Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 4/1 pp. 11-15
  • Yadda Mala’iku Ke Taimakon ’Yan Adam

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Mala’iku Ke Taimakon ’Yan Adam
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ta Yaya Mala’iku Suka Wanzu?
  • Wane Hakki ne Mala’iku Suke Cikawa?
  • Taimakon Mala’iku a Zamanin Kristi
  • Taimakon Mala’iku a Wannan Zamani
  • Aiki na Musamman da Mala’iku Za Su Yi a Nan Gaba
  • Mala’iku ‘Ruhohi Ne Masu-hidima’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Yadda Mala’iku Suke Taimaka Maka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Su Waye ne ko Kuma Mene ne Ake Nufi da Mala’iku?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Taimako Daga Malai’ikun Allah
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 4/1 pp. 11-15

Yadda Mala’iku Ke Taimakon ’Yan Adam

“Bayan wannan na ga wani mala’ika yana saukowa daga sama, yana da hukunci dayawa . . . Ya tada murya da ƙarfi, ya ce, Faɗaɗiya ce, faɗaɗiya ce Babila babba.”—RU’YA TA YOHANNA 18:1, 2.

1, 2. Menene ya nuna cewa Jehobah yana amfani da mala’iku wajen cika nufinsa?

SA’AD da yake zaman bauta a tsibirin Batmusa, an nuna wa manzo Yohanna da ya tsufa wahayi na annabci. Ya ga aukuwa masu ban mamaki sa’ad da yake “cikin ruhu” ya kasance cikin “ranar Ubangiji.” Wannan ranar ta soma sa’ad da aka naɗa Yesu Kristi sarki a shekara ta 1914, kuma zai ci gaba har ƙarshen Sarautarsa ta Shekara Dubu.—Ru’ya ta Yohanna 1:10.

2 Jehobah Allah bai nuna wa Yohanna wannan wahayi kai tsaye ba. Ya yi amfani da wata hanya. Ru’ya ta Yohanna 1:1 ta ce: “Ru’ya ta Yesu Kristi, wadda Allah ya ba shi domin shi bayana ma bayinsa, al’amura ke nan da za su faru ba da jinkiri ba: ya kuma aiko ya shaida ta bakin mala’ikansa zuwa ga bawansa Yohanna.” Ta wurin Yesu, Jehobah ya yi amfani da mala’ika ya sanar da Yohanna abubuwa masu ban al’ajabi game da “ranar Ubangiji.” Akwai lokacin da Yohanna ya “ga wani mala’ika yana saukowa daga sama, yana da hukunci dayawa.” Menene aikin wannan mala’ikan? “Ya tada murya da ƙarfi, ya ce, Faɗaɗiya ce, faɗaɗiya ce Babila babba.” (Ru’ya ta Yohanna 18:1, 2) Wannan mala’ika mai iko yana da gatar yin shela game da faɗuwar Babila Babba, wato, daular duniya ta addinin ƙarya. Babu shakka, Jehobah yana amfani da mala’iku a hanya mai muhimmanci wajen cika nufinsa. Kafin mu bincika matsayin mala’iku wajen cika nufin Allah da kuma yadda suke taimakonmu, bari mu bincika asalin waɗannan halittu na ruhu.

Ta Yaya Mala’iku Suka Wanzu?

3. Wane ra’ayi ne da bai dace ba mutane da yawa suke da shi game da mala’iku?

3 Mutane da yawa a yau sun gaskata cewa akwai mala’iku. Amma mutane da yawa suna kuskure a ra’ayinsu game da su da kuma asalinsu. Alal misali, wasu masu bin addini suna tunani cewa sa’ad da mutum ya mutu, ana kai mutumin sama kuma ya zama mala’ika. Wannan shi ne kuwa abin da Kalmar Allah take koyarwa game da halittar, wanzuwa da kuma amfanin mala’iku?

4. Menene Nassi ya gaya mana game da tushen mala’iku?

4 Ana kiran mala’ikan da ya fi iko, wato shugaban mala’iku, Mika’ilu. (Yahuda 9) Kuma shi ne Yesu Kristi. (1 Tassalunikawa 4:16) Shekaru aru aru, sa’ad da Jehobah yake son ya soma halitta, abu na farko da ya fara halitta shi ne wannan Ɗa mala’ika. (Ru’ya ta Yohanna 3:14) Bayan haka, Jehobah ya yi amfani da wannan Ɗansa na fari ya halicci dukan mala’iku na ruhu. (Kolossiyawa 1:15-17) Da yake maganar waɗannan ’ya’yansa halittu, Jehobah ya tambayi Ayuba uban iyali: “Ina ka ke sa’anda na sanya tussan duniya? Shaida dai, idan kana da fahimi. Wanene ya sanya dutsen ƙusurwarta; sa’anda taurarin safiya suka yi waƙa, dukan ’ya’yan Allah kuwa suka yi sowa don farinciki?” (Ayuba 38:4, 6, 7) Hakika, Allah ne ya halicci mala’iku kuma sun soma wanzuwa da daɗewa kafin ’yan adam.

5. Ta yaya aka tsara mala’iku?

5 “Allah ba Allah na yamutsai ba ne, amma na kwanciyar rai ne” in ji 1 Korinthiyawa 14:33. Jehobah ya tsara ’ya’yansa na ruhu zuwa rukuni uku: Na (1) da akwai mala’iku da ake kira saraphim, waɗanda suke tsayawa a kursiyin Allah, suke shelar tsarkinsa, kuma suke tsarkake mutanensa a ruhaniya, na; (2) Kerub, suna ɗaukaka ikon mallakar Jehobah, da kuma na; (3) sauran mala’iku da suke cika nufinsa. (Zabura 103:20; Ishaya 6:1-3; Ezekiel 10:3-5; Daniel 7:10) Waɗanne hanyoyi ne waɗannan halittu na ruhu masu yawa suke taimakon ’yan adam?—Ru’ya ta Yohanna 5:11.

Wane Hakki ne Mala’iku Suke Cikawa?

6. Ta yaya Jehobah ya yi amfani da mala’iku kerub a lambun Adnin?

6 An yi magana na farko kai tsaye game da halittu na ruhu a Farawa 3:24, kuma ta ce: “[Jehobah] ya fa kore mutumin; a gabashin gonar Adnin kuma ya sanya Cherubim, da takobi mai-harshen wuta mai-juyawa a kowace fuska, domin a tsare hanyar itace na rai.” Waɗannan kerub sun hana Adamu da Hauwa’u su sake shiga gidansu na lambu na asali. Wannan ya faru a somawar tarihin ’yan adam. Wane hakki ne mala’iku suke cikawa tun lokacin?

7. Menene ma’anar kalmomin yare na asali na “mala’ika” ya nuna game da ɗaya cikin hakkokin da mala’iku suke cika wa?

7 An ambata mala’iku kusan sau 400 a cikin Littafi Mai Tsarki. Ana iya fassara kalmar nan “mala’ika” zuwa “manzo” a Ibrananci da Helenanci. Allah ya yi amfani da mala’iku wajen sadawa da ’yan adam. Kamar yadda aka faɗa a sakin layi na ɗaya da na biyu na wannan talifin, Jehobah ya yi amfani da wani mala’ika ya idar da saƙonsa ga manzo Yohanna.

8, 9. (a) Ta yaya ziyarar mala’ika ta shafi Manoah da matarsa? (b) Menene iyaye za su koya daga ziyarar da mala’ikan Allah ya yi wa Manoah?

8 An yi amfani da mala’iku wajen taimako da kuma ƙarfafa bayin Allah a duniya. Alal misali, a lokacin Alƙalawa a Isra’ila, Manoah da matarsa bakararriya suna neman haihuwa. Jehobah ya aika mala’ikansa ya gaya wa matar Manoah cewa za ta haifi ɗa. Labarin ya gaya mana cewa: “Ga shi, za ki yi ciki, za ki haifi ɗa; aska ba za ta ga kansa ba: gama yaron za ya zama Naziri ga Allah tun daga ciki. Shi za shi fara ceton Isra’ila daga hannun Philistiyawa.”—Alƙalawa 13:1-5.

9 Matar Manoah kuwa ta haifi ɗa Samson, wanda ya zama sananne a labarin Littafi Mai Tsarki. (Alƙalawa 13:24) Kafin a haifi ɗan, Manoah ya yi roƙo mala’ikan ya dawo ya umurce su game da yadda za su yi renon yaron. Manoah ya yi tambaya: “Wane irin goyo za mu yi ma yaron, mi za mu yi masa kuma?” Mala’ikan Jehobah ya maimaita umurnin da ya ba matar Manoah. (Alƙalawa 13:6-14) Babu shakka wannan ya ƙarfafa Manoah! Mala’iku ba sa ziyarar mutane a yau, amma kamar Manoah, iyaye za su nemi umurnin Jehobah sa’ad da suke renon yaransu.—Afisawa 6:4.

10, 11. (a) Ta yaya rundunar Suriya da suka kai hari suka shafi Elisha da bawansa? (b) Ta yaya za mu amfana ta wurin bincika wannan aukuwa?

10 Da akwai misali mai ban sha’awa game da yadda mala’ika ya ba da taimako a kwanakin annabi Elisha. Elisha yana zama a Dothan, wani birni a Isra’ila. Wata rana sa’ad da bawan Elisha ya tashi da sassafe ya kalli waje, sai ya ga cewa dawakai da karusai sun kewaye birnin. Sarkin Suriya ya aika da runduna masu ƙarfi su kama Elisha. Menene bawan Elisha ya yi? Ya ji tsoro sosai, wataƙila yana rawan jiki, sai ya ta da murya ya yi ihu: “Kaito ubanɗakina! yaya za mu yi?” A gare shi babu bege. Amma Elisha ya amsa: “Ka da ka ji tsoro: gama waɗanda ke tare da mu sun fi waɗanda ke tare da su yawa.” Menene yake nufi?—2 Sarakuna 6:11-16.

11 Elisha ya sani cewa rundunar mala’iku suna nan su taimake shi. Amma bawansa bai ga kome ba. Sai “Elisha ya yi addu’a, ya ce, ya Ubangiji, ina roƙonka, ka buɗe idanunsa domin shi gani. Ubangiji kuwa ya buɗe idanun sarmayin; ya gani; ga shi kuwa, dutsen yana cike da dawakai, da karusai na wuta kewaye da Elisha.” (2 Sarakuna 6:17) Sai bawan ya ga rundunan mala’iku. Da fahimi na ruhaniya, mun san cewa dukan mala’iku da suke ƙarƙashin Jehobah da Kristi ne suke taimakon mutanen Jehobah kuma suke kāre su.

Taimakon Mala’iku a Zamanin Kristi

12. Wane taimako ne Maryamu ta samu daga mala’ika Jibra’ilu?

12 Ka yi la’akari da taimako da budurwa Maryamu Bayahudiya ta samu sa’ad da ta sami wannan labarin: “Za ki yi ciki, za ki haifi ɗa, za ki ba shi suna Yesu.” Kafin ya ba da wannan saƙo mai ban mamaki, mala’ika Jibra’ilu, wanda Allah ya aika ya ce mata: “Kada ki ji tsoro, Maryamu, gama kin sami tagomashi wurin Allah.” (Luka 1:26, 27, 30, 31) Babu shakka waɗannan kalmomi masu ban ƙarfafa sun tabbatar wa Maryamu cewa ta sami tagomashin Allah!

13. Ta yaya mala’iku suka taimaki Yesu?

13 Wani misali na taimakon mala’iku ya faru bayan Yesu ya tsayayya wa gwaji uku da Shaiɗan ya yi masa a cikin jeji. Labarin ya gaya mana cewa bayan gwajin, “Shaiɗan ya rabu da shi; ga mala’iku kuma suka zo, suka yi masa hidima.” (Matta 4:1-11) Irin wannan abu ya faru a daren da Yesu zai mutu. Cikin baƙin ciki Yesu ya durƙusa ya soma addu’a yana cewa: “Ubana, in ka yarda, ka kawas mani da wannan ƙoƙo: amma dai ba nawa nufi ba, naka za a yi. Sai mala’ika daga sama ya bayana gareshi, yana ƙarfafa shi.” (Luka 22:42, 43) Wane irin taimako na mala’iku ne muke samu a yau?

Taimakon Mala’iku a Wannan Zamani

14. Wane tsanantawa ne Shaidun Jehobah suka jimre a zamaninmu, kuma menene sakamakonsa?

14 Idan muka bincika tarihin aikin wa’azi na Shaidun Jehobah na zamani, ba mu ganin tabbacin taimako na mala’iku? Alal misali, mutanen Jehobah sun jimre hari da ’yan Nazi a Jamus da kuma Yammacin Turai suka kai musu kafin Yaƙin Duniya na biyu da kuma lokacin yaƙin (wato shekara 1935 zuwa 1945). A ƙarƙashin mulkin Wariya na cocin Katolika a Italiya, Spain, da Portugal, Shaidu sun jimre wa tsanantawa na dogon lokaci. Kuma cikin shekaru da yawa sun jimre wa tsanantawa a Rasha ta dā da ƙasashen da ke ƙarƙashinta. Wani misali kuma shi ne tsanantawa da Shaidu suka jimre a wasu ƙasashen Afirka.a Kwanan nan, bayin Jehobah sun sha wahala mai tsanani a ƙasar Georgia. Shaiɗan ya yi iya ƙoƙarinsa ya sa Shaidun Jehobah su daina aikinsu. Duk da haka, ƙungiyar ta tsira wa irin wannan hamayya kuma ta yi nasara. Wannan ya kasance haka domin kāriyar da mala’iku suka ba da.—Zabura 34:7; Daniel 3:28; 6:22.

15, 16. Wane taimako na mala’iku ne Shaidun Jehobah suke samu a hidimarsu na dukan duniya?

15 Shaidun Jehobah ba sa wasa da aikinsu na wa’azin bishara na Mulkin Allah a dukan duniya kuma suna almajirantarwa ta koya wa mutane masu son saƙon gaskiyar Littafi Mai Tsarki a ko’ina. (Matta 28:19, 20) Amma sun san cewa sai da taimakon mala’iku ne za su iya cika wannan aikin. Saboda haka, abin da aka rubuta a Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7 abin ƙarfafa ne a gare su. Wurin ya ce: “[Ni manzo Yohanna] na ga wani mala’ika kuma yana firiya a tsakiyar sararin sama, yana da bishara ta har abada wadda za ya yi shelarta ga mazaunan duniya, ga kowane iri da ƙabila da harshe da al’umma; da babbar murya kuwa ya ce, Ku ji tsoron Allah, ku ba shi daraja; gama sa’ar hukuncinsa ta zo: ku yi sujjada ga wanda ya yi sama da duniya da teku da maɓulɓulan ruwaye.”

16 Waɗannan kalmomin sun nuna sarai cewa mala’iku suna goyon bayan aikin bishara da Shaidun Jehobah suke yi a dukan duniya kuma suna yi wa aikin ja-gora. Jehobah yana amfani da mala’ikunsa ya yi wa sahihan mutane ja-gora zuwa wurin Shaidunsa. Mala’iku sun yi wa Shaidu ja-gora zuwa wurin mutanen da suka cancanta. Wannan ya bayyana dalilin da ya sa sau da yawa, Shaidun Jehobah suna saduwa da mutum daidai lokacin da shi ko ita yake ko take fuskantar wahala kuma yake ko take bukatar taimako na ruhaniya.

Aiki na Musamman da Mala’iku Za Su Yi a Nan Gaba

17. Menene ya faru da mutanen Assuriya sa’ad da mala’ika guda ya kai musu hari?

17 Ban da yin hidima na manzanni da kuma ƙarfafa masu bauta wa Jehobah, mala’iku suna biyan wata bukata. A dā suna idar da hukuncin Allah. A ƙarni na takwas K.Z., sojojin Assuriya sun yi wa Urushalima barazana. Menene Jehobah ya yi? Ya ce: “Zan yi ma wannan birni kāriya garin in cece ta, sabili da kaina, sabili da bawana Dauda kuma.” Labarin Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abin da ya faru: “A daren nan fa ya zama mala’ikan Ubangiji ya fita, ya buga mutum zambar ɗari da tamanin da biyar cikin sansanin Assuriyawa: sa’anda aka tashi da safe ga dukan mutane matattu gawaye.” (2 Sarakuna 19:34, 35) Sojojin mutum ba komi ba ne idan aka gwada da ƙarfin mala’ika guda!

18, 19. Wane aiki na musamman ne mala’iku za su yi nan gaba, kuma yaya wannan zai shafi ’yan adam?

18 Allah zai yi amfani da mala’iku wajen zartar da hukunci a nan gaba. Ba da daɗewa ba, Yesu zai zo “da mala’iku na ikonsa cikin wuta mai-huruwa.” Aikinsu shi ne su yi “ramako bisa waɗanda ba su san Allah ba, da waɗanda sun ƙi yin biyayya da bisharar.” (2 Tassalunikawa 1:7, 8) Wannan zai shafi ’yan adam sosai! Za a halaka waɗanda suka ƙi su saurari bisharar Mulkin Allah da ake wa’azinsa yanzu a dukan duniya. Sai waɗanda suka biɗi Jehobah, da adalci, da tawali’u ne za ‘a ɓoye su a cikin ranar fushin Ubangiji’ kuma ba abin da zai same su.—Zephaniah 2:3.

19 Za mu yi godiya cewa Jehobah yana amfani da mala’ikunsa masu iko ya tallafa kuma ya ƙarfafa masu bauta masa a duniya. Fahimtar matsayin mala’iku a nufin Allah yana da ban ƙarfafa, tun da yake da akwai mala’iku da suka yi wa Jehobah tawaye kuma suna ƙarƙashin sarautar Shaiɗan. Talifi na gaba zai bayyana matakai da Kiristoci na gaskiya suka ɗauka don su kāre kansu daga ikon Shaiɗan Iblis da aljannunsa.

[Hasiya]

a Don bayani na dalla-dalla game da wannan tsanantawa, ka duba littafin nan Yearbook of Jehovah’s Witnesses na shekara ta 1983 (Angola), 1972 (Czechoslovakia), 2000 (Jamhuriyar Czech), 1992 (Ethiopia), 1974 da 1999 (Jamus), 1982 (Italiya), 1999 (Malawi), 2004 (Moldova), 1996 (Mazambik), 1994 (Poland), 1983 (Portugal), 1978 (Spain), 2002 (Ukraine), da kuma 2006 (Zambiya).

Menene Ka Koya?

• Ta yaya mala’iku suka wanzu?

• Ta yaya aka yi amfani da mala’iku a lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki?

• Menene Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7 suka bayyana game da ayyukan mala’iku a yau?

• Wane aiki na musamman ne mala’iku za su yi a nan gaba?

[Hoto a shafi na 12]

Mala’ika ya ƙarfafa Manoah da matarsa

[Hoto a shafi na 13]

“Waɗanda ke tare da mu sun fi waɗanda ke tare da su yawa”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba