Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 9/1 pp. 14-18
  • Gajiyayyu Amma Ba Su Karai Ba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gajiyayyu Amma Ba Su Karai Ba
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Kiristanci Ba Ya Zaluntawa
  • “Mu Yar da Abin da Ya Nauyaya Mana”
  • Ana Bukatar Nagarin Tunani da Kuma Filako
  • Jehovah Allah Yana Ƙarfafa Mu
  • Kada Ka Yi Karai
  • Ruhu Mai Tsarki Yana Ba Da Ƙarfi A Jimre Da Gwaji Da Kuma Sanyin Gwiwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Yadda Za Ka Daina Yin Sanyin Gwiwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Jehovah Yana Ƙarfafa Masu Kasala
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Jehobah Yana Ceton Wanda Yake Wahala
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 9/1 pp. 14-18

Gajiyayyu Amma Ba Su Karai Ba

“Ubangiji Madawwamin Allah ne . . . Ya halicci dukkan duniya. . . . Yakan ƙarfafa masu kasala da masu jin gajiya.”—ISHAYA 40:28, 29.

1, 2. (a) Wace gayya mai kyau ce aka yi wa dukan waɗanda suke bauta ta gaskiya? (b) Me zai iya ɓata ruhaniyarmu?

MU ALMAJIRAN Yesu mun sani sarai game da gayyatarsa: “Ku zo gare ni dukanku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku. . . . Domin bautata sassauƙa ce, kayana kuma marar nauyi ne.” (Matiyu 11:28-30) “Ubangiji kuma kansa ya riƙa wartsakar da” Kiristoci. (Ayyukan Manzanni 3:19) Babu shakka ka shaida wartsakewa da ake samu daga koyon gaskiyar Littafi Mai Tsarki, kasancewa da bege mai kyau domin nan gaba, da kuma yin amfani da ƙa’idodin Jehovah a rayuwarka.

2 Duk da haka wasu cikin masu bauta wa Jehovah suna fama da gajiya ƙwarai na jiye-jiye. A wasu lokatai, irin lokacin sanyin gwiwan nan na ɗan lokaci ne. A wasu lokatai kuma sanyin gwiwan yakan ci gaba na dogon lokaci. A kwana a tashi, wasu sukan ji hakkinsu na Kirista ya zama kaya maimakon ya zama abin wartsakewa daidai da alkawarin Yesu. Irin wannan jiye-jiye yana ɓata dangantakar Kirista da Jehovah.

3. Me ya sa Yesu ya ba da gargaɗin da ke a Yahaya 14:1?

3 Ba da daɗewa ba kafin a kama shi a kashe, Yesu ya gaya wa almajiransa: “Kada ku damu. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni.” (Yahaya 14:1) Yesu ya furta waɗannan kalmomi sa’ad da manzannin za su fuskanci aukuwa ta ban mamaki. Tsanantawa ƙwarai za ta bi bayan wannan. Yesu ya san cewa manzanninsa za su iya su yi tuntuɓe domin sanyin gwiwa. (Yahaya 16:1) Idan ba su lura ba, baƙin ciki zai iya sa su raunana a ruhaniya kuma ya sa su kasa dogara ga Jehovah. Wannan ma haka yake game da Kiristoci na gaskiya a yau. Baƙin ciki na dogon lokaci yana jawo damuwa sosai kuma zuciyarmu sai ta karai. (Irmiya 8:18) Mutumi na ciki zai iya raunana. A cikin irin wannan matsin za mu iya ragargaje a jiye-jiye da kuma a ruhaniya har ba za mu yi sha’awar bauta wa Jehovah kuma ba.

4. Menene zai taimake mu mu kiyaye zukatanmu na alama daga gajiya?

4 Wannan gargaɗin Littafi Mai Tsarki ya dace sosai: “Tunane-tunanenka mafarin rai ne kansa, ka kiyaye su abin mallakarka ne mafi daraja.” (Karin Magana 4:23) Littafi Mai Tsarki ya ba da shawarar da za ta taimake mu mu kiyaye zuciyarmu ta alama daga raunana da kuma gajiya ta ruhaniya. Da farko, muna bukatar mu san dalilin gajiyarmu.

Kiristanci Ba Ya Zaluntawa

5. Wane saɓani ne kamar akwai game da almajiranci na Kirista?

5 Gaskiya ne cewa zama Kirista tana bukatar ƙoƙari sosai. (Luka 13:24) Yesu ma ya ce: “Duk wanda bai ɗauki [gungumensa] ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba.” (Luka 14:27) Kamar dai waɗannan kalmomi sun saɓa da abin da Yesu ya ce kayansa marar nauyi ne kuma cewa zai hutasshe su, da gaske kam babu saɓani.

6, 7. Me ya sa za a ce irin bauta da muke yi ba wadda take jawo gajiya ba ce?

6 Ko da yake ƙoƙari da kuma aiki tuƙuru yana gajiyar da jiki, ana samun gamsuwa da kuma wartsakewa sa’ad da aka yi shi da niyyar kirki. (Mai Hadishi 3:13, 22) Akwai abin da ya fi gaya wa maƙwabtanmu gaskiyar Littafi Mai Tsarki ne? Haka kuma, ba za mu tuna da faman da muke yi mu yi rayuwa daidai da mizanai masu girma na Allah ba sa’ad da muka sami fa’idodin hakan. (Karin Magana 2:10-20) Sa’ad da aka tsananta mana, ɗaukaka ne gare mu mu sha wahala domin Mulkin Allah.—1 Bitrus 4:14.

7 Kayan Yesu mai wartsakewa ne, musamman idan muka gwada shi da yanayin duhu na ruhaniya na waɗanda suke ƙarƙashin karkiyar addinin ƙarya. Allah yana ƙaunarmu sosai, kuma ba ya bukatar abin da ya fi ƙarfinmu. ‘Umarnin Jehovah ba matsananta ba ne.’ (1 Yahaya 5:3) Yadda aka bayyana Kiristanci na gaskiya cikin Nassosi, babu zalunci cikinsa. A bayyane yake cewa, bauta da muke yi ba ta jawo gajiya da sanyin gwiwa.

“Mu Yar da Abin da Ya Nauyaya Mana”

8. Sau da yawa me ke jawo gajiya ta ruhaniya?

8 Idan muna gajiya ta ruhaniya wataƙila sau da yawa domin wani nauyi da wannan zamani na ɓatanci ya daɗa mana ne. Saboda “duniya duka kuwa tana hannun Mugun” abubuwan da za su iya nauyaya mu suna iya gajiyar da mu kuma su ɓata daidaitawarmu na Kirista. (1 Yahaya 5:19) Abubuwa marasa amfani za su iya damun tsarinmu na Kirista. Waɗannan ƙarin nauyi za su iya nauyaya kuma ragargaje mu. Littafi Mai Tsarki ya faɗa daidai cewa mu “tuɓe kowane abin nauwaitawa.”—Ibraniyawa 12:1-3.

9. Ta yaya biɗe-biɗen abin duniya zai nauyaya mu?

9 Alal misali, yadda duniya ta shaƙu da yin suna, kuɗi, nishaɗi, tafiye-tafiye don annashuwa, da wasu biɗe-biɗe na abin duniya za su iya shafi tunaninmu. (1 Yahaya 2:15-17) Wasu Kiristoci a ƙarni na farko da suke biɗan arziki sun dagula rayuwarsu. Manzo Bulus ya bayyana haka: “Masu ɗokin yin arziki kuwa, sukan zarme da jaraba, su faɗa tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda ke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da halaka. Ai, son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Don tsananin jarabar kuɗi kuwa waɗansu mutane, har sun bauɗe wa bangaskiya, sun jawo wa kansu baƙin ciki iri iri masu sukan rai.”—1 Timoti 6:9, 10.

10. Me za mu iya koya game da wadata daga misalin Yesu na mai shuka?

10 Sa’ad da muka gaji kuma muna sanyin gwiwar bauta wa Allahnmu, saboda biɗe-biɗenmu ne na abin duniya da za ta gurgunta ruhaniyarmu? Wannan na yiwuwa a yadda Yesu ya nuna a misalinsa na mai shuka. Yesu ya gwada “taraddadin duniya, da jarabar dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa” da ƙayayuwa da “sukan shiga su sarƙe” iri na kalmar Allah a zukatanmu. (Markus 4:18, 19) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu: “Kada halinku ya zama na son kuɗi. Ku dangana da abin da kuke da shi, gama Allah kansa ya ce, har abada ba zan bar ka ba. ‘Har abada kuma ba zan yashe ka ba.’ ”—Ibraniyawa 13:5.

11. Ta yaya za mu iya kawar da abubuwa da suke nauyaya mu?

11 Wani lokaci dai, abin da yake ɗimauce rayuwarmu ba biɗan abubuwa ba ne amma abin da muke yi ne da kayan da muke da su. Wasu suna shaida gajiya ta jiye-jiye na shekaru da yawa domin rashin lafiya da kuma mutuwar waɗanda suke ƙauna, ko kuma wasu matsaloli. Sun ga ya dace su yi gyara a wani lokaci. Wasu ma’aurata suka kawar da wasu ayyukansu marasa muhimmanci. Sun bincika kayayyakinsu kuma suka kwashe dukan waɗanda suke na waɗancan ayyuka kuma suka kawar da su. A wasu lokatai, akwai amfani idan muka bincika halayenmu da kuma abin da muke da su domin mu tuɓe kowane nauyi da ba wajibi ba ne domin kada mu gaji kuma mu karai.

Ana Bukatar Nagarin Tunani da Kuma Filako

12. Me za mu fahimta game da namu kuskuren?

12 Kuskuren kanmu ma a ƙananan batu za su iya ɗimauce rayuwarmu. Gaskiyar kalmomin Dauda kuwa: “Ina nutsewa cikin ambaliyar zunubaina, ina jin nauyinsu, sun danne ni ƙasa.” (Zabura 38:4) Sau da yawa idan muka yi wasu gyara za mu sami sauƙi.

13. Ta yaya sanin ya kamata zai taimake mu mu daidaita a hidimarmu?

13 Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu kasance da ‘hikima da basira.’ (Karin Magana 3:21, 22) “Hikiman nan ta Sama, . . . saliha ce,” in ji Littafi Mai Tsarki. (Yakubu 3:17) Wasu suna tsananta wa kansu a son su yi daidai da abin da wasu Kiristoci suke yi a hidima. Amma Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu: “Kowa yā auna aikinsa ya gani, sa’an nan ne zai iya taƙama da maƙaminsa shi da kansa, ba sai ya gwada kansa da wani ba. Lalle kowa ya ji da kayansa.” (Galatiyawa 6:4, 5) Gaskiya kam, nagarin misali na ’yan’uwa Kirista zai iya ƙarfafa mu mu bauta wa Jehovah da zuciya ɗaya, amma fahimi da sanin ya kamata zai taimake mu mu fahimci abin da za mu iya yi daidai da yanayinmu.

14, 15. Ta yaya za mu iya kasance da hikima a kula da bukatunmu na jiki da kuma na jiye-jiye?

14 Kasancewa da sanin ya kamata a fasalolin abubuwa da kamar ba su da muhimmanci sa taimaka mana idan muka gaji. Alal misali, muna koyan halaye da suka dace da za su sa mu sami lafiyar jiki? Ka yi la’akari da misalin ma’aurata da suke hidima a wani ofis na reshe na Shaidun Jehovah. Sun fahimci yadda za su iya kawar da gajiya. Matarsa ta ce: “Ko yaya yawan aikin da muke da shi, muna ƙoƙari mu shiga barci a lokaci da muka saba kowane dare. Muna wasan jiki kuma a kai a kai. Wannan yana taimakonmu. Mun san iyakarmu, kuma muna bi daidai hakan. Ba ma gwada kanmu da waɗanda kamar ƙarfinsu ba ya ƙarewa.” Muna bin tsari mai kyau na cin abinci kuma mu samu isashen barci? Idan muka kula da lafiyar jikinmu za mu iya rage gajiya ta jiye-jiye da kuma ta ruhaniya.

15 Wasu cikinmu suna da bukatu da suka bambanta. Alal misali, wata ’yar’uwa Kirista ta yi hidima na cikakken lokaci a yankuna da yawa da suke da wuya. Tana rashin lafiya sosai har da ciwon daji. Me ya taimake ta ta jure da yanayi na wahala haka? Ta ce: “Yana da kyau na sami lokaci da zan kaɗaita kuma na lumana. Duk lokacin da na ji kamar gajiya tana yawa, nan da nan sai in ga ya dace na sami lokaci na lumana da zan yi karatu kuma in huta.” Hikima da kuma tunanin kirki na taimaka mana mu gane kuma mu iya gamsar da bukatunmu da haka muna guje wa gajiya ta ruhaniya.

Jehovah Allah Yana Ƙarfafa Mu

16, 17. (a) Me ya sa kula da lafiyarmu ta ruhaniya take da muhimmanci sosai? (b) Me ya kamata mu haɗa da ayyukanmu na kowace rana?

16 Kula da lafiyarmu ta ruhaniya ce ta fi muhimmanci. Idan muna da dangantaka ta kud da kud da Jehovah Allah, ƙila muna iya gajiya amma ba za mu gaji da bauta masa ba. Jehovah ne “yakan ƙarfafa masu kasala da masu jin gajiya.” (Ishaya 40:28, 29) Manzo Bulus wanda ya shaida abin da ke cikin kalmomin nan ya rubuta: “Ba mu karai ba, ko da ya ke jikinmu na mutuntaka na ta lalacewa, duk da haka ruhunmu kowace rana sabunta shi ake yi.”—2 Korantiyawa 4:16.

17 Ka lura da furcin nan “kowace rana.” Wannan yana nufin yin amfani da abin da Jehovah ya yi tanadinsa ne kowace rana. Wata mai wa’azi a ƙasashen waje ta yi hidima da aminci na shekaru 43 ta sha wahalar gajiyar jiki da sanyin gwiwa, amma ba ta yi karai ba. Ta ce: “Na saba tashiwa da sassafe, kafin na soma wani aiki sai na ɓad da lokaci sosai cikin addu’a ga Jehovah kuma na karanta Kalmarsa. Wannan hali na kullum ya taimake ni na jimre har wa yanzu.” Za mu tabbata game da ikon Jehovah ya kiyaye mu kullum, “kowace rana,” mu yi addu’a gare shi kuma mu yi bimbini game da halayensa da alkawuransa masu girma.

18. Wace ta’aziyya Littafi Mai Tsarki ya yi tanadinta wa amintattu da suka tsufa ko kuma da suke ciwo?

18 Wannan yana da muhimmanci musamman ga waɗanda suke sanyin gwiwa domin tsufa da kuma rashin lafiya. Irin waɗannan sukan raunana ba domin sun gwada kansu da wasu ba, amma domin sun gwada kansu da yadda suke a dā. Abin ƙarfafa ne sanin cewa Jehovah yana daraja tsofaffi! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Furfurar tsufa rawanin daraja ce, sakamako ne ga ran mai adalci.” (Karin Magana 16:31) Jehovah ya san gwargwadon abin da muke iya yi kuma yana daraja bauta da muke yi ta zuciya ɗaya sosai duk da raunanarmu. Kuma nagargarun ayyuka da muka yi Allah yana tuna da su. Nassosi sun tabbatar mana: “Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi.” (Ibraniyawa 6:10) Muna farin ciki sosai mu ga waɗanda suke da aminci ga Jehovah na shekaru da yawa a tsakaninmu!

Kada Ka Yi Karai

19. Ta yaya muke amfana daga taƙurewa a yin aikin nagari?

19 Mutane da yawa suna jin cewa ayyuka na kullum da ƙwazo yana kawar da gajiya. Haka ma, ayyuka na ruhaniya a kai a kai yana taimakawa a rage gajiya na tsotsuwar rai ko kuma ta ruhaniya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada mu yi sanyi da yin aiki nagari, don za mu yi girbi a kan kari, in ba mu karai ba. To, saboda haka, in hali ya yi, sai mu kyautata wa kowa, tun ba ma waɗanda ke jama’ar masu ba da gaskiya ba.” (Galatiyawa 6:9, 10) Ka lura da furcin nan “yin aiki nagari” da kuma na ‘kyautatawa.’ Wannan na bukatar mu yi wani abu. Yin aiki nagari ga mutane yana taimakonmu kada mu gaji da hidimarmu ga Jehovah.

20. Don mu yaƙi sanyin gwiwa, waɗanne irin mutane za mu kauce tarayya da su?

20 Akasarin haka, yin tarayya da aiki da mutanen da ba sa ƙaunar dokokin Allah yana da ban gajiya ƙwarai. Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi: “Dutse da yashi suna da nauyi ƙwarai, amma nauyin wahalar da wawa zai haddasa ya fi nasu duka.” (Karin Magana 27:3) Don mu yaƙi sanyin gwiwa da kuma gajiya zai dace mu kauce wa waɗanda suke mugun tunani da kuma masu saurin tuhumar wasu.

21. Ta yaya za mu ƙarfafa mutane a taron Kirista?

21 Taron Kirista tanadi ne daga Jehovah da zai ba mu ƙarfi na ruhaniya. A wajen muna da zarafi na ƙarfafa juna kuma mu sami koyarwa da tarayya mai kyau. (Ibraniyawa 10:25) Dukan waɗanda suke ikilisiya su ba da ƙarfafa sa’ad da suke ba da kalami ko kuma suke jawabi daga kan dakalin magana. Waɗanda suke ja-gora, masu koyarwa musamman suna da hakkin ƙarfafa mutane. (Ishaya 32:1, 2) Ko sa’ad da akwai bukatar kashedi da tsautawa, ya kamata su yi gargaɗi da zai wartsake mutum. (Galatiyawa 6:1, 2) Ƙaunar da muke da ita wa mutane za ta taimake mu mu bauta wa Jehovah ba tare da gajiya ba.—Zabura 133:1; Yahaya 13:35.

22. Duk da ajizancinmu, me ya sa za mu yi gaba gaɗi?

22 Bauta wa Jehovah a wannan zamani na ƙarshe ya ƙunshi aiki. Kiristoci su ma suna gajiya, suna shan azaba, kuma suna shaida yanayi na wahala. Yanayinmu na ajizai, raunana, kama yake da tukunyar ƙasa. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wannan wadata da muke da ita kuwa cikin kasake take, wato jikunanmu, don a nuna mafificin ikon nan na Allah ne, ba namu ba.” (2 Korantiyawa 4:7) Hakika, za mu gaji, amma kada mu karai. Maimako, bari da “gabagaɗi, mu ce, ‘Ubangiji shi ne mataimakina.’ ”—Ibraniyawa 13:6.

Ɗan Maimaitawa

• Waɗanne kaya masu nauyi za mu iya tuɓewa?

• Ta yaya za mu iya sa hannu a “yin aiki nagari” wajen ’yan’uwa Kiristoci?

• Ta yaya Jehovah yake kiyaye mu sa’ad da muka gaji ko kuma muka yi sanyin gwiwa?

[Hoto a shafi na 15]

Yesu ya sani cewa idan manzannin suka yi sanyin gwiwa da daɗewa, zai dame su

[Hoto a shafi na 16]

Wasu sun riga sun daina wasu ayyuka da kuma abubuwa marasa muhimmanci

[Hoto a shafi na 18]

Duk da kasawarmu Jehovah yana daraja bautarmu da zuciya ɗaya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba