Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 4/1 p. 8-p. 10 par. 15
  • Darussa Daga Littafin Ayuba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Ayuba
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “BAR RANA DA AKA HAIFE NI TA LALACE”
  • (Ayuba 1:1–3:26)
  • “BA NI RABUWA DA GASKIYATA!”
  • (Ayuba 4:1–31:40)
  • “NA TUBA CIKIN ƘURA DA TOKA”
  • (Ayuba 32:1–42:17)
  • Ka Yi Koyi da “Jimrewar Ayuba”
  • Ayuba Ya Ɗaukaka Sunan Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • “Ba Zan Daina Tsare Mutuncina Ba!”
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • Jehobah Ya Warkar da Shi
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • “Sa Zuciya ga Yahweh”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 4/1 p. 8-p. 10 par. 15

Maganar Jehobah Rayayyiya Ce

Darussa Daga Littafin Ayuba

AYUBA uban iyali yana da zama a ƙasar Uz, da yanzu ke Arabiya. Isra’ilawa da yawa suna da zama a ƙasar Masar a lokacin. Ko da yake shi ba Baisra’ile ba ne, Ayuba yana bauta wa Jehobah Allah. Littafi Mai Tsarki ya ce game da shi: “Babu mai-kama da shi cikin duniya, kamili ne, mutum mai-adalci, mai tsoron Allah, yana ƙin mugunta.” (Ayuba 1:8) Wannan bayan mutuwar Yusufu ɗan Yakubu ne kuma kafin Musa ya zama annabi.

Musa da ake tsammanin shi ne ya rubuta littafin Ayuba, wataƙila ya sami tarihin Ayuba ne sa’ad da ya yi shekara 40 a Midiya wadda take kusa da ƙasar Uz. Mai yiwuwa Musa ya ji game da shekarun Ayuba na ƙarshe sa’ad da Isra’ilawa suke kusa da ƙasar Uz, a ƙarshen tafiyarsu ta shekara 40 a cikin jeji.a An rubuta labarin Ayuba da kyau wanda hakan ya sa aka ɗauki labarin adabi mafi kyau. Fiye da haka ma, ya amsa tambayoyi kamar su: Me ya sa mutanen kirki suke wahala? Me ya sa Jehobah ya ƙyale mugunta? Mutane ajizai za su iya ci gaba da kasancewa da aminci ga Allah kuwa? Da yake yana cikin hurarriyar Kalmar Allah, saƙon littafin Ayuba rayayye ne kuma mai aiki har wa yau.—Ibraniyawa 4:12.

“BAR RANA DA AKA HAIFE NI TA LALACE”

(Ayuba 1:1–3:26)

Wata rana Shaiɗan ya ƙalubalanci amincin Ayuba a gaban Allah. Jehobah ya yarda da ƙalubalen kuma ya ƙyale Shaiɗan ya gwada Ayuba da masifu iri-iri. Amma Ayuba ya ƙi ya “la’anta Allah.”—Ayuba 2:9.

Abokan Ayuba guda uku suka zo su “ta’azantadda shi.” (Ayuba 2:11) Suka zauna tare da shi ba su ce uffan ba har sai sa’ad da Ayuba ya yi magana yana cewa: “Bar rana da aka haife ni ta lalace.” (Ayuba 3:3) Ya yi fata ya zama kamar “jariran da ba su taɓa ganin haske ba,” ko waɗanda aka haife su a mace.—Ayuba 3:11, 16.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

1:4—Yaran Ayuba sun yi bikin ranan haihuwa ne? A’a, ba su yi ba. Kalmomi a yaren asali na ‘rana’ da ‘ranar haihuwa’ sun bambanta, kowace tana da tata ma’ana. (Farawa 40:20) An yi amfani da kalmar nan ‘rana’ a Ayuba 1:4, wannan na nuni daga fitowar rana zuwa faɗuwarta. Mai yiwuwa ’ya’yan Ayuba maza bakwai suna yi wa iyalin liyafa na kwana bakwai sau ɗaya a shekara. Sa’anda kwanakin liyafar ya kewayo, kowane ɗansa da aka yi liyafar a gidansa a “ranassa,” ne mai masaukin baƙi.

1:6; 2:1—Su waye ne aka ƙyale su bayana a gaban Jehobah? Makaɗaicin Ɗan Allah, wato Kalman; da ‘ ’ya’yan Allah’ mala’iku masu aminci; da mala’iku masu tawaye, har da Shaiɗan Iblis ne suka bayana a wurin Jehobah. (Yohanna 1:1, 18) Ba a kawar da Shaiɗan da aljannunsa daga sama ba sai bayan da aka kafa Mulkin Allah a shekara ta 1914. (Ru’ya ta Yohanna 12:1-12) Da yake ya ƙyale su su bayana a gabansa, Jehobah yana gabatar da ƙalubalen Shaiɗan da kuma batun da ya ta da ga dukan halittun ruhu.

1:7; 2:2—Jehobah ya yi wa Shaiɗan magana ne kai tsaye? Littafi Mai Tsarki bai ba da cikakken bayani ba game da yadda Jehobah yake magana da halittu na ruhu. Amma, annabi Mikaiah ya sami wahayi a nan ya ga wani mala’ika yana magana kai tsaye da Jehobah. (1 Sarakuna 22:14, 19-23) Saboda haka, wataƙila Jehobah ya yi wa Shaiɗan magana da kansa.

1:21—Ta yaya Ayuba zai koma ‘cikin uwarsa’? Tun da yake Jehobah Allah ya sifanta mutum “daga turɓayar ƙasa” an yi amfani da kalmar nan ‘uwa’ a alamance wajen yin nuni ga turɓaya.—Farawa 2:7.

2:9—Wane yanayi matar Ayuba take ciki sa’ad da ta gaya wa mijinta ya la’anci Allah ya mutu? Matar Ayuba ta yi hasara da mijinta ya yi. Babu shakka tana baƙin ciki sosai ganin mijinta mai kuzari a dā yana wahala sosai don cuta mai ban ƙyama. Ta yi rashin yaranta da take ƙauna. Mai yiwuwa ta rikice sosai saboda dukan waɗannan abubuwa da suka same ta, wannan ya sa ta manta cewa dangantakarsu da Allah shi ne ya fi muhimmanci.

Darussa Dominmu:

1:8-11; 2:3-5. Yadda labarin Ayuba ya nuna, ban da ayyuka da kuma furcin da suka dace, idan muna son mu kasance da aminci, muna bukatar mu bauta wa Jehobah da ra’ayi mai kyau.

1:21, 22. Ta wajen kasancewa da aminci ga Jehobah a yanayi mai kyau da kuma marar kyau, za mu nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne.—Misalai 27:11.

2:9, 10. Kamar Ayuba, ya kamata mu kasance da bangaskiya ko idan waɗanda suke cikin iyalinmu ba sa ganin darajar yadda muke biɗan abubuwa na ruhaniya ko kuma idan suna matsa mana mu bar bangaskiyarmu.

2:13. Abokan Ayuba ba su da abin kirki da za su ce game Allah da kuma alkawuransa domin ba su da ruhaniya.

“BA NI RABUWA DA GASKIYATA!”

(Ayuba 4:1–31:40)

Ainihin abin da abokan Ayuba uku suka faɗa a furcinsu shi ne cewa Ayuba ya yi wani mugun abu shi ya sa Allah yake masa horo mai tsanani. Elifaz ne ke ja-gora. Bildad ya bi bayan Elifaz da baƙar magana mafi tsanani. Zofar ne ya fi furcin reni.

Ayuba bai yarda da tunanin ƙarya na baƙinsa ba. Da yake bai fahimci abin da ya sa Allah ya ƙyale shi yake wahala ba, ya damu ainun game da kansa. Duk da haka, Ayuba yana ƙaunar Allah kuma ya furta: “Har in mutu ba ni rabuwa da gaskiyata.”—Ayuba 27:5.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

7:1; 14:14—Menene ake nufi da “kwanakin bauta”? Domin tsananin wahalarsa, Ayuba yana ganin rayuwa kwanakin bauta ne. (Ayuba 10:17) Tun da yake sa’ad da mutum ya mutu dole ne ya kasance a cikin Sheol har sai tashin matattu, Ayuba ya kamanta lokacin da kwanakin bauta.

7:9, 10; 10:21; 16:22—Waɗannan furcin na nuna cewa Ayuba bai gaskata da tashin matattu ba ne? Ayuba ya yi waɗannan kalamai game da mutuwarsa ne. To, menene yake nufi? Wataƙila yana nufin cewa idan ya mutu, zuriyarsa ba za su gan shi kuma ba. A ra’ayinsu, ba zai dawo gidansa ba ko kuma a san da shi har sai lokacin da Allah ya ka’ide. Mai yiwuwa Ayuba yana nufin cewa babu wanda zai iya dawowa daga Sheol da kansa. Ayuba 14:13-15 sun nuna sarai cewa Ayuba yana da begen tashin matattu na nan gaba.

10:10—Ta yaya Jehobah ya ‘tsiyayadda Ayuba kamar madara kuma ya daskare shi kamar cuku’? Wannan kwatanci ne na alama na yadda aka sifanta Ayuba cikin mahaifar mamarsa.

19:20—Menene Ayuba yake nufi da furci “da ƙyat na tsira”? Da wannan furci, ƙila Ayuba yana nufin cewa bai tsira da kome ba.

Darussa Dominmu:

4:7, 8; 8:5, ; 11:13-15. Bai kamata mu yi saurin kammala cewa mutum da ke shan wahala yana girbe abin da ya shuka ne kuma ba shi da amincewar Allah.

4:4:18, 19; 22:2, 3. Ya kamata mu ba da gargaɗi bisa Kalmar Allah, ba namu ra’ayi ba.—2 Timothawus 3:16.

10:1. Baƙin ciki ya rufe wa Ayuba ido, saboda haka bai yi tunanin wasu abubuwa da ƙila suka hadassa wahalarsa ba. Kada mu yi baƙin ciki ainun sa’ad da muke wahala, tun da yake mun san dalilan.

14:7, 13-15; 19:25; 33:24. Begen tashin matattu zai kiyaye mu a kowane gwaji da Shaiɗan zai hadassa mana.

16:5; 19:2. Bai kamata kalmominmu su sa mutane fushi ba, amma ya kamata su ƙarfafa su.

22:5-7. Gargaɗi da aka ba da ta wajen zargi ba na gaskiya ba, ba shi da amfani kuma yana da lahani.

27:2; 30:20, 21. Mutum ba ya bukatar ya kamilta kafin ya kasance da aminci. Zargin da Ayuba ya yi wa Allah ba daidai ba ne.

27:5. Ayuba ne da kansa zai iya daina kasancewa da aminci domin aminci bisa ƙauna ne da mutum yake wa Allah. Saboda haka ya kamata mu ƙaunaci Jehobah sosai.

28:1-28. ’Yan adam sun san inda dukiyar duniya take. Sa’ad da suke neman dukiya, iyawarsu na kai su wurare da ke ɓoye da babu tsuntsu da ke hangen nesa da zai iya gani. Amma, ana samun hikima ta Allah ta wajen jin tsoron Jehobah.

29:12-15. Ya kamata mu yi wa mabukata alheri da son rai.

31:1, 9-28. Ayuba ya kafa mana misali da yake ya guje wa kwarkwasa, zina, son abin duniya, bautar gunki, amma ya yi juyayin mutane kuma ya bi da su yadda ya dace.

“NA TUBA CIKIN ƘURA DA TOKA”

(Ayuba 32:1–42:17)

Wani matashi mai suna Elihu yana saurararsu cikin haƙuri. Bayan haka sai ya yi magana. Ya sa Ayuba da abokansa uku masu matsa masa su gyara ra’ayinsu.

Ba da daɗewa ba bayan Elihu ya gama magana, Jehobah ya yi magana daga cikin guguwa. Bai faɗi dalilin da ya sa Ayuba ke wahala ba. Amma ta wajen yin tambayoyi masu yawa, Maɗaukaki Duka ya sanar da Ayuba ƙarfinsa mai ban mamaki da kuma hikimarsa mai girma. Ayuba ya yarda ya yi magana ba tare da fahimi ba kuma ya ce: “Ina jin ƙyamar kaina, na tuba cikin ƙura da toka.” (Ayuba 42:6) An saka wa Ayuba don amincinsa, sa’ad da gwajinsa ya ƙare.

Tambayoyi na Nassi da Aka Amsa:

32:1-3—Yaushe ne Elihu ya zo? Tun da yake Elihu ya ji dukan abubuwa da suka faɗa, wataƙila yana nan kusa kafin Ayuba ya soma magana bayan kwanaki bakwai da abokansa guda uku suka yi ba su yi magana ba.—Ayuba 3:1, 2.

34:7—Ta yaya Ayuba ya zama kamar mutum “mai-shanyen ba’a kamar ruwa”? A yanayinsa na baƙin ciki, Ayuba ya yi na’am da ba’ar baƙinsa guda uku kamar shi suke yi wa, ko da yake ainihi suna magana ne game da Allah. (Ayuba 42:7) Ta haka, yana na’am da ba’a kamar wanda yake shan ruwa da farin ciki.

Darussa Dominmu:

32:8, 9. Ba tsufa ba ne kawai yake kawo hikima. Ana bukatar samun fahimi na Kalmar Allah da ja-gorar ruhunsa.

34:36. Muna nuna mu masu aminci ne idan aka ‘auna mu har ƙarshe’ a wasu hanyoyi.

35:2. Elihu ya saurara sosai kuma ya fahimci ainihin batun kafin ya soma magana. (Ayuba 10:7; 16:7; 34:5) Kafin su ba da gargaɗi, dole ne dattawa su saurara sosai su san ainihin gaskiyar batun, kuma su fahimci batutuwa da suka dace sarai.—Misalai 18:13.

37:14; 38:1-39:30. Idan muka yi bimbini game da ayyukan Jehobah masu ban mamaki da kuma yadda ya nuna ikonsa da hikima, wannan zai sa mu kasance da tawali’u kuma zai sa mu ga cewa kunita ikon mallakarsa ya fi muhimmanci da kowane abu na kanmu da muke biɗa.—Matta 6:9, 10.

40:1-4. Sa’ad muka ji kamar za mu yi gunaguni game da Maɗaukaki, ya kamata mu ‘sa hannunmu a bakinmu.’

40:15–41:34. Dorina da Kada suna da ƙarfi sosai! Don mu jimre a hidimar Allah, mu ma muna bukatar ƙarfi daga Mahaliccin waɗannan dabbobi masu ƙarfi, wanda yake ƙarfafa mu.—Filibbiyawa 4:13.

42:1-6. Jin maganar Jehobah da kuma tuna wa Ayuba game da yadda ya nuna ikonsa ya taimake shi ya “ga Allah” ko kuma ya san gaskiya game da shi. (Ayuba 19:26) Wannan ya sa ya daidaita ra’ayinsa. Idan aka yi mana gyara da Nassosi, ya kamata mu amince da kuskurenmu kuma mu yi gyara.

Ka Yi Koyi da “Jimrewar Ayuba”

Littafin Ayuba ya nuna sarai cewa Allah ba shi da alhakin wahalar ’yan adam. Shaiɗan ne yake da alhaki. Da yake Allah ya ƙyale mugunta a duniya, ya ba mu zarafin nuna ra’ayinmu a batutuwan ikon mallakar Jehobah da kuma amincinmu.

Kamar Ayuba, za a gwada dukan waɗanda suke ƙaunar Jehobah. Labarin Ayuba ya ba mu tabbaci cewa za mu iya jimrewa. Ya tuna mana cewa matsalolinmu ba za su kasance har abada ba. Yaƙub 5:11 ta ce: “Kun ji labarin jimrewar Ayuba, kun ga ƙarkon Ubangiji kuma.” Jehobah ya saka wa Ayuba don amincinsa. (Ayuba 42:10-17) Muna da bege mai girma, wato rai madawwami a cikin Aljanna a duniya! Kamar Ayuba, bari mu ƙuduri aniyar kasancewa da aminci.—Ibraniyawa 11:6.

[Hasiya]

a Littafin Ayuba ya ba da tarihin fiye da shekaru 140, tsakanin 1657 da kuma 1473 K.Z.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba