Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 12/15 pp. 11-15
  • Ka “Fahimci” Batun Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka “Fahimci” Batun Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MAI WATSA IRI DA YA YI BARCI
  • KWATANCIN TARU
  • ƊA MUBAZZARI
  • Ba Ka San Inda Zai Yi Albarka Ba!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • ‘Ka Saurara Kuma Ka Fahimta’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • ‘Allah Ne Mai Ba Da Amfani’!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Jehobah Yana Kaunar Wadanda Suke Yin Wa’azi da Jimiri
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 12/15 pp. 11-15

Ka “Fahimci” Batun Kuwa?

“Ya buɗe hankalinsu, domin su fahimci littattafai.”—LUK. 24:45.

WANE DARASI NE KA KOYA DAGA KWATANCIN

  • mai watsa iri da ya yi barci?

  • taru?

  • ɗa mubazzari?

1, 2. Ta yaya Yesu ya ƙarfafa almajiransa a ranar da ya tashi daga matattu?

A RANAR da Yesu ya tashi daga matattu, almajiransa biyu suna tafiya zuwa wani ƙauye mai nisan kilomita 11 daga Urushalima. Ba su san cewa an ta da Yesu daga matattu ba, suna baƙin ciki sosai domin abubuwa da suka faru a kwanaki da suka shige. Farat ɗaya, sai Yesu ya bayyana a gare su kuma ya yi tafiya tare da su don ya ƙarfafa su. Ta yaya? “Ya soma kuwa tun daga Musa da dukan annabawa, cikin dukan littattafai yana fassara musu al’amura na bisa kansa.” (Luk. 24:13-15, 27) Da suka ji hakan, sai zuciyarsu ta fara ƙuna domin “yana bayyana” musu Nassosi.—Luk. 24:32.

2 A yammar ranar, waɗannan almajirai biyu suka koma Urushalima. Da suka sami manzannin, sai suka gaya musu abin da ya faru. Yayin da suke kan magana, sai Yesu ya bayyana a gare su. Amma, manzannin sun tsorata kuma suka soma shakka. Ta yaya Yesu ya ƙarfafa su? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya buɗe hankalinsu, domin su fahimci littattafai.”—Luk. 24:45.

3. Waɗanne ƙalubale ne za mu iya fuskanta, kuma mene ne zai iya taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace game da hidimarmu?

3 Kamar waɗannan almajirai, mukan yi baƙin ciki sosai a wani lokaci. Wataƙila muna wa’azi da ƙwazo amma da yake ba ma ganin sakamakon, sai mu soma sanyin gwiwa. (1 Kor. 15:58) Ko kuma waɗanda muke nazari da su ba sa ci gaba sosai. Wasu da muke taimaka wa za su iya daina bauta wa Jehobah. Mene ne za mu iya yi don mu kasance da ra’ayin da ya dace game da hidimarmu? Fahimtar kwatance-kwatancen Yesu da ke Nassosi zai iya taimaka mana. Bari mu tattauna uku daga cikin waɗannan kwatance-kwatancen kuma mu ga darussa da za mu iya koya.

MAI WATSA IRI DA YA YI BARCI

4. Mene ne ma’anar kwatancin Yesu game da mai watsa iri da ya yi barci?

4 Karanta Markus 4:26-29. Mene ne ma’anar kwatancin Yesu game da mai watsa iri da ya yi barci? Mutum mai watsa iri a cikin kwatancin yana wakiltar masu wa’azin bisharar Mulki. Wannan iri shi ne wa’azin da ake wa mutanen kirki. Kamar sauran mutane, mai watsa iri yana “kwana ya tashi.” Kafin irin ya tsira kuma ya yi girma zai ɗauki lokaci, wato daga lokacin da aka shuka irin zuwa lokacin girbi. A wannan lokacin irin zai “tsira ya yi girma.” Irin yana girma da ‘kansa,’ a hankali kuma a yanayi dabam-dabam. Hakazalika, mutum yana kusantar Jehobah a hankali da kuma a yanayi dabam-dabam. Sa’ad da mutum ya sami ci gaba har hakan ya motsa shi ya bauta wa Allah, sai ya ba da ’ya’ya ta ba da kansa ga Jehobah kuma ya yi baftisma.

5. Me ya sa Yesu ya yi kwatancin mai watsa iri da ya yi barci?

5 Me ya sa Yesu ya yi wannan kwatanci? Yesu ya taimaka mana mu fahimci cewa Jehobah ne yake sa gaskiyar ta yi tasiri a zukatan mutanen kirki. (A. M. 13:48; 1 Kor. 3:7) Muna shuki da kuma ban ruwa, amma ba mu da iko mu sa shi girma. Ba za mu iya sa irin ya yi girma tilas ko kuma mu hanzarta girmar ba. Kamar mutumin da ke cikin kwatancin, ba mu san yadda abin da muka shuka yake girma ba. Irin yana girma ba tare da saninmu ba, wato sa’ad da muke harkokinmu na yau da kullum. Amma, da shigewar lokaci irin zai ba da ’ya’ya. Sai mutumin ya zama mai shela kuma yana wa’azi tare da mu. Muna samun ƙarfafa yayin da ya yi hakan.—Yoh. 4:36-38.

6. Me ya kamata mu yi la’akari da shi game da ci gabar wanda muke nazari da shi?

6 Wane darasi ne za mu koya daga wannan kwatancin? Na farko, ya kamata mu san cewa ci gabar wanda muke nazarin Littafi Mai Tsarki da shi ba a hannunmu yake ba. Kasancewa da tawali’u zai sa mu guji matsa ko kuma tilasta wa wanda muke nazari da shi ya yi baftisma. Ko da yake za mu yi iya ƙoƙarinmu mu taimaka da kuma tallafa masa, bai kamata mu matsa shi ya yi baftisma ba. Maimakon haka, za mu fahimci cewa shi da kansa ne zai tsai da shawara ko zai ba da kansa ga Allah a cikin addu’a. Hakan zai nuna cewa yana ƙaunar Jehobah daga zuciyarsa. Idan mutum ya yi hakan ne kawai Jehobah zai amince da shi.—Zab. 51:12; 54:6; 110:3.

7, 8. (a) Waɗanne darussa kuma muka koya daga kwatancin Yesu na mai watsa iri da ya yi barci? Ka ba da misali. (b) Mene ne wannan kwatancin ya koya mana game da Jehobah da kuma Yesu?

7 Na biyu, fahimtar darasin wannan kwatancin zai taimaka mana kada mu yi sanyin gwiwa idan da farko ba ma ganin sakamakon aikinmu. Muna bukatar mu zama masu haƙuri. (Yaƙ. 5:7, 8) Ko da irin bai ba da ’ya’ya ba duk da ƙoƙarin da muka yi don mu taimaka wa wanda muke nazari da shi, hakan ba ya nufin cewa ba mu yi iya ƙoƙarinmu ba. Jehobah yana barin irin da muka shuka wato, wa’azin da muka yi ya yi tasiri a zukatan mutanen da suke da tawali’u ne kawai. (Mat. 13:23) Saboda haka, bai kamata mu ɗauka cewa sakamako mai kyau a wa’azi ne yake nuna cewa muna yin iya ƙoƙarinmu ba. Jehobah ba ya gwada albarkar da muke samu a wa’azi da yadda mutane suke jin saƙon bishara. Maimakon haka, yana ganin ƙoƙarinmu ko da mun sami sakamako mai kyau ko a’a.—Karanta Luka 10:17-20; 1 Korintiyawa 3:8.

8 Na uku, ba za mu iya sanin dukan canje-canje da mutum yake yi ba. Alal misali, wasu ma’aurata da wani ɗan’uwa mai wa’azi a ƙasar waje yake nazari da su sun gaya masa cewa suna so su zama masu shela. Sai ya gaya musu cewa kafin su cancanta, wajibi ne su daina shan sigari. Ya yi mamaki sosai da suka gaya masa cewa sun daina shan sigari watanni da suka shige. Me ya sa suka daina? Sun fahimta cewa Jehobah zai iya ganin suna shan taba a ɓoye kuma ya tsani munafurci. Don haka ne suka tsai da shawara ko su sha taba a gaban ɗan’uwan da ke nazari da su ko kuma su daina sha gaba ɗaya. Da yake suna ƙaunar Jehobah, sun ɗauki wannan matakin da ya dace. Sun ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah ko da yake mai wa’azi a ƙasar wajen bai san da haka ba.

KWATANCIN TARU

9. Mene ne ma’anar kwatancin taru?

9 Karanta Matta 13:47-50. Mene ne ma’anar kwatancin Yesu game da taru? Yesu ya kwatanta wa’azin Mulkin da ake yi wa dukan mutane da jefa babban taru a cikin teku. Kamar yadda wannan taru yakan kama “kowane irin kifi,” hakazalika, wa’azin da muke yi yakan jawo mutane da yawa kuma iri-iri. (Isha. 60:5) Yawan mutanen da suke halartan manyan taronmu da kuma taron Tuna da mutuwar Yesu a kowace shekara yana tabbatar da hakan. Wasu cikin waɗannan kifaye na alama “masu-kyau” ne kuma ana tattara su zuwa cikin ikilisiyar Kirista. Wasu kuma “munana” ne; ba dukan waɗanda aka tara ba ne Jehobah ya amince da su.

10. Me ya sa Yesu ya yi kwatancin taru?

10 Me ya sa Yesu ya yi wannan kwatancin? Ware kifaye na alama ba ya nufin hukunci na ƙarshe da za a yi a lokacin ƙunci mai girma. Maimakon haka, yana nufin abin da zai faru a kwanaki na ƙarshe. Yesu ya nuna cewa ba dukan waɗanda suka yi marmarin koyon gaskiya ba ne za su bauta wa Jehobah. Mutane da yawa suna halartar taronmu. Wasu kuma suna so a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su amma ba sa so su ɗauki matakin bauta wa Jehobah. (1 Sar. 18:21) Har ila wasu sun daina halartan taro. An yi rainon wasu matasa a cikin ƙungiyar Jehobah, amma ba sa son bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Ko da yaya yanayin yake, Yesu ya nanata cewa kowa zai tsai da shawara da kansa. Ana ɗaukan waɗanda suka yi hakan a matsayin ‘muradi’ ko abubuwa masu tamani daga “dukan dangogi.”—Hag. 2:7.

11, 12. (a) Ta yaya za mu amfana daga kwatancin taru? (b) Mene ne wannan ya koya mana game da Jehobah da kuma Yesu?

11 Ta yaya za mu amfana daga kwatancin taru? Fahimtar wannan kwatancin zai taimaka mana kada mu riƙa damuwa ainun idan waɗanda muke nazarin Littafi Mai Tsarki da su ko kuma yaranmu ba su tsai da shawarar bauta wa Jehobah ba. Hakan zai iya faruwa ko da mun yi iya ƙoƙarinmu mu koyar da su. Idan mutum ya amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi ko kuma iyayensa da Shaidun Jehobah ne suka yi rainon sa, hakan ba ya nufin cewa mutumin zai ƙulla dangantaka na kud da kud da Jehobah. Za a ware waɗanda suka ƙi su goyi bayan sarautar Jehobah daga mutanen Allah.

Wasu da suka so saƙon Littafin Mai Tsarki, za su bauta wa Jehobah (Duba sakin layi na 9-12)

12 Wannan yana nufin cewa ba za a ƙyale waɗanda suka bar ƙungiyar Jehobah su dawo ba ne? Ko kuma idan wani ya ƙi ya keɓe kansa ga Jehobah fa, hakan yana nufin cewa shi ‘mummunar’ kifi na alama ne? A’a. Har ila suna da zarafin tsai da shawarar bauta wa Jehobah kafin ƙunci mai girma. Kamar Jehobah yana gaya musu cewa: “Ku juyo wurina, ni ma zan koma wurinku.” (Mal. 3:7) An nanata wannan batun a wani kwatancin da Yesu ya yi na ɗa mubazzari.—Karanta Luka 15:11-32.

ƊA MUBAZZARI

13. Mene ne ma’anar kwatancin ɗa mubazzari?

13 Mene ne ma’anar kwatancin Yesu game da ɗa mubazzari? Mahaifi mai juyayi a wannan kwatancin yana wakiltar Jehobah Ubanmu na sama mai ƙauna. Ɗa da ya ce a ba shi gādonsa kuma ya yi almubazzaranci da shi yana wakiltar waɗanda suka bar ƙungiyar Jehobah. Ta wajen barin ikilisiya, yana kamar sun yi tafiya zuwa “ƙasa mai-nisa,” wato, duniyar Shaiɗan wadda take a ware daga Jehobah. (Afis. 4:18; Kol. 1:21) Da shigewar lokaci, wasu sun dawo hankalinsu kuma suka dawo ƙungiyar Jehobah. Ubanmu mai jin ƙai yana sake amincewa da waɗannan masu tawali’u da suka dawo ƙungiyarsa.—Isha. 44:22; 1 Bit. 2:25.

14. Me ya sa Yesu ya yi kwatancin ɗa mubazzari?

14 Me ya sa Yesu ya yi wannan kwatancin? Yesu ya nuna cewa Jehobah yana son waɗanda suka daina bauta masa su dawo. Mahaifi da ke cikin wannan kwatanci ya sa rai cewa ɗansa zai dawo. Sa’ad da ya hango ɗansa daga nesa yana dawowa, “tun yana da nisa,” mahaifin ya tashi a guje don ya marabce shi. Ya kamata wannan kwatanci ya motsa waɗanda suka bar ƙungiyar Jehobah su dawo nan da nan, ko ba haka ba? Wataƙila sun kasala kuma suna jinkirin dawowa don kunya da kuma wasu ƙalubale. Amma hakan ƙwalliya ce da ke biyan kuɗin sabulu don Jehobah da Yesu da kuma mala’iku za su yi farin ciki sosai.—Luk. 15:7.

15, 16. (a) Waɗanne darussa za mu koya daga kwatancin Yesu game da ɗa mubazzari? Ka ba da wasu misalai. (b) Mene ne wannan ya koya mana game da Jehobah da kuma Yesu?

15 Ta yaya za mu amfana daga kwatancin ɗa mubazzari? Ya kamata mu yi koyi da Jehobah. Bai kamata mu “cika yin adalci” har mu ƙi marabtar masu zunubi da suka tuba ba. Hakan zai “hallaka” ko kuma ɓata dangantakarmu da Jehobah. (M. Wa. 7:16) Za mu iya koyon wani darasi daga wannan kwatancin. Ya kamata mu ɗauki wanda ya bar ikilisiya a matsayin “ɓatacciyar tunkiya” ba wanda ba zai iya jin kira ba. (Zab. 119:176) Idan muka haɗu da wanda ya bar ikilisiya, shin za mu yi iya ƙoƙarinmu mu taimaka masa ya dawo ba? Za mu gaya wa dattawa nan da nan don su taimaka masa? Hakika, za mu yi hakan idan muka yi amfani da darasi da muka koya daga kwatancin ɗa mubazzari.

16 Wasu da suka dawo cikin ƙungiyar Jehobah sun nuna godiya ga yadda Jehobah ya nuna musu jin ƙai da ƙauna da kuma yadda ’yan’uwa a ikilisiya suka taimaka musu. Wani ɗan’uwa da aka yi masa yankan zumunci shekara 25 ya ce: “Farin ciki da nake yi tun aka dawo da ni ya ci gaba da ƙaruwa yayin da Jehobah ya sa na ‘wartsake.’ (A. M. 3:19) ’Yan’uwa suna ta ƙarfafa ni cikin ƙauna! A yanzu, ina tare da ’yan’uwa masu ƙaunata a cikin ƙungiyar Jehobah.” Wata matashiya da ta yi shekara biyar da barin ƙungiyar Jehobah ta dawo kuma ta ce: “Ba zan iya kwatanta muku yadda nake ji sa’ad da ’yan’uwa suka nuna mini irin ƙaunar da Yesu ya yi maganarta ba. Kasancewa a cikin ƙungiyar Jehobah ba ƙaramin gata ba ne!”

17, 18. (a) Waɗanne darussa masu muhimmanci ne muka koya daga kwatance-kwatance uku da muka tattauna? (b) Me ya kamata mu ƙudura niyyar yi?

17 Waɗanne darussa masu muhimmanci muka koya daga waɗannan kwatance-kwatance uku? Na farko, ya kamata mu san cewa ci gabar wanda muke nazarin Littafi Mai Tsarki da shi ba a hannunmu yake ba. Yana hannun Jehobah. Na biyu, kada mu ɗauka cewa dukan waɗanda suke halartar taronmu da kuma muke nazari da su ne za su bauta wa Jehobah. Ko da yake wasu za su daina bauta wa Jehobah, kada mu taɓa fid da rai cewa ba za su dawo ba. Idan suka dawo, ya kamata mu karɓe su da hannu bibbiyu kamar yadda Jehobah ya karɓe su.

18 Bari kowannenmu ya ci gaba da biɗan ilimi da fahimi da kuma hikima. Yayin da muke karanta kwatance-kwatancen Yesu, mu yi tambaya don mu gane ma’anar, da dalilin da ya sa aka rubuta su a cikin Littafi Mai Tsarki, da yadda za mu iya amfani da darussan da kuma abin da suke koya mana game da Jehobah da kuma Yesu. Yin hakan zai nuna cewa muna fahimtar ma’anar koyarwar Yesu.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba