haɗa da akwati na “Almajirtar da ’Yan Kasuwa.”)

18 A wasu ɓangarorin duniya, yin wa’azi a wuraren da za a iya samun mutane ita ce hanyar almajirantarwa mafi muhimmanci. Waɗanda suka ƙware a aikin almajirantarwa suna daɗa mai da hankali a yin wa’azi a wurare dabam dabam. Ban da yin wa’azi na gida gida, masu shela suna wa’azi a tashan jirgin sama, ofisoshi, kantuna, wajen ajiye motoci, wajen tsayawar sufuri, a kan tituna, a mashaƙata, a bakin kogi, da kuma wasu wurare. A irin wuraren nan aka sami sababbin Shaidu da aka yi musu baftisma a Hawaii. Idan muka yi amfani da hanyoyi dabam dabam, zai taimake mu mu idar da umurnin Yesu na mu almajirtar.—1 Korantiyawa 9:22, 23.

19. Waɗanne fasalolin umurnin da Yesu ya bayar ne za mu tattauna a talifi na gaba?

19 Aikin da Yesu ya bayar na almajirantarwa ya ƙunshi fiye da dalilin da kuma inda ya kamata mu yi aikin, ya haɗa da abin da za mu yi wa’azinsa da kuma har yaushe za mu ci gaba da yi. Za mu tattauna waɗannan fasaloli biyu na umurnin da Yesu ya ba mu cikin talifi na gaba.

[Hasiya]

a Za mu fara da tambayoyi biyu cikin wannan talifin. Sai kuma mu bincika saura biyun a cikin talifi na gaba.

b Za a iya samun ƙarin dalilai don wa’azi a Karin Magana 10:5; Amos 3:8; Matiyu 24:42; Markus 12:17; Romawa 1:14, 15.

c Domin ƙarin bayani a kan wannan annabci, dubi Hasumiyar Tsaro na 1 ga Yuni, 2001, shafi na 6, da kuma Littafi na 2 na Isaiah’s Prophecy—Light for All Mankind, shafi na 408, da Shaidun Jehovah suka buga.

Ka Tuna?

• Domin waɗanne dalilai da buri muke sa hannu a wa’azin Mulki da almajirantarwa?

• Yaya girman yadda bayin Jehovah a yau suke cika umurnin Yesu su almajirtar da mutanen dukan al’ummai yake?

• Ta yaya za mu iya bambanta hanyoyinmu na ‘kamun kifi,’ kuma me ya sa za mu yi haka?

[Box/Hotuna a shafi na 16]

Littattafai Domin Makafi

Albert, wani dattijo Kirista ne kuma mai hidima na cikakken lokaci da yake zama a Amirka. Makaho ne. Yin amfani da littattafan Littafi Mai Tsarki na rubutun makafi ya taimake shi a hidimarsa har da ayyukansa na mai kula da hidima sosai. Yaya yake bi da aikinsa na ikilisiya?

Ba mu taɓa samun wani mai kula da hidima a ikilisiyarmu da ya fi Albert ba,” in ji James, shugaban dattawan. Albert ɗaya ne cikin makafi 5,000 cikin Amirka da yake samun littattafai na Littafi Mai Tsarki a Turanci da kuma a rubutun makafi na Sfanisanci. Hakika, daga shekara ta 1912 zuwa gaba, rukunin amintaccen bawa sun yi tanadin littattafai da yawa a rubutun makafi. Ta wurin yin amfani da fasaha hanyoyi na zamani, maɗaba’ai na Shaidun Jehovah suna buga miliyoyin shafuffuka kowace shekara cikin harsuna fiye da goma kuma suna rarrabawa a ƙasashe fiye 70. Ka san wani da zai amfana daga littattafai masu tushe daga Littafi Mai Tsarki waɗanda aka buga domin makafi?

[Box/Hoto a shafi na 17]

Bebenci da Almajirantarwa

Shaidu dubbai a kewayen duniya, haɗe da matasa masu ƙwazo sun koyi bebenci don su taimaki kurame su zama almajiran Kristi. Ga sakamakon, a Brazil kawai, an yi wa kurame 63 baftisma a wata shekara kuma Shaidu kurame 35 a wurin yanzu suna hidima ta cikakken lokaci. Da akwai ikilisiyoyi da kuma rukunoni na bebenci 1,200 a dukan duniya. Da’ira ta bebenci da take a Rasha, ita ce ta fi girma cikin Rasha da kuma dukan duniya!

[Akwati a shafi na 18]

Almajirtar da ’Yan Kasuwa

Sa’ad da take ziyarar ’yan kasuwa a ofisoshinsu, wata Mashaidiya a Hawaii ta sadu da mai kula da kamfanin sufuri. Ko da yake ya taƙure, mutumin ya yarda zai yi nazarin Littafi Mai Tsarki na minti 30 kowane mako a ofis ɗinsa. Kowacce ranar Laraba da safe, sai ya gaya wa ma’aikatansa su amsa duk kirar da za a yi masa saboda ya iya mai da hankali ga nazarinsa. Wata Mashaidiya kuma a Hawaii tana nazarin Littafi Mai Tsarki sau ɗaya a mako da mai shagon gyaran takalma. Suna nazarin a kan kanta na shagon ne. Idan mai ciniki ya zo, sai Mashaidiyar ta matsa gefe. Sa’ad da mai cinikin ya tafi sai su ci gaba da nazarin.

An iya samun mai kula da sufuri da mai shagon domin Shaidun sun ɗauki mataki su jefa “tarunan” su ne a wurare dabam dabam. Za ka iya tunanin wani wuri a yankin ikilisiyarka da za ka iya samun mutane da yake da wuya a same su a gida?

[Hoto a shafi na 18]

Za ka iya yin hidima a yanki na wani yare?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba