Ayuba Ya Ɗaukaka Sunan Jehobah
“Albarka ga sunan Ubangiji.”—AYU. 1:21.
1. Wanene wataƙila ya rubuta littafin Ayuba, kuma a wane lokaci?
MUSA yana da kusan shekara 40 sa’ad da ya gudu daga ƙasar Masar zuwa ƙasar Midiya don guje wa fushin Fir’auna. (A. M. 7:23, 29) Sa’ad da yake zaune a ƙasar Midiya, wataƙila ya ji labari game da gwajin da Ayuba wanda ke zaune kusa da su a ƙasar Uz ya fuskanta. Bayan shekaru da yawa, sa’ad da Musa da ’yan Isra’ila suke kusa da Uz gab da fitowarsu daga jeji, wataƙila Musa ya sami bayani game da kwanakin ƙarshe na Ayuba. Tarihin Yahudawa ya nuna cewa Musa ya rubuta littafin Ayuba bayan mutuwar Ayuba.
2. Ta yaya ne littafin Ayuba abin ƙarfafa ne ga bayin Jehobah a zamaninmu?
2 Littafin Ayuba yana ƙarfafa bangaskiyar bayin Allah a zamanin nan. A waɗanne hanyoyi? Labarin ya taimaka mana mu fahimci abubuwa masu muhimmanci sosai da suka faru a sama kuma ya jawo hankali ga zancen ikon mallakar Allah na dukan sararin samaniya. Labarin Ayuba ya kuma zurfafa fahimtarmu game da manufar kasancewa da aminci kuma ya taimaka mana mu fahimci dalilin da ya sa Jehobah yake ƙyale bayinsa su sha wahala a wasu lokatai. Bugu da ƙari, littafin Ayuba ya bayyana cewa Shaiɗan Iblis ne babban Maƙiyin Jehobah da kuma na ’yan adam. Littafin ya kuma nuna cewa mutane ajizai kamar Ayuba za su iya kasancewa da aminci ga Jehobah komi tsananin gwaji. Bari mu bincika wasu abubuwan da suka faru da aka bayyana a littafin Ayuba.
Shaiɗan Ya Gwada Ayuba
3. Menene muka sani game da Ayuba, kuma menene ya sa ya zama abin farmaki ga Shaiɗan?
3 Ayuba mutum ne mai wadata kuma mai tasiri, uban iyali mai halaye masu kyau. Babu shakka shi mai kula da mabukata ne. Mafi muhimmanci, Ayuba yana tsoron Allah. An kwatanta Ayuba a matsayin mutumi “kamili . . . mai-adilci, yana tsoron Allah, yana kuwa bada baya ga mugunta.” Ba wadatar Ayuba da ikonsa ba ne ya sa ya zama abin farmaki ga Shaiɗan Iblis, amma ibadarsa ga Allah ce ta sa.—Ayu. 1:1; 29:7-16; 31:1.
4. Menene aminci?
4 Littafin Ayuba ya fara ne da ba da bayani game da taron da aka yi a sama sa’ad da mala’iku suka tsaya a gaban Jehobah. Shaiɗan ma ya halarci taron, kuma a nan ne ya zargi Ayuba. (Karanta Ayuba 1:6-11.) Ko da yake Shaiɗan ya ambata wadatar Ayuba, ya mai da hankalinsa ne ga ƙalubalantar amincinsa. Kalmar nan “aminci” tana nufin mutunci, marar aibi, adali, da kuma marar kuskure. Kamar yadda yake a cikin Littafi Mai Tsarki, amincin ’yan adam yana nufin bauta wa Jehobah da dukan zuciya.
5. Menene Shaiɗan ya ce game da Ayuba?
5 Shaiɗan ya yi da’awar cewa Ayuba yana bauta wa Allah saboda son kai, ba don nagarta ba. Shaiɗan ya yi zargi cewa Ayuba zai kasance da aminci ga Jehobah ne kawai idan Allah ya ci gaba da ba shi arziki da kāriya. Don amsa zargin da Shaiɗan ya yi, Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya jarraba wannan mutumi mai aminci. A sakamakon hakan, cikin kwana ɗaya, Ayuba ya sami labari cewa an sace ko kuma kashe dabbobinsa, an kashe yawancin bayinsa, kuma yaransa guda goma sun rasa rayukansu. (Ayu. 1:13-19) Wannan hari na Shaiɗan ya sa Ayuba sanyin gwiwa ne? Hurarren labarin ya kwatanta abin da Ayuba ya ce game da bala’in: “Ubangiji ya bayas, Ubangiji ya karɓa, albarka ga sunan Ubangiji.”—Ayu. 1:21.
6. (a) Menene ya faru sa’ad da aka sake yin wani taro a sama? (b) Wanene Shaiɗan yake maganarsa sa’ad da ya ƙalubanci nagartar Ayuba ga Jehobah?
6 Daga baya, an sake yin wani taro a sama. Shaiɗan ya sake jefa wasu zargi game da Ayuba, ya ce: “Ai, fata a bakin fata, hakika dukan abin da mutum ya ke da shi, ya bayar a bakin ransa. Miƙa hannunka yanzu kaɗai, ka taɓa ƙashinsa da namansa, sai shi la’anta ka a fuskarka.” Ka lura cewa Shaiɗan ya faɗaɗa zarginsa. Ta cewa, ‘Dukan abin da mutum yake da shi, ya bayar a bakin ransa,’ Iblis ya ƙalubalanci amincin duk ‘mutumin’ da ke bauta wa Jehobah ba Ayuba kaɗai ba. Bayan hakan, Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya bugi Ayuba da ciwo. (Ayu. 2:1-8) Amma gwajin da Ayuba ya fuskanta bai tsaya a nan ba.
Abin da Za Mu Koya Daga Imanin Ayuba
7. A waɗanne hanyoyi ne matar Ayuba da baƙinsa suka matsa masa?
7 A farkon gwajin, matar Ayuba ta fuskanci irin wahalar da mijinta ya fuskanta. Rashin ’ya’yanta da kuma wadatarsu ya sa ta baƙin ciki sosai. Ta yi baƙin cikin ganin mijinta yana shan wahala domin ciwo mai tsanani. Ta yi wa Ayuba kuka: “Har yanzu kana riƙe da gaskiyarka? Ka la’anta Allah, ka mutu.” Bayan haka, Eliphaz, Bildad, da Zophar suka iso wurinsa, da sunan yi masa ta’aziyya. Maimakon haka, sun yi amfani da tunanin ruɗu kuma suka zama “masu-ta’aziya na ban takaici.” Alal misali, Bildad ya faɗi cewa ’ya’yan Ayuba sun yi zunubi ne shi ya sa suka mutu. Eliphaz kuma ya ce wahalar da Ayuba yake sha horo ne na zunuban da ya yi a dā. Har cewa ya yi wai waɗanda suke da aminci ba su da daraja a gaban Allah! (Ayu. 2:9, 11; 4:8; 8:4; 16:2; 22:2, 3) Duk da irin wannan mugun matsin, Ayuba ya kasance da aminci. Hakika, bai yi daidai ba sa’ad da ya ce “ya fi Allah gaskiya.” (Ayu. 32:2) Duk da haka, ya kasance da aminci har ƙarshe.
8. Wane misali mai kyau ne Elihu ya kafa wa masu ba da shawara a yau?
8 Bayan haka, mun karanta game da Elihu, wanda shi ma ya zo ya ziyarci Ayuba. Elihu ya fara saurarar abubuwan da Ayuba da abokanansa guda uku suka ce. Ko da yake su a mutanen huɗu shi ne ɗan ƙarami, Elihu ya nuna hikima sosai. Ya yi magana da Ayuba da daraja. Elihu ya yaba wa Ayuba domin amincinsa. Amma ya ce Ayuba ya mai da hankali sosai ga nuna cewa shi marar aibi ne. Bayan haka, Elihu ya tabbatar wa Ayuba cewa bauta wa Allah cikin aminci kwalliya ce da za ta biya kuɗin sabulu. (Karanta Ayuba 36:1, 11.) Wannan misali ne mai kyau ga waɗanda suke son su ba da shawara a yau! Elihu ya nuna haƙuri, ya saurara sosai, ya yi yabo a inda ya kamata, kuma ya ba da shawara masu ƙarfafawa.—Ayu. 32:6; 33:32.
9. Yaya Jehobah ya taimaka wa Ayuba?
9 A ƙarshe, Ayuba ya samu baƙo mafi girma! Labarin ya ce: “Ubangiji ya amsa ma Ayuba daga cikin hadari.” Ta wajen yin amfani da tambayoyi, Jehobah ya taimaka wa Ayuba ya daidaita tunaninsa. Da son rai, Ayuba ya karɓi horon, sai ya ce: “Ga ni, ba wani abu ba ne . . . Na tuba cikin ƙura da toka.” Bayan da Jehobah ya yi magana da Ayuba, sai ya nuna fushinsa ga abokansa uku domin ba su faɗa “gaskiya ba.” Ayuba ya yi masu addu’a. Sai “Ubangiji kuma ya fito da Ayuba daga bautar, sa’anda ya yi ma abokansa addu’a: Ubangiji kuwa ya ba Ayuba biyuɗin abin da ya ke da shi a dā.”—Ayu. 38:1; 40:4; 42:6-10.
Yaya Ƙarfin Ƙaunarmu ga Jehobah?
10. Menene ya sa Jehobah bai yi banza ko kuma ya halaka Shaiɗan ba?
10 Jehobah shi ne Mahaliccin sararin samaniya, Mamallakin dukan halitta. Me ya sa bai yi banza da tuhumar Iblis ba? Allah ya san cewa yin banza da Shaiɗan ko halaka shi ba zai daidaita batun da ya ta da ba. Iblis ya yi da’awar cewa Ayuba, wanda fitaccen bawa ne na Jehobah, ba zai kasance da aminci ba idan ya rasa wadatarsa. Amma Ayuba ya kasance da aminci. Bayan haka, Shaiɗan ya yi da’awar cewa kowane mutum zai daina bauta wa Allah idan ya sha wuya ta zahiri. Ayuba ya sha wahala, amma bai karya amincinsa ba. Saboda haka, an ƙaryata Shaiɗan a batun amincin wannan mutumin, duk da cewa ajizi ne. Sauran masu bauta wa Allah fa?
11. Ina yadda Yesu ya ba da cikakken amsa ga zargin Shaiɗan?
11 Watau, duk mai bauta wa Allah da ya kasance da aminci ko da menene Shaiɗan ya sa ya fuskanta, zai nuna cewa zargin da wannan maƙiyin ya yi ƙarya ne. Yesu ya zo duniya kuma ya nuna dalla-dalla cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. Yesu kamiltacce ne, kamar ubanmu na fari, Adamu. Amincin Yesu har mutuwa ya nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne kuma da’awarsa ƙarya ne.—R. Yoh. 12:10.
12. Kowane bawan Jehobah yana da wane zarafi da kuma hakki?
12 Duk da haka, Shaiɗan ya ci gaba da jarraba masu bauta wa Jehobah. Kowannenmu na da zarafi da hakkin nunawa ta amincinmu cewa muna bauta wa Jehobah saboda muna ƙaunarsa, ba don son kai ba. Yaya muke ɗaukan wannan hakkin? Gata ne na musamman mu kasance da aminci ga Jehobah. Mun sami ƙarfafa ta wajen sanin cewa Jehobah yana ba mu ƙarfin jurewa, kuma kamar Ayuba, yana kafa iyaka ga gwajin da muke fuskanta.—1 Kor. 10:13.
Shaiɗan, Mugun Magabci da Kuma Ɗan Ridda
13. Waɗanne bayanai ne littafin Ayuba ya bayyana game da Shaiɗan?
13 Nassosin Ibrananci ya yi bayani dalla-dalla game da matsayin Shaiɗan na rashin kunya ta wajen ƙalubalantar Jehobah da kuma ruɗan ’yan adam. A Nassosin Helenanci na Kirista, mun samu ƙarin bayani game da hamayyar da Shaiɗan yake yi da Jehobah, kuma a littafin Ru’ya ta Yohanna, mun koyi game da kunita ikon mallaka na Jehobah da kuma halakar da Shaiɗan. Littafin Ayuba ya daɗa ga saninmu game da tawayen Shaiɗan. Sa’ad da Shaiɗan ya halarci taron da aka yi a sama, bai je da niyyar yaba wa Jehobah ba. Iblis matsegunci ne kuma mugu ne. Bayan ya zargi Ayuba kuma ya sami izinin jarraba shi, sai Shaiɗan “ya fita daga wurin Ubangiji.”—Ayu. 1:12; 2:7.
14. Wane hali ne Shaiɗan ya nuna wa Ayuba?
14 Saboda haka, littafin Ayuba ya bayyana Shaiɗan a matsayin abokin gaban ’yan adam marar tausayi. Akwai lokaci da ba mu san iyakarsa ba tsakanin taron da aka yi a sama wadda aka ambata a littafin Ayuba 1:6 da kuma wanda aka kwatanta a Ayuba 2:1, da Ayuba ya fuskanci wannan gwajin. Amincin Ayuba ya sa ya yiwu Jehobah ya ce wa Shaiɗan: “Har yanzu ma [Ayuba] yana riƙe da gaskiyassa, ko da ku cakune ni in yi gāba da shi, in hallaka shi ba dalili.” Amma Shaiɗan bai yarda cewa an ƙaryata shi ba. Akasin haka, ya bukaci a ƙara jarraba Ayuba da wani gwajin mai tsanani. Da haka, Iblis ya gwada Ayuba sa’ad da yake da wadata da kuma sa’ad da ya rasa su. Babu shakka, Shaiɗan ba shi da juyayi ga mabukaci ko kuma waɗanda suke fuskantar bala’i. Ya ƙi jinin masu aminci. (Ayu. 2:3-5) Duk da haka, amincin Ayuba ya nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne.
15. Wane irin jituwa ne ke tsakanin ’yan ridda na zamani da Shaiɗan?
15 Shaiɗan ne halitta na farko da ya zama ɗan ridda. ’Yan ridda na zamani suna nuna irin halayen Iblis. Suna iya soma sukar waɗanda suke ikilisiya, dattawa Kirista, ko kuma Hukumar Mulki. Wasu ’yan ridda ba sa so a yi amfani da sunan Jehobah. Ba sa so su koya game da Jehobah ko kuma su bauta masa. Kamar ubansu, Shaiɗan, ’yan ridda suna kai hari ga masu aminci. (Yoh. 8:44) Shi ya sa bayin Jehobah ba sa kusantar su ko kaɗan!—2 Yoh. 10, 11.
Ayuba Ya Ɗaukaka Sunan Jehobah
16. Wane irin hali ne Ayuba ya nuna ga Jehobah?
16 Ayuba ya yi amfani da sunan Jehobah kuma ya yabe shi. Ko lokacin da aka gaya masa game da mutuwar yaransa, Ayuba bai yi saɓo ba ga Allah. Ko da yake cikin rashin sani Ayuba ya ɗora laifin hasarar da ya yi ga Allah, duk da haka, ya ɗaukaka sunan Jehobah. A wani karin magana, Ayuba ya ce: “Ga shi, tsoron Ubangiji, shi ne hikima, rabuwa da mugunta kuma shi ne fahimi.”—Ayu. 28:28.
17. Menene ya taimaka wa Ayuba ya riƙe amincinsa?
17 Menene ya taimaka wa Ayuba ya riƙe amincinsa? Babu Shakka, kafin bala’in ya faɗa masa, ya riga ya ƙulla dangantaka na kud da kud da Jehobah. Ko da yake ba mu da shaidar da ta nuna cewa ya san cewa Shaiɗan ya ƙalubalanci Jehobah, Ayuba ya ƙudurta kasancewa da aminci. Ya ce: “Har in mutu ba ni rabuwa da gaskiyata.” (Ayu. 27:5) Yaya Ayuba ya ƙulla wannan dangantaka na kud da kud? Babu shakka, ya daraja abubuwan da ya ji game da yadda Allah ya bi da Ibrahim, Ishaƙu, da Yakubu, waɗanda danginsa ne na nesa. Kuma ta wajen lura da halitta, Ayuba ya fahimci halayen Jehobah da yawa.—Karanta Ayuba 12:7-9, 13, 16.
18. (a) Ta yaya Ayuba ya nuna ibadarsa ga Jehobah? (b) A waɗanne hanyoyi ne za mu iya yin koyi da misali mai kyau na Ayuba?
18 Abin da Ayuba ya koya ya ba shi marmarin faranta ran Jehobah. Da tunanin cewa wataƙila iyalinsa sun yi zunubi ga Allah ko kuma sun yi “saɓon Allah a zuciyarsu,” Ayuba yana yin hadayu babu fasawa. (Ayu. 1:5) Ko a lokacin da aka gwada shi, Ayuba ya faɗi abubuwa masu kyau game da Jehobah. (Ayu. 10:12) Wannan misali ne mai kyau! Ya kamata mu ma mu riƙa ɗaukan cikakken sani na Jehobah da ƙudurinsa. Mu kasance da halaye masu kyau na nazari, halartan taro, yin addu’a, da kuma yin wa’azin bishara. Ƙari ga haka, muna yin iya ƙoƙarinmu mu sanar da sunan Jehobah. Kuma kamar yadda amincin Ayuba ya faranta wa Jehobah rai, haka ma amincin bayin Allah a yau yake faranta zuciyar Jehobah. Za mu tattauna wannan batun a talifi na gaba.
Ka Tuna?
• Menene ya sa Shaiɗan Iblis ya gwada Ayuba?
• Waɗanne gwaji ne Ayuba ya jimre, kuma menene ya yi?
• Menene zai taimaka mana mu riƙe amincinmu kamar Ayuba?
• Menene muka koya game da Shaiɗan a littafin Ayuba?
[Hotunan da ke shafi na 4]
Labarin Ayuba ya sa mu san batu mai girma na ikon mallakar Allah ta sararin samaniya
[Hotunan da ke shafi na 6]
A wane yanayi ne za a iya jarraba amincinka?