Ka Kasance Da Ra’ayin Kristi Game Da Girma
“Duk wanda ke son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku.”—MATIYU 20:26.
1. Menene ra’ayin duniya game da girma?
KUSA da birnin Masar na Thebes na dā (Karnak na zamani), kusan mil 300 daga kudancin Alkahira, akwai wani mutum-mutumin Fir’auna Amenhotep na III a tsaye mai tsawon ƙafa 60. Za ka gan kanka ɗan mitsitsi idan ka gwada kanka da wannan babbar sifa. An kafa wannan abin tunawa, domin a ɗaukaka sarkin, wannan ya nuna ra’ayin duniya game da girma—da ke sa mutum ya ɗauki kansa da girma kuma ya kwaɓe wa wasu mutunci.
2. Wane misali ne Yesu ya kafa wa mabiyansa, kuma waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu?
2 Ka saɓa wannan ra’ayi na girma da wanda Yesu Kristi ya koyar. Ko da yake shi ne ‘Ubangiji da Malamin’ mabiyansa, Yesu ya koya musu cewa mutum na samun girma daga yi wa wasu hidima. A ranarsa ta ƙarshe a nan duniya, Yesu ya nuna ma’anar abin da ya koyar sa’ad da ya wanke ƙafafun almajiransa. Wannan hidima ce ta tawali’u! (Yahaya 13:4, 5, 14) Ka yi hidima ko a yi maka—wanne ka fi so? Misalin Kristi ya sabonta marmarin ka na zama mai tawali’u kamarsa? Saboda haka, bari mu duba ra’ayin Kristi game da girma da ya bambanta da ra’ayin da ta zama ruwan dare a cikin duniya.
Ka Guje wa Ra’ayin Duniya Game da Girma
3. Waɗanne misalai na Littafi Mai Tsarki ne ya nuna sakamako na baƙin ciki na waɗanda suka nemi ɗaukaka daga wurin mutane?
3 Akwai misalai masu yawa na Littafi Mai Tsarki da suka nuna cewa ra’ayin duniya game da girma tana jawo halaka. Ka yi tunanin Haman mai iko, wanda shahararre ne a fadar sarauta ta Fasiya a kwanakin Esta da Mordekai. Domin yana sha’awar ɗaukaka, wannan ya jawo wa Haman cin mutunci da mutuwa. (Esta 3:5; 6:10-12; 7:9, 10) Nebukadnezzar mai girman kai, wanda ya haukace duk da ƙarfin ikonsa kuma fa? Ya furta tunaninsa na girma da bai dace ba da kalmomin nan: “Ashe, wannan ba ita ce Babila babba wadda ni da kaina na gina, da ƙarfin ikona don ta zama fāɗar sarauta, don darajar ɗaukakata?” (Daniyel 4:30) Bayan haka muna da misalin Hirudus Agaribas na I mai fahariya, wanda ya karɓi ɗaukaka wa kansa maimakon Allah. “Sai tsutsotsi suka yi ta cinsa har ya mutu.” (Ayyukan Manzanni 12:21-23) Domin sun ƙi gane ra’ayin Jehovah game da girma, shi ya kai dukan waɗannan mutane ga cin mutunci.
4. Wanene ya jawo ruhun fahariya na wannan duniyar?
4 Zai dace mu yi amfani da rayuwarmu a hanyar da za ta kawo mana ɗaukaka da daraja. Duk da haka, Iblis yana amfani da wannan sha’awa ta wurin ɗaukaka ruhun fahariya, wadda ke nuna dogon burinsa. (Matiyu 4:8, 9) Kada ku manta cewa shi ne “sarkin zamanin nan,” kuma ya ƙudura ya ɗaukaka tunaninsa a nan duniya. (2 Korantiyawa 4:4; Afisawa 2:2; Wahayin Yahaya 12:9) Tun da shi ke mun san tushen irin wannan tunanin, ya kamata Kiristoci su guje wa ra’ayin duniya game da girma.
5. Abin da aka cim ma, yin suna, da arziki na ba da gamsarwa na dindindin? Ka ba da bayani.
5 Wani ra’ayi da Iblis yake ɗaukakawa shi ne cewa yin suna a duniya, ɗaukaka daga wajen mutane, da kuɗi cike da aljihu suna kawo farin ciki a rayuwa. Gaskiya ne? Abin da aka cim ma, yin suna, da arziki zai iya kawo rayuwa mai gamsarwa kuwa? Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu kada mu yarda wa irin wannan tunanin ya ruɗar da mu. Sulemanu, Sarki mai hikima ya rubuta: “Na gane dalilin da ya sa mutane suke aiki ƙwarai don su ci nasara, so suke su fi kowa samu. Wannan ma aikin banza ne harbin iska kawai.” (Mai Hadishi 4:4) Mutane da yawa da suka ba da rayuwarsu ga samun arziki a wannan duniyar za su iya ba da shaidar gaskiyar wannan hurarriyar shawara ta Littafi Mai Tsarki. Misali guda shi ne na mutumin da ya taimaka ya zana, ya ƙera, kuma ya gwada kumbo da mutane suke amfani da shi zuwa duniyar wata. Ya ce: “Na yi aiki tuƙuru kuma na zama gwani a aikin da na yi. Duk da haka ya zama wofi, ko marar amfani, wajen samar mini farin ciki da kwanciyar hankali na dindindin.”a Ra’ayin duniya game da girma, a wajen kasuwanci, guje-guje, ko wartsakarwa, bai kawo gamsarwa ta dindindin.
Samun Girma Daga Hidimar da Ƙauna ta Motsa
6. Menene ya nuna cewa Yakubu da Yahaya suna da ra’ayin da bai dace ba game da girma?
6 Wata aukuwa a rayuwar Yesu ta bayyana abin da girma ya ƙunsa. Yesu da almajiransa suna cikin tafiya zuwa Urushalima domin Idin Ƙetarewa na shekara ta 33 A.Z. A kan hanyarsu, ’ya’yan babarsa biyu, Yakubu da Yahaya, sun nuna ra’ayin da bai dace ba game da girma. Ta wurin mamarsu sun roƙi Yesu: ‘Ka yi umarni mu zauna ɗaya a damanka, ɗaya a hagunka, a mulkinka.’ (Matiyu 20:21) A tsakanin Yahudawa, ana ɗaukan zama a hannun dama ko hagu da girma sosai. (1 Sarakuna 2:19) Yakubu da Yahaya sun so su sami wurare mafi daraja. Suna son su sami wannan matsayi na iko. Yesu ya san abin da suke tunani a zuciyarsu sai ya yi amfani da wannan zarafin ya daidaita ra’ayin da suka nuna da bai dace ba game da girma.
7. Ta yaya ne Yesu ya kwatanta abin da ke sa Kirista ya sami girma ta gaske?
7 Yesu ya sani cewa a wannan duniyar ta fahariya, mutumin da ake ɗauka mai babban matsayi shi ne ke umurta kuma yana iko da mutane, wanda zai iya sa a biya masa bukatarsa a ƙyafatar ido. Amma a tsakanin mabiyan Yesu, hidima ta tawali’u ne ke sa mutum ya zama mai girma. Yesu ya ce: “Duk wanda ke son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku. Wanda duk kuma ke so ya shugabance ku, lalle ne ya zama bawanku.”—Matiyu 20:26, 27.
8. Menene ake nufi da bara, kuma waɗanne tambayoyi ne za mu yi wa kanmu?
8 Kalmar Helenanci da aka fassara “bara” a Littafi Mai Tsarki yana kwatanta wanda yake ba da kansa da ƙwazo da kuma naciya domin ya yi wa wasu hidima. Yesu yana koya wa almajiransa muhimmin darasi: Umurtar mutane su yi wani abu ba ya sa mutum ya sami girma; amma yi wa wasu hidima da ƙauna ta motsa na kawo girma. Ka tambayi kanka: ‘Me zan yi da a ce ni ne Yakubu ko Yahaya? Da zan gane da gaske cewa ana samun girma ta yin hidima domin ƙauna?’—1 Korantiyawa 13:3.
9. Wane misali ne Yesu ya kafa a sha’aninsa da mutane?
9 Yesu ya nuna wa almajiransa cewa yadda duniya take ɗaukan girma ba daidai ba ne da ra’ayin Kristi game da girma. Bai taɓa tunanin nuna ya fi waɗanda yake yi wa hidima ko ƙasƙantar da su ba. Mutane iri-iri—maza, mata, da yara, masu kuɗi, talakawa, da masu iko, da sanannun masu zunubi—duk sun sake a wajensa. (Markus 10:13-16; Luka 7:37-50) Mutane a wani lokaci ba sa haƙuri da waɗanda suke da kumamanci. Amma Yesu ba haka yake ba. Ko da yake a wasu lokatai almajiransa suna garaje kuma suna fāɗa, yana umurtar su a cikin haƙuri, yana kuma nuna musu cewa shi mai tawali’u ne da ƙasƙantar zuciya.—Zakariya 9:9; Matiyu 11:29; Luka 22:24-27.
10. Ta yaya ne rayuwar Yesu ta nuna hidima ta rashin son kai domin mutane?
10 Wannan misali na rashin son kai da Ɗan Allah ya kafa ya nuna abin da girma yake nufi. Yesu bai zo duniya ba don a yi masa hidima amma domin ya yi wa wasu hidima, ya warkar da “cuta iri-iri” kuma ya ’yantar da mutane daga ikon aljani. Ko da yake yana gajiya kuma yana bukatar hutu, yana sa bukatun mutane gaba da nasa, ta wajen daurewa domin ya yi musu ta’aziyya. (Markus 1:32-34; 6:30-34; Yahaya 11:11, 17, 33) Ƙauna tana motsa shi ya yi wa mutane taimako ta ruhaniya, don haka yana tafiyar wurare masu nisa a kan hanyar mai ƙura domin ya yi wa’azin albishir na Mulki. (Markus 1:38, 39) Babu shakka, Yesu ya ɗauka yin wa mutane hidima da muhimmanci.
Ka Yi Koyi da Tawali’un Kristi
11. Waɗanne halaye ne ake bukata daga ’yan’uwa maza da aka naɗa domin su yi hidima na masu kula a cikin ikilisiya?
11 Kusan ƙarshen shekarun 1800, an tattauna halin da ya kamata Kiristoci masu kula su nuna sa’ad da aka zaɓi maza waɗanda za su zama wakilai masu ziyara su biya bukatun mutanen Allah. Waɗanda ake bukata, in ji Zion’s Watch Tower na 1 ga Satumba, shekara ta 1894, su ne maza “masu tawali’u—domin kada su ɗaga kai . . . , masu tawali’u waɗanda ba sa yaɗa ra’ayoyinsu, amma na Kristi ne—ba sa nuna iliminsu, amma na Kalmarsa cikin sauƙi da iko.” Babu shakka, bai kamata Kiristoci su nemi a ba su hakki ba domin su cim ma nasu burin, da fatan za su shahara, su sami iko, kuma su mallaki wasu. Mai kula da yake da tawali’u zai dinga tuna cewa hakkinsa ya haɗa da yin “aiki mai kyau,” ba matsayi mai girma ba domin ya samar wa kansa ɗaukaka. (1 Timoti 3:1, 2) Duka dattawa da bayi masu hidima su ƙoƙarta su yi aikin bauta cikin tawali’u kuma su yi ja-gora cikin tsarkakkan hidima, suna kafa misalin da ya kamata a bi.—1 Korantiyawa 9:19; Galatiyawa 5:13; 2 Timoti 4:5.
12. Waɗanne tambayoyi ne masu burin aikin kula a ikilisiya ya kamata su yi wa kansu?
12 Duk wani ɗan’uwa wanda yake da burin aikin kula da ikilisiya yana bukatar ya tambayi kansa: ‘Ina neman damar in yi wa wasu hidima, ko kuwa so ni ke wasu su yi mini hidima? A shirye ni ke na taimaka wa mutane?’ Alal misali, wani ɗan’uwa matashi zai so ya ba da jawabi a ikilisiyar Kirista amma ba zai so ya taimaki tsofaffi ba. Yana iya jin daɗin tarayya da ’yan’uwa da suke da hakki amma ba zai so ya je wa’azi ba. Wannan ɗan’uwan ya kamata ya tambayi kansa: ‘Ina mai da hankali kawai ne ga fannin hidimar Allah da za a san da ni kuma a yaba mini? Ina so ne in shahara a gaban wasu?’ Idan mun nemi mu ɗaukaka kanmu, babu shakka, ba ma bin misalin Kristi ke nan.—Yahaya 5:41.
13. (a) Ta yaya ne misalin wani mai kula mai ziyara da ya nuna tawali’u zai iya shafan wasu? (b) Me ya sa za a iya cewa tawali’u, ko kuwa ƙasƙantar da rai ba batun zaɓi sonka ba ne ga Kirista?
13 Sa’ad da muka yi ƙoƙarin yin koyi da tawali’un Kristi, wannan zai motsa mu mu yi wa wasu hidima. Ka yi la’akari da misalin wani mai ziyara mai kula da reshe wanda yake bincika ayyuka na wani ofishin reshe na Shaidun Jehovah. Duk da cewa ayyuka sun yi masa yawa da kuma hakki mai nauyi da ke kansa, wannan mai kula ya tsaya ya taimaka wa wani ɗan’uwa da ke faman daidaita wata na’urar ɗinka littattafai. “Abin ya ba ni mamaki!” in ji ɗan’uwan. “Ya gaya mini cewa ya yi aiki da irin wannan na’urar sa’ad da yake matashi kuma da yake hidima a Bethel, ya tuna yadda daidaita wannan na’urar ta yi masa wuya. Mun yi aiki tare a kan na’urar nan na tsawon lokaci duk da cewa yana da wasu muhimman abubuwan da zai yi. Wannan ya burge ni ƙwarai.” Har yanzu wannan ɗan’uwan, wanda shi ma ya zama mai kula a wani ofishin reshe na Shaidun Jehovah, yana tunawa da wannan hali na tawali’u. Kada mu taɓa tunanin cewa mun fi ƙarfin yin ƙananan aiki. Maimako, muna bukatar mu ɗaura wa gindinmu “tawali’u.” Wannan ba batun son rai ba ne. Sashe ne na “sabon mutum” wanda Kirista ya kamata ya yafa.—Filibiyawa 2:3; Kolosiyawa 3:10, 12; Romawa 12:16.
Yadda Za a Sami Ra’ayin Kristi Game da Girma
14. Ta yaya ne yin bimbini a kan dangantakarmu da Allah da ’yan’uwanmu zai taimaka mana mu kasance da ra’ayin Kristi game da girma?
14 Ta yaya ne za mu iya samun ra’ayin da ya dace game da girma? Hanya ta farko ita ce yin bimbini a kan dangantakarmu da Jehovah Allah. Girmansa, ikonsa, da hikimarsa ta ɗaukaka shi fiye da dukan ayyukan mutane. (Ishaya 40:22) Yin bimbini a kan dangantakarmu da ’yan’uwanmu zai taimaka mana mu kasance masu ƙasƙantar rai. Alal misali, muna iya fin wasu sanin wasu ayyuka, amma suna iya fin mu a wasu ɓangarori na rayuwa da ke da muhimmanci sosai, ko kuwa wani ɗan’uwanmu Kirista yana da wasu halaye da ba mu da su. Hakika, mutane da yawa da suke da tamani a idanun Allah sun ƙi su zama shahararru saboda halayensu na tawali’u.—Karin Magana 3:34; Yakubu 4:6.
15. Yaya ne amincin mutanen Allah ya nuna cewa babu wanda yake da dalilin jin cewa ya fi wasu?
15 Labaran Shaidun Jehovah da suke fuskantar gwaji domin bangaskiyarsu ta nuna wannan batu. Sau da yawa, waɗanda duniya take ɗauka talakawa su ne suke riƙe amincinsu ga Allah lokacin da suke fuskantar gwadawa mai tsanani. Yin bimbini a kan irin waɗannan misalan zai taimaka mana mu kasance masu tawali’u kuma zai koya mana ‘kada mu ɗauki kanmu fiye da yadda ya kamata.’—Romawa 12:3.b
16. Ta yaya ne duka a cikin ikilisiya za su yi koyi da Yesu game da girma?
16 Dukan Kiristoci, tsofaffi da matasa, dole ne su kasance da ra’ayin Kristi game da girma. Akwai ayyuka da yawa da ake yi a ikilisiya. Kada ka ji haushi cewa an ba ka ƙaramin aiki. (1 Sama’ila 25:41; 2 Sarakuna 3:11) Iyaye, kuna ƙarfafa yaranku da matasa su yi aikin da aka ba su a Majami’ar Mulki, manyan taro, ko a filin taron gunduma da farin ciki? Suna ganin kuna ƙananan ayyuka? Wani ɗan’uwa da ke aiki a hedkwatar Shaidun Jehovah na duniya ya tuna misalin iyayensa. Ya ce: “Yadda suke ɗaukan aikin tsabtace Majami’ar Mulki da wurin taron gunduma ya nuna mini cewa suna ɗaukan ta da muhimmanci. Sau da yawa suna ba da kansu su yi aikin da zai amfane ikilisiya ko kuwa ’yan’uwanci, kome ƙanƙantar aikin. Irin wannan halin ya taimaka mini in yi kowane irin aiki da son rai a nan Bethel.”
17. A waɗanne hanyoyi ne mata masu tawali’u za su iya su zama tamani ga ikilisiya?
17 Game da sa bukatun wasu a gaban namu, muna da misali mafi kyau na Esta, wadda ta zama sarauniyar Daular Fasiya a ƙarni na 5 K.Z. Ko da yake tana zaune a fada, duk da haka ta yarda ta kasadar da ranta domin mutanen Allah daidai da nufinsa. (Esta 1:5, 6; 4:14-16) Ko da yaya yanayinsu yake, Kiristoci mata suna iya nuna irin halin Esta ta wajen ƙarfafa masu baƙin ciki, a ziyarar marasa lafiya, yin wa’azi, da kuma haɗa kai da dattawa. Irin waɗannan ’yan’uwa mata masu tawali’u gata ce mai tamani ga ikilisiya!
Albarkar Kasance da Ra’ayin Kristi na Girma
18. Wace albarka ake samu idan muka nuna ra’ayin Kristi game da girma?
18 Za ka sami albarka idan ka kasance da ra’ayin Kristi game da girma. Yin hidima marar son kai domin wasu zai kawo maka da kuma mutanen farin ciki. (Ayyukan Manzanni 20:35) Yayin da kake aiki matuƙa na son rai domin ’yan’uwanka, ta haka kana matsa wajensu. (Ayyukan Manzanni 20:37) Mafi muhimmanci shi ne, Jehovah zai ɗauki abin da ka yi domin ɗaukaka lafiyar ’yan’uwa Kiristoci a matsayin hadaya ta yabo zuwa gare shi.—Filibiyawa 2:17.
19. Menene zai zama ƙudurinmu na ra’ayin Kristi game da girma?
19 Kowanenmu na bukatar ya binciki zuciyarsa kuma ya tambayi kansa: ‘Faɗa kawai nake yi cewa a kasance da ra’ayin Kristi game da girma, ko kuwa zan yi aiki tuƙuru domin in yi amfani da shi?’ Ra’ayin Jehovah game da masu girman kai a bayyane yake. (Karin Magana 16:5; 1 Bitrus 5:5) Bari halayenmu ya nuna cewa muna son kasance da ra’ayin Kristi game da girma, ko a cikin ikilisiya ta Kirista, a zaman iyalinmu, ko kuwa a sha’aninmu na yau da kullum da ’yan’uwanmu mutane—mu yi kome domin ɗaukaka da kuma girmama Allah.—1 Korantiyawa 10:31.
[Hasiya]
a Ka duba Hasumiyar Tsaro, 1 ga Mayu,1982, shafi na 3-6, “In Search of Success” (Turanci).
b Domin misalai, duba 1992 Year Book of Jehovah’s Witnesses, shafi na 181-182 da kuma Hasumiyar Tsaro na 1 ga Satumba, 1993, shafi na 27-31 (Turanci).
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Me ya sa ya kamata mu guje wa ra’ayin duniya game da girma?
• Yaya ne Yesu ya ɗauki girma?
• Ta yaya ne masu kula za su iya yin koyi da tawali’un Kristi?
• Menene zai taimake mu mu kasance da ra’ayin Kristi game da girma?
[Akwati a shafi na 27]
Wanene Yake da Ra’ayin Kristi na Girma?
Wanda yake son a yi masa hidima ko kuwa wanda yake son ya yi wa wasu hidima?
Wanda yake neman girma ko kuwa wanda yake yin ƙananan ayyuka da tawali’u?
Mai ɗaukaka kansa ko kuwa wanda ke ɗaukaka wasu?
[Hoto a shafi na 24]
Mutum-mutumi mai girma na Fir’auna Amenhotep na III
[Hoto a shafi na 25]
Ka san abin da ya jawo faɗuwar Haman?
[Hotuna a shafi na 26]
Kana neman zarafin yi wa wasu hidima?