Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 1/1 pp. 8-13
  • Jehobah Shi Ne Mataimakinmu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Shi Ne Mataimakinmu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Tushen Taimako da ba ya Ƙarewa
  • Taimako Daga Mala’iku
  • Taimako ta Ruhu Mai Tsarki
  • Taimako Daga Kalmar Allah
  • Taimako ta ’Yan’uwa Masu Bi
  • Kana Amincewa Da Taimakon Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Taimako Daga Malai’ikun Allah
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Yadda Mala’iku Suke Taimaka Maka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Ka Yi Ƙarfin Zuciya, Jehobah Zai Taimake Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 1/1 pp. 8-13

Jehobah Shi Ne Mataimakinmu

“Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa.”—ZABURA 121:2.

1, 2. (a) Me ya sa za a ce dukanmu muna bukatar taimako wani lokaci? (b) Wane irin Mataimaki ne Jehobah?

ACIKINMU waye bai taɓa bukatar taimako ba? Hakika, wani lokaci dukanmu muna bukatar taimako don mu jimre wa babbar matsala, rasuwar wanda muke ƙauna, da kuma gwaji mai tsanani. Sa’ad da mutane suke bukatar taimako, sukan je wajen amini. Jimre damuwarmu zai kasance da sauƙi idan muka gaya wa amini. Amma ba dukan abu ba ne ɗan adam zai iya yi mana. Ban da haka, ba koyaushe ba ne mutane za su iya taimaka maka sa’ad da kake da damuwa.

2 Amma, da Mataimaki da yake da iko da mallaka marar iyaka. Ƙari ga haka, ya tabbatar mana cewa ba zai taɓa yasar da mu ba. Shi ne mai Zabura ya yi maganarsa da cikakken tabbaci: “Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji.” (Zabura 121:2) Me ya sa mai Zabura ya tabbata cewa Jehobah zai taimake shi? Domin a amsa wannan tambayar, bari mu bincika Zabura 121. Yin haka zai taimake mu mu ga abin da ya sa mu ma za mu iya zuba wa Jehobah ido ya taimake mu.

Tushen Taimako da ba ya Ƙarewa

3. Wane dutse ne mai Zabura ya kalla, kuma me ya sa?

3 Mai Zabura ya soma ta wajen nuna cewa za mu iya kasancewa da tabbaci ga Jehobah da yake shi ne mahalicci: “Na duba wajen duwatsu, daga ina taimakona zai zo? Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa.” (Zabura 121:1, 2) Ba kowanne dutse mai Zabura yake maganarsa ba. Sa’ad da aka rubuta waɗannan kalmomi, haikalin Jehobah yana Urushalima. Wannan birnin da ke kan dutsen Yahuza, wurin zaman Jehobah ne na alama. (Zabura 135:21) Wataƙila mai Zabura yana kallon dutsen da aka gina haikalin Jehobah a kai a Urushalima, yana neman taimakon Jehobah. Me ya sa mai Zabura yake da tabbaci cewa Jehobah zai iya taimakonsa? Domin shi ne “ya yi sama da ƙasa.” Wato, mai Zabura cewa yake, ‘Hakika, ba abin da zai hana Mahalicci maɗaukaki duka ya taimake ni!’—Ishaya 40:26.

4. Ta yaya mai Zabura ya nuna cewa Jehobah yana faɗake ga bukatar mutanensa, kuma me ya sa wannan yake da ban ƙarfafa?

4 Mai Zabura kuma ya yi bayani cewa Jehobah yana shirye koyaushe ya biya bukatar bayinsa: “Ba zai bar ka ka fāɗi ba, Makiyayinka, ba zai yi barci ba! Makiyayin Isra’ila, ba ya gyangyaɗi ko barci!” (Zabura 121:3, 4) Allah ba zai ƙyale waɗanda suke dogara gare shi su “fāɗi” ba, ko kuma su yi faɗuwar da ba za su iya tashi ba. (Karin Magana 24:16) Me ya sa? Domin Jehobah yana kama da makiyayi da ke a faɗake yana kiyaye tumakinsa. Wannan yana da ban ƙarfafa, ko ba haka ba? Ba zai daina mai da hankali ko na ɗan lokaci ga bukatar mutanensa ba. Yana lura da su dare da rana.

5. Me ya sa aka ce Jehobah yana “kusa da [hannun damanka]”?

5 Da yake mai Zabura ya tabbata cewa Jehobah yana kiyaye mutanensa, ya rubuta: “Ubangiji [yana] lura da kai, Yana [hannun damanka] domin ya kiyaye ka. Ba za ka sha rana ba, ko farin wata da dare.” (Zabura 121:5, 6) A Gabas ta Tsakiya, wuri mai inuwa zai kāre mai tafiya daga ƙunar rana. Jehobah yana kama da inuwa ga mutanensa, yana kāre su daga ƙunar masifa. Ka lura cewa Jehobah yana [hannun damanka]”? A yaƙe-yaƙe na dā, garkuwa ba ta kāre hannun dama na soja domin yana riƙe ta da hannun hagu. Amini zai kāre abokinsa ta wajen tsayawa a gefen hannunsa na dama ya yi faɗa. Kamar irin wannan abokin, Jehobah yana tsayawa kusa da masu bauta masa, yana shirye koyaushe ya taimake su.

6, 7. (a) Ta yaya mai Zabura ya tabbatar mana cewa Jehobah ba zai taɓa daina taimakon mutanensa ba? (b) Me ya sa za mu kasance da tabbaci kamar mai Zabura?

6 Jehobah zai daina taimakon mutanensa ne? Ba zai taɓa yin haka ba. Mai Zabura ya kammala: “Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan hatsari, zai sa ka zauna lafiya. Zai kiyaye shigarka da fitarka, tun daga yanzu har abada.” (Zabura 121:7, 8) A aya ta 5, mai Zabura ya ce: “Ubangiji [yana] lura da kai.” Amma a wannan ayoyi, mai Zabura ya rubuta: ‘Ubangiji zai kiyaye ka,’ wato a nan gaba. Da haka masu bauta ta gaskiya suna da tabbacin cewa Jehobah zai taimake su har a nan gaba. Zai taimake su a dukan inda suka je da kuma kowace irin masifa da ta same su.—Karin Magana 12:21.

7 Hakika, marubucin Zabura ta 121 yana da tabbacin cewa Mahalicci Maɗaukaki yana lura da bayinsa da kyau kamar yadda makiyayi mai ƙauna da kuma mai gadi da ke a faɗake suke yi. Muna da dalilin kasancewa da tabbaci kamar mai Zabura domin Jehobah ba ya sākewa. (Malakai 3:6) Wannan yana nufi ne cewa koyaushe za a riƙa kāre mu a zahiri? A’a, amma muddin muka nemi taimakonsa, zai kāre mu daga abubuwa da za su yi mana lahani a ruhaniya. Za mu iya tambaya ‘Ta yaya Jehobah yake taimakonmu?’ Bari mu bincika hanyoyi huɗu da yake yin haka. A wannan talifin, za mu tattauna yadda ya taimaki bayinsa a lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki. A talifi na gaba, za mu tattauna yadda yake taimakon mutanensa a yau.

Taimako Daga Mala’iku

8. Me ya sa ba abin mamaki ba ne da mala’iku suke son bayin Allah su zauna lafiya?

8 Jehobah yana da mala’iku miliyoyi da yake amfani da su. (Daniyel 7:9, 10) Waɗannan ’ya’ya na ruhu suna yin nufinsa cikin aminci. (Zabura 103:20) Sun sani sarai cewa Jehobah yana ƙaunar ’yan adam masu bauta masa kuma yana son ya taimake su. Shi ya sa mala’iku suke so bayin Allah na duniya su zauna lafiya. (Luka 15:10) Babu shakka, mala’iku suna farin ciki Jehobah ya yi amfani da su wajen taimakon mutane. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya yi amfani da mala’iku ya taimaki bayinsa na dā?

9. Ka ba da misali na yadda Allah ya ba mala’iku iko su kāre ’yan adam masu aminci.

9 Allah ya ba mala’iku iko su kāre kuma su ceci ’yan adam masu aminci. Mala’iku biyu sun taimaki Lutu da ’ya’yansa mata su tsira daga halakar Saduma da Gwamrata. (Farawa 19:1, 15-17) Mala’ika guda ya kashe sojojin Assuriya 185,000 da suke yi wa Urushalima barazana. (2 Sarakuna 19:35) Sa’ad da aka jefa Daniyel cikin kogon zakoki, Jehobah “ya aiko mala’ikunsa ya rufe bakunan zakoki.” (Daniyel 6:21, 22) Mala’ika ya ceci manzo Bitrus daga kurkuku. (Ayyukan Manzanni 12:6-11) Littafi Mai Tsarki ya ambata misalai da yawa na kāriya da mala’iku suka yi, wannan ya tabbatar da abin da Zabura 34:7 ta ce: “Mala’ikansa yana tsaron waɗanda ke tsoron Ubangiji, ya cece su daga hatsari.”

10. Yaya Jehobah ya yi amfani da mala’ika ya ƙarfafa annabi Daniyel?

10 Wani lokaci, Jehobah yana amfani da mala’iku wajen ƙarfafa ’yan adam masu aminci. Misali mai ban tausayi na cikin littafin Daniyel sura 10. A lokacin, wataƙila shekarun Daniyel sun kusa 100. Annabin ya yi sanyin gwiwa sosai, mai yiwuwa domin yanayin kango na Urushalima kuma ana jinkirin sake gina haikalin. Kuma ya damu sosai bayan ya ga wahayi mai ban tsoro. (Daniyel 10:2, 3, 8) Allah cikin ƙauna ya aiko mala’ika ya ƙarfafa shi. Mala’ikan ya tuna wa Daniyel ba sau ɗaya ba cewa a gaban Allah ana ‘sonsa ƙwarai.’ Menene sakamakon? Annabin da ya tsufa ya gaya wa mala’ikan: “Ka sa na sami ƙarfi.”—Daniyel 10:11, 19.

11. Wane misali ne ya nuna yadda ake amfani da mala’iku wajen ja-gorar aikin wa’azin bishara?

11 Jehobah ya yi amfani da mala’iku wajen yi wa aikin wa’azin bishara ja-gora. Mala’ika ya ja-goranci Filibbus ya yi wa Habashi bābā wa’azi game da Kristi, sai ya yi baftisma. (Ayyukan Manzanni 8:26, 27, 36, 38) Ba da daɗewa ba bayan haka, ya kasance nufin Allah ne a yi wa ’yan Al’umma marasa kaciya wa’azin bishara. Mala’ika ya bayyana wa Karniliyas ɗan Al’umma mai jin tsoron Allah ta wajen wahayi, kuma ya gaya wa Karniliyas ya aika a kirawo manzo Bitrus. Sa’ad da manzannin Karniliyas suka sami Bitrus, suka ce: “Karniliyas . . . wani tsattsarkan mala’ika ya umarce shi, ya aiko ka je gidansa, ya ji maganarka.” Bitrus ya je gidansa, kuma ’yan Al’umma marasa kaciya na farko suka shigo cikin ikilisiyar Kirista. (Ayyukan Manzanni 10:22, 44-48) Babu shakka, za ka yi farin ciki idan ka san mala’ika ya taimake ka ka sadu da mai zuciyar kirki!

Taimako ta Ruhu Mai Tsarki

12, 13. (a) Me ya sa manzannin Yesu suke da dalili na gaskata cewa ruhu mai tsarki zai iya taimakonsu? (b) Ta yaya ruhu mai tsarki ya ba Kiristoci na ƙarni na farko ƙarfi?

12 Kafin ya mutu, Yesu ya tabbatar wa manzanninsa cewa za a taimake su. Uban zai ba su “Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki.” (Yahaya 14:26) Manzannin suna da kyakkyawan dalili na gaskata cewa ruhu mai tsarki zai taimake su. Ballantana ma, Nassosi na cike da misalan yadda Jehobah ya yi amfani da ruhu mai tsarki, iko mafi ƙarfi ya taimaki mutanensa.

13 A lokatai da yawa, an yi amfani da ruhu mai tsarki don a ƙarfafa mutane su yi nufin Jehobah. Ruhu mai tsarki ya ba Alƙalai iko su ceci Isra’ila. (Littafin Mahukunta 3:9, 10; 6:34) Wannan ruhun ya ƙarfafa Kiristoci na ƙarni na farko su ci gaba da wa’azi da gabagaɗi duk da hamayya. (Ayyukan Manzanni 1:8; 4:31) Nasara da suka yi a hidimarsu ta ba da tabbaci sosai cewa ruhu mai tsarki yana aiki. Idan ba haka ba, ta yaya mutane “marasa ilimi . . . talakawa kuma,” za su iya yaɗa saƙon Mulki a dukan duniya na lokacin?—Ayyukan Manzanni 4:13; Kolosiyawa 1:23.

14. Ta yaya Jehobah ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki wajen wayar da mutanensa?

14 Jehobah ya kuma yi amfani da ruhu mai tsarki wajen wayar da mutanensa. Da taimakon ruhun Allah, Yusufu ya bayyana mafarkin annabci na Fir’auna. (Farawa 41:16, 38, 39) Jehobah ya yi amfani da ruhunsa ya bayyana alkawuransa ga masu tawali’u amma ya ɓoye wa masu fahariya. (Matiyu 11:25) Game da abubuwa da Jehobah ya shirya wa “masu ƙaunarsa,” manzo Bulus ya ce: “Mu ne Allah ya bayyana wa, ta Ruhu.” (1 Korantiyawa 2:7-10) Sai da taimakon ruhu mai tsarki mutum zai iya fahimtar nufin Allah.

Taimako Daga Kalmar Allah

15, 16. Menene aka gaya wa Joshuwa ya yi domin ya yi nasara?

15 Kalmar Jehobah hurarriya “mai amfani ne kuwa wajen koyarwa,” kuma tana taimakon bayin Allah su zama cikakku, shiryayyu sosai “ga kowane kyakkyawan aiki.” (2 Timoti 3:16, 17) Littafi Mai Tsarki na ɗauke da misalai da yawa na yadda Kalmarsa ta taimaki mutanen Allah na lokacin dā.

16 Nassosi sun taimaka wajen yi wa masu bauta wa Allah ja-gora da kyau. Sa’ad da aka ɗanka wa Joshuwa hakkin ja-gorar Isra’ila, an gaya masa: “Kada wannan littafin dokoki [da Musa ya rubuta] ya rabu da bakinka, amma zai zama abin da za ka yi ta tunani a kansa dare da rana domin ka kiyaye, ka kuma aikata bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki, gama ta haka za ka yi ta albarka cikin hanyarka, ta haka kuma za ka yi nasara.” Ka lura cewa Allah bai yi alkawarin zai ba wa Joshuwa hikima ta mu’ujiza ba. Amma, Joshuwa zai yi nasara ne idan ya karanta kuma ya yi bimbini a kan “littafin dokoki.”—Joshuwa 1:8; Zabura 1:1-3.

17. Ta yaya Nassosi da suke da shi a dā ya taimaki Daniyel da Sarki Yosiya?

17 Rubutacciyar Kalmar Allah ta bayyana nufinsa da ƙudurinsa. Alal misali, Daniyel ya fahimci tsawon lokacin da Urushalima za ta kasance kango ta rubuce-rubucen Irmiya. (Irmiya 25:11; Daniyel 9:2) Ka yi la’akari da abin da ya faru a lokacin sarautar Sarki Yosiya na Yahuza. A lokacin, al’ummar ta fanɗare daga Jehobah, babu shakka domin sarakunan ba su sa a rubuta musu Dokar ba kuma ba su yi amfani da ita ba. (Maimaitawar Shari’a 17:18-20) Amma da ake gyaran haikalin, aka sami “littafin dokoki” da wataƙila Musa ya rubuta. Wannan wataƙila na asali ne, da aka gama rubutawa shekaru 800 da suka shige. Bayan da aka karanta masa abin da yake ciki, Yosiya ya fahimci cewa al’ummar ta ƙetare nufin Jehobah ƙwarai, kuma sarkin ya ɗauki matakai ya yi abin da aka rubuta a cikin littafin. (2 Sarakuna 22:8; 23:1-7) Ba a bayane yake ba cewa Nassosi Masu Tsarki da mutanen Allah suke da shi dā ya taimake su?

Taimako ta ’Yan’uwa Masu Bi

18. Duk sa’ad da wani mai bauta ta gaskiya ya taimaki wani me ya sa za mu ce Jehobah ne ya sa hakan ya faru?

18 Taimakon Jehobah sau da yawa ta wurin ’yan’uwa masu bi ne. Hakika, Allah ne yake sa masu bauta ta gaskiya su taimaki juna. Me ya sa muka faɗi haka? Domin dalilai biyu. Na farko, ruhu mai tsarki na Allah na aiki. Wannan ruhun yana ba da ’ya’ya, da suka ƙunshi ƙauna da nagarta, ga waɗanda suke nemi ’ya’yan su rinjaye su. (Galatiyawa 5:22, 23) Shi ya sa, sa’ad da bayin Allah suka motsa su taimaki juna, tabbaci ne cewa ruhun Jehobah yana aiki. Na biyu, an halicce mu cikin siffar Allah. (Farawa 1:26) Wannan yana nufin cewa muna iya nuna halayensa, da alherinsa da juyayinsa. Saboda haka, duk sa’ad da wani bawan Jehobah ya taimaki wani, ainihi ana nuna halin Tushen taimako ne.

19. Bisa ga abin da aka faɗa cikin Littafi Mai Tsarki, ta yaya Jehobah yake ba da taimako ta ’yan’uwa masu bi?

19 A lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, ta yaya Jehobah ya yi taimako ta ’yan’uwa masu bi? Jehobah sau da yawa na sa wani cikin bayinsa ya yi wa wani gargaɗi, yadda Irmiya ya yi wa Baruk gargaɗin da ya ceci ransa. (Irmiya 45:1-5) Wani lokaci, masu bauta ta gaskiya sun motsa su agaza wa ’yan’uwa masu bi, yadda Kiristoci a Makidoniya da Akaya suka yi ɗokin taimakon ’yan’uwansu mabukata a Urushalima. Manzo Bulus ya ce irin wannan alherin ya zama sanadin “godiya ga Allah.”—2 Korantiyawa 9:11.

20, 21. A waɗanne yanayi ne ’yan’uwa daga Roma suka ƙarfafa manzo Bulus?

20 Musamman ma labaran yadda bayin Jehobah suka ƙarfafa juna na da ban tausayi. Ka yi la’akari da misalin da ya shafi manzo Bulus. Da yake tafiya zuwa Roma a cikin sarƙa, Bulus ya bi babban hanyar Roma da ake kira Hanyar Abiyus. Kusan ƙarshen tafiyar musamman ba ta da daɗi, domin matafiyan dole ne su bi cikin fadama.a ’Yan’uwa da suke ikilisiya a Roma sun san cewa Bulus yana zuwa. Menene za su yi? Za su jira a gidajensu ne har sai Bulus ya isa birni su je su gaisa?

21 Luka, marubuci na Littafi Mai Tsarki, wanda ya bi Bulus a tafiyar ya gaya mana abin da ya faru: “ ’Yan’uwa na can [Roma] suka ji labarinmu, sai da suka zo tarye mu har Kasuwar Abiyus, da kuma wurin nan da ake kira Maciya Uku.” Za ka iya ƙaga wannan yanayin? Da yake sun san Bulus yana zuwa, ’yan’uwa wakilai suka yi tafiya daga Roma su tarye shi. Wasu sun jira a Kasuwar Abiyus, sananniyar masauƙin matafiya da ta kai kusan mil 46 daga Roma. Sauran ’yan’uwan kuma suka jira a Maciya Uku, wurin hutu da ke misalin mil 36 daga birnin. Menene Bulus ya yi? Luka ya ba da rahoto: “Da . . . ya sadu da su, ya yi godiya ga Allah, jikinsa kuma ya yi ƙarfi.” (Ayyukan Manzanni 28:15) Ka yi tunanin wannan, ganin ’yan’uwa da suka yi tafiya haka mai nisa ya ƙarfafa Bulus kuma ya sanyaya masa zuciya! Wanene Bulus ya gode wa don wannan taimako? Ya gode wa Jehobah Allah, wanda ya sa aka taimake shi.

22. Menene jigonmu na shekara ta 2005, menene za a bincika a talifi na gaba?

22 A bayane yake cewa hurarren labarin yadda Allah ya yi sha’ani da mutane ya nuna cewa shi mataimaki ne. Mataimaki da babu na biyunsa. Daidai da haka, kalmomin da ke Zabura 121:2 ne jigon shekara ta 2005 na Shaidun Jehobah: “Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji.” Amma yaya Jehobah yake taimakonmu a yau? Za a bincika wannan a talifi na gaba.

[Hasiya]

a Mawaƙin Barome, Horace (65—8 K.Z.), wanda ya yi irin wannan tafiya, ya yi maganar wahalar wannan wurin. Horace ya kwatanta Kasuwar Abiyus da cewa ta “matsu da matuƙan jirgin ruwa da masu maciya marowata.” Ya yi maganar “kwarkwata da kwaɗi” da “ɓātaccen ruwa.”

Ka Tuna?

A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya ba da taimako—

• ta mala’iku?

• ta ruhunsa mai tsarki?

• ta hurarriyar Kalmarsa?

• ta ’yan’uwa masu bi?

[Bayanin da ke shafi na 11]

Jigon shekara ta 2005 shi ne: “Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji.”—Zabura 121:2.

[Hoto a shafi na 12]

Bulus ya yi wa Allah godiya domin taimako da ’yan’uwa a Roma suka yi masa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba