Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 2/1 pp. 3-8
  • Girman Jehovah Ya Fi Ƙarfin Ganewa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Girman Jehovah Ya Fi Ƙarfin Ganewa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Misalan Girman Allah
  • Manyan Ayyuka Kuma na Ban Mamaki
  • Ɗaukakar Jehovah da Daraja da Kuma Girma
  • Halin Ɗabi’a na Allah na Ɗaukaka Shi!
  • Ka Kasance Da Ra’ayin Kristi Game Da Girma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Jehobah Mai Girma Ne Kuma Ya “Isa Yabo Kwarai”
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Mu Yabi Jehobah Allahnmu!
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
  • Ka Ɗaukaka Jehobah Ta Wajen Kasancewa Da Mutunci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 2/1 pp. 3-8

Girman Jehovah Ya Fi Ƙarfin Ganewa

“Mai-girma ne Ubangiji, ya kuwa isa yabo ƙwarai; Girmansa kuma ya fi gaban bincike.”—ZABURA 145:3.

1, 2. Wane irin mutumi ne Dauda, kuma yaya yake ganin kansa wajen Allah?

WANDA ya rubuta waƙar Zabura ta 145 ɗaya ne cikin mutane shahararru na tarihi. Da yake yaro, ya fuskanci ƙato mai makamai kuma ya kashe shi. Da yake shi sarki ne mayaƙi, wannan mai Zaburar ya ci nasarar magabta da yawa. Sunansa Dauda ne, kuma shi ne sarki na biyu a Isra’ila ta dā. Halin kirki na Dauda ya bi shi har bayan mutuwarsa ma, shi ya sa mutane da yawa a yau suka iya saninsa.

2 Duk da yadda Dauda ya ci nasarori, bai yi girman kai ba. Ya rera game da Jehovah: “Sa’anda ina lura da sammanka, aikin yatsotsinka, wata kuma da taurari waɗanda ka sanya; Wane abu ne mutum, da ka ke tuna da shi? Ɗan adam kuma da ka ke ziyartassa?” (Zabura 8:3, 4) Maimakon ya yi tunanin cewa shi kansa ke da girma, Dauda ya yabi Jehovah domin ceton da ya samu daga dukan magabtansa kuma ya ce game da Allah: “Ka kuma ba ni garkuwar cetonka: Nasiharka kuma ta maishe ni mai-girma.” (2 Samu’ila 22:1, 2, 36) Jehovah ya nuna tawali’u a yi wa masu zunubi jinƙai kuma Dauda ya yi godiya ga alherin Allah.

‘Zan Ɗaukaka Allah Sarki’

3. (a) Wane ra’ayi Dauda yake da shi game da mulkin Isra’ila? (b) Yaya girman yadda Dauda yake sha’awar ya yabi Jehovah yake?

3 Ko da yake Allah ne ya naɗa Dauda ya zama sarki, ya aza cewa Jehovah ne ainihi Sarki na Isra’ila. Dauda ya ce: “Mulki naka ne, ya Ubangiji, ka ɗaukaka kuma bisa kan kome.” (1 Labarbaru 29:11) Hakika kuwa Dauda ya girmama Allah cewa Mai Mulki ne! “Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, ya Sarki,” ya rera, “zan albarkaci sunanka kuma har abada abadin. Kowacce rana zan albarkace ka; zan yabi sunanka kuma har abada abadin.” (Zabura 145:1, 2) Muradin Dauda ne ya yabi Jehovah Allah a dukan yini har dawwama.

4. Wace da’awar ƙarya Zabura ta 145 ta fallasa?

4 Zabura ta 145 amsa ce ta rinjaya ga da’awar Shaiɗan na cewa Allah mai sarautar son kai ne, ba ya ba wa halittunsa ’yanci. (Farawa 3:1-5) Wannan zaburar ma ta fallasa ƙaryan Shaiɗan na cewa waɗanda suke biyayya ga Allah suna yin haka ne domin samun ribar kansu, ba domin suna ƙaunar Allah ba. (Ayuba 1:9-11; 2:4, 5) Kamar Dauda, Kiristoci na gaskiya a yau suna amsa tuhumar ƙarya ta Iblis. Suna daraja begensu na rai na har abada cikin sarautar Mulkin saboda suna da burin su yi yabon Jehovah duk dawwama. A yau, miliyoyi sun fara yin haka ta wurin kasance da bangaskiya ga hadayar fansa ta Yesu kuma ta bauta wa Jehovah yadda yake so domin ƙaunarsa ga waɗanda suka keɓe kansu gare shi, masu bauta da suka yi baftisma.—Romawa 5:8; 1 Yohanna 5:3.

5, 6. Waɗanne hanyoyi ne za a albarkaci kuma a yi yabon Jehovah?

5 Ka yi tunanin hanyoyi da yawa da mu bayin Jehovah ke da su da za mu albarkaci kuma yi yabonsa. Za mu iya yin haka cikin addu’a sa’ad da wani abin da muka karanta cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki ya motsa mu. Za mu iya yin yabo da godiya sa’ad da hanyar da Allah yake bi da mutanensa ko sa’ad da wani fasalin halittarsa na mu’ujiza ya motsa mu. Muna albarkaci Jehovah Allah ma sa’ad da muka tattauna nufe-nufensa da ’yan’uwa masu bi a taron Kirista ko kuma a lokacin wani taɗi. Hakika, dukan ‘ayyuka masu-kyau’ da ake yi don batun Mulkin Allah na kawo yabo ga Jehovah.—Matta 5:16.

6 Misalan kwanan bayan nan game da irin ayyukan nan masu kyau sun haɗa da ginin wuraren bauta da yawa da mutanen Jehovah suka yi a ƙasashe masu talauci. An gina yawancin waɗannan ta wurin taimakon kuɗi da ’yan’uwa masu bi a wasu ƙasashe suka bayar ne. Wasu Kiristoci sun taimaka ta ba da kansu su je wuraren nan su sa hannu a aikin gini na Majami’un Mulki. Kuma muhimmin aiki na dukan ayyuka masu kyau shi ne a yabi Jehovah ta wurin yin wa’azin bisharar Mulkinsa. (Matta 24:14) Kamar yadda ayoyi na gaba a Zabura ta 145 suka nuna, Dauda ya fahimci sarautar Allah kuma yana ɗaukaka Mulkinsa. (Zabura 145:11, 12) Kai ma ka fahimci hanya kuwa ta ƙauna da Allah yake sarauta? Kana wa wasu magana a kai a kai kuwa game da Mulkinsa?

Misalan Girman Allah

7. Ka ambata muhimmin dalili na yabon Jehovah.

7 Zabura 145:3 ta ba da muhimmin dalilin yabon Jehovah. Dauda ya rera haka: “Mai-girma ne Ubangiji, ya kuwa isa yabo ƙwarai; Girmansa kuma ya fi gaban bincike.” Girman Jehovah babu iyaka. Mutane ba za su iya su gane ta, su fahimce ta, ko kuma gwada ta ba. Amma za mu amfana sarai ta bincika misalai na girman Jehovah da ya fi ƙarfin ganewa.

8. Menene sararin samaniya ya bayyana game da girma da kuma ikon Jehovah?

8 Ka tuna lokacin da kake ƙauye a hasken wata sai kā kalli sararin sama daddare. Ba ka yi mamakin yawan taurari da suke cikin sararin nan ba? Ba ka motsa ka yabi Jehovah domin girmansa a halittar dukan waɗannan abubuwan sama ba? Amma, abin da ka gani, mitsitsi ne kawai cikin yawan taurari da ke cikin damin taurari har da duniya ma take cikinsa. Ban da haka, an kimanta akwai damin taurari sama da biliyan ɗari, kuma tsari uku ne kawai cikinsu da ake iya gani ba tare da madubin kawo nesa kusa ba. Hakika, taurari da ba a iya ƙirgawa da kuma daminsu da su ne sararin samaniya suna tabbatar da ikon halitta da kuma girman Jehovah da ya fi ƙarfin kome.—Ishaya 40:26.

9, 10. (a) Waɗanne fasalolin girman Jehovah ne suka bayyana game da Yesu Kristi? (b) Yaya ta da Yesu daga matattu ya kamata ya shafe bangaskiyarmu?

9 Ka sake bincika wasu fasalin girman Jehovah—da suka shafi Yesu Kristi. Girman Allah ya bayyana a yadda ya halicci Ɗansa ya yi aiki da shi na shekaru da yawa “gwanin mai-aiki.” (Misalai 8:22-31) Girman ƙaunar Jehovah ta bayyana sa’ad da ya ba da Ɗansa makaɗaici hadayar fansa domin mutane. (Matta 20:28; Yohanna 3:16; 1 Yohanna 2:1, 2) Jiki marar mutuwa mai daraja da Jehovah ya shirya wa Yesu a tashinsa daga matattu ya fi gaban fahimtawa.—1 Bitrus 3:18.

10 Tashin Yesu daga matattu ya haɗa da fasaloli da yawa na girman Jehovah da ya fi ƙarfin ganewa. Babu shakka Allah ya sa Yesu ya tuna da aikin da ya yi a halittar abubuwa marar ganuwa da kuma waɗanda ake gani. (Kolossiyawa 1:15, 16) Waɗannan sun haɗa da wasu halittun ruhu, sararin samaniya, duniya mai ni’ima, da dukan ire-iren rayuka a duniyarmu. Ban da maido da sanin da Ɗansa yake da shi a dukan tarihin rayuwarsa ta samaniya da ta duniya da ya shaida kafin ya zama mutum, Jehovah ya maido wa Yesu tunanin abubuwan da ya shaida na mutum kamili. Hakika, girman Jehovah da ya fi ƙarfin ganewa ya bayyana a ta da Yesu daga matattu. Ban da haka ma, wannan aiki mai girma tabbaci ne cewa zai yiwu a tashe wasu daga matattu. Ya kamata ya ƙarfafa bangaskiyarmu cewa Allah zai maido da miliyoyin matattu da yake tuna da su.—Yohanna 5:28, 29; Ayukan Manzanni 17:31.

Manyan Ayyuka Kuma na Ban Mamaki

11. Wane aiki mai girma na Jehovah aka fara a Fentakos shekara ta 33 A.Z.?

11 Tun da aka ta da Yesu daga matattu, Jehovah ya yi wasu manyan ayyuka kuma na ban mamaki. (Zabura 40:5) A Fentakos shekara ta 33 A.Z., Jehovah ya samo sabuwar al’umma, “Isra’ila na Allah,” almajiran Kristi ne da aka shafe su da ruhu mai tsarki. (Galatiyawa 6:16) A hanya mai girma, wannan sabuwar al’umma ta ruhaniya ta faɗaɗa kuma aka san ta a dukan duniya. Duk da ridda da ta kawo Kiristendam bayan mutuwar manzannin Yesu, Jehovah ya ci gaba da yin ayyuka na ban mamaki don ya tabbatar da nufinsa.

12. Wane tabbaci ne ake da shi cewa akwai Littafi Mai Tsarki cikin dukan manyan harsunan duniya?

12 Alal misali, an tsare Littafi Mai Tsarki sukutum, daga baya kuma aka fassara shi cikin dukan manyan harsuna na duniya a yau. Sau da yawa ana fassarar Littafi Mai Tsarki cikin yanayi mai wuya har da burgar mutuwa a hannun wakilan Shaiɗan. Hakika, an fassara Littafi Mai Tsarki cikin harsuna 2,000 abin da da ba a iya cim ma ba ke nan da ba domin girman Allah Jehovah da ya fi ƙarfin ganewa ba!

13. Tun shekara ta 1914, ta yaya girman Jehovah yake a bayyane game da nufe-nufen Mulkinsa?

13 Girman Jehovah ya bayyana game da nufe-nufen Mulkinsa. Alal misali, a shekara ta 1914, ya naɗa Ɗansa, Yesu Kristi, Sarki na samaniya. Ba da daɗewa ba, Yesu ya soma yaƙi da Shaiɗan da aljanunsa. An fitar da su daga sama kuma aka tura su zuwa duniya, inda suke jiran a saka su a rami. (Ru’ya ta Yohanna 12:9-12; 20:1-3) Tun lokacin, shafaffun mabiyan Yesu sun daɗa shan tsanani. Duk da haka, Jehovah ya toƙara musu a wannan lokacin bayyanuwar Kristi.—Matta 24:3; Ru’ya ta Yohanna 12:17.

14. Wane aiki na ban mamaki ne Jehovah ya yi a 1919, kuma me wannan ya kawo?

14 A shekara ta 1919 kuma, Jehovah ya yi wani aiki na ban mamaki da ya nuna girmansa. Ya maido da shafaffun mabiyan Yesu da aka ɗaure su a rashin aiki na ruhaniya. (Ru’ya ta Yohanna 11:3-11) Tun lokacin, shafaffun suna ta yin wa’azin bishara na Mulkin samaniya da aka kafa. An tattara wasu shafaffu kuma suka cika adadi na 144,000. (Ru’ya ta Yohanna 14:1-3) Kuma ta wurin shafaffun mabiyan Kristi, Jehovah ya kafa tushe na “sabuwar duniya,” na jam’iyyar mutane masu adalci. (Ru’ya ta Yohanna 21:1) Amma menene zai faru a “sabuwar duniya” bayan shafaffu masu aminci duka sun je sama?

15. Wane aiki ne shafaffun Kiristoci suke ja-gorarsa, kuma da wane sakamako?

15 A shekara ta 1935, fitar 1 ga Agusta da na 15 ga Agusta na wannan jaridar suna ɗauke da talifofi da suke game da “taro mai-girma” da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna sura 7. Shafaffun Kiristoci da ƙwazo suna neman kuma kawo waɗannan ’yan’uwa masu bauta daga dukan al’ummai, ƙabilai, mutane, da kuma harsuna cikin tarayyarsu. Wannan “taro mai-girma” za su tsira wa “babban tsananin” tare da begen madawwamin rai cikin Aljanna, su ne za su zauna dindindin cikin “sabuwar duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 7:9-14) Saboda wa’azin Mulki da kuma almajirantarwa da shafaffun Kiristoci suke ja-gorarsa, an samu mutane sama da miliyan shida yanzu da suke da begen rai marar matuƙa a aljanna a duniya. Wa za a yaba wa game da irin ƙaruwar nan duk da hamayya daga Shaiɗan da lalataciyar duniyarsa? (1 Yohanna 5:19) Jehovah ne kaɗai yake haka, ta wurin amfani da ruhunsa mai tsarki.—Ishaya 60:22; Zechariah 4:6.

Ɗaukakar Jehovah da Daraja da Kuma Girma

16. Me ya sa mutane ba za su ga ‘mashahuriyar ɗaukaka’ ta girman Jehovah ba?

16 Ko yaya, “ayyuka masu-iko” da “ayyuka masu-ban mamaki,” na Jehovah suke ba za a taɓa manta da su ba. Dauda ya rubuta: “Tsara za ta yaba ma tsara ayyukanka, su bayyana ayyukanka masu-iko. An yi bimbini da mashahuriyar ɗaukaka ta darajarka, da dukan ayyukanka masu-ban mamaki. Mutane kuma za su ambata ikon ayyukanka masu-ban razana; ni ma in bayyana girmanka.” (Zabura 145:4-6) Duk da haka, har yaya Dauda zai san mashahuriyar ɗaukakar Jehovah da yake “Allah ruhu ne” kuma mutane ba sa ganinsa?—Yohanna 1:18; 4:24.

17, 18. Ta yaya Dauda ya iya ƙara godiyarsa ga ‘mashahurin ayyukan Jehovah da girmansa’?

17 Ko da yake bai ga Allah ba, Dauda yana da hanyoyi da zai ƙara yin godiya ga girman Jehovah. Alal misali, zai iya karatun labarin manyan ayyukan Allah daga Nassosi, halakar duniyar miyagu ta wurin rigyawar dukan duniya. Ƙila, Dauda ya tuna yadda allolin ƙarya na Masar suka sha kunya sa’ad da Allah ya ceci Isra’ilawa daga bautar Masarawa. Irin aukuwan nan tabbacin daraja da girman Jehovah ne.

18 Babu shakka, Dauda ya ci gaba da nuna godiya ga darajar Allah ba ta wurin karatun Nassosi kawai ba amma ta yin bimbini a kansu. Alal misali, ƙila ya yi bimbini a kan abin da ya faru sa’ad da Jehovah ya ba Isra’ila Doka. Aradu sun yi tsawa, an yi walƙiya, da gajimare mai yawa, da kuma ƙara mai girma kamar ta ƙaho. Dutsen Sinai ya girgiza kuma yi hayaƙi. Da suke a tare a ƙasan dutsen, Isra’ilawa suka ji “Kalmomi Goma” daga tsakiyar wuta da gajimare sa’ad da Jehovah yake magana da su ta wurin wakili mala’ika. (Kubawar Shari’a 4:32-36; 5:22-24; 10:4; Fitowa 19:16-20; Ayukan Manzanni 7:38, 53) Lallai kuwa nuni ne mai girma na Jehovah! Masu ƙaunar Kalmar Allah da suke bimbini a kan waɗannan labarai za su motsa ƙwarai domin ‘mashahurin ayyukan Jehovah da girmansa.’ Hakika, a yau muna da cikakken Littafi Mai Tsarki, da ke ɗauke da wahayi dabam dabam na ɗaukaka da ke sahinta girman Jehovah.—Ezekiel 1:26-28; Daniel 7:9, 10; Ru’ya ta Yohanna sura 4.

19. Me zai daɗa sa mu fahimci girman Jehovah?

19 Wata hanya kuma da ƙila Dauda ya burge da girman Allah ita ce ta yin nazarin dokokin Allah ga Isra’ilawa. (Kubawar Shari’a 17:18-20; Zabura 19:7-11) Yin biyayya ga dokokin Jehovah ta daraja al’ummar Isra’ila kuma ta ware su daga sauran mutane. (Kubawar Shari’a 4:6-8) Yadda ya faru wa Dauda, karatun Nassosi a kai a kai, yin bimbini sosai, da kuma yin nazarinsu ƙwarai zai daɗa sa mu fahimci girman Jehovah.

Halin Ɗabi’a na Allah na Ɗaukaka Shi!

20, 21. (a) Zabura 145:7-9 ta ɗaukaka girman Jehovah game da waɗanne halaye ne? (b) Ta yaya halayen Allah da aka ambata a nan suke shafan waɗanda suke ƙaunarsa?

20 Kamar yadda muka lura a ayoyi shida na Zabura ta 145 ta ba mu dalilai masu kyau na yabon Jehovah domin abubuwan da suke game da girmansa da ya fi ƙarfin ganewa. Ayoyi 7 zuwa 9 sun ɗaukaka girman Allah ta yin nuni ga halayensa na ɗabi’a. Dauda ya rera haka: “Za su furta zancen alherinka mai-girma, su raira adalcinka. Ubangiji mai-alheri ne, cike da tausayi kuma; mai-jinkirin fushi, mai-yawan jinƙai kuma. Ubangiji mai-alheri ne ga dukan mutane; Jiyejiyenƙansa a bisa dukan ayyukansa ne.”

21 A nan, Dauda ya nanata nagartan Jehovah da kuma adalcinsa farko—halaye da Shaiɗan Iblis ya tuhume su. Yaya halayen nan suke shafan waɗanda suke ƙaunar Allah kuma suna biyayya da sarautarsa? Hakika, nagartan Jehovah da hanyar sarautarsa ta adalci tana sa masu bauta su yi farin ciki da ba za su iya daina yabonsa ba. Ban da haka ma, nagartan Jehovah ga “kowa” ne. Muna fatan wannan zai taimaki wasu da yawa su tuba kuma su zama masu bauta wa Allah na gaskiya kafin lokaci ya kure.—Ayukan Manzanni 14:15-17.

22. Yaya Jehovah yake bi da bayinsa?

22 Dauda kuma ya daraja halayen da Allah kansa ma ya nanata sa’ad da Yake “gibta a gaban [Musa], ya furta kuma, Ubangiji, Ubangiji, Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai da gaskiya.” (Fitowa 34:6) Saboda haka, Dauda ya ce: “Ubangiji mai-alheri ne, cike da tausayi kuma; mai-jinkirin fushi, mai-yawan jinƙai kuma.” Ko da yake girman Jehovah ya fi ƙarfin ganewa, yana daraja bayinsa mutane ta wurin bi da su cikin alheri. Yana da yawan jinƙai, a shirye yake ya gafarta wa masu zunubi da suka tuba bisa hadayar fansar Yesu. Jehovah ma ba ya saurin fushi, domin yana ba bayinsa zarafin su sha kan kumamancinsu da zai hana su iya shigar sabuwar duniya ta adalci.—2 Bitrus 3:9, 13, 14.

23. Waɗanne halaye masu kyau ne za a bincika a talifi na gaba?

23 Dauda ya ɗaukaka alherin Allah, ko kuma ƙauna ta soyayya. Hakika, sauran Zabura ta 145 ta nuna yadda Jehovah yake nuna halayen nan da kuma yadda bayinsa masu aminci suke martani ga alherinsa. Za a tattauna waɗannan a talifi na gaba.

Yaya Za Ka Amsa?

• Waɗanne hanyoyi ne za mu yabi Jehovah a “dukan yini”?

• Waɗanne misalai suka nuna cewa girman Jehovah ya fi ƙarfin ganewa?

• Ta yaya za mu daɗa godiyarmu ga girman ɗaukaka ta Jehovah?

[Hoto a shafi na 3]

Tsarin taurari na sararin halitta sun tabbatar da girman Jehovah

[Inda aka Dauko]

Anglo-Australian Observatory ne suka bayar, hoton da David Malin ya ɗauka

[Hoto a shafi na 5]

Ta yaya girman Jehovah ta bayyana game da Yesu Kristi?

[Hoto a shafi na 6]

Sa’ad da Isra’ilawa suka karɓi Dokar a Dutsen Sinai, sun ga bahasin ɗaukakar Jehovah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba