Neman ‘Lu’ulu’u Mai Tamanin Gaske’ A Yau
“Za a kuma yi bisharan nan ta Mulkin Sama ko’ina a duniya domin shaida.”—MATIYU 24:14.
1, 2. (a) Yaya Yahudawa na zamanin Yesu suka ji game da Mulkin Allah? (b) Menene Yesu ya yi domin ya sa a fahimci batun Mulkin da kyau, kuma menene sakamakon haka?
MULKIN Allah ne batun da Yahudawa suke so sosai sa’ad da Yesu yake duniya. (Matiyu 3:1, 2; 4:23-25; Yahaya 1:49) Amma, da farko yawancinsu ba su fahimci yadda mulkin zai yi sarauta ba; kuma ba su fahimci cewa zai zama gwamnati ne na samaniya ba. (Yahaya 3:1-5) Waɗanda suka zama mabiyan Yesu ma ba su fahimci ko menene Mulkin Allah ba kuma ba su fahimci abin da za su yi domin su sami albarkar zama abokan sarauta da Kristi ba.—Matiyu 20:20-22; Luka 19:11; Ayyukan Manzanni 1:6.
2 Da shigewar lokaci, Yesu ya koya wa almajiransa abubuwa da yawa cikin haƙuri, har da almarar lu’ulu’u mai tamanin gaske da aka bincika a talifin da ya gabata, ya nuna musu muhimmancin mutum ya mazakuta kansa wajen biɗan Mulkin samaniya. (Matiyu 6:33; 13:45, 46; Luka 13:23, 24) Babu shakka, wannan ya motsa zukatansu sosai domin ba da daɗewa ba sun zama masu shelar bisharar Mulkin har iyakar duniya da gaba gaɗi, littafin Ayyukan Manzanni ya ba da tabbacin wannan.—Ayyukan Manzanni 1:8; Kolosiyawa 1:23.
3. Game da zamaninmu, menene Yesu ya ce game da Mulkin?
3 Yau kuma fa? Ana yi wa miliyoyin mutane wa’azi game da albarkar da mulkin zai kawo a aljanna ta duniya. A cikin annabcinsa na “ƙarewar zamani” Yesu ainihi ya ce: “Za a kuma yi bisharan nan ta Mulkin Sama ko’ina a duniya domin shaida ga dukkan al’ummai. Sa’an nan kuma sai ƙarshen ya zo.” (Matiyu 24:3, 14; Markus 13:10) Ya kuma bayyana cewa za a yi wannan aiki mai girma ko da za a fuskanci tangarɗa da ƙalubale masu wuya, har ma da tsanantawa. Duk da haka, ya ba da wannan tabbacin: “Duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu.” (Matiyu 24:9-13) Dukan waɗannan na bukatar irin sadaukarwa da attajirin cikin almarar Yesu ya yi. Shin da mutane a yau da suke biɗan Mulkin da irin wannan bangaskiya da himma?
Farin Cikin Gano Gaskiya
4. Ta yaya gaskiya ta Mulki take shafan mutane a yau?
4 Attajirin cikin almarar Yesu ya yi farin ciki matuƙa sa’ad da ya gano “lu’ulu’u ɗaya mai tamanin gaske.” Farin cikin ya sa shi ya yi iyakar ƙoƙarinsa ya samu lu’ulu’un. (Ibraniyawa 12:1) Hakanan ma a yau, gaskiya game da Allah da Mulkinsa na jawo mutane kuma tana motsa su su aikata. Wannan ya tuna mana maganar Ɗan’uwa A. H. Macmillan, wanda ya rubuta a cikin littafin nan Faith on the March, (Bangaskiya na Ci Gaba) game da yadda ya nemi Allah da nufinsa don ’yan adam. Ya ce: “Kowace shekara mutane da yawa har ila suna samun abin da na samu. Mutane ne kamar ni da kai, domin sun fito daga dukan ƙasashe, ƙabilu, masu matsayi da kuma shekaru dabam dabam. Gaskiya ba ta wariya. Tana jawo dukan iri-irin mutane.”
5. Waɗanne sakamako masu kyau aka samu a rahoton shekarar hidima ta 2004?
5 Ana ganin gaskiyar waɗannan kalmomi kowace shekara sa’ad da bisharar Mulkin Allah ta motsa dubban mutane masu zuciyar kirki su keɓe kansu ga Jehobah kuma su yi nufinsa. An ga wannan a shekarar hidima ta 2004, daga watan Satumba 2003 zuwa Agusta 2004. A waɗannan watanni 12, mutane 262,416 ne suka nuna sun keɓe kansu ga Jehobah ta wajen baftisma a fili. An yi wannan a ƙasashe 235 da Shaidun Jehobah kowane mako suke gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na gida wajen guda 6,085,387 domin su taimaki mutane daga dukan yanayin rayuwa, al’ummai, ƙabilu, da harsuna su sami gaskiya mai ba da rai daga Kalmar Allah.—Wahayin Yahaya 7:9.
6. Me ya sa aka sami ƙari cikin shekaru da suka shige?
6 Me ya sa dukan waɗannan suka yiwu? Domin Jehobah yana jawo mutane masu zuciyar kirki wajensa. (Yahaya 6:65; Ayyukan Manzanni 13:48) Kuma ba za a manta da rashin son kai da ƙoƙari na waɗanda suka ba da kansu a biɗan Mulkin ba. Sa’ad da yake da shekara 79, Ɗan’uwa Macmillan ya rubuta: “Tun lokaci na farko da na koyi game da alkawura da aka yi wa ’yan adam masu ciwo da mutuwa, begena game da abin da saƙon Littafi Mai Tsarki ya bayyana bai yi yaushi ba. A lokacin na ƙuduri aniya na ƙara koyon abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa domin in taimaki mutane iri na da suke neman su san Allah Maɗaukaki, Jehobah, da alkawuransa masu kyau game da ’yan adam.”
7. Wane labari ya nuna farin ciki da ƙwazon waɗanda suka gano gaskiyar Littafi Mai Tsarki?
7 Ana samun irin wannan ƙwazo tsakanin bayin Jehobah a yau. Muna da misalin Daniela daga birnin Vienna na Austriya. Ta ce: “Allah aminina ne tun ina ’yar yarinya. Na so na san sunansa domin a gare ni ba a kusantar Allah. Sa’ad da Shaidun Jehobah suka zo gidanmu ina ’yar shekara 17. Suka bayyana mini dukan abin da nake so na sani game da Allah. A ƙarshe na gano gaskiya kuma tana da ban sha’awa! Na soma yi wa kowa da na sadu da shi wa’azi domin ina farin ciki matuƙa.” Ba da daɗewa ba abokan makarantarta suka soma yi mata ba’a domin ƙwazonta. Daniela ta ci gaba da cewa, “a gare ni kamar ina ganin cikar annabcin Littafi Mai Tsarki ne, domin na koya cewa Yesu ya ce za a ƙi mabiyansa kuma a tsananta musu domin sunansa. Na yi farin ciki da kuma mamaki.” Ba da daɗewa ba Daniela ta keɓe kanta ga Jehobah, ta yi baftisma kuma ta soma aikin wa’azi a ƙasan waje. Bayan aurenta, Daniela da mijinta Helmut suka soma aikin wa’azi a inda mutanen Afirka, Sin, Filifino, da kuma Indiyawa suke da zama a Vienna. Daniela da Helmut suna hidima yanzu a kudu maso yammacin Afirka.
Ba Su Yi Kasala Ba
8. Wace hanya ɗaya ce mai ban albarka mutane da yawa suka nuna suna ƙaunar Allah kuma suka nuna amincinsu ga Mulkinsa?
8 Aikin wa’azi a ƙasar waje hanya ɗaya ce da mutanen Jehobah a yau suke nuna suna ƙaunar Allah kuma suna nuna amincinsu ga Mulkinsa. Kamar attajirin cikin almarar Yesu, waɗanda suke wannan hidima suna da niyyar zuwa wurare masu nisa domin Mulkin. Hakika, waɗannan masu wa’azi a ƙasashen waje ba sa zuwa domin su ji bisharar Mulkin; suna kai bishara ce ga mutane da suke zama a wurare masu nisa na duniya, suna koya musu da kuma taimakonsu su zama almajiran Yesu Kristi. (Matiyu 28:19, 20) A ƙasashe da yawa suna jimre wa wahala mai tsanani. Amma ana samun albarka ta jimirinsu.
9, 10. Waɗanne labarai masu kyau masu hidima a wurare masu nisa suka ba da, kamar Afirka ta Tsakiya?
9 Alal misali a Afirka ta Tsakiya, mutane 16,184 ne suka halarci Bikin Tuna mutuwar Kristi a shekarar da ta shige, wannan ya fi adadin masu shelar Mulki sau bakwai a ƙasar. Tun da yake babu wutan lantarki a yawancin wurare a ƙasar, mutanen suna ayyukansu na kullum a waje a ƙarƙashin inuwar itace. Hakan ne masu hidima na ƙasashen wajen suke aikinsu—suna gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki a ƙarƙashin itace. Ban da cewa waje ya fi haske da kuma iska, akwai wani amfani. Mutanen suna son Littafi Mai Tsarki, kuma suna zancen batutuwa na addini yadda wasu al’adu suke zancen wasanni. Sau da yawa, idan masu wucewa suka ga ana nazari, sai su ma su zo a yi da su.
10 Sa’ad da wani mai hidima a wata ƙasa yake gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki a waje, wani saurayi da yake da zama a ƙetaren hanya ya zo ya ce tun da ba a gayyace shi ba, shi ma zai so mai hidimar ya zo ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Mai hidimar ya yi farin ciki, kuma saurayin yana ci gaba sosai. A wannan ƙasar, sau da yawa ’yan sanda suna tsayar da Shaidu ba don su yi musu faɗa ba amma domin su nemi Hasumiyar Tsaro da Awake! sababbin fita ko kuma su gode musu don wani talifi da suka ji daɗin karantawa.
11. Duk da gwaji, yaya masu hidima a ƙasar waje da suka jima suke ji game da hidimarsu?
11 Waɗanda suka soma hidimar wa’azi a ƙasashen waje shekaru 40 ko 50 da suka shige har ila suna hidimar cikin aminci. Wannan misalin bangaskiya ne da naciya ga dukanmu! A cikin shekara 42 da ta shige, wasu ma’aurata sun yi hidima a ƙasashe uku. Mijin ya ce: “Da matsaloli. Alal misali, mun jimre da zazzaɓin cizon sauro na shekara 35. Duk da haka, ba mu yi nadama muna wa’azi a ƙasar waje ba.” Matar ta daɗa cewa: “Da abin da ya sa za mu yi godiya. Hidimar fagen na kawo farin ciki kuma tana da sauƙi a soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da ka ga ɗaliban sun zo taro kuma suka san juna, kamar iyali ce take taruwa kowane lokaci.”
Sun “Ɗauki Dukkan Abubuwa Hasara Ne”
12. Ta yaya mutum zai nuna yana daraja Mulkin?
12 Sa’ad da attajirin ya sami lu’ulu’u mai tamanin gaske “sai ya je ya sai da dukan mallaka tasa, ya saye shi.” (Matiyu 13:46) Waɗanda suke ɗaukan Mulkin da tamani ne suke barin dukan mallakarsu. Da yake yana da gatar samun ɗaukakar Mulki tare da Kristi, manzo Bulus ya ce: “Na ɗauki dukkan abubuwa hasara ne, a kan mafificiyar darajar sanin da nake yi na Almasihu Yesu Ubangijina. Saboda shi ne na zaɓi yin hasarar dukkan abubuwa, har ma na mai da su tozari domin Almasihu yā zama nawa.”—Filibiyawa 3:8.
13. Ta yaya wani a Jamhuriyar Czech ya nuna ƙaunarsa ga Mulkin?
13 Hakanan ma, mutane da yawa a yau suna da niyyar canja tafarkin rayuwarsu domin su sami albarkar Mulkin. Alal misali, a watan Oktoba 2003, wani shugaban makaranta ɗan shekara 60 a Jamhuriyar Czech ya ga littafin nan na nazarin Littafi Mai Tsarki, Sanin da Ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada. Bayan ya karanta littafin, nan da nan ya je ya sami Shaidun Jehobah da suke yankinsu su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Ya samu ci gaba sosai, ba da daɗewa ba ya soma halartar dukan taro. Shirin da yake yi kuma fa na tsayawa takarar magajin gari kuma bayan haka ya zama ɗan majalisar dattawa? Ya zaɓi ya bi wani tafarki—ya zama mai shelar Mulki. Ya ce, “Na ba daliɓaina littattafai na Littafi Mai Tsarki da yawa.” Ya keɓe kansa ga Jehobah ta wajen wankan nitsarwa a wani taron gunduma a watan Yuli 2004.
14. (a) Menene bisharar Mulkin ta motsa mutane miliyoyi su yi? (b) Waɗanne tambayoyi masu sa tunani kowanenmu ya kamata ya yi wa kansa?
14 Ta haka mutane miliyoyi a dukan duniya sun saurari bisharar Mulkin. Sun fito daga wannan muguwar duniya, sun tuɓe tsohon halinsu, sun bar abokansu na dā, kuma suka daina biɗe-biɗensu na duniya. (Yahaya 15:19; Afisawa 4:22-24; Yakubu 4:4; 1 Yahaya 2:15-17) Me ya sa suka yi haka? Domin suna daraja albarkar Mulkin Allah fiye da kome da za su samu a wannan zamanin. Kana jin haka game da bisharar Mulkin? Shin ka motsa ka yi canje-canje da suka dace don salon rayuwarka, abubuwa da kake daraja su, da makasudinka su yi daidai da abin da Jehobah yake bukata? Yin hakan zai kawo maka albarka na dindindin a yanzu da kuma a nan gaba.
Girbi Yana Kaiwa Ƙarshensa
15. Menene aka annabta mutanen Allah za su yi a kwanaki na ƙarshe?
15 Mai Zabura ya rubuta: “A ranar da za ka yi yaƙi da maƙiyanka, jama’arka za su kawo maka gudunmawa don kansu.” Waɗanda suka ba da kansu sun haɗa da ‘samari kamar raɓa’ da kuma “mata masu yawa [da] suka baza labari.” (Zabura 68:11; 110:3) Menene sakamakon ƙwazo da sadaukar da kai na mutanen Jehobah—maza da mata, da kuma yara da tsofaffi a wannan kwanaki na ƙarshe?
16. Ka ba da misalin yadda bayin Allah suke taimakon mutane su koyi game da Mulkin.
16 Wata majagaba a Indiya ta damu da yadda za a taimaki kurame fiye da miliyan biyu da suke ƙasar su koyi game da Mulkin. (Ishaya 35:5) Ta yanke shawara ta shiga makaranta a Bangalore ta koyi bebenci. A wajen ta gaya wa kurame da yawa game da begen Mulki, kuma aka kafa rukunin nazarin Littafi Mai Tsarki. Cikin ’yan makonni mutane da yawa suka soma halartar taro a Majami’ar Mulki. Bayan haka, a wata liyafar bikin aure, majagabar ta sadu da wani saurayi kurma da ya fito daga garin Kalkutta kuma ya yi tambayoyi da yawa kuma ya nuna yana son ya ƙara sanin Jehobah. Amma da matsala. Saurayin ya kamata ya koma Kalkutta, da ke da nisan mil 1,000 don ya soma kwaleji kuma babu Shaidu da suka san bebenci a wurin. Ya yi ƙoƙari sosai ya rinjayi babansa ya ƙyale shi ya je makaranta a Bangalore domin ya ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki. Ya samu ci gaba sosai a ruhaniya kuma bayan misalin shekara guda, ya keɓe kansa ga Jehobah. Shi ma ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kurame da yawa har da abokinsa da suka yi yaranta. Ofishin reshe na Indiya yanzu yana shirya majagaba su koyi bebenci don su taimaka wa kurame.
17. Ka faɗi abin da ya fi ƙarfafa ka a rahoton hidima na shekara ta 2004 a shafofi na 23 zuwa 26.
17 A shafofi 23 zuwa 26 na wannan jaridar za ka samu rahoto na hidimar Shaidun Jehobah a dukan duniya na shekara ta 2004. Ka ɗan ba da lokaci ka bincika shi, kuma ka ga tabbacin cewa bayin Jehobah a dukan duniya sun mai da hankali sosai wajen biɗan “lu’ulu’u . . . mai tamanin gaske.”
‘Muhimmin Abu na Farko, Ka Ƙwallafa Rai ga Mulkin’
18. Wane bayani ne Yesu bai ba da ba cikin almarar attajirin nan, kuma me ya sa?
18 Idan mun sake bincika almarar Yesu game da attajirin nan, Yesu bai ce kome ba game da yadda attajirin zai biya bukatarsa bayan ya sayar da kome da yake da shi. Wasu suna iya tambaya: ‘Yaya attajirin zai samu abinci, tufafi, da wurin kwanciya yanzu da ba shi da kuɗi? Wane amfani ne wannan lu’ulu’u mai tamanin gaske zai yi masa?’ Waɗannan tambayoyin sun dace a ra’ayin ’yan adam. Amma Yesu ya aririce almajiransa: “Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa.” (Matiyu 6:31-33) Muhimmin darasi na almarar shi ne, muna bukatar mu bauta wa Allah da dukan zuciyarmu kuma mu kasance da himma don Mulkin. Shin da darassi da muka koya daga wannan?
19. Wane darassi na musamman za mu iya koya daga almarar Yesu na lu’ulu’u mai tamanin gaske?
19 Ko ba da daɗewa ba muka koyi game da bishara mai ban al’ajabi na Mulkin, ko kuwa mun daɗe muna biɗansa kuma muna gaya wa mutane game da albarkarsa, dole ne mu ci gaba da mai da hankali ga Mulkin. Muna cikin zamani mai wuya, amma muna da dalilai ƙarfafa na gaskata cewa muna biɗan abu da babu na biyunsa—kamar lu’ulu’u da attajirin nan ya samu. Abubuwa da suke faruwa a duniya da suke cika annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki sun ba da tabbacin cewa muna zama cikin “ƙarewar zamani.” (Matiyu 24:3) Kamar wannan attajirin, ka nuna himma don Mulkin Allah da dukan zuciyarka kuma ka yi farin ciki don gatar shelar bishara.—Zabura 9:1, 2.
Ka Tuna?
• Cikin shekaru da yawa me ya sa masu bauta ta gaskiya suke samun ƙaruwa?
• Wane irin hali waɗanda suke hidima a ƙasar waje suke da shi?
• Waɗanne canje-canje mutane suka yi domin bisharar Mulki?
• Wane darassi mai kyau za mu iya koya daga almarar Yesu na lu’ulu’u mai tamanin gaske?
[Hoto a shafi na 18]
“Gaskiya . . . na jawo mutane iri- iri.”—A. H. Macmillan
[Hoto a shafi na 19]
Daniela da Helmut sun yi wa’azi a yankunan wasu harsuna a Vienna
[Hotuna a shafuffuka na 20, 21]
Kamar attajirin nan, masu hidima a ƙasar waje suna samun albarka a yau
[Hoto a shafi na 21]
“Jama’arka za su kawo maka gudunmawa don kansu”