“Ya Sami Lu’ulu’u Ɗaya Mai Tamanin Gaske”
“Mulkin Sama yana shan kutse, masu kutsawa kuwa sukan ribce shi.”—Matiyu 11:12.
1, 2. (a) Wane kyakkyawan hali Yesu ya kwatanta a ɗaya cikin almararsa na Mulki? (b) Menene Yesu ya ce a cikin almararsa na lu’ulu’u mai tamanin gaske?
SHIN da akwai abin da kake ɗauka da tamani da zai sa ka sayar da dukan abin da kake da shi don ka saye shi? Ko da yake mutane suna aiki tuƙuru don su sami—kuɗi, matsayi, iko, ko kuma su yi suna, da kyar mutum ya ga wani abu da yake so sosai da zai sa ya sayar da dukan abin da ya mallaka don ya saye shi. Yesu Kristi ya yi maganar wannan kyakkyawan hali a cikin wata almara mai sa tunani game da Mulkin Allah.
2 Almara ce, ko kwatanci na lu’ulu’u mai tamanin gaske da Yesu ya gaya wa almajiransa su kaɗai. Ga abin da Yesu ya ce musu: “Mulkin Sama kamar attajiri yake, mai neman lu’ulu’u masu daraja. Da ya sami lu’ulu’u ɗaya mai tamanin gaske, sai ya je ya sai da dukan mallaka tasa, ya saye shi.” (Matiyu 13:36, 45, 46) Menene Yesu yake son masu sauraronsa su koya daga wannan kwatanci? Ta yaya za mu amfana daga maganar Yesu?
Tamanin Gaske na Lu’ulu’ai
3. Me ya sa lu’ulu’ai masu daraja suke da tamanin gaske a zamanin dā?
3 A zamanin dā, lu’ulu’u kayan ado ne mai tamani. Wata majiya ta lura cewa, Pliny Babba wani marubuci na Roma ya ce, “a cikin dukan kayayyaki masu daraja lu’ulu’u ya fi tamani.” Ba kamar zinariya ko azurfa ko wasu kayayyakin ado ba, ana samun lu’ulu’u ne daga wasu halittu masu rai. An san cewa wasu irin ƙumba suke mai da ƙananan duwatsu su zama lu’ulu’ai masu kyau ta wajen rufe su da abin da ake kira nakta. A zamanin dā, ana samun lu’ulu’u mafi daraja a cikin Jar Teku, Tekun Pashiya, da Tekun Indiya, wurare masu nisa daga ƙasar Isra’ila. Shi ya sa Yesu ya yi maganar “attajiri . . . mai neman lu’ulu’u masu daraja.” Ana bukatar aiki tuƙuru domin a sami lu’ulu’ai masu tamanin gaske.
4. Wane muhimmin darassi yake cikin almarar Yesu na attajiri?
4 Ko da yake tun da daɗewa lu’ulu’ai masu daraja suna da tsada sosai, ba farashin su ba ne yake da muhimmanci a cikin almarar Yesu. Yesu bai kamanta Mulkin Allah da lu’ulu’ai masu tamanin gaske ba, amma ya kamanta shi da “attajiri . . . mai neman lu’ulu’u masu daraja” da kuma abin da ya yi sa’ad da ya sami lu’ulu’un. Ba kamar mai kanti ba ana iya kiran mai fataucin lu’ulu’u gwani a sana’ar, domin ya san abubuwa da suke sa lu’ulu’u ya kasance mai daraja. Ya san mai kyau kuma ba za a ruɗe shi da jabu ba.
5, 6. (a) Menene abu na musamman da za a lura da shi game da attajirin almarar Yesu? (b) Almarar dukiya da aka binne ta bayyana menene game da attajirin?
5 Da wani abu mai muhimmanci da ya kamata a lura da shi game da wannan attajirin. Wani ɗan kasuwa zai bincika nawa farashin lu’ulu’un a kasuwa don ya san nawa zai saya don ya sami riba. Yana iya tunani ko irin wannan lu’ulu’u yana da kasuwa don ya sayar da sauri. Zai so ya sami riba da wuri daga jari da ya zuba, ba ya sami nasa lu’ulu’un ba. Amma ba haka attajirin almarar Yesu yake son ya yi ba. Bai damu da riba ba. Hakika, yana shirye ya sayar da “dukan mallaka tasa” mai yiwuwa dukan kayansa da dukiyarsa, domin ya samu abin da yake nema.
6 Ga yawancin attajirai wannan mutumin na almarar Yesu ya yi wauta. Ɗan kasuwa mai hikima ba zai yi tunanin sa jari a irin wannan sana’a ba. Amma mizanin attajirin almarar Yesu game da abu mai daraja ya bambanta. Ladarsa ita ce farin ciki da gamsuwa na samun abin da ya fi tamani ba riba ba. An bayyana darassin sosai cikin wani misalin kamar wannan da Yesu ya bayar. Ya ce: “Mulkin Sama kamar dukiya yake da ke binne a gona, wadda wani ya samu, ya sāke binnewa. Yana tsaka da murna tasa, sai ya je yā sai da dukan mallaka tasa, ya sayi gonar.” (Matiyu 13:44) Hakika, farin cikin ganin dukiyar da kuma samunta ya isa ya motsa mutumin ya sai da dukan abin da yake da shi. Shin da irin waɗannan mutanen a yau? Shin da dukiyar da za ta sa a yi irin wannan sadaukarwa?
Waɗanda Suka Fahimci Tamaninsa
7. Ta yaya Yesu ya nuna cewa ya daraja tamanin Mulkin?
7 Yesu yana maganar “Mulkin sama” ne a cikin almararsa. Ya fahimci cewa Mulkin yana da tamanin gaske. Labaran Linjila sun ba da shaida sosai game da wannan. Bayan da ya yi baftisma a shekara ta 29 A.Z., Yesu “ya fara wa’azi, yana cewa, ‘Ku tuba domin Mulkin Sama ya kusato.’ ” Ya yi shekara uku da rabi yana koya wa mutane game da Mulkin. Ya yi tafiya a dukan ƙasar, yana “zazzaga birni da ƙauye yana wa’azi, yana yin bisharar Mulkin Allah.”—Matiyu 4:17; Luka 8:1.
8. Menene Yesu ya yi don ya nuna abin da Mulkin zai yi a nan gaba?
8 Ya yi mu’ujizai da yawa a dukan ƙasar—ya warkar da masu ciwo, ya ciyar da mayunwata, ya tsawata wa iskar sai ta lafa ta yi tsit, har ya tashi matattu, ta haka Yesu ya nuna abin da Mulkin Allah zai yi a nan gaba. (Matiyu 14:14-21; Markus 4:37-39; Luka 7:11-17) Bayan haka, ya nuna amincinsa ga Allah da kuma Mulkin ta wurin ba da ransa, ya mutu a kan gungumen azaba domin imaninsa. Yadda wannan attajirin ya sayar da dukan abin da yake da shi don ‘lu’ulu’u mai tamanin gaske,’ haka Yesu ya rayu ya kuma mutu domin Mulkin.—Yahaya 18:37.
9. Wane kyakkyawan hali ne almajiran Yesu na farko suke da shi?
9 Yesu ya mai da hankali ga Mulkin kuma ya tara ƙaramin rukunin mabiya. Waɗannan su ma sun fahimci tamanin gaske na Mulkin. Andarawas, wanda dama almajirin Yahaya Mai Baftisma ne yana cikinsu. Da suka ji Yahaya ya faɗi cewa Yesu “Ɗan Rago na Allah” ne, Andarawas da wani cikin almajiran Yahaya, wataƙila ɗaya cikin ’ya’yan Zabadi da shi ma ana kiransa Yahaya, nan da nan suka motsa su je wajen Yesu suka zama mabiyansa. Amma ba a nan aka ƙare ba. Nan da nan, Andarawas ya je wajen ɗan’uwansa Saminu ya ce masa: “Mun sami Almasihu.” Ba da daɗewa ba, Saminu (wanda aka sani da Kefas, ko Bitrus) da kuma Filibus da abokinsa Nata’ala suka fahimci cewa Yesu ne Almasihu. Hakika, Nata’ala ya ce wa Yesu: “Kai Ɗan Allah ne! Kai Sarkin Isra’ila ne!”—Yahaya 1:35-49.
An Motsa Su Su Yi Aiki
10. Ta yaya almajiran suka aikata sa’ad da Yesu ya kira su bayan lokaci na farko da ya sadu da su?
10 Za a iya kwatanta farin cikin da Andarawas, Bitrus, Yahaya, da sauran suka yi sa’ad da suka gano Almasihu da farin cikin da attajirin ya yi sa’ad da ya samu lu’ulu’u mai tamanin gaske. Menene za su yi yanzu? Linjila ba ta gaya mana abin da suka yi ba nan da nan da sun sadu da Yesu da farko. Mai yiwuwa, yawancinsu sun koma rayuwarsu ta yau da kullum. Amma bayan kusan shekara guda, Yesu ya sake saduwa da Andarawas, Bitrus, Yahaya, da Yakubu ɗan’uwan Yahaya wurin da suke aikinsu na kamun kifi a Tekun Galili.a Da ya gan su, Yesu ya ce: “Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.” Menene suka yi? Labarin Matiyu ya ce game da Bitrus da Andarawas: “Nan da nan sai suka watsar da tarunansu, suka bi shi.” Game da Yakubu da Yahaya mun karanta cewa: “Nan take suka bar jirgin duk da ubansu, suka bi shi.” Labarin Luka ya daɗa cewa “suka bar kome duka suka bi shi.”—Matiyu 4:18-22; Luka 5:1-11.
11. Wane dalili wataƙila ya sa almajiran suka bi Yesu nan da nan da ya kira su?
11 A take ne almajiran Yesu suka tsai da shawarar binsa? Da kyar! Ko da yake sun koma sana’ar iyalansu na kama kifi bayan sun sadu da Yesu da farko, babu shakka abin da suka gani kuma suka ji a lokacin yana zukatansu. Shigewar kusan shekara guda ta ba su isashen lokaci su yi tunani a kan batun. Yanzu lokaci ya yi da za su tsai da shawara. Shin za su zama kamar attajirin nan da ya yi farin cikin samun lu’ulu’u mai tamanin gaske, “sai ya je” ya yi abin da ya kamata, ya sayi lu’ulu’un yadda Yesu ya kwatanta? E. Abin da suka gani kuma suka ji ya motsa zukatansu. Sun fahimci cewa lokacin aikatawa ya kai. Yadda labarin ya gaya mana, babu ɓata lokaci suka daina dukan abubuwa da suke yi suka zama mabiyan Yesu.
12, 13. (a) Yaya mutane da yawa da suka saurari Yesu suka aikata? (b) Menene Yesu ya ce game da almajiransa masu aminci, kuma menene kalmominsa suke nufi?
12 Waɗannan amintattun dabam suke da waɗanda aka ambata daga baya a cikin labarin Linjila! Yesu ya warkar kuma ya ciyar da mutane da yawa amma waɗannan sun ci gaba da rayuwarsu na yau da kullum. (Luka 17:17, 18; Yahaya 6:26) Wasu har sun ba da hujja sa’ad da Yesu ya gayyace su su zama mabiyansa. (Luka 9:59-62) Abin da Yesu ya ce game da almajiransa masu aminci ya bambanta, ya ce: “Tun daga zamanin Yahaya Mai baftisma har ya zuwa yanzu, Mulkin Sama yana shan kutse, masu kutsawa kuwa sukan ribce shi.”—Matiyu 11:12.
13 Menene kalmomi “kutse” da “kutsawa” suke nufi? Game da aikatau na Helenanci inda aka samo waɗannan kalmomi, littafin nan Vine’s Expository Dictionary of Old and New Testament Words ya ce: “Wannan aikatau na nuna ƙoƙartawa sosai.” Kuma manazarcin Littafi Mai Tsarki Heinrich Meyer, ya ce game da wannan ayar: “Haka aka kwatanta ɗoki, kokawa da fama da ake yi game da mulkin Almasihu da ke zuwa . . . Ana aiki tuƙuru ne (ba a jiran) mulkin.” Kamar attajirin nan, waɗannan mutane kalilan sun fahimci abin da yake da tamani na gaske, kuma suka bar dukan abin da suke da shi don Mulkin.—Matiyu 19:27, 28; Filibiyawa 3:8.
Wasu Sun Sa Hannu Wajen Nema
14. Yaya Yesu ya shirya manzanninsa don aikin wa’azin Mulki, da wane sakamako?
14 Da Yesu yake hidimarsa, ya koyar kuma ya taimaki wasu su biɗi Mulkin. Ya fara zaɓan mutane 12 cikin almajiransa su zama manzanni. Yesu ya yi wa waɗannan bayani dalla-dalla game da yadda za su yi hidimarsu kuma ya yi musu kashedi game da ƙalubale da wahala da za su sha. (Matiyu 10:1-42; Luka 6:12-16) Sun yi wa’azi shekara biyu tare da Yesu a cikin dukan ƙasar ko ma fiye da haka, kuma sun more dangantaka ta kusa da shi. Sun saurari koyarwarsa, sun ga ayyukansa masu ban al’ajabi da kuma misalinsa. (Matiyu 13:16, 17) Waɗannan abubuwa sun motsa manzannin sosai, kamar attajirin nan sun kasance da himma kuma sun biɗi Mulkin da zuciya ɗaya.
15. Menene Yesu ya ce ainihi abin da zai sa mabiyansa su yi farin ciki?
15 Ban da manzannin 12, Yesu “ya zaɓi waɗansu mutum saba’in, ya aike su biyu biyu, su riga shi gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da shi kansa za shi.” Ya kuma gaya musu za su fuskanci gwaji da wahala nan gaba kuma ya umarce su su gaya wa mutane: “Mulkin Allah ya kusato ku.” (Luka 10:1-12) Sa’ad da mutane saba’in suka dawo, sun yi farin ciki sosai kuma suka ba Yesu wannan rahoto: “Ya Ubangiji, har aljannu ma suna mana biyayya albarkacin sunanka!” Wataƙila sun yi mamaki da Yesu ya gaya musu za su fi farin ciki nan gaba domin himmarsu ga Mulkin. Ya gaya musu: “Kada ku yi farin cikin aljannu na yi muku biyayya, sai dai ku yi farin cikin an rubuta sunayenku a Sama.”—Luka 10:17, 20.
16, 17. (a) Menene Yesu ya gaya wa manzaninsa masu aminci da yake tare da su a dare na ƙarshe? (b) Ta yaya kalmomin Yesu suka sa manzaninsa farin ciki kuma suka sa su kasance da tabbaci?
16 A dare na ƙarshe na 14 ga Nisan 33 A.Z., da Yesu yake tare da manzanninsa, ya kafa abin da ake kira Jibin Maraice na Ubangiji kuma ya umarce su su riƙa yin bikin. A wannan maraicen, Yesu ya gaya wa manzanninsa 11 da suka rage: “Ku ne kuka tsaya gare ni a gwajegwajen da na sha. Kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka ni ma nake ba ku iko, ku ci ku sha tare da ni a mulkina, ku kuma zauna a kursiyai, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra’ila.”—Luka 22:19, 20, 28-30.
17 Sa’ad da manzannin suka ji kalmomin Yesu sun yi farin ciki sosai kuma sun sami gamsuwa! An ba su ɗaukaka da gata da ta fi girma. (Matiyu 7:13, 14; 1 Bitrus 2:9) Kamar wannan attajirin, sun bar dukan abin da suke yi don su bi Yesu a biɗan Mulkin. Yanzu an tabbatar musu cewa sadaukarwa da suka yi ba a banza ba ne.
18. Ban da manzanni 11 su waye ne za su amfana daga Mulkin?
18 Ban da manzanni da suke tare da Yesu a wannan daren, wasu ma za su amfana daga Mulkin. Nufin Jehobah ne mutane 144,000 su kasance cikin alkawarin Mulkin kuma su zama abokan sarauta na Yesu Kristi a Mulki mai ɗaukaka na samaniya. Ƙari ga haka, manzo Yahaya a cikin wahayi ya “ga wani ƙasaitaccen taro, wanda ya fi gaban ƙirge, . . . suna tsaitsaye a gaban kursiyin, a gaban Ɗan Ragon kuma . . . suna cewa, ‘Yin ceto ya tabbata ga Allahnmu wanda ke zaune a kan kursiyin, da kuma Ɗan Rago!’ ” Waɗannan za su zama talakawan Mulkin a nan duniya.b—Wahayin Yahaya 7:9, 10; 14:1, 4.
19, 20. (a) Wane zarafi mutanen dukan al’ummai suke da shi? (b) Wace tambaya ce za a tattauna a talifi na gaba?
19 Kafin ya haura zuwa sama Yesu ya umurci mabiyansa masu aminci: “Ku je ku almajirtar da dukkan al’ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki, kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har matuƙar zamani.” (Matiyu 28:19, 20) Ta haka ne mutanen dukan al’ummai za su zama almajiran Yesu Kristi. Waɗannan ma za su sa zuciyarsu ga Mulki—ko ladarsu a sama ko kuma a nan duniya—yadda attajiri ya sa zuciyarsa ga lu’ulu’u nan mai tamani.
20 Kalmomin Yesu sun nuna za a yi aikin almajirantarwa har “matuƙar zamani.” A zamaninmu, shin akwai mutanen da suke son su ba da dukan abin da suke da shi don biɗan Mulkin Allah, kamar attajirin nan? Za a tattauna wannan tambaya a talifi na gaba.
[Hasiya]
a Wataƙila, Yahaya ɗan Zabadi ya bi Yesu ya ga wasu abubuwa da ya yi bayan da suka sadu da farko, shi ya sa Yahaya ya rubuta su a nasa labarin Linjila. (Yahaya, surori 2-5) Duk da haka, ya koma sana’ar iyalinsu na kama kifi na ɗan lokaci kafin Yesu ya sake kiransa.
b Don ƙarin bayani ka dubi babi na 10 na littafin nan Sanin Da Ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
Za Ka Iya Ba da Bayani?
• Menene darassi na musamman na almarar attajiri?
• Yaya Yesu ya nuna yana ɗaukan Mulkin da tamanin gaske?
• Me ya sa Andarawas, Bitrus, Yahaya, da wasu suka bi Yesu nan da nan da ya kira su?
• Wane zarafi na musamman mutanen dukan al’ummai suke da shi?
[Hoto a shafi na 14]
‘Sun bar kome suka bi Yesu’
[Hoto a shafi na 16]
Kafin ya haura sama, Yesu ya umurci mabiyansa su almajirantar