An Koyar Da Su Domin Su Yi Wa’azi Da Kyau
“Za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”—AYYUKAN MANZANNI 1:8.
1, 2. Wane umarni aka yi wa Bitrus, kuma wa ya ba da umurnin?
“YESU BANAZARE . . . Ya kuma umarce mu mu yi wa mutane wa’azi, mu kuma tabbatar cewa shi ne wanda Allah ya sa mai hukunta rayayyu da matattu.” (Ayyukan Manzanni 10:38, 42) Da waɗannan kalmomi, manzo Bitrus ya yi wa Karniliyus da kuma iyalinsa bayanin umurni da aka yi masa ya zama mai wa’azi.
2 Yaushe ne Yesu ya ba da wannan umurnin? Wataƙila, Bitrus yana tunanin abin da Yesu da ya tashi daga matattu ya faɗa kafin ya haura zuwa sama. A wannan lokacin, Yesu ya gaya wa manzanninsa masu aminci: “Za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.” (Ayyukan Manzanni 1:8) Amma, kafin wannan lokacin, Bitrus ya sani cewa tun da shi almajirin Yesu ne, yana bukatar ya gaya wa wasu game da bangaskiyarsa ga Yesu.
Shekaru Uku na Koyarwa
3. Menene ya faru sa’ad da Yesu ya gayyaci Bitrus ya zama mabiyinsa?
3 Watanni da yawa bayan baftismarsa a shekara ta 29 A.Z., Yesu ya yi wa’azi a wurin da Bitrus da Andarawas suke aikin sū a bakin Tekun Galili. Sun fita kamun dare amma ba su sami kome ba. Duk da haka, Yesu ya gaya musu: “Zakuɗa da jirgin zuwa wuri mai zurfi, ku saki tarunanku, ku janyo kifi.” Da suka yi abin da Yesu ya gaya musu, “suka kamo kifi jingim, har ma tarunansu suka fara kecewa.” Da ganin wannan mu’ujizar, sai tsoro ya kama Bitrus, amma Yesu ya kwantar masa da zuciya yana cewa: “Kada ka ji tsoro. Nan gaba mutane za ka riƙa kamowa.”—Luka 5:4-10.
4. (a) Ta yaya Yesu ya shirya almajiransa su yi wa’azi? (b) Idan aka gwada hidimar Yesu da ta almajiransa wace ta fi girma?
4 Nan da nan, Bitrus da Andarawas da kuma Yakubu da Yahaya ’ya’yan Zabadi suka bar jirginsu suka bi Yesu. Sun kasance tare da Yesu na kusan shekara uku, suna tare da shi a tafiye-tafiyensa na wa’azi kuma ya koyar da su su zama masu wa’azi. (Matiyu 10:7; Markus 1:16, 18, 20, 38; Luka 4:43; 10:9) A ƙarshen wannan lokacin, a ranar 14 ga Nisan, 33 A.Z., Yesu ya gaya musu: “Duk wanda ke gaskatawa da ni, ayyukan da nake yi, shi ma haka zai yi. Har ma zai yi ayyukan da suka fi waɗannan.” (Yahaya 14:12) Mabiyan Yesu za su yi wa’azi da kyau sai dai nasu zai fi faɗaɗawa. Ba da daɗewa ba suka fahimci cewa su da waɗanda za su zama almajirai a nan gaba za su yi wa’azi a “dukkan al’ummai,” har “matuƙar zamani.”—Matiyu 28:19, 20.
5. A waɗanne hanyoyi ne za mu amfana daga yadda Yesu ya koyar da mabiyansa?
5 Muna rayuwa ne a “ƙarewar zamani.” (Matiyu 24:3) Ba kamar almajirai na farko ba, mu ba mu yi tafiya tare da Yesu ba kuma ba mu lura da yadda yake wa’azi ga mutane ba. Duk da haka, za mu amfana daga yadda ya koyar ta wurin karanta Littafi Mai Tsarki da kuma umurnai da ya ba wa mabiyansa. (Luka 10:1-11) Ƙari ga haka, wannan talifi zai tattauna wani abin da yake da muhimmanci da Yesu ya gwada wa almajiransa, wato, halin da ya dace domin aikin wa’azi.
Yin Juyayin Mutane
6, 7. Wane hali ne na Yesu ya sa hidimar sa ta kasance da kyau, kuma ta yaya za mu yi koyi da wannan?
6 Me ya sa Yesu ya yi wa’azi da kyau? Dalili guda shi ne ƙauna da kuma juyayinsa ga mutane. Mai Zabura ya annabta cewa Yesu zai “ji tausayin gajiyayyu da matalauta.” (Zabura 72:13) Hakika, ya cika wannan annabci. Littafi Mai Tsarki ya ba da labarin abin da ya faru a wani lokaci: “Da ya ga taro masu yawa sai ya ji tausayinsu, domin suna shan wahala, suna nan a warwatse kamar tumaki ba makiyayi.” (Matiyu 9:36) Har masu yin zunubi da fahariya sun fahimci juyayinsa kuma sun kusace shi.—Matiyu 9:9-13; Luka 7:36-38; 19:1-10.
7 Mu ma a yau za mu yi wa’azi da kyau idan muka ji juyayin mutane. Kafin ka fita hidima, ka ɗauki ɗan lokaci ka yi bimbini a kan yadda mutane suke bukatar saƙon da kake gabatar musu. Ka yi tunanin matsaloli da suke da su da Mulkin ne kawai zai iya magancewa. Ka ƙuduri niyyar yi wa kowa wa’azi, tun da ba ka san wanda zai karɓi saƙon ba. Wa ya sani ko mutumin da za ka tunƙara a gaba ya yi ta addu’a wani kamar ka ya zo ya taimake shi!
Ƙauna ta Motsa Shi
8. Wajen koyi da Yesu, me ke motsa mabiyansa su yi wa’azin bishara?
8 Albishir da Yesu ya yi shelarsa na cika nufin Jehobah ne, na tsarkake sunansa ne, na ɗaukaka mulkin mallakarsa ne, wato, batutuwa masu muhimmanci da ’yan adam suke fuskanta. (Matiyu 6:9, 10) Domin yana ƙaunar Ubansa, Yesu ya motsa ya kasance da aminci har matuƙa kuma ya yi wa’azi da kyau game da Mulkin da zai magance waɗannan batutuwa. (Yahaya 14:31) Ƙauna take motsa mabiyan Yesu a yau, suna wa’azi da kyau sa’ad da suka fita hidima. Manzo Yahaya ya ce: “Ƙaunar Allah ita ce mu bi umarninsa,” har da umurnin mu yi wa’azin bishara kuma mu yi almajirai.—1 Yahaya 5:3; Matiyu 28:19, 20.
9, 10. Ban da ƙaunar Allah, wace ƙauna ce kuma take motsa mu mu yi wa’azi da kyau?
9 Yesu ya gaya wa mabiyansa: “In dai kuna ƙaunata, za ku bi umarnina. Duk wanda ya san umarnaina, yake kuma binsu, shi ne mai ƙaunata.” (Yahaya 14:15, 21) Saboda haka, ƙaunar Yesu ya kamata ta motsa mu mu yi wa’azi game da gaskiya kuma mu bi sauran abubuwa da Yesu ya umurce mu. A ɗaya cikin bayyanarsa bayan ya tashi daga matattu, Yesu ya aririci Bitrus: “Ka yi kiwon ’ya’yan tumakina. . . . Ka kiyaye tumakina. . . . Ka yi kiwon tumakina.” Me ya kamata ya motsa Bitrus ya yi wannan? Yesu ya ba da amsar sa’ad da ya yi ta tambayar Bitrus: ‘Kana ƙaunata? . . . Kana sona? . . . Kana sona?’ Hakika, ƙaunar da Bitrus yake wa Yesu, sonsa da yake, zai motsa shi ya yi wa’azi da kyau, ya nemi “tumakin” Yesu, kuma daga baya ya kiyaye su a ruhaniya.—Yahaya 21:15-17.
10 A yau, ba mu san Yesu ba a zahiri kamar yadda Bitrus ya san shi. Duk da haka, mun fahimci muhimmancin abin da Yesu ya yi dominmu. Matuƙar ƙauna da ta sa shi ya “mutu saboda kowa,” ta motsa zukatanmu. (Ibraniyawa 2:9; Yahaya 15:13) Muna ji kamar yadda Bulus ya ji, sa’ad da ya rubuta: “Ƙaunar Almasihu gare mu ita ke mallakarmu, . . . Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin waɗanda ke raye, kada su yi zaman ganin dama nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su.” (2 Korantiyawa 5:14, 15) Idan muka ɗauki umurnin Yesu mu yi wa’azi da kyau da muhimmanci, muna nuna cewa mun ɗauki ƙaunar Yesu da martaba, mu ma muna ƙaunarsa. (1 Yahaya 2:3-5) Kada mu ɗauki aikin wa’azi da wasa, domin kada mu nuna cewa ba mu ɗauki hadayar Yesu a bakin kome ba.—Ibraniyawa 10:29.
Kada Mu Ƙyale Wani Abu Ya Rinjaye Mu
11, 12. Domin wane dalili Yesu ya zo duniya, kuma ta yaya ya mai da hankalinsa a kan wa’azi?
11 Sa’ad da Yesu yake gaban Bilatus Babunti, ya ce: “Domin haka musamman aka haife ni, don haka kuma musamman na shigo duniya, domin in shaidi gaskiya.” (Yahaya 18:37) Yesu bai bari kome ya rinjaye shi ba daga yin wa’azi game da gaskiya. Nufin Allah ke nan a gare shi.
12 Hakika, Shaiɗan ya jarrabi Yesu da wannan. Ba da daɗewa ba bayan Yesu ya yi baftisma, Shaiɗan ya yi masa tayin mai da shi mutum mai martaba a wannan duniyar, zai ba shi “dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu.” (Matiyu 4:8, 9) Daga baya, Yahudawa suka so su mai da shi sarki. (Yahaya 6:15) Wasu za su yi tunanin amfanin karɓan wannan tayin, wataƙila su ce idan Yesu ya zama sarki a duniya zai amfani ’yan adam ƙwarai. Amma, Yesu ya ƙi irin wannan tunanin. Hankalinsa yana kan yin wa’azi game da gaskiya.
13, 14. (a) Menene ya kasa rinjayar Yesu daga aikinsa? (b) Ko da yake Yesu ba mamallaki ba ne na abin duniya, menene ya cim ma?
13 Ƙari ga haka, neman arziki bai rinjayi Yesu ba. Saboda haka, bai yi rayuwar mai dukiya ba. Ba shi ma da gidan kansa. A wani lokaci ya ce: “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da wurin kwanansu, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.” (Matiyu 8:20) Sa’ad da Yesu ya mutu, aba mai tsada da aka rubuta cewa ya mallaka ita ce taguwarsa, da sojojin Roma suka yi ƙuri’a a kanta. (Yahaya 19:23, 24) To, za a ce ne rayuwar Yesu hasara ce? Ko kaɗan!
14 Yesu ya yi abin da babu wani mai arzikin da zai iya yi. Bulus ya ce: “Kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu, ko da ya ke shi mawadaci ne, sai ya zama matalauci sabili da ku, domin ta wurin talaucinsa ku wadata.” (2 Korantiyawa 8:9; Filibiyawa 2:5-8) Ko da yake ba mamallaki ba ne na abin duniya, Yesu ya buɗe hanya ga mutane masu tawali’u su more rai madawwami cikin kamilta. Muna masu godiya a gare shi! Kuma a yau muna morewa domin lada da ya samu domin ya mai da hankalinsa ga yin nufin Allah!—Zabura 40:8; Ayyukan Manzanni 2:32, 33, 36.
15. Menene ya fi arziki muhimmanci?
15 Kiristoci a yau da suke yin ƙoƙari su yi koyi da Yesu sun ƙi su ƙyale neman arziki ya rinjaye su. (1 Timoti 6:9, 10) Sun sani cewa arziki yana ba da rayuwar sukuni, amma sun kuma sani cewa babu abin da arziki yake yi domin rayuwarsu ta har abada. Sa’ad da Kirista ya mutu, arzikinsa ba shi da wani muhimmanci a gare shi kamar yadda tufafin Yesu ba su da wani muhimmanci a gare shi sa’ad da ya mutu. (Mai Hadishi 2:10, 11, 17-19; 7:12) Sa’ad da Kirista ya mutu, aba mai muhimmanci da ya mallaka ita ce dangantakarsa da Jehobah da kuma Yesu Kristi.
Hamayya Ba ta Karya Masa Lago Ba
16. Ta yaya Yesu ya fuskanci hamayya?
16 Hamayya ba ta rinjaye Yesu ba daga yin wa’azi game da gaskiya. Sanin cewa hidimarsa a duniya za ta ƙare da mutuwarsa ta hadaya bai karya shi ba. Bulus ya ce game da Yesu: “Domin farin cikin da aka sa gabansa ya daure wa . . .[gungumen azaba], bai mai da shi wani abin kunya ba, yanzu kuma a zaune yake dama ga kursiyin Allah.” (Ibraniyawa 12:2) Ka lura cewa Yesu “bai mai da shi wani abin kunya ba.” Abin da ’yan hamayya suka ce da shi bai dame shi ba. Ya mai da hankalinsa ga yin nufin Allah.
17. Menene za mu koya daga jimirin Yesu?
17 Wajen amfani da darasin jimiri na Yesu, Bulus ya ƙarfafa Kiristoci: “Ku fa, dubi wannan da ya jure irin gāban nan da masu zunubi suka sha yi da shi, don kada ku gaji, ko kuwa ku karai.” (Ibraniyawa 12:3) Hakika, fuskantar hamayya ko kuma ba’a kullum yana iya sa mutum ya karaya. Yana iya gajiyarwa, mutum ya riƙa tsayayya wa yaudarar duniya, wataƙila kuma dangi da suke ƙarfafa mu mu “nemi abin kanmu” ba sa jin daɗi. Duk da haka, kamar Yesu mu zuba wa Jehobah idanu domin taimako sa’ad da muka ƙuduri niyyar saka Mulki farko a rayuwarmu.—Matiyu 6:33; Romawa 15:13; 1 Korantiyawa 2:4.
18. Wane darasi za mu koya daga kalmomin Yesu ga Bitrus?
18 Ƙi da Yesu ya yi ya ƙyale wani abu ya rinjaye shi ya bayyana sa’ad da ya fara gaya wa almajiransa game da mutuwarsa da take zuwa. Bitrus ya ƙarfafa Yesu ya ce “Allah ya sawwaƙe” masa kuma ya tabbatar masa cewa “wannan har abada ba zai same ka ba!” Yesu ya ƙi ya saurari dukan wani abin da zai raunana niyyarsa ya yi nufin Jehobah. Ya juya bayansa ga Bitrus ya ce: “Ka yi nesa da ni, ya Shaiɗan! Tarko kake a gare ni. Ba ka tattalin al’amuran Allah, sai na mutane.” (Matiyu 16:21-23) Dole ne mu ma mu ƙuduri niyyar ƙin tunanin mutane. Maimakon haka, bari ko da yaushe tunanin Allah ya yi mana ja-gora.
Zai Kawo Amfani na Dindindin
19. Ko da yake ya yi mu’ujizai, menene ne ɓangaren hidimar Yesu mafi muhimmanci?
19 Yesu ya yi mu’ujizai masu yawa domin ya nuna cewa shi ne Almasihu. Har ya ta da matattu. Waɗannan ayyukan sun tara mutane, amma Yesu bai zo duniya domin kawai ya yi aiki ga jama’a ba. Ya zo ne ya yi wa’azi game da gaskiya. Ya sani cewa dukan wani abu na zahiri na mutane mai shuɗewa ne. Har waɗanda aka ta da su za su sake mutuwa. Sai dai ta wajen yin wa’azi game da gaskiya zai taimaki mutane su sami rai madawwami.—Luka 18:28-30.
20, 21. Ta yaya Kiristoci suke daidaito wajen ayyukan kirki?
20 A yau wasu mutane suna ƙoƙarin su yi koyi da ayyukan kirki na Yesu ta wajen gina asibitoci da kuma yi wa talakawa hidima. A wasu lokatai ma suna kashe kuɗi mai yawa, kuma hakkan abin yabo ne; amma dukan wani taimako da za su yi na ɗan lokaci ne. Mulkin ne kawai zai magance matsalolin. Saboda haka, Shaidun Jehobah suka mai da hankali wajen yin wa’azin game da gaskiyar Mulki.
21 Hakika, Kiristoci na gaskiya suna ayyukan kirki. Bulus ya rubuta: “To, saboda haka, in hali ya yi, sai mu kyautata wa kowa, tun ba ma waɗanda ke jama’ar masu ba da gaskiya ba.” (Galatiyawa 6:10) A lokatai na bala’i ko kuma sa’ad da wani yake da bukata, kada mu yi jinkirin “kyautata” wa maƙwabtanmu da kuma Kiristoci ’yan’uwanmu. Duk da haka, mu mai da hankalinmu wurin da ya kamata, wato, wurin wa’azi game da gaskiya.
Ka Koya Daga Misalin Yesu
22. Me ya sa Kiristoci suke yi wa maƙwabtansu wa’azi?
22 Manzo Bulus ya rubuta: “Kaitona in ba na yin bishara!” (1 Korantiyawa 9:16) Ba ya wasa da bishara domin wa’azinta rai ne a gare shi da kuma waɗanda suka saurare shi. (1 Timoti 4:16) Haka muke ɗaukan hidimarmu. Muna so mu taimaki maƙwabtanmu. Muna so mu nuna ƙaunarmu ga Jehobah. Muna so mu nuna ƙaunarmu ga Yesu kuma mu nuna godiyarmu don matuƙar ƙauna da ya nuna mana. Saboda haka, muke wa’azin bishara kuma muke zama ba don “muguwar sha’awar zuciya ba, sai dai nufin Allah.”—1 Bitrus 4:1, 2.
23, 24. (a) Wane darassi muka koya daga mu’ujizar kifi? (b) Su waye a yau suke yin wa’azi da kyau?
23 Kamar Yesu, ba ma bari ba’a ko kuma ƙin saƙonmu cikin fushi ya janye mana hankali. Mun koyi darassi daga mu’ujiza da Yesu ya yi sa’ad da ya kira Bitrus ya zama mabiyinsa. Mun fahimci cewa idan muka yi wa Yesu biyayya, muka zuba tarunmu cikin ruwan da kamar babu kome, za mu yi kamu mai yawa. Kiristoci da yawa masu sū na mutane sun sami kamu mai yawa bayan ɗawainiya na shekaru a cikin wurin da kamar babu kome. Wasu sun ƙaura zuwa wurare da suke ba da kamu kuma sun sami kamu a can. Amma, kada mu ƙi zuba tarunmu. Domin mun sani cewa Yesu bai yi yekuwan cewa aikin wa’azi ya ƙare ba a ko’ina a duniya.—Matiyu 24:14.
24 Shaidun Jehobah fiye da miliyan shida a yanzu suna wa’azi a fiye da ƙasashe 230. Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Fabrairu, 2005, za ta fito da rahoton shekara shekara na ayyukansu na shekarar hidima ta 2004. Wannan rahoton zai nuna albarka mai yawa da Jehobah ya sa wa aikin wa’azi. A ɗan lokaci da ya rage wa wannan zamanin, mu ci gaba da tuna kalmomi masu motsawa na Bulus: “Ka yi wa’azin Maganar Allah, ka dimanta a kai ko da yaushe.” (2 Timoti 4:2) Mu ci gaba da yin wa’azi da kyau har sai Jehobah ya ce aiki ya ƙare.
Kamawa daga wannan shekarar, Rahoton Shekarar Hidima na Shaidun Jehobah na Dukan Duniya zai bayyana a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Fabrairu. Maimakon ta 1 ga Janairu.
Za ka Iya Ba da Amsa?
• Ta yaya za mu amfana daga abin da Yesu ya koyar da almajiransa?
• Yaya Yesu ya ɗauki mutane da ya yi wa wa’azi?
• Menene ke motsa mu mu yi wa’azi da kyau?
• A waɗanne hanyoyi ne za mu iya mai da hankalinmu ga yin nufin Allah kamar yadda Yesu ya yi?
[Hoto a shafi na 27]
Za mu yi hidimarmu da kyau idan muka nuna juyayi ga mutane kamar yadda Yesu ya yi
[Hoto a shafi nas 28, 29]
Yesu ya zo duniya ne ainihi domin ya yi wa’azin gaskiya
[Hotuna a shafi na 29]
Shaidun Jehobah sun mai da hankali ne wajen yin wa’azi da kyau