Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 9/1 pp. 4-9
  • An Ƙi Su Ba Dalili

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • An Ƙi Su Ba Dalili
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Tushen Ƙiyayya da Bai Dace Ba
  • “Sa’ad da Mutane Suka Zage Ku”
  • Jimrewa da Zargi
  • Ka Ƙarfafa Bangaskiyarka Yanzu
  • Rayuwa a Hanyar da Take Faranta wa Allah Rai
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Ayuba Ya Ɗaukaka Sunan Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ta Yaya Za Ka Iya Zama Aminin Allah?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Ayuba Mutumi Ne Mai Jimiri Da Aminci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 9/1 pp. 4-9

An Ƙi Su Ba Dalili

“Sun ƙi ni ba dalili.”—YAHAYA 15:25.

1, 2. (a) Me ya sa wasu suke mamaki sa’ad da ake zargin Kiristoci, amma me ya sa ba ma mamakin wannan? (b) Wane azanci na “ƙi” ne za mu yi la’akari da shi a cikin wannan talifin? (Dubi hasiya.)

SHAIDUN JEHOVAH suna ƙoƙarin su bi ƙa’idodin Kalmar Allah a rayuwarsu. Domin haka, suna da farin jini a ƙasashe da yawa. Amma, a wasu lokatai ana ƙaryata su. Alal misali, wani wakilin gwamnati a birnin St. Petersburg a Rasha ya faɗi cewa: “An gaya mana cewa Shaidun Jehovah rukuni ne na asiri, suna karkashe yara kuma suna karkashe junansu.” Amma bayan da ya yi aiki da Shaidun Jehovah a wani taronsu na ƙasashe, mutumin ya ce: “Yanzu na ga mutane ne da suke murmushi, . . . Masu salama masu lumana, suna ƙaunar juna sosai.” Ya daɗa cewa: “Ban san dalilin da ya sa mutane suke ƙarya haka game da su ba.”—1 Bitrus 3:16.

2 Bayin Allah ba sa jin daɗin ƙarya da ake ɗora musu cewa su miyagu ne, amma ba sa mamaki sa’ad da mutane suka kushe su. Yesu ya yi wa mabiyansa gargaɗi: “In duniya ta ƙi ku, ku sani sai da ta ƙi ni kafin ta ƙi ku. . . . Domin a cika maganar da ke rubuce cikin Shari’arsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’ ”a (Yahaya 15:18-20, 25; Zabura 35:19; 69:4) Dā ma can ya gaya wa almajiransa: “In har sun kira maigida Ba’alzabul, to, mutanen gidansa kuma fa?” (Matiyu 10:25) Kiristoci sun sani cewa jimre da wannan zargi yana tattare cikin ‘gungumen azaba’ da suka amince da shi domin su zama mabiyan Kristi.—Matiyu 16:24.

3. Yaya yawan yadda ake tsananta wa masu bauta ta gaskiya yake?

3 Tsananta wa masu bauta ta gaskiya ta soma da daɗewa can baya a lokacin “Habila adali.” (Matiyu 23:34, 35) Bai ƙare da wasu ’yan tsanantawa ba ne kawai. Yesu ya ce ‘kowa kuma zai ƙi’ mabiyansa domin sunansa. (Matiyu 10:22) Ban da haka, manzo Bulus ya rubuta cewa dukan bayin Allah—su yi tsammanin tsanantawa—wato, kowannenmu. (2 Timoti 3:12) Me ya sa?

Tushen Ƙiyayya da Bai Dace Ba

4. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya bayyana tushen dukan ƙiyayya da bai dace ba?

4 Kalmar Allah ta bayyana cewa a farko, akwai mai zugi da ba a gani. Ka yi la’akari da mugun kisan da aka yi wa Habila, mai aminci na farko. Littafi Mai Tsarki ya ce ɗan’uwansa, Kayinu, da ya kashe shi “na Mugun” ne, Shaiɗan Iblis. (1 Yahaya 3:12) Kayinu ya bi halin Shaiɗan, kuma Iblis ya yi amfani da shi ya cika mugun nufinsa. Littafi Mai Tsarki ya yi bayani yadda Shaiɗan ya sa hannu a yi wa Ayuba da kuma Yesu Kristi mugun farmaki. (Ayuba 1:12; 2:6, 7; Yahaya 8:37, 44; 13:27) Littafin Wahayin Yahaya ya bayyana tushen tsanantawa wa mabiyan Yesu sarai, yana cewa: ‘Iblis yana shirin jefa waɗansunku a kurkuku don a gwada ku.’ (Wahayin Yahaya 2:10) Hakika kuwa, Shaiɗan ne tushen dukan ƙiyayya da bai dace ba a kan mutanen Allah.

5. Menene ke motsa ƙiyayyar Shaiɗan a kan masu bauta ta gaskiya?

5 Menene dalilin ƙiyayyar Shaiɗan a kan masu bauta ta gaskiya? Shaiɗan ya yi gāba da “Sarkin zamanai” Jehovah Allah, ta wurin ɗaga kansa. (1 Timoti 1:17; 3:6) Ya ce sarautar Allah tana da tsanani a kan halittu kuma babu wanda yake bauta wa Jehovah da nagarin nufi, cewa mutane suna bauta masa domin son kansu ne kawai. Shaiɗan ya yi da’awar cewa idan aka ƙyale shi, zai iya hana kowa bauta wa Allah. (Farawa 3:1-6; Ayuba 1:6-12; 2:1-7) A cikin ƙaryansa cewa Jehovah mazalunci ne, maƙaryaci, kuma marar riƙon amana, Shaiɗan ya nemi ya ɗaukaka kansa ya zama mamallaki na biyu. Da haka, dalilin fushinsa a kan bayin Allah shi ne yana son su bauta masa.—Matiyu 4:8, 9.

6. (a) Yaya batun ikon mallaka na Jehovah ya shafi kowannenmu? (b) Ta yaya fahimtar wannan batun zai taimake mu mu ci gaba da riƙe aminci? (Duba akwati, shafi na 8.)

6 Ka ga yadda wannan batun ya shafi rayuwarka? Ƙila kai bawan Jehovah ka fahimci cewa yin nufin Allah yana bukatar ƙoƙari ƙwarai, amma fa’idodin sun gaza ƙoƙarin. Idan yanayin rayuwarka ya sa ya zama da wuya, har ma da azaba ka ci gaba da yin biyayya da dokokin Jehovah da kuma ƙa’idodinsa fa? Idan kuma kamar ba ka samun wani lada ne fa? Za ka kammala ne cewa babu amfanin ci gaba da bauta wa Jehovah? Ko kuwa ƙauna ga Jehovah da godiya ga muhimman halayensa ya motsa ka ka ci gaba da tafiya a hanyarsa? (Maimaitawar Shari’a 10:12, 13) Jehovah yana ba wa kowannenmu zarafi mu amsa ƙalubalen Shaiɗan ta wurin ƙyale wahalar da yake jawowa a kanmu.—Karin Magana 27:11.

“Sa’ad da Mutane Suka Zage Ku”

7. Wace dabara ce Iblis yake amfani da ita a ƙoƙarin ya juyar da mu daga Jehovah?

7 Yanzu bari mu bincika sosai wata dabarar da Shaiɗan yake amfani da ita domin ya nuna matsayinsa a batun—wato, yadda yake amfani da zagin ƙarya. Yesu ya kira Shaiɗan “uban ƙarya.” (Yahaya 8:44) Wannan sunan kwatanci, Iblis, da yake nufin “Mai tsegumi,” ya nuna shi ne wanda ya fara tsegunta Allah, nagarin kalmarsa, da kuma sunansa mai tsarki. Iblis yana amfani da habaici, tuhumar ƙarya, da kuma ƙarya kai tsaye a zargin ikon mallakar Jehovah, kuma yana yin hakan ma a ɓata sunan bayin Allah masu aminci. Yakan sa ya zama da wuya sosai su iya jimre wa gwaji mai tsanani, ta wurin jibga zargi a kan waɗannan Shaidu.

8. Ta yaya Shaiɗan ya jawo wa Ayuba zargi, da wane sakamako?

8 Ka yi la’akari da abin da ya faru da Ayuba, wanda sunansa ke nufin “Abin Ƙi.” Bayan ya jawo hasarar mallakarsa, yaransa, da kuma sa shi ciwo, Shaiɗan ya sa ya zama kamar Ayuba mai zunubi ne da Allah yake masa horo. Ko da yake ana daraja Ayuba sosai a dā, a lokacin nan danginsa har da abokansa sun rena shi. (Ayuba 19:13-19; 29:1, 2, 7-11) Ban da haka, ta wurin masu ta’aziyyar azaba, Shaiɗan ya nemi ya “azabta” Ayuba da “maganganu,” da farko, ya yi haka ta wurin nuna cewa lalle Ayuba ya yi wani zunubi ne mai tsanani da ake hukunta shi, cewa shi mai laifi ne. (Ayuba 4:6-9; 19:2; 22:5-10) Lalle wannan na da ban ciwo ga Ayuba!

9. Yaya aka mai da Yesu ya zama kamar mai zunubi?

9 A matsayin wanda ya fi goyon bayan ikon mallaka na Jehovah, Ɗan Allah ya zama abin ƙi na Shaiɗan. Sa’ad da Yesu ya zo duniya, Shaiɗan ya nemi ya ɓata shi a azanci na ruhaniya yadda ya yi da Ayuba, ya so ya sa ya zama cewa Yesu mai zunubi ne. (Ishaya 53:2-4; Yahaya 9:24) Mutane suka ce da shi mashayi kuma mai zarin ci, kuma cewa “mai iska ne.” (Matiyu 11:18, 19; Yahaya 7:20; 8:48; 10:20) An yi masa tuhumar ƙarya cewa yana saɓo. (Matiyu 9:2, 3; 26:63-66; Yahaya 10:33-36) Wannan ya ɓata wa Yesu rai domin ya san cewa wannan ya kawo zargin da bai dace ba ga Ubansa. (Luka 22:41-44) A ƙarshe, aka tsire Yesu sai ka ce la’antacce. (Matiyu 27:38-44) Yesu ya jimre “gāban nan da masu zunubi” suka yi masa.—Ibraniyawa 12:2, 3.

10. Ta yaya raguwar shafaffu suka zama abin ƙi na Shaiɗan a zamanin yau?

10 A zamanin yau, raguwar shafaffun mabiyan Kristi ma sun zama abin ƙi na Iblis. An kwatanta Shaiɗan da “mai ƙarar ’yan’uwan [Kristi] . . . , da yake ƙararsu dare da rana a gun Allahnmu.” (Wahayin Yahaya 12:9, 10) Tun da aka fitar da shi daga sama kuma jefo shi duniya, Shaiɗan ya daɗa ƙoƙarinsa ya ɓata ’yan’uwan Kristi cewa su juji ne. (1 Korantiyawa 4:13) A wasu ƙasashe, ana kiransu ɗarika mai haɗari, yadda aka yi da Kiristoci na ƙarni na farko. (Ayyukan Manzanni 24:5, 14; 28:22) Kamar yadda yake a farko, an ɓata sunansu ta wurin zargin ƙarya. Duk da haka, ta wurin ‘ɗaukaka, wulakanci, da yabo,’ shafaffun ’yan’uwan Kristi, da abokansu “waɗansu tumaki” da ke goya musu baya, suna ƙoƙarin ‘kiyaye umurnan Allah kuma ci gaba da aikin shaida Yesu.’—2 Korantiyawa 6:8; Yahaya 10:16; Wahayin Yahaya 12:17.

11, 12. (a) Me yakan zama dalilin zargi da wasu Kiristoci suke fuskanta? (b) A waɗanne hanyoyi Kirista zai iya shan wuya domin bangaskiyarsa?

11 Amma ba dukan zargin da kowannen bayin Allah ke fuskanta ke domin “adalci” ba. (Matiyu 5:10) Wasu matsaloli domin ajizancinmu ne. Babu wani abin fahariya idan muna ‘yin zunubi ana kuwa mammarinmu muna jimrewa.’ Amma idan Kirista domin ‘nagarta, yana shan wuya domin kuwa, ya yi haƙuri, wannan abin karɓa’ ne wurin Jehovah. (1 Bitrus 2:19, 20) Wane yanayi wannan zai iya faruwa?

12 Wasu sun sha zargi domin sun ƙi su sa hannu a wasu al’adu da ba na Nassi ba. (Maimaitawar Shari’a 14:1) Ana ba matasa Shaidu suna domin sun manne wa mizanan ɗabi’a na Jehovah. (1 Bitrus 4:4) Ana ɗaukan wasu iyaye Kirista da cewa “ba sa kula” ko kuma “masu zalunci” domin sun biɗi jinyar da ba a ƙarin jini wa yaransu. (Ayyukan Manzanni 15:29) Wasu dangi ko maƙwabtan Kiristoci sun kore su domin sun zama bayin Jehovah. (Matiyu 10:34-37) Dukan waɗannan suna bin tafarkin da annabawa da kuma Yesu suka kafa ne a shan wahala domin gaskiya.—Matiyu 5:11, 12; Yakubu 5:10; 1 Bitrus 2:21.

Jimrewa da Zargi

13. Me zai taimake mu mu riƙe daidaitarmu ta ruhaniya sa’ad da muke fuskantar zargi mai tsanani?

13 Sa’ad da muke fuskantar zargi mai tsanani domin bangaskiyarmu, za mu iya sanyin gwiwa yadda annabi Irmiya ya yi, har mu ji ba za mu iya ci gaba da bauta wa Allah ba. (Irmiya 20:7-9) Me zai iya taimaka mana mu daidaita a ruhaniya? Ka ɗauki batun yadda Jehovah yake ɗaukansa. Yana ɗaukan waɗanda suka kasance da aminci masu nasara, ba waɗanda suka kasa ba. (Romawa 8:37) Ka yi ƙoƙari ka hangi waɗanda suka ɗaukaka ikon mallaka na Jehovah duk da kowanne irin cin mutunci da Iblis ya kawo a kansu—maza da mata kamar su Habila, Ayuba, Maryamu mamar Yesu, da wasu amintattu na dā, da kuma ’yan’uwanmu na zamani. (Ibraniyawa 11:35-37; 12:1) Ka yi bimbini game da tafarkinsu na aminci. Wannan babban garke masu aminci suna mana maraba mu haɗu da su a wurin da aka keɓe wa waɗanda suka yi nasara da duniya ta wurin bangaskiyarsu.—1 Yahaya 5:4.

14. Ta yaya yin addu’a sosai za ta ƙarfafa mu mu ci gaba da aminci?

14 Idan ‘alhininmu na damunmu sosai,’ za mu iya zuwa wajen Jehovah cikin addu’a, za ya yi mana ta’aziyya kuma ya ƙarfafa mu. (Zabura 50:15; 94:19) Zai ba mu hikima da za mu jimre da gwaji kuma da zai taimake mu mu mai da hankali ga batun ikon mallakar Jehovah da ya sa bayinsa suke fuskantar ƙiyayya da bai dace ba. (Yakubu 1:5) Jehovah zai kuma iya ba mu “salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta.” (Filibiyawa 4:6, 7) Irin wannan kwanciyar rai daga Allah na taimakonmu mu kasance da lumana kuma mu ƙudura niyya mu fuskanci matsi mai tsanani, da ba za mu yi shakka ko ji tsoro ba. Ta wurin ruhunsa, Jehovah zai iya kiyaye mu a duk abin da ya ƙyale ya faru mana.—1 Korantiyawa 10:13.

15. Me zai taimake mu kada mu yi fushi sa’ad da muke shan wahala?

15 Me zai taimake mu kada mu yi fushin waɗanda suke ƙinmu ba dalili? Ka tuna cewa Shaiɗan da kuma aljannu ne manyan maƙiyanmu. (Afisawa 6:12) Ko da yake waɗansu suna tsananta mana da gangan, da yawa cikin waɗanda suke hamayya da mutanen Allah suna yin haka ne domin rashin sani ko kuma wasu sun iza su su yi hakan. (Daniyel 6:4-16; 1 Timoti 1:12, 13) Jehovah yana son “dukkan [ire-iren] mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya.” (1 Timoti 2:4) Hakika, wasu da suke hamayya da mu dā sun zama ’yan’uwanmu Kiristoci yanzu domin sun lura da nagarin halinmu. (1 Bitrus 2:12) Ban da haka, za mu iya samun wani misali kuma daga ɗan Yakubu, Yusufu. Ko da yake Yusufu ya sha wahala ƙwarai domin ’yan’uwansa, bai yi musu nukura ba. Me ya sa? Domin ya fahimci nufin Jehovah a batun, yana sa abubuwa su auku don su cika nufinsa. (Farawa 45:4-8) Jehovah ma zai iya yin amfani da wata wahala da muke sha don ya ɗaukaka sunansa.—1 Bitrus 4:16.

16, 17. Me ya sa ba za mu yi alhini ba game da ƙoƙarce-ƙoƙarcen ’yan hamayya su hana aikin wa’azi?

16 Ba ma bukatar mu damu ainu idan kamar masu hamayya suna nasara na ɗan lokaci da ke hana ci gaban bishara. Yanzu Jehovah yana raurawar da al’ummai ta wurin wa’azi na dukan duniya da ake yi, kuma muradi suna shigowa. (Haggai 2:7) Yesu Kristi, Nagarin Makiyayi ya ce: ‘Tumakin nan nawa sukan saurari muryata, na san su, suna kuma bina. Ina ba su rai madawwami, . . . ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.’ (Yahaya 10:27-29) Mala’iku masu tsarki ma suna cikin babban girbin nan na ruhaniya. (Matiyu 13:39, 41; Wahayin Yahaya 14:6, 7) Saboda haka, babu abin da ’yan hamayya suka faɗa ko za su yi da zai iya kawar da nufin Allah.—Ishaya 54:17; Ayyukan Manzanni 5:38, 39.

17 Sau da yawa ƙoƙarce-ƙoƙarcen ’yan hamayya don su tsananta mana yakan koma kansu. A wata ƙasar Afirka, an yaɗa ƙaryace-ƙaryace sosai game da Shaidun Jehovah har da cewa su masu bauta wa Iblis ne. Saboda haka, Grace takan gudu zuwa bayan gidansu duk lokacin da Shaidun suka zo gidansu, har su tafi. Wata rana fasto na cocinta ya nuna musu wani littafinmu kuma ya gaya wa dukansu kada su karanta shi domin cewa zai sa su bar imaninsu. Wannan ya sa Grace ta so ta sani game da su. Da Shaidun suka zo gidansu, maimakon ta ɓoye, sai ta soma taɗi da su kuma aka ba ta nata littafin. Aka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ita, kuma a shekara ta 1996 ta yi baftisma. Yanzu Grace tana amfani da lokacinta don ta nemi waɗanda ake yi musu ƙarya game da Shaidun Jehovah.

Ka Ƙarfafa Bangaskiyarka Yanzu

18. Me ya sa muke bukatar mu ƙarfafa bangaskiyarmu kafin gwaji mai tsanani ya taso, kuma ta yaya za mu iya yin hakan?

18 Tun da yake a ko yaushe Shaiɗan zai iya harzuƙa ƙiyayya da bai dace ba, muna bukatar mu ƙarfafa bangaskiyarmu yanzu. Ta yaya za mu yi wannan? Rahoto daga wata ƙasa inda ake tsananta wa mutanen Jehovah ya ce: “Abu ɗaya ya fita sarai: Waɗanda suke da hali mai kyau na ruhaniya kuma suke son gaskiyar Littafi Mai Tsarki sosai ba su da matsalar jurewa sa’ad da gwaji ya zo. Amma waɗanda ba sa zuwan taro a ‘lokaci mai kyau’ kuma ba sa fita wa’azi, kuma suna karya ƙa’ida a ƙananan batutuwa su suke kasawa lokacin da gwaji mai tsanani ya zo.” (2 Timoti 4:2) Idan ka ga inda za ka iya yin gyara, ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka yi hakan.—Zabura 119:60.

19. Menene amincin bayin Allah duk da ƙiyayya da bai dace ba?

19 Yadda masu bauta ta gaskiya suke riƙe aminci duk da ƙiyayyar Shaiɗan tabbaci ne sarai cewa ikon mallaka na Jehovah daidai ne, ya cancanta, kuma yana da adalci. Amincinsu yana faranta wa Allah rai. Ko da mutane za su iya jibga mana zargi, wanda ya fi kowa daraja a sama da ƙasa “ba ya jin kunya a ce da shi Allahn[mu].” Hakika, za a iya ce game da irin waɗannan masu aminci: “Duniya ba ta ma cancanci su zauna a cikinta ba.”—Ibraniyawa 11:16, 38.

[Hasiya]

a An yi amfani da kalmar nan “ƙi” a cikin Nassosi da ma’ana dabam dabam. Littafi Mai Tsarki na Hausa ya yi amfani da furci kamar su, maƙiya, ƙiyayya, ƙi jininsa, fi ƙauna, ko kuma ƙyama a wasu matani. (Maimaitawar Shari’a 21:15, 16) “Ƙi” yana iya nufi ƙin mutum ba da niyyar yi masa wani lahani ba, amma ba ka son ganinsa domin kana ƙyamarsa. Haka nan kuma kalmar nan “ƙi” tana iya nufin ƙiyayya ƙwarai da ta daɗe, wadda take tattare da yin lahani. Wannan ma’anar ce za a tattauna cikin wannan talifin.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Menene dalilin ƙiyayya da bai dace ba da ake wa masu bauta ta gaskiya?

• Ta yaya Shaiɗan ya yi amfani da zargi a ƙoƙarin karye amincin Ayuba da Yesu?

• Ta yaya Jehovah yake ƙarfafa mu mu tsaya da ƙarfi duk da ƙiyayyar Shaiɗan?

[Box/Hoto a shafi na 8]

Sun Fahimci Ainihin Batun

Wani Mashaidin Jehovah a Ukraine, inda aka hana aikin wa’azin Mulki na shekaru 50 ya lura haka: “Ba zai dace a ɗauki yanayin Shaidun Jehovah cewa yin mutane ba ne. . . . Yawancin manyan ma’aikata suna idar da aikin da aka ba su ne. Sa’ad da gwamnati ta canja, haka ma biyayyar ma’aikatan ke canjawa, mu kam ba ma canjawa. Daga cikin Littafi Mai Tsarki mun fahimci ainihin tushen wahalarmu.

“Ba ma ɗaukan cewa masu hamayya kawai dai sun tsane mu ne ba. Abin da yake taimakonmu mu jimre, fahimtar batun da aka tayar a gonar Adnin ne—batun cancantar sarautar Allah. . . . Mun tsaya tsayin daka ba domin wani batun ’yan Adam ba amma domin Ikon Mallaka ne na dukan sararin samaniya. Mun fi fahimtar batun da ke ƙunshe a ciki. Wannan ya ba mu ƙarfi don mu riƙe amincinmu har cikin yanayi mai tsanani.

[Picture]

An tsare Victor Popovych a shekara ta 1970

[Hoto a shafi na 5]

Wanene tushen zargin da aka yi wa Yesu?

[Hotuna a shafi na 7]

Ayuba, Maryamu, da kuma bayin Allah na zamani kamar su Stanley Jones sun ɗaukaka ikon mallaka na Jehovah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba