DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 142-150
Jehobah Mai Girma Ne Kuma Ya “Isa Yabo Ƙwarai”
145:1-5
Dauda ya lura cewa girman Jehobah ba shi da iyaka kuma hakan ya motsa shi ya yabe shi har abada
145:10-12
Bayin Jehobah masu aminci suna kamar Dauda domin suna shelar ayyuka masu girma na Jehobah a koyaushe
145:14
Dauda yana da tabbaci cewa Jehobah yana so kuma yana da ikon kula da dukan bayinsa