Abin Da Muka Koya Daga Wurin Yesu
Yadda Za a Samu Farin Ciki
Mene ne ke kawo farin ciki?
▪ Yesu ya ambata farin ciki a kalma ta farko ta sanannen huɗubarsa. Ya ce: “Masu farin ciki ne waɗanda suka san bukatarsu ta ruhaniya.” (Matta 5:3, NW) Mene ne yake nufi? Mene ne bukatunmu na ruhaniya?
Don mu rayu, muna bukatar mu yi numfashi, mu sha ruwa, kuma mu ci abinci, kamar yadda dabbobi suke yi. Amma akwai wani abu da ya bambanta mu da dabbobi. Muna bukatan Allah, domin shi ne Mahalicci, da haka, shi kaɗai ne zai iya taimaka mana mu fahimci ma’anar rayuwa. Muna bukatan mu fahimci hakan idan muna son mu kasance da farin ciki. Saboda haka, Yesu ya ce: “Ba da abinci kaɗai ba mutum za ya rayu, amma da kowace magana da ke fitowa daga bakin Allah.” (Matta 4:4) Waɗanda suka san bukatarsu ta ruhaniya suna farin ciki domin sun kusaci Jehobah, Allah “mai-albarka,” kuma ya ba su begen da ke kawo farin ciki.—1 Timotawus 1:11.
Ta yaya Yesu ya ba da bege?
▪ Yesu ya ce: “Masu-albarka ne masu-tawali’u: gama su za su gāji duniya.” (Matta 5:5) Yesu ya ba ’yan Adam bege ta wajen warkar da marasa lafiya da kuma ta da matattu zuwa rai a duniya. Ya kuma zo da saƙo mai cike da bege. Ya bayyana: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gare shi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” (Yohanna 3:16) Mutanen da suke biyayya ga Allah za su more rai na har abada a cikin duniya. Ka yi tunanin yin rayuwa tare da masu tawali’u da ba za su taɓa tsufa ba. Shi ya sa Kalmar Allah ta ce: “Kuna murna cikin bege.” (Romawa 12:12) Yesu ya kuma tattauna yadda za a iya samun farin ciki a yanzu.
Wace hanyar rayuwa ta farin ciki ce Yesu ya koyar?
▪ Yesu ya ba da shawara masu amfani a kan batutuwa kamar su dangantakarmu da mutane, aure, tawali’u, da kuma kasancewa da daidaitaccen ra’ayi game da dukiya. (Matta 5:21-32; 6:1-5, 19-34) Bin umurnin Yesu zai taimaka maka ka samu farin ciki.
Nuna karimci yana kawo farin ciki. (Ayyukan Manzanni 20:35) Alal misali, Yesu ya ce: “In za ka kira biki, sai ka gayyato gajiyayyu, da musakai, da guragu, da makafi, za ka kuwa sami albarka [“farin ciki” NW], da ya ke ba su da hanyar sāka maka.” (Luka 14:13, 14, Littafi Mai Tsarki) Za mu yi farin ciki idan muka sa wasu farin ciki.
Mene ne tushe mafi muhimmanci na farin ciki?
▪ Yin abubuwa ga mutane zai iya sa ka farin ciki, amma za ka fi samun farin ciki idan ka yi wa Allah hidima. Farin cikin da muke samu don yi wa Allah hidima ya ɗara na iyaye masu ƙaunar yaransu. Abin da ya faru wata rana sa’ad da Yesu yake wa’azi ne ya bayyana hakan dalla-dalla. “Wata mace a taron ta ɗaga murya ta ce masa, ‘Albarka [“Farin ciki” NW] tā tabbata ga wadda ta haife ka, wadda ka sha mamanta.’ Amma ya ce, ‘I, amma albarka [“farin ciki” NW] tā fi tabbata ga waɗanda ke jin Maganar Allah, suke kuma kiyaye ta.’”—Luka 11:27, 28, LMT.
Yesu da kansa ya samu gamsuwa da farin ciki wajen yin nufin Ubansa na samaniya. Nufin Allah shi ne mutane su ji saƙon begen rai na har abada. Bayan ya bayyana wa wani mai son saƙonsa begen, sai Yesu ya ce: “Abincina ke nan, in yi nufin wanda ya aiko ni.” (Yohanna 4:13, 14, 34) Kai ma za ka iya samun farin cikin yin abin da ke faranta wa Allah rai ta wajen gaya wa mutane gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki.
Don ƙarin bayani, ka duba babi na 1 na littafin nan, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? shaidun Jehobah ne suka wallafa.
[Hoton da ke shafi na 16]
Ana samun farin ciki na gaske ta wajen biyan bukatarmu ta fahimtar ma’anar rai