Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 10/1 p. 6-p. 9 par. 14
  • Taƙaici Daga Littafin Maimaitawar Shari’a

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Taƙaici Daga Littafin Maimaitawar Shari’a
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “KADA KU MANTA DA ABUBUWAN DA KUKA GANI DA IDONKU”
  • (Maimaitawar Shari’a 1:1–4:49)
  • KA ƘAUNACI JEHOVAH, KUMA KA YI BIYAYYA DA DOKOKINSA
  • (Maimaitawar Shari’a 5:1–26:19)
  • “KU ZAƁI RAI”
  • (Maimaitawar Shari’a 27:1–34:12)
  • Yana da Muhimmanci a Gare Mu
  • Yadda Za Ka San Hanyoyin Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Kada Ka Mance da Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Allah Ya Ceci ’Ya’yan Isra’ila
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • Jehobah Ya Ba Da Dokokinsa
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 10/1 p. 6-p. 9 par. 14

Maganar Jehovah Rayayyiya Ce

Taƙaici Daga Littafin Maimaitawar Shari’a

SHEKARA ta 1473 K.Z., ce. Shekara arba’in ta shige tun lokacin da Jehovah ya ceci Isra’ilawa daga bauta a Masar. Bayan sun yi gantali shekaru da yawa a jeji, har ila Isra’ila al’umma ce da ba ta da ƙasa. Amma a ƙarshe, suka tsaya a iyakar Ƙasar Alkawari. Menene zai faru musu sa’ad da suka mallake ta? Waɗanne matsaloli ne za su fuskanta, kuma yaya ya kamata su bi da matsalolin?

Kafin Isra’ila ta ƙetare Kogin Urdun zuwa ƙasar Kan’ana, Musa ya shirya ikilisiyar don babban aiki da ke gaba. Ta yaya? Ya ba da jawabai don ya ƙarfafa su, ya gargaɗe su, kuma ya ba da kashedi. Ya tuna wa Isra’ilawa cewa Jehovah Allah ya cancanci a bauta masa shi kaɗai kuma kada su yi koyi da al’ummai da suka kewaye su. Waɗannan jawaban ne sashe na musamman na littafin Maimaitawar Shari’a da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Kuma gargaɗin da ke ciki shi muke bukata a yau, don mu ma muna zama a duniya wadda bauta wa Jehovah kaɗai yake da wuya.—Ibraniyawa 4:12.

Musa ne ya rubuta dukan littafin Maimaitawar Shari’a ban da sura ta ƙarshe, an rubuta littafin fiye da wata biyu.a (Maimaitawar Shari’a 1:3; Joshuwa 4:19) Bari mu ga yadda abin da aka rubuta a ciki zai taimake mu mu ƙaunaci Jehovah Allah da dukan zuciyarmu kuma mu bauta masa da aminci.

“KADA KU MANTA DA ABUBUWAN DA KUKA GANI DA IDONKU”

(Maimaitawar Shari’a 1:1–4:49)

A jawabi na farko, Musa ya ba da labarin wasu abubuwa da suka faru cikin jeji—musamman waɗanda za su amfani Isra’ilawa yayin da suke shirin mallakar Ƙasar Alkawari. Labarin yadda aka naɗa alƙalai ya tuna musu cewa Jehovah yana shirya mutanensa a hanyar da za a kula da su. Musa ya kuma ba da labarin cewa mummunan rahoto na ’yan leƙen asiri goma ya hana zuriyar da ta gabata shigar ƙasar alkawari. Ka yi tunanin yadda wannan gargaɗin ya shafi masu sauraron Musa yayin da suke ganin ƙasar da idonsu.

Tunawa da nasarar da Jehovah ya bai wa ’ya’yan Isra’ila kafin su ƙetare Urdun ya ƙarfafa su yayin da suke shiri su soma cin nasararsu a ƙetaren kogin. Ƙasar da za su mallaka ta cika da bautar gumaka. Ya dace da Musa ya ba da gargaɗi sosai game da bautar gumaka!

An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi:

2:4-6, 9, 19, 24, 31-35; 3:1-6—Me ya sa Isra’ilawa suka halaka wasu mutane da suke zaune a gabashin Urdun amma ba su halaka sauran ba? Jehovah ya umurci Isra’ilawa kada su yi yaƙi da ’ya’yan Isuwa. Me ya sa? Domin su zuriyar ɗan’uwan Yakubu ne. Isra’ilawa ba za su dami ko su yi yaƙi da Mowabawa da kuma Ammoniyawa ba, domin su zuriyar Lutu ne ɗan wan Ibrahim. Amma, Sarakunan Amoriyawa Sihon da Og ba su da irin wannan nasaba ga ƙasar da ke ƙarƙashin ikonsu. Shi ya sa, sa’ad da Sihon ya ƙi Isra’ilawa su wuce ta ƙasarsa kuma Og ya yi yaƙi da su, Jehovah ya umurci Isra’ilawa su halaka biranensu, ba wanda ya tsira.

4:15-20, 23, 24—Hani da aka yi na sassaƙa siffofi na nufin cewa bai da kyau a yi wani sassaƙa ta ado ne? A’a. An hana yin siffofi don bauta—kada a ‘yi ma gumaka sujada da kuma bauta musu.’ Nassosi bai hana sassaƙa siffofi don ado ba.—1 Sarakuna 7:18, 25.

Darussa da Za Mu Koya:

1:2, 19. ’Ya’yan Isra’ila sun yi ta gantali a jeji na shekaru 38, ko da Kadesh-barneya “tafiyar kwana goma sha ɗaya ne daga Horeb [ƙasar duwatsun Jejin Sinai inda aka ba da Dokoki Goma] . . . ta hanyar Dutsen Seyir.” Wannan mummunan sakamako ne na yi wa Jehovah Allah rashin biyayya!—Littafin Ƙidaya 14:26-34.

1:16, 17. Mizanan Allah na shari’a ɗaya ne har a yau ma. Waɗanda aka danƙa wa hakkin yin shari’a ba za su ƙyale son kai ko kuma tsoron mutum ya rinjayi shari’arsu ba.

4:9. Yana da muhimmanci ‘kada [Isra’ilawa] su manta da abubuwan da suka gani da idonsu’ idan za su yi nasara. Yayin da sabuwar duniya da aka yi alkawarinta take kusa, wajibi ne mu ma mu ci gaba da mai da hankali ga ayyuka masu ban al’ajabi na Jehovah ta wurin zama ɗalibai masu nazarin Kalmarsa ƙwarai.

KA ƘAUNACI JEHOVAH, KUMA KA YI BIYAYYA DA DOKOKINSA

(Maimaitawar Shari’a 5:1–26:19)

A jawabinsa na biyu, Musa ya ba da labarin ba da Dokar a Jejin Sinai kuma ya sake ambata Dokoki Goma. An ambata ainihin al’ummai bakwai da za a halaka gaba ɗaya. An tuna wa Isra’ilawa muhimmin darasi da suka koya a jeji: “Ba da abinci kaɗai mutum ke rayuwa ba, amma mutum yana rayuwa da kowane irin abin da yake fitowa daga wurin Ubangiji.” A sabon yanayinsu, dole ne su “kiyaye dukan umarnan.”—Maimaitawar Shari’a 8:3; 11:8.

Yayin da suke ƙasar alkawari, Isra’ilawa za su bukaci dokoki ba kawai game da bauta ba amma kuma don shari’a, sarauta, yaƙi, da zaman rayuwa ta kowace rana a yankin da kuma na kansu. Musa ya maimaita waɗannan dokoki kuma ya nanata bukatar ƙaunar Jehovah da kuma kiyaye dokokinsa.

An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi:

8:3, 4—Ta yaya ne tufafin Isra’ilawa ba su yayyage ba kuma ƙafafunsu ba su kumbura ba sa’ad da suke gantali a jeji? Wannan mu’ujiza ce daidai da yadda ake ba su manna a kai a kai. Isra’ilawa sun yi amfani da tufafi da takalmi da suka soma gantalin da shi, mai yiwuwa suna bayarwa yayin da yaran suke girma kuma manyan suka mutu. Tun da yake ƙirge biyu da aka yi a somawa da kuma ƙarshen gantalin ya nuna cewa adadin Isra’ilawa bai ƙaru ba, yawan tufafi da takalma da suke da shi dā zai ishe su.—Littafin Ƙidaya 2:32; 26:51.

14:21—Me ya sa Isra’ilawa za su ba bare ko kuma su sayar wa baƙo mushe da ba za su ci ba? A cikin Littafi Mai Tsarki kalmar nan ‘bare’ za ta iya nuni ga wanda ba Baisra’ile ba ne da ya zama shigagge ko kuma mazauni da yake bin dokokin ƙasar amma ba ya bauta wa Jehovah. Baƙo da kuma bare da ba su zama shigaggu ba, ba sa bin Dokar kuma za su iya yin amfani da mushe a hanyoyi dabam dabam. An yarda wa Isra’ilawa su sayar ko kuma ba su irin waɗannan dabbobi. A wata sassa kuma, Dokar alkawari ta hana shigagge yin hakan. Yadda aka nuna a Littafin Firistoci 17:10, an hana irin wannan mutum ya ci jinin dabba.

24:6—Me ya sa aka kamanta karɓan jinginar “dutsen niƙa ko ɗan dutsen niƙa” da karɓar jinginar “rai”? Dutsen niƙa ko ɗan dutsen niƙa na wakiltar ‘ran’ mutum ko kuma abin biyan bukatar rayuwarsa. Karɓan kowanne cikinsu zai hana dukan iyalin abincinsu na kullum.

25:9—Mecece ma’anar kwaɓe takalmi da tofa yau a fuskar mutumin da ya ƙi yin wajibin ɗan’uwan miji? Bisa “al’adar Isra’ilawa a dā a kan sha’anin fansa . . . mai sayarwar ya tuɓe takalminsa ya ba mai sayen.” (Rut 4:7) Kwaɓe takalmin mutum da ya ƙi yin wajibin ɗan’uwan miji ya tabbatar cewa ya ƙi matsayinsa da daman haifa wa ɗan’uwansa marigayi magaji. Wannan abin kunya ne. (Maimaitawar Shari’a 25:10) Tofa yau a fuskarsa na nuna wulaƙanci.—Littafin Ƙidaya 12:14.

Darussa da Za Mu Koya:

6:6-9. Yadda aka umurci Isra’ilawa su san Dokar, mu ma dole ne mu san umurnin Allah, mu tuna da su koyaushe, kuma mu koya wa yaranmu. Dole mu ‘ɗaura su a hannunmu don alama’ ta wurin ayyukanmu—da hannunmu ke wakilta—wannan na nuna cewa muna yi wa Jehovah biyayya. Kuma kamar ‘alama a goshi,’ dole dukan mutane su ga cewa muna biyayya.

6:16. Kada mu jaraba Jehovah yadda Isra’ilawa cikin rashin bangaskiya suka yi a Masaha, inda suka yi gunaguni game da rashin ruwa.—Fitowa 17:1-7.

8:11-18. Son abin duniya na iya sa mu manta da Jehovah.

9:4-6. Dole mu mai da hankali da adalcin kai.

13:6. Kada mu ƙyale kowa ya janye mu daga bauta wa Jehovah.

14:1. Zane a jiki na nuna rashin daraja ga jikin ’yan Adam, yana iya alaƙa da addinin ƙarya, kuma dole a guje shi. (1 Sarakuna 18:25-28) Begenmu na tashin matattu zai sa yawan makoki a kan matattu ya zama abin da bai dace ba.

20:5-7; 24:5. Ya kamata a yi la’akari da waɗanda suke da bukata ta musamman ko idan abin da ka ke yi yana da muhimmanci.

22:23-27. Kāriyar da ta fi kyau ita ce mace ta yi kururuwa sa’ad da ake son a fyaɗe ta.

“KU ZAƁI RAI”

(Maimaitawar Shari’a 27:1–34:12)

A jawabinsa na uku, bayan sun ƙetare Urdun Musa ya ce, dole Isra’ilawa su rubuta Dokar a manyan duwatsu kuma su furta la’anar rashin biyayya su kuma furta albarkar yin biyayya. Jawabi na huɗu ya soma da sabonta alkawari tsakanin Jehovah da Isra’ila. Musa ya kuma yi musu kashedi game da rashin biyayya ya kuma gargaɗi mutanen su “zabi rai.”—Maimaitawar Shari’a 30:19.

Ban da jawabai huɗu da ya bayar, Musa ya tattauna canjin shugabanci kuma ya koya wa Isra’ilawa waƙa mai daɗi da ke yabon Jehovah, ya kuma yi musu kashedi game da wahala da rashin bangaskiya za ta kawo. Bayan an albarkaci ƙabilun, Musa ya mutu a shekararsa ta 120 kuma aka binne shi. An yi makoki kwanaki 30, daidai da kusan rabin lokaci da aka rubuta littafin Maimaitawar Shari’a.

An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi:

32:13, 14—Tun da yake an hana Isra’ilawa su ci kitse, menene yake nufi su ci “kitse daga ’yan raguna”? An yi amfani da furcin nan cikin alama kuma yana nufin garke da ya fi kyau. An nuna cewa na alama ne da yake ayar kuma ta yi maganar “jinin anab [Litafi Mai- Tsarki].”

33:1-29—Me ya sa ba a ambata Saminu a albarkar da Musa ya yi wa ’ya’yan Isra’ila ba? Domin Saminu da kuma Lawi sun aikata da ‘fushi,’ kuma fushinsu “mai tsanani ne.” (Farawa 34:13-31; 49:5-7) Gadōnsu bai yi daidai da na sauran ƙabilun ba. Lawi ya sami birane 48, kuma na Saminu na cikin yankin Yahuza ne. (Joshuwa 19:9; 21:41, 42) Shi ya sa, Musa bai ambata Saminu ba. Amma, albarkar Saminu na cikin dukan albarkar da aka yi wa Isra’ila.

Darussa da Za Mu Koya:

31:12. Ya kamata yara su zauna da manya a taron ikilisiya kuma su yi ƙoƙari su saurara kuma su koya.

32:4. Dukan ayyukan Jehovah suna da kyau da yake yana nuna halayensa na yin gaskiya, hikima, ƙauna da iko daidai.

Yana da Muhimmanci a Gare Mu

Littafin Maimaitawar Shari’a ya nuna cewa Jehovah “Ubangiji ɗaya ne.” (Maimaitawar Shari’a 6:4) Littafi ne game da mutane da suke da dangantaka ta musamman da Allah. Littafin Maimaitawar Shari’a ya yi kashedi game da bautar gumaka kuma ya nanata bukatar bauta wa Allah na gaskiya shi kaɗai.

Hakika, littafin Maimaitawar Shari’a yana da muhimmanci a gare mu sosai! Ko da ba ma ƙarƙashin Dokar, za mu koya abubuwa da yawa daga ciki da zai taimake mu mu ‘ƙaunaci Ubangiji Allahnmu da zuciya ɗaya, dukan ranmu, da ƙarfinmu.’—Maimaitawar Shari’a 6:5.

[Hasiya]

a Ƙila Joshuwa ne ya daɗa sura ta ƙarshen, da ke ɗauke da labarin mutuwar Musa, ko kuma Babban Firist Ele’azara.

[Taswira a shafi na 6]

SEYIR

Kadesh- barneya

Dutsen Sinai (Horeb)

Jar Teku

[Inda aka Dauko]

Daga taswirori da Pictorial Archive suke da hakkin wallafawa (Near Eastern History) Est. and Survey of Israel

[Hoto a shafi na 6]

Jawaban Musa ne sashe na musamman na littafin Maimaitawar Shari’a

[Hoto a shafi na 8]

Wane darasi ne manna da Jehovah ya yi tanadinsa ya koyar?

[Hoto a shafi na 8]

An kamanta karɓan jinginar dutsen niƙa ko kuma ɗan dutsen niƙa da karɓan jinginar “rai”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba