Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 12/15 pp. 6-10
  • ‘Ka Saurara Kuma Ka Fahimta’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ka Saurara Kuma Ka Fahimta’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YADDA ZA KA AMFANA DAGA KOYARWAR YESU
  • ƘWAYAR MUSTARD
  • YISTI
  • MAI FATAUCI DA ƁOYAYYUN DUKIYA
  • Ba Ka San Inda Zai Yi Albarka Ba!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ka “Fahimci” Batun Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Kwatanci Game da Mulki da Kuma Ma’anarsu
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • “Ya Sami Lu’ulu’u Ɗaya Mai Tamanin Gaske”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 12/15 pp. 6-10

‘Ka Saurara Kuma Ka Fahimta’

“Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimta.” —MAR. 7:14, Littafi Mai Tsarki.

WANE DARASI NE KA KOYA DAGA KWATANCIN YESU GAME DA

  • ƙwayar mustard?

  • yisti?

  • mai fatauci da kuma dukiyar da aka ɓoye?

1, 2. Me ya sa mutane da yawa da suka saurari Yesu sun kasa fahimtarsa?

MUTUM zai iya jin muryar wani da ke masa magana har ma ya gane wanda yake maganar. Amma hakan ba zai amfane shi ba idan bai fahimci abin da ake maganarsa ba. (1 Kor. 14:9) Hakazalika, dubban mutane sun ji koyarwar Yesu. Ƙari ga haka, ya yi magana a yarensu. Amma, ba dukansu ba ne suka fahimci abubuwan da ya faɗa. Hakan ne ya sa Yesu ya gaya wa masu sauraronsa cewa: “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimta.”—Mar. 7:14, LMT.

2 Me ya sa mutane da yawa ba su fahimci abin da Yesu ya faɗa ba? Wasu suna da ra’ayoyi da kuma tunanin da bai dace ba. Game da irin waɗannan mutanen, Yesu ya ce: “Sarai ne kuna ƙin dokar Allah, domin ku kiyaye takalidinku.” (Mar. 7:9) Waɗannan mutanen ba su mai da hankali don su fahimci Yesu ba. Ba sa son su canja halayensu da kuma ra’ayoyinsu. Kunnuwansu a buɗe suke, amma ba su fahimci abin da Yesu yake koyarwa ba! (Karanta Matta 13:13-15.) Shin, ta yaya za mu natsu, mu fahimci koyarwar Yesu kuma mu amfana?

YADDA ZA KA AMFANA DAGA KOYARWAR YESU

3. Me ya sa almajiran Yesu suka fahimci koyarwarsa?

3 Ya kamata mu bi misalin almajiran Yesu masu tawali’u. Yesu ya ce game da su: “Idanunku masu-albarka ne, gama suna gani; kunnuwanku kuma, gama suna ji.” (Mat. 13:16) Me ya sa suka fahimci koyarwar Yesu amma wasu kuma ba su fahimta ba? Na ɗaya, sun yi tambaya da kuma bincike don su gane ainihin abin da Yesu yake nufi. (Mat. 13:36; Mar. 7:17) Na biyu, sun nemi ƙarin bayani a kan abin da suka sani game da Allah da kuma nufinsa. (Karanta Matta 13:11, 12.) Na uku, sun yi amfani da abubuwan da suka koya don su taimaka wa kansu da kuma sun yi ƙoƙarin taimaka wa wasu.—Mat. 13:51, 52.

4. Waɗanne matakai uku ne muke bukata mu ɗauka idan muna son mu fahimci kwatance-kwatancen Yesu?

4 Idan muna son mu fahimci kwatance-kwatancen da Yesu ya yi amfani da su a koyarwarsa, ya kamata mu yi koyi da almajiransa. Muna bukata mu ɗauki matakai uku. Na farko, ya kamata mu keɓe lokaci don yin nazari da kuma bimbini a kan koyarwar Yesu kuma mu yi bincike da tambayoyin da suka dace. Hakan zai sa mu sami ilimi. (Mis. 2:4, 5) Na biyu, muna bukata mu ga alaƙar abin da muka koya da abin da muka sani a dā da kuma yadda hakan zai amfane mu. Hakan zai sa mu fahimci batun. (Mis. 2:2, 3) A ƙarshe, ya kamata mu yi amfani da abin da muka koya a rayuwarmu. Yin hakan hikima ce a gare mu.—Mis. 2:6, 7.

5. Ka nuna yadda ilimi da fahimi da kuma hikima suka bambanta da juna.

5 Ta yaya sani, wato ilimi da fahimi da kuma hikima suka bambanta? Alal misali: A ce kana so ka tsallake hanya sai ga bas yana tahowa. Da farko, za ka gane cewa bas ne ke zuwa, kana da masaniya ke nan, wannan shi ne ilimi. Ƙari ga haka, ka san cewa idan ka ci gaba da tsallakewa, bas ɗin zai kaɗe ka, wannan shi ne fahimi! Saboda haka, sai ka bar hanyar don bas ɗin ya wuce, ka nuna hikima ke nan! Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce mu “kiyaye sahihiyar hikima.” Hakan zai ceci ranmu!—Mis. 3:21, 22; 1 Tim. 4:16.

6. Waɗanne tambayoyi huɗu ne za mu tattauna yayin da muke bincika kwatance-kwatance bakwai na Yesu? (Ka duba akwatin da ke shafi na 8.)

6 Za mu tattauna kwatance-kwatance bakwai da Yesu ya yi a wannan talifin da kuma na gaba. Yayin da muke hakan, za mu tattauna waɗannan tambayoyin: Mene ne ma’anar kwatancin? (Hakan zai sa mu sami ilimi.) Me ya sa Yesu ya yi wannan kwatancin? (Hakan zai sa mu sami fahimi.) Ta yaya za mu yi amfani da darasin don mu taimaka wa kanmu da kuma wasu? (Hikima ke nan.) A ƙarshe, mene ne kwatancin ya koya mana game da Jehobah da kuma Yesu?

ƘWAYAR MUSTARD

7. Mene ne ma’anar kwatancin ƙwayar mustard?

7 Karanta Matta 13:31, 32. Mene ne ma’anar kwatancin Yesu na ƙwayar mustard? Ƙwayar mustard ɗin tana wakiltar wa’azin Mulkin da kuma ikilisiyar Kirista, wato sakamakon da aka samu saboda wa’azin Mulki. Kamar ƙwayar mustard da “ta fi dukan iri ƙanƙanta,” ikilisiyar Kirista ƙarama ce da aka kafa ta a shekara ta 33 a zamaninmu. Amma cikin ’yan shekaru, ikilisiyar ta ƙaru sosai kuma ta bunƙasa fiye da yadda aka zata. (Kol. 1:23) Wannan ƙaruwar tana da amfani don Yesu ya ce “tsuntsayen sama su kan zo su sauka cikin ressanta.” Waɗannan tsuntsayen suna nufin mutane masu zuciyar kirki da suke neman ƙulla dangantaka da Allah da kuma mafaka a cikin ikilisiyar Kirista.—Gwada Ezekiel 17:23.

8. Me ya sa Yesu ya yi kwatancin ƙwayar mustard?

8 Me ya sa Yesu ya yi wannan kwatancin? Yesu ya yi kwatanci da ƙwayar mustard da yake saurin girma don ya nuna yadda Mulkin Allah yake bunƙasa da kāre da kuma shawo kan dukan matsaloli. Tun shekara ta 1914, ƙungiyar Allah a duniya ta sami ƙaruwa sosai! (Isha. 60:22) An kāre waɗanda suke tarayya da ƙungiyar Jehobah daga abin da zai ɓata dangantakarsu da shi. (Mis. 2:7; Isha. 32:1, 2) Ƙari ga haka, babu abin da zai hana wa’azin Mulki da ake yi a faɗin duniya, duk da hamayya da ake fuskanta.—Isha. 54:17.

9. (a) Wane darasi ne muka koya daga kwatancin ƙwayar mustard? (b) Mene ne wannan ya koya mana game da Jehobah da kuma Yesu?

9 Wane darasi ne za mu iya koya daga kwatancin ƙwayar mustard? Wataƙila muna zama a wurin da Shaidu ba su da yawa ko kuma ba ma ganin sakamakon wa’azi da muke yi nan da nan. Duk da haka, idan muka tuna cewa Mulkin zai shawo kan dukan matsaloli, hakan zai sa mu jimre. Alal misali, sa’ad da Ɗan’uwa Edwin Skinner ya je ƙasar Indiya a shekara ta 1926, Shaidu kaɗan ne kawai ke ƙasar. Da farko, kamar aikin ba ya samun ci gaba. Amma ya ci gaba da wa’azi kuma ya ga yadda wa’azin Mulki ya sa aka sha kan matsaloli da yawa. A yau, akwai Shaidu sama da 37,000 a ƙasar Indiya kuma mutane fiye da 108,000 ne suka halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu a shekarar da ta shige. Ka kuma yi la’akari da yadda wa’azin Mulki ya sami ci gaba sosai a wata ƙasa. A shekarar da Ɗan’uwa Skinner ya je ƙasar Indiya ne aka soma wa’azi a ƙasar Zambiya. A yau, masu shela fiye da 170,000 ne suke wa’azi a ƙasar, kuma mutane 763,915 ne suka halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu a shekara ta 2013. Hakan ya nuna cewa mutum ɗaya cikin mutane 18 da ke ƙasar Zambiya ne ya halarci taron. Wannan ba ƙaramin ci gaba ba!

YISTI

10. Mene ne ma’anar kwatancin yisti?

10 Karanta Matta 13:33. Mene ne ma’anar kwatancin yisti? Wannan kwatancin yana nuni ga wa’azin Mulkin da yadda yake canja rayuwar mutane. ‘Garin’ yana wakiltar dukan ƙasashe kuma yadda yistin yake sa garin ya kumbura yana nuna yadda wa’azin Mulkin da ake yi yake yaɗuwa. Ko da yake ana ganin girman ƙwayar mustard, da farko ba a ganin yadda yistin yake sa garin ya kumbura. Sai bayan wani lokaci ne za a gane cewa garin ya kumbura.

11. Me ya sa Yesu ya yi kwatancin yisti?

11 Me ya sa Yesu ya yi wannan kwatancin? Yesu ya nuna cewa wa’azin Mulki yana da tasiri sosai kuma yana canja halaye. Ana yin wa’azin Mulki har “iyakan duniya.” (A. M. 1:8) A wasu lokatai ba a yawan ganin yadda wa’azin yake sa mutane su canja halayensu. Ana samun canji ba ga yawan mutane kawai ba, amma wa’azin Mulkin yana shafan waɗanda suka amince da shi har ya sa su canja halayensu.—Rom. 12:2; Afis. 4:22, 23.

12, 13. Ka ba da misalai da suka nuna yadda aka sami ƙaruwa a yin wa’azi kamar yadda aka nuna a kwatancin yisti.

12 Sau da yawa ba a ganin sakamakon da ake samu a wa’azi sai bayan wasu shekaru. Alal misali, Franz da Margit da suke hidima yanzu a wani ofishin Shaidun Jehobah, sun yi hidima a ofishin da ke Brazil a shekara ta 1982. Sa’ad da suke wa’azi a wani ƙaramin gari a ƙasar. Sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa, ɗaya daga cikin waɗanda suke nazari da su tana da yara guda huɗu. A lokacin, ɗanta na fari yana da shekara 12, shi mai jin kunya ne sosai kuma yakan ɓuya kafin su soma nazarin. Ma’auratan ba su ci gaba da nazarin ba don daga baya, sun ƙaura daga yankin. Amma, bayan shekaru 25, sun kai ziyara a wannan garin. Mene ne suka tarar? Sun ga cewa akwai ikilisiya da ke da masu shela 69, kuma 13 cikinsu majagaba na kullum ne, dukansu suna halartar taro a sabuwar Majami’ar Mulki. Wannan yaron mai jin kunya kuma fa? Yanzu shi ne mai tsara ayyukan rukunin dattawa a ikilisiyarsu! Kamar yisti na kwatancin Yesu, wa’azin Mulki ya yaɗu sosai kuma ya sa mutane da yawa sun canja halayensu. Hakan ya sa ma’auratan farin ciki sosai!

13 Wa’azin Mulkin yana tasiri a yadda yake sa mutane su canja halayensu har ma a ƙasashen da aka hana ’yan’uwa yin wa’azi. Yana da wuya a san yawan yadda aka yaɗa saƙon a irin waɗannan ƙasashe, kuma sau da yawa muna mamaki a sakamakon da muke samu. Alal misali, an soma wa’azi a ƙasar Cuba a shekara ta 1910, kuma Ɗan’uwa Russell ya ziyarci Cuba a shekara ta 1913. Amma da farko, ba a sami ci gaba da sauri ba. Yanzu ’yan’uwa nawa muke da su a ƙasar Cuba? Akwai masu shela sama da 96,000 da suke wa’azi, kuma mutane 229,726 ko kuma mutum ɗaya cikin mutane 48 da ke ƙasar ne ya halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu a shekara ta 2013. Ko a ƙasashen da ba a hana aikinmu ba, an yaɗa saƙon Mulki zuwa wuraren da Shaidu da ke yankin suke ganin ba za a iya yin wa’azi a wurin ba.—M. Wa. 8:7; 11:5.

14, 15. (a) Ta yaya za mu amfana daga darasin da muka koya daga kwatancin yisti? (b) Mene ne wannan ya koya mana game da Jehobah da kuma Yesu?

14 Ta yaya za mu amfana daga abin da Yesu ya koya mana a kwatancin yisti? Yin bimbini a kan ma’anar kwatancin da Yesu ya yi zai taimaka mana mu daina damuwa a kan yadda za a yi wa miliyoyin mutanen da ba su ji saƙon Mulkin ba wa’azi. Jehobah ya san yadda za a cim ma hakan. Mu kuma fa, mene ne aikinmu? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Da safe sai ka shuka irinka, da yamma kuma kada ka ja hannunka; gama ba ka san wanda za ya yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuwa duk za su yi kyau baki ɗaya.” (M. Wa. 11:6) Hakika, bai kamata mu manta da yin addu’a don a sami nasara a wa’azi ba, musamman a ƙasashen da aka hana aikinmu.—Afis. 6:18-20.

15 Ƙari ga haka, bai kamata mu yi sanyin gwiwa ba idan da farko ba mu ga sakamakon aikin da muke yi ba. Bai kamata mu rena “ranar ƙananan abu” ba. (Zak. 4:10) Daga baya, za a iya samun sakamakon sosai fiye da yadda muke tsammani!—Zab. 40:5; Zak. 4:7.

MAI FATAUCI DA ƁOYAYYUN DUKIYA

16. Mene ne ma’anar kwatancin mai fatauci da kuma na dukiyar da aka ɓoye?

16 Karanta Matta 13:44-46. Mene ne ma’anar kwatancin mai fatauci da kuma ɓoyayyun dukiya? A zamanin Yesu, wasu masu fatauci sukan yi tafiya zuwa Tekun Indiya don su sayo lu’ulu’ai masu tamani sosai. Mai fatauci a wannan kwatancin yana wakiltar mutanen kirki da suke ƙwazo sosai don su koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Lu’ulu’u “ɗaya mai-tamani dayawa” yana wakiltar koyarwa game da Mulkin. Sa’ad da mai fataucin ya ga amfanin wannan lu’ulu’u, sai ya sayar da dukan abubuwan da yake da su nan da nan don ya sayi lu’ulu’un. Yesu kuma ya ba da kwatancin wani mutum da yake aiki a gona kuma ya tarar da dukiya da aka “ɓoye.” Ba kamar mai fatauci ba, wannan mutum ba ya neman dukiya. Amma, kamar mai fataucin, yana shirye ya sayar da “dukan” mallakarsa don ya sayi dukiyar.

17. Me ya sa Yesu ya ba da kwatancin mai fatauci da kuma na dukiyar da aka ɓoye?

17 Me ya sa Yesu ya ba da waɗannan kwatance-kwatance biyu? Yana son ya nuna cewa ana sanin gaskiyar Littafi Mai Tsarki a hanyoyi da yawa. Wasu mutane suna neman wannan gaskiyar kuma sun yi aiki tuƙuru don su samu. Wasu ba su yi ƙwazo a neman gaskiyar ba amma sun same ta, wataƙila don an zo har gida an yi musu wa’azi. Ko ta yaya suka sami gaskiyar, kowannensu ya fahimci cewa gaskiyar tana da tamani kuma ya yi sadaukarwa don ya bauta wa Allah.

18. (a) Ta yaya za mu amfana daga waɗannan kwatance-kwatance biyu? (b) Mene ne wannan ya koya mana game da Jehobah da kuma Yesu?

18 Ta yaya za mu amfana daga waɗannan kwatance-kwatance biyu? (Mat. 6:19-21) Ka tambayi kanka: ‘Ina da halin da waɗannan maza suke da shi kuwa? Ina ɗaukan koyarwar Littafi Mai Tsarki a matsayin dukiya kamar yadda suka yi? Ina a shirye na yi sadaukarwa don na same ta ko kuma ina barin wasu abubuwa kamar biyan bukatun rayuwa ta yau da kullum su raba hankalina?’ (Mat. 6:22-24, 33; Luk. 5:27, 28; Filib. 3:8) Idan muna son gaskiyar da muka koya daga Littafi Mai Tsarki sosai, za mu ɗauka da muhimmanci sosai a rayuwarmu.

19. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

19 Bari mu nuna cewa mun saurara kuma mun fahimci ma’anar waɗannan kwatance-kwatance game da Mulki. Ya kamata mu san ma’anarsu da kuma yi amfani da darussan a rayuwarmu. A talifi na gaba, za mu ƙara tattauna kwatance-kwatance uku da kuma darussan da za mu iya koya.

Sa’ad da kake karanta kwatance-kwatancen Yesu, ka yi waɗannan tambayoyin:

  • Mene ne ma’anar wannan kwatancin?

  • Me ya sa Yesu ya yi wannan kwatancin?

  • Ta yaya zan yi amfani da darasin da na koya daga wannan kwatancin?

  • Mene ne wannan kwatancin ya koya mini game da Jehobah da kuma Yesu?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba