Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 1/1 pp. 13-18
  • Kana Amincewa Da Taimakon Jehobah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Amincewa Da Taimakon Jehobah?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Taimako ta Wurin Mala’iku
  • Taimako Daga Shugaban Mala’iku
  • Taimako na Ruhu Mai Tsarki
  • Taimako Daga Kalmar Allah
  • Taimako Daga ’Yan’uwa Masu Bi
  • Jehobah Shi Ne Mataimakinmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Yadda Mala’iku Suke Taimaka Maka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Mala’iku ‘Ruhohi Ne Masu-hidima’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Yadda Mala’iku Ke Taimakon ’Yan Adam
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 1/1 pp. 13-18

Kana Amincewa Da Taimakon Jehobah?

“Ubangiji shi ne mataimakina, ba zan ji tsoro ba.”—IBRANIYAWA 13:6.

1, 2. Me ya sa yake da muhimmanci mu yi na’am da taimakon Jehobah da ja-gorarsa a rayuwarmu?

KA YI tunanin kana tafiya wani wuri da ba ka taɓa zuwa ba cikin dare. Kana tare da wani da ya ce zai raka ka, ya san hanyar sosai kuma yana raka ka da haƙuri. Ya lura cewa kana yawan tuntuɓe. Don ba ya son ka faɗi, sai ya gaya maka gefen da za ka bi don kada ka riƙa yin tuntuɓe. Za ka ƙi shawararsa ne? A’a, don kana cikin haɗari.

2 Mu Kiristoci muna bin tafarki mai wuya. Za mu iya bin tafarkin ne ba tare da taimako ba? (Matiyu 7:14) A’a, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah Allah ne gwanin rakiya da muke da shi, kuma yana ƙyale mutane su yi tafiya da shi. (Farawa 5:24; 6:9) Jehobah yana taimakon mutanensa sa’ad da suke tafiya kuwa? Ya ce: “Ni ne Ubangiji Allahnku, na ƙarfafa ku, na kuwa faɗa muku, ‘Kada ku ji tsoro, ni zan taimake ku.’ ” (Ishaya 41:13) Kamar mai ja-gorar kwatancinmu, Jehobah na taimakon waɗanda suke nema su yi tafiya da shi kuma yana abokantaka da su. Hakika ba wani cikinmu da zai ƙi taimakonsa!

3. Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika a wannan talifi?

3 A talifin da ya gabata, mun tattauna hanyoyi huɗu da Jehobah ya taimaki mutanensa a lokacin dā. Yana taimakon mutanensa haka kuwa a yau? Ta yaya za mu tabbata cewa mun sami irin wannan taimakon? Bari mu tattauna waɗannan tambayoyin. Ta yin hakan za mu ƙara kasancewa da tabbaci cewa Jehobah Mataimakinmu ne da gaske.—Ibraniyawa 13:6.

Taimako ta Wurin Mala’iku

4. Me ya sa bayin Allah a yau suke da tabbaci cewa mala’iku za su tallafa musu?

4 Mala’iku suna taimakon bayin Jehobah na zamani kuwa? E, suna taimakonsu. Hakika, ba sa fitowa a zahiri don su ceci bayi masu bauta ta gaskiya daga haɗari a yau. Har a lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki ma, da kyar mala’iku suke yin hakan. Mutane ba sa ganin yawancin abin da suke yi, yadda yake a yau. Duk da haka, bayin Allah da suka fahimci cewa mala’iku na shirye su tallafa musu sun sami ƙarfafa. (2 Sarakuna 6:14-17) Muna da dalili mai kyau mu ji haka.

5. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mala’iku suna sa hannu a aikin wa’azi a yau?

5 Mala’ikun Jehobah musamman suna son aikin da muke yi. Wane aiki ne wannan? Za mu sami amsar a Wahayin Yahaya 14:6: “Na ga wani mala’ika yana kaɗawa a tsakiyar sararin sama, yana tafe da madawwamiyar bishara domin ya sanar da ita ga mazaunan duniya, wato ga kowace al’umma, da kabila, da harshe, da jama’a.” Wannan “madawwamiyar bishara” tana da alaƙa da “bisharan nan ta Mulkin,” da Yesu ya annabta “za a kuma yi . . . ko’ina a duniya domin shaida ga dukkan al’ummai” kafin ƙarshen wannan zamani. (Matiyu 24:14) Hakika, mala’iku ba sa wa’azi kai tsaye. Yesu ya ba wa mutane ne wannan aikin mai muhimmanci. (Matiyu 28:19, 20) Ba abin ƙarfafa ba ne, mu sani cewa muna samun taimako daga mala’iku masu tsarki masu iko da hikima, sa’ad da muke wannan aikin?

6, 7. (a) Menene ya nuna cewa mala’iku suna tallafa mana a aikinmu na wa’azi? (b) Ta yaya za mu kasance da tabbacin samun taimakon mala’ikun Jehobah?

6 Da tabbaci sosai cewa mala’iku na taimakonmu a aikin da muke yi. Alal misali, sau da yawa muna jin cewa sa’ad da Shaidun Jehobah suke hidima suna saduwa da mutane da suka yi addu’a, Allah ya taimake su su sami gaskiya. Muna samun irin waɗannan labaran a kai a kai, saboda haka ba za a ce sa’a ba ce kawai. Ta wurin taimakon mala’iku, ƙarin mutane suna koyon su yi abin da “mala’ika [da ke] kaɗawa a tsakiyar sararin sama” ya yi shelarsa: “Ku ji tsoron Allah, ku ɗaukaka shi.”—Wahayin Yahaya 14:7.

7 Kana ɗokin samun taimako daga mala’iku masu girma na Jehobah? Sai ka yi iyakacin ƙoƙarinka a hidimarka. (1 Korantiyawa 15:58) Yayin da muka ba da kanmu a wannan aikin Jehobah na musamman, mu tabbata cewa za mu sami taimakon mala’ikunsa.

Taimako Daga Shugaban Mala’iku

8. Wane matsayi mai girma Yesu yake da shi a sama, me ya sa abin ƙarfafa ne a gare mu?

8 Jehobah yana yi mana wani salon taimakon mala’iku. Wahayin Yahaya 10:1 ta kwatanta “wani ƙaƙƙarfan mala’ika” mai ban mamaki wanda “fuska tasa kamar rana.” Wannan mala’ika da aka gani a wahayi babu shakka Yesu Kristi ne a ɗaukakarsa na iko a samaniya. (Wahayin Yahaya 1:13, 16) To, shi Yesu mala’ika ne? E, za a iya faɗan haka, tun da yake shi babban mala’ika ne. (1 Tasalonikawa 4:16) Yesu ya fi dukan ’ya’yan ruhu na Jehobah. Jehobah ya sa shi ya zama shugaban dukan rundunarsa ta mala’iku. Wannan babban mala’ika mai iko tushen taimako ne. A waɗanne hanyoyi?

9, 10. (a) Ta yaya Yesu ya zama ‘mai taimakonmu’ sa’ad da muka yi zunubi? (b) Ta yaya misalin Yesu zai taimake mu?

9 Manzo Yahaya da ya tsufa ya rubuta: “In kuwa wani ya yi zunubi, muna da Mai Taimako a gun Uba, wato Yesu Almasihu mai adalci.” (1 Yahaya 2:1) Me ya sa Yahaya ya ce Yesu ‘Mai Taimakonmu ne’ musamman sa’ad da muka “yi zunubi”? Muna zunubi kullum, kuma sakamakon zunubi mutuwa ne. (Mai Hadishi 7:20; Romawa 6:23) Amma, Yesu ya ba da ransa hadaya don zunubanmu. Kuma yana gefen Ubanmu mai jinƙai yana roƙo dominmu. Kowanenmu na bukatar irin wannan taimako. Ta yaya za mu yi amfani da irin wannan taimako? Muna bukatar mu tuba daga zunubanmu kuma mu nemi gafara bisa hadayar Yesu. Muna kuma bukatar mu guje wa maimaita zunubanmu.

10 Ban da cewa ya mutu dominmu, Yesu ya kafa misali mai kyau da za mu bi. (1 Bitrus 2:21) Misalinsa na yi mana ja-gora, yana taimakonmu mu tsara tafarkinmu don mu kauce wa zunubi mai tsanani kuma mu faranta wa Jehobah Allah rai. Muna godiya don irin wannan taimako. Yesu ya yi wa mabiyansa alkawarin wani mai taimako.

Taimako na Ruhu Mai Tsarki

11, 12. Menene ruhun Jehobah, ta yaya yake da iko, me ya sa muke bukatar taimakonsa a yau?

11 Yesu ya yi alkawari: “Zan roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimako ya kasance tare da ku har abada. Shi ne Ruhu na gaskiya, wanda duniya ba ta iya samunsa.” (Yahaya 14:16, 17) Wannan “ruhu na gaskiya,” ko ruhu mai tsarki ba mutum ba ne amma iko ne, ikon aiki na Jehobah. Iko ne marar iyaka. Iko ne da Jehobah ya yi amfani da shi ya halicce sararin samaniya, da shi ya yi mu’ujizai na ban mamaki, kuma da shi ya bayyana nufinsa ta wahayi. Tun da yake Jehobah ba ya amfani da ruhunsa a waɗannan hanyoyi a yau, yana nufi ne cewa ba ma bukatar taimakon ruhun?

12 A’a! Mun fi bukatar taimakon ruhun Jehobah a wannan “zamanin ƙarshe [da] za a sha wuya ƙwarai.” (2 Timoti 3:1) Yana ƙarfafa mu mu jimre wa gwaji. Yana taimakonmu mu koyi halaye masu kyau da ke sa mu kusaci Jehobah da ’yan’uwanmu na ruhaniya. (Galatiyawa 5:22, 23) Ta yaya za mu amfana daga wannan taimako mai girma daga Jehobah?

13, 14. (a) Me ya sa za mu tabbata cewa Jehobah yana ba mutanensa ruhunsa mai tsarki da yardan rai? (b) Ta waɗanne ayyuka za mu nuna cewa ba ma son kyautar ruhu mai tsarki?

13 Na farko, muna bukatar mu yi addu’a don ruhu mai tsarki. Yesu ya ce: “Ku da kuke mugaye ma kuka san yadda za ku ba ’ya’yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama zai ba da Ruhu Mai Tsarki ga masu roƙonsa.” (Luka 11:13) Hakika, Jehobah shi ne Uba mafi kyau. Idan tare da bangaskiya muka roƙi ruhu mai tsarki, babu shakka zai ba mu kyauta. To, tambayar ita ce, Muna roƙonsa kuwa? Ya kamata muna roƙon wannan duk lokacin da muke addu’a.

14 Na biyu, za mu samu wannan kyauta ta yin aiki cikin jituwa da shi. Alal misali: A ce Kirista yana fama da raunin kallon hotunan bātsa. Ya yi addu’a don ruhu mai tsarki ya taimake shi ya daina wannan ƙazamin hali. Ya nemi shawara daga dattawa Kirista, kuma suka shawarce shi ya daina ma zuwa kusa da irin wannan mummunar abu. (Matiyu 5:29) Idan ya yi banza da gargaɗinsu, kuma ya ci gaba da kallon irin wannan abu sa’ad da jarabar ta zo fa? Yana aiki cikin jituwa da addu’arsa cewa ruhu mai tsarki ya taimake shi kuwa? Ko kuwa yana cikin haɗarin ɓata wa ruhun Allah rai kuma ya yi hasarar wannan kyautar? (Afisawa 4:30) Hakika, dukanmu muna bukatar mu yi iyaka ƙoƙarinmu mu tabbata cewa mun ci gaba da samun wannan taimako mai ban al’ajabi daga Jehobah.

Taimako Daga Kalmar Allah

15. Ta yaya za mu nuna cewa muna ɗaukan Littafi Mai Tsarki da muhimmanci?

15 Littafi Mai Tsarki ya taimaki amintattu bayin Jehobah cikin ƙarnuka masu yawa. Maimakon mu ɗauki Littafi Mai Tsarki da rashin muhimmanci, muna bukatar mu tuna cewa tushen mai iko ne na taimako. Samun wannan taimako na bukatar ƙoƙari. Muna bukatar mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai.

16, 17. (a) Ta yaya Zabura 1:2, 3 suka kwatanta albarkar karanta dokar Allah? (b) Ta yaya Zabura 1:3 ta zana hoton aiki tuƙuru?

16 Zabura 1:2, 3 sun yi maganar mutum mai ibada: “Yana jin daɗin karanta shari’ar Allah, yana ta nazarinta dare da rana. Yana kama da itacen da ke a gefen ƙorama, yakan ba da ’ya’ya a kan kari, ganyayensa ba sa yin yaushi, yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.” Ka ga darassi mafi muhimmanci a wannan ayar? Yana da sauƙi bayan an karanta wannan a kammala da cewa ana maganar yanayi ne mai ni’ima, wuri mai itatuwa da ke girma a bakin ƙorama. Irin wannan wuri na da daɗin hutu da tsakar rana! Amma wannan zabura ba ta kwatanta mana yanayi mai ni’ima na hutu. Tana maganar aiki ne da ƙwazo. Ta yaya?

17 Itace da ake maganarsa a nan ba bishiya ba ce mai ba da inuwa da ke girma kusa da ƙorama. Bishiya ce mai ba da ’ya’ya, da aka shuka a “gefen ƙorama.” Ta yaya bishiya guda za ta yi girma a gefen ƙorama? Mai garka zai iya gina tushen ruwa ga saiwoyin bishiyoyinsa masu ba da amfani. Yanzu darasin a bayane yake! Idan muka yi girma a azanci na ruhaniya kamar wannan itace, domin wani ya taimake mu ne sosai. Muna tarayya da ƙungiyar da ke kawo mana ruwa ta gaskiya, amma dole mu yi namu aikin. Muna bukatar mu ba da kanmu mu sha wannan ruwa mai tamani, mu yi bimbini da bincike da ake bukata don mu sahinta gaskiyar Kalmar Allah a zuciyarmu. Ta haka mu ma za mu ba da ’ya’ya masu kyau.

18. Menene ake bukata don mu samu amsoshin Littafi Mai Tsarki ga tambayoyinmu?

18 Littafi Mai Tsarki ba zai amfane mu ba idan yana kan kanta ne kawai ba a buɗewa. Littafi Mai Tsarki ba laya ba ne, ba za mu rufe idanunmu mu buɗe ba, mu yi tsammanin za mu sami amsar tambayarmu a shafin da ke gabanmu. Idan muna son mu tsai da shawara, muna bukatar mu tona “sanin Allah” kamar dukiya da aka binne. (Karin Magana 2:1-5) Sau da yawa ana bukatar a yi bincike sosai domin a samu gargaɗi na Nassi da ya yi maganar bukatunmu. Muna da littattafai da yawa daga Littafi Mai Tsarki da za su taimake mu mu yi bincike. Idan mun yi amfani da waɗannan don mu tona abubuwa masu kyau na Kalmar Allah, za mu amfana daga taimakon Jehobah.

Taimako Daga ’Yan’uwa Masu Bi

19. (a) Me ya sa za a ɗauki talifofin Hasumiyar Tsaro da Awake! a madadin taimako daga ’yan’uwa masu bi? (b) Ta yaya wani talifi cikin jaridunmu ya taimake ka?

19 Bayin Jehobah koyaushe suna taimakon juna. Jehobah ya canja ne? Ko kaɗan. Kowannenmu babu shakka zai iya tuna lokacin da ya sami taimako da yake bukata daga ’yan’uwa a daidai lokacin da yake bukatar haka. Alal misali, za ka iya tuna wani talifi cikin Hasumiyar Tsaro ko Awake! da ya ƙarfafa ka sa’ad da kake bukatarsa ko kuma ya taimake ka ka magance wata matsala ko tangarɗa ga bangaskiyarka? Jehobah ne ya yi maka wannan taimako ta “amintaccen bawan nan mai hikima” da aka ce ya riƙa ba da ‘abinci a kan kari.’—Matiyu 24:45-47.

20. A waɗanne hanyoyi ne dattawa Kirista suka zama “ ’yan adam bayabaye”?

20 Amma, sau da yawa taimako da muke samu daga ’yan’uwa masu bi na kai tsaye ne. Wataƙila dattijo Kirista ya ba da jawabi da ya motsa zuciyarmu, ko kuma ya ziyarce mu ya taimake mu a lokaci mai wuya, ko kuma ya ba da gargaɗi da ya taimake mu mu sha kan wani kumammanci. Wata mata Kirista ta rubuta game da taimako da wani dattijo ya yi mata: “A hidimar fage ya ƙarfafa ni sosai. Daddare kafin lokacin, na yi wa Jehobah addu’a ya nuna mini wanda zan iya yi masa magana. Washegari, wannan ɗan’uwan ya yi mini magana da juyayi. Ya taimake ni na ga yadda Jehobah yake taimako na da daɗewa. Na gode wa Jehobah da ya aiko mini wannan dattijo.” Ta haka, dattawa Kirista suna nuna su “ ’yan adam bayabaye,” ne da Jehobah ya yi tanadinsu ta Yesu Kristi su taimake mu mu jimre a hanyar rai.—Afisawa 4:8.

21, 22. (a) Wace albarka waɗanda suke cikin ikilisiya za su samu idan suka yi amfani da gargaɗin da ke Filibiyawa 2:4? (b) Me ya sa ƙananan ayyukan alheri suke da muhimmanci?

21 Ban da dattawa, ya kamata kowanne Kirista mai aminci ya yi amfani da umurnin nan “kada ya kula da harkar kansa kawai, sai dai ya kula, har da ta ɗan’uwansa ma.” (Filibiyawa 2:4) Sa’ad da waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista suka yi amfani da wannan gargaɗi, sun yi alheri ke nan. Alal misali, wata iyali ta sha wahalar masifu farat ɗaya. Baban ya tafi kanti da ’yarsa ƙarama. Da suke komawa gida, suka yi haɗarin mota. ’Yar ta mutu, baban ya ji rauni sosai. Da aka sallame shi daga asibiti, bai iya yin kome ba da farko. Matarsa ta yi baƙin ciki sosai da ba za ta iya kula da shi ita kaɗai ba. Ma’aurata cikin ikilisiya suka kai wannan mata da miji da suke baƙin ciki gidansu suka kula da su na makonni da yawa.

22 Hakika, ba dukan ayyukan alheri suka shafi irin wannan masifa da sadaukar da kai ba. Wasu taimako da muke samu kaɗan ne. Amma ko yaya alherin yake, ya kamata mu yi godiya, ko ba haka ba? Ka tuna lokacin da alheri ko kuma ayyuka da ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta yi ya taimaka maka? Jehobah yana kula da mu a waɗannan hanyoyi.—Karin Magana 17:17; 18:24.

23. Yaya Jehobah yake ji sa’ad da muka yi ƙoƙari mu taimaki juna?

23 Za ka so Jehobah ya yi amfani da kai a taimakon mutane? Kana da irin wannan gatar. Jehobah yana daraja irin wannan aikin. Kalmarsa ta ce: “Sa’ad da ka bayar ga matalauci kamar ka ba Ubangiji rance ne, gama Ubangiji zai sāka maka.” (Karin Magana 19:17) Muna farin ciki sosai sa’ad da muka ba da kanmu mu taimaki ’yan’uwanmu. (Ayyukan Manzanni 20:35) Waɗanda da gangan ba sa kula da mutane ba sa farin ciki ko ƙarfafawa da ake samu ta wajen ba da taimako. (Karin Magana 18:1) Saboda haka, cikin aminci mu ci gaba da zuwa tarurruka na Kirista don mu ƙarfafa juna.—Ibraniyawa 10:24, 25.

24. Me ya sa ba za mu ji an hana mu abu ba domin ba mu ga mu’ujizai na ban mamaki da Jehobah ya yi ba a dā?

24 Ba abu mai kyau ba ne mu yi tunanin hanyoyi da Jehobah yake taimakonmu? Ko da ba ma lokacin da Jehobah yake mu’ujizai na musamman don ya cika nufe-nufensa, bai kamata mu ji an hana mu wani abu ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne cewa Jehobah yana ba da taimako da muke bukata domin mu kasance da aminci. Idan muka jimre tare da bangaskiya, za mu rayu mu ga ayyuka na Jehobah da suka fi ɗaukaka a dukan tarihi! Mu ƙuduri niyyar samu da kuma yin amfani da taimako daga Jehobah don mu ce cikin jituwa da kalmomin jigonmu na shekara ta 2005: “Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji.”—Zabura 121:2.

Me Ka Ce?

Ta yaya Jehobah yake taimakonmu a yau—

• ta mala’iku?

• ta ruhunsa mai tsarki?

• ta hurarriyar Kalmarsa?

• ta ’yan’uwa masu bi?

[Hoto a shafi na 14]

Yana da ban ƙarfafa mu san cewa mala’iku suna goyon bayan aikin wa’azi

[Hoto a shafi na 17]

Jehobah yana iya amfani da ’yan’uwanmu ya yi mana taimako da muke bukata

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba