Neman Farin Ciki
SHEKARU kalilan da suka shige, an yi wa mutanen Amirka, Britaniya Babba, Faransa da kuma Jamus tambaya cewa, “Menene yake kawo farin ciki?” Kashi 89 bisa ɗari na waɗanda aka gana da su sun ce ana bukatar lafiyar jiki; kashi 79 bisa ɗari sun ambata aure ko kuma tarayya mai gamsarwa; kashi 62 bisa ɗari sun ce albarkar zama iyaye; kuma kashi 51 bisa ɗari suna tunanin cewa ana bukatar aiki mai kyau don a sami farin ciki. Ko da an koya wa yawancin mutane cewa kuɗi ba ya kawo farin ciki, kashi 47 bisa ɗari da aka yi musu tambaya sun tabbata cewa kuɗi yana kawo farin ciki. Mecece gaskiyar batun?
Na farko, ka duba alaƙa da ke tsakanin kuɗi da farin ciki. Bincike da aka yi na mutane ɗari da suka fi kuɗi a Amirka ya nuna cewa ba su fi sauran mutane farin ciki ba. Ban da haka ma, gwanaye na lafiyar jiki sun ce mutane da yawa a Amirka sun daɗa abubuwan mallakarsu ninki biyu shekara talatin da ta shige, duk da haka farin cikinsu bai fi na dā ba. Hakika, wani rahoto ya ce: “Daidai lokacin, baƙin ciki ya ƙaru. Adadin matasa masu shekara goma sha da suke kashe kansu ya ƙaru sau uku. Adadin kashe aure ya yi ninki biyu.” A ƙasashe 50, masu bincike da suka yi nazarin alaƙa da ke tsakanin kuɗi da farin ciki sun kammala cewa kuɗi ba zai iya kawo farin ciki ba.
Yaya lafiyar jiki, aure mai gamsarwa da aiki mai kyau suke da muhimmanci a samun farin ciki? To, idan ana bukatar waɗannan abubuwa don a yi farin ciki, miliyoyin mutane da suke ciwo da dukan waɗanda ba su da aure mai gamsarwa fa? Ma’aurata da ba su da yara da kuma dukan maza da mata da ba su da aiki mai kyau kuma fa? Dukan waɗannan ba za su yi rayuwa ta farin ciki ba ke nan? Waɗanda suke morar lafiyar jiki mai kyau da aure mai gamsarwa yanzu, za su ci gaba da farin ciki kuwa idan yanayinsu ya canja?
Muna Neman Farin Ciki a Inda Ya Dace Kuwa?
Kowa yana son ya yi farin ciki. Wannan ba abin mamaki ba ne domin an kwatanta Mahalicci cewa “Allah [mai farin ciki ne],” kuma an halicci mutum cikin siffar Allah. (1 Timoti 1:11; Farawa 1:26, 27) Saboda haka, daidai ne ’yan Adam su nemi farin ciki. Amma, mutane da yawa suna ganin cewa neman farin ciki yana kama da riƙe yashi—duka sai su sulluɓe da sauƙi.
Zai yiwu cewa wasu suna neman farin ciki da ƙarfi da yaji ne? Falsafa na zaman mutane, Eric Hoffer ya yi tunani hakan. Ya lura cewa: “Neman farin ciki shi ne abu na musamman da ke kawo baƙin ciki.” Haka yake idan muna neman farin ciki a inda bai dace ba. Ta hakan za mu fuskanci ɓacin rai da takaici. Ƙoƙarin zama mai arziki; neman suna ko yin suna; siyasa, nishaɗi, ko kuma burin samun kuɗi; ko son kai da gamsar da sha’awarmu nan da nan ba sa kawo farin ciki. Shi ya sa wasu suka bi furci na mamaki na wani marubuci, wanda ya ce: “Idan za mu daina neman farin ciki za mu yi farin ciki”!
Ƙirge da aka ambata a baya cikin wannan talifin ya nuna cewa mutane 4 cikin 10 suna jin cewa ana samun farin ciki ta yin abu mai kyau da taimakon mutane. Amma mutum 1 cikin mutane 4 yana nanata cewa kasancewa da bangaskiya da tabbaci na addini na kawo farin ciki. Hakika, muna bukatar mu mai da hankali ga abin da ake bukata don a yi farin ciki.