‘Allah Ne Mai Ba Da Amfani’!
“Wanda ya dasa ba wani abu ba ne, ko shi wanda ya yi ban ruwa kuma; shi Allah wanda ke bada amfani.”—1 KOR. 3:7.
1. A wace hanya ce muka zama “abokan aiki na Allah”?
“ABOKAN aiki na Allah.” Haka manzo Bulus ya kwatanta gatar da dukanmu za mu iya samu. (Ka karanta 1 Korinthiyawa 3:5-9.) Bulus yana nufin aikin almajirantarwa. Ya kwatanta shi da shuki da kuma zuba wa iri ruwa. Idan muna so mu yi nasara a wannan aiki mai muhimmanci, muna bukatar taimakon Jehobah. Bulus ya tuna mana cewa ‘Allah ne mai ba da amfani.’
2. Me ya sa sanin cewa ‘Allah ne mai ba da amfani’ yake taimakon mu mu kasance da ra’ayin da ya dace game da hidimarmu?
2 Wannan tabbaci ya sa mu kasance da ra’ayi da ya dace game da hidimarmu. Za mu iya yin ƙoƙari sosai a wa’azi da koyarwa, amma ya cancanta a yaba wa Jehobah idan wani ya zama almajiri. Me ya sa? Saboda komin ƙoƙarin da muka yi, babu wanda ya san yadda mutum ya ƙulla dangantaka da Allah, balle a ce mu hanzarta ci gabansa. Sarki Sulemanu ya nuna gaskiyar yanayin sa’ad da ya rubuta: “Ba ka san aikin Allah ba, mai-yin abu duka.”—M. Wa. 11:5.
3. Menene kamani da ke tsakanin aikin shuka iri a zahiri da yin almajirantarwa?
3 Shin rashin fahimtar yadda mutum yake zama almajiri yana sa aikinmu ya zama marar amfanin ne? A’a. Amma yana sa mu farin ciki, da kuma ban sha’awa. Sarki Sulemanu ya ce: “Da safe sai ka shuka irinka, da yamma kuma kada ka ja hannunka; gama ba ka san wanda za ya yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuwa duk za su yi kyau baki ɗaya.” (M. Wa. 11:6) Hakika, idan ya zo ga shuka iri a zahiri, ba za mu san ko zai tsira ba. Akwai abubuwa da yawa da ba za mu iya fahimta ba. Haka yake da aikin almajirantarwa. Yesu ya nanata wannan gaskiyar a kwatanci biyu da aka rubuta mana a Linjilar Markus sura 4. Bari mu ga abin da za mu koya daga waɗannan kwatanci biyu.
Ƙasa Dabam Dabam
4, 5. Ka taƙaita kwatancin mai shuki da ya yafa iri.
4 Kamar yadda aka rubuta a Markus 4:1-9, Yesu ya kwatanta mai shuki da ya yafa iri da suka faɗi a wurare dabam dabam: “Ku kasa kunne: ku duba, mai-shibka ya fita domin shibka: ananan sa’anda yana shibka, waɗansu iri suka faɗi a kan hanya, tsuntsaye suka zo suka cinye. Waɗansu kuma suka faɗi wurin marmara, inda ba su da ƙasa dayawa; nan da nan suka tsira, domin babu zurfin ƙasa garesu. sa’anda rana ta yi, suka ƙone; kuma domin ba su da saiwa, suka yi yaushi. Waɗansu kuma suka faɗi a cikin ƙayayuwa; ƙayayuwa suka yi girma suka shaƙe su, ba su haifu ba. Waɗansu kuma suka faɗi cikin ƙasa mai-kyau, suka bada anfani, suna yin girma, suna ƙaruwa; suna haifuwa, waɗansu riɓi talatin, waɗansu kuwa sattin, waɗansu ɗari.”
5 A lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, ana yafa iri ne a ƙasa. Mai shuki yakan zuba iri a cikin rigarsa ko kuma a cikin moɗa sai ya riƙa yayyafa. A wannan kwatanci, ba da sanin mai shuki ba ne yake yafa iri a ƙasa dabam dabam. Amma, irin da ya yafa suna faɗawa a wurare dabam dabam.
6. Yaya Yesu ya bayyana kwatanci na mai shuki?
6 Ba zai yiwu mu san ma’anar wannan kwatancin ba. Yesu ya ba da bayanin kwatancin da ke Markus 4:14-20: “Mai-shibka yana shibka magana. Na kan hanya ke nan, wurin da a ke shibka magana; sa’anda sun ji, nan da nan Shaitan ya zo, ya amshe magana da aka shibka a cikinsu. Hakanan kuwa waɗanda a ke shibkassu wurin marmara ke nan; su, sa’anda sun ji magana, nan da nan su kan karɓe ta da farinciki; ba su da asali a cikinsu ba, amma su kan jimre kwanaki kaɗan; sa’annan lokacinda ƙunci ko tsanani ya tashi sabili da magana, nan da nan su kan yi tuntunɓe. Waɗansu kuma da a ke shukarsu wurin ƙayayuwa ke nan; waɗanda su kan ji magana, amma ɗawainiyar duniya, da ruɗin dukiya, da sha’awar waɗansu abu masu-shigowa, su kan shaƙe magana, ta zama mara-amfani. Waɗannan kuma da aka shibka su a cikin ƙasa mai-kyau ke nan; waɗanda su kan ji magana, suna ƙarɓanta, suna bada anfani, wani riɓi talatin, wani sattin, wani kuma ɗari.”
7. Menene iri da ƙasa dabam dabam suke wakilta?
7 Ka lura cewa Yesu bai ce an yi amfani da iri dabam dabam ba. Maimakon haka, ya ce iri ɗaya ne ya faɗa a ƙasa dabam dabam, suka ba da amfani dabam dabam. Ƙasa ta fari tana da tauri; ta biyun kuma ba ta da zurfi; ta ukun cike take da ƙayoyi; ta huɗun kuma ƙasa ce mai kyau da take ba da amfani mai kyau. (Luk 8:8) Menene irin? Saƙon Mulki da ke cikin Kalmar Allah ne. (Mat. 13:19) Menene ƙasa dabam dabam suke wakilta? Mutane masu yanayin zuciya dabam dabam.—Ka karanta Luka 8:12, 15.
8. (a) Wanene mai shuki yake wakilta? (b) Me ya sa yadda mutane suka saurari saƙon Mulki ya bambanta?
8 Wanene mai shuki yake wakilta? Yana wakilta abokan aiki na Allah, waɗanda suke shelar bisharar Mulki. Kamar Bulus da Afolos, sun yi shuki kuma sun zuba ruwa. Ko da yake sun yi aiki sosai, ladar ta bambanta. Me ya sa? Saboda yanayin zuciyar waɗanda suka ji saƙon ya bambanta. A kwatancin, mai shuki ba zai iya sanin sakamakon ba. Hakan zai ƙarfafa amintattun ’yan’uwanmu waɗanda suka yi hidima shekaru da yawa, har na ƙarnuka, amma ba sa samun nasara sosai!a Me ya sa hakan abin ƙarfafa ne?
9. Wace gaskiya mai ban ƙarfafa ce manzo Bulus da Yesu suka nanata?
9 Ba a gwada amincin mai shuki da sakamakon aikinsa. Bulus ya nuna hakan sa’ad da ya ce: ‘Kowane za ya sami nasa lada gwalgwadon wahalatasa.’ (1 Kor. 3:8) Ladar don ƙoƙarin da aka yi ne ba don sakamakon abin da aka cim ma ba. Yesu ya nanata wannan batu sa’ad da almajiransa suka dawo daga wa’azi. Sun yi farin ciki saboda ta wurin amfani da sunan Yesu sun kawar da aljanu. Sa’ad da suke farin cikin, Yesu ya ce musu: “Kada ku yi murna, saboda ruhohi suna ƙalƙashin ikonku; amma ku yi murna saboda an rubuta sunayenku cikin sama.” (Luka 10:17-20) Ko da aikin mai shuki bai ba da amfani da yawa ba, hakan ba ya nufin cewa bai yi aiki sosai ba ko kuma ya fi sauran aminci. Hakika, lada ya dangana da yanayin zuciyar mai saurara. Amma Allah ne ke ba da amfani!
Hakkin Waɗanda Suka Ji Maganar
10. Menene zai nuna ko mutumin da ya ji kalmar yana kama da ƙasa mai kyau ko marar kyau?
10 Waɗanda suka saurari kalmar kuma fa? An ƙaddara yadda za su aikata ne? A’a. Su za su zaɓa ko za su yi kama da ƙasa mai kyau ko ba su yi ba. Hakika, yanayin zuciyar mutum zai iya canja zuwa abu mai kyau ko marar kyau. (Rom. 6:17) A kwatancinsa, Yesu ya ce “sa’anda [wasu] sun ji” kalmar, Shaiɗan ya zo ya ɗauke ta. Amma bai kamata hakan ya faru ba. A Yaƙub 4:7, an ƙarfafa Kiristoci su “tsayayya da Shaiɗan,” zai guje musu. Yesu ya ce da farko wasu sun amince kalmar da farin ciki, amma sun yi sanyi saboda “ba su da asali a cikinsu.” Amma an gargaɗi bayin Allah su zama “dasassu [da] kafaffu” don su fahimci “menene fāɗin da ratar da tsawon da zurfin ƙaunar Kristi, ku sani kuma ƙaunar Kristi wadda ta wuce gaban a san ta.”—Afis. 3:17-19; Kol. 2:6, 7.
11. Ta yaya ne mutum zai guji barin ɗawainiya da dukiya su shaƙe maganar?
11 An kwatanta wasu da suka ji kalmar cewa sun ƙyale “ɗawainiyar duniya, da ruɗin dukiya” su shiga su shaƙe maganar. (1 Tim. 6:9, 10) Ta yaya za su guji hakan? Manzo Bulus ya amsa: “Ku kawarda hankalinku daga ƙaunar kuɗi; ku haƙura da abin da ku ke da shi: gama shi da kansa ya ce, Daɗai ba ni tauye maka ba, daɗai kuwa ba ni yashe ka ba.”—Ibran. 13:5.
12. Me ya sa waɗanda suke wakilta ƙasa mai kyau suke ba da amfani dabam dabam?
12 A ƙarshe, Yesu ya ce waɗanda suka yi shuki a ƙasa mai kyau “suna bada anfani, wani riɓi talatin, wani sattin, wani kuma ɗari.” Ko da yake waɗanda suka saurari kalmar suna da zuciya mai kyau kuma suna ba da amfani, abin da suka iya yi wajen shelar bishara ya bambanta bisa ga yanayinsu. Alal misali, tsufa ko kuma ciwo mai tsanani zai iya rage abin da wasu za su iya yi a aikin wa’azi. (Ka gwada Markus 12:43, 44.) Mai shuki kuma ba zai iya hana hakan ba, amma zai yi murna idan ya ga cewa Jehobah ya ba da amfani.—Ka karanta Zabura 126:5, 6.
Mai Shuki da Ya Yi Barci
13, 14. (a) Ka taƙaita kwatancin Yesu na mutum da ya yafa iri. (b) Wanene ke wakilta mai shuki, kuma menene iri da aka suka?
13 Markus 4:26-29 yana ɗauke da wani kwatanci game da wani mai shuki: “Mulkin Allah haka ya ke, watau kamar mutum ya watsa iri a kasa; ya kwana ya tashi dare da rana, iri kuma ya tsira ya yi girma, shi kuwa ba ya san yadda ya ke yi ba. Ƙasa tana bada anfani don kanta, soshiya tukuna, kana zangarniya, bayan wannan zangarniya da ƙwaya nunanna a ciki. Sa’anda anfani ya nuna, nan da nan sai ya sa magirbi, domin lokaci girbi ya yi.”
14 Wanene wannan mai shuki? A koyarwar Kiristendom sun ce Yesu ne da kansa. Amma yaya za a ce Yesu ya yi barci kuma bai san yadda irin suka girma ba? Hakika, Yesu yana sane da yadda suke girma. Maimakon haka, wannan mai shuki kamar wanda aka ambata a baya, yana wakilta masu shelar Mulki ne, waɗanda suka shuka iri na Mulki ta wurin ƙwazonsu a aikin wa’azi. Iri da aka yafa a ƙasa shi ne kalmar da suke wa’azinta.b
15, 16. Wace gaskiya game da girma a zahiri da ta ruhaniya ce Yesu ya bayyana a kwatancinsa na mai shuki?
15 Yesu ya ce mai shuki “ya kwana ya tashi dare da rana.” Hakan ba kuskure ba ne daga mai shuki. Yana nuna ainihin rayuwar da mutane suke yi ne. Kalaman da aka yi amfani da su a wannan ayar sun nuna aikin da ake yi da rana kuma a yi barci da dare. Yesu ya bayyana abin da ya faru a wannan lokacin. Ya ce: “Iri kuma ya tsira ya yi girma.” Sai Yesu ya daɗa: “Shi kuwa ba ya san yadda ya ke yi ba.” Abin da aka nanata shi ne irin ya yi girma ‘don kansa.’c
16 Menene Yesu yake nufi a nan? Ka lura cewa ya mai da hankali a kan girma ne da kuma yadda hakan ya faru a hankali. ‘Ƙasa tana bada anfani don kanta, soshiya tukuna, kana zangarniya, bayan wannan zangarniya da ƙwaya nunanna a cikin.’ (Mar. 4:28) Wannan girman ta soma a sannu sannu kuma a lokaci dabam dabam. Ba za a iya tilasta mata ba ko kuma a sa ta yi sauri. Hakan yake da girma ta ruhaniya. Wannan yana faruwa a lokaci dabam dabam yayin da Jehobah yake barin gaskiya ta yi girma a zuciyar mutane da suke da zuciyar kirki.—A. M. 13:48; Ibran. 6:1.
17. Wanene yake farin ciki sa’ad da irin ya yi ’ya’ya?
17 Ta yaya mai shuki yake girbi “sa’anda anfani ya nuna”? Sa’ad da Jehobah ya sa gaskiyar Mulki ta yi girma a zuciyar sababbin almajirai, daga baya suka sami ci gaba har ƙaunarsu ga Allah ta motsa su suka keɓe kansu gare shi. Sun nuna keɓe kansu ta wurin yin baftisma. ’Yan’uwa maza da suka ci gaba da girma a ruhaniya sun sami ƙarin hakki a hankali a hankali a cikin ikilisiya. Mai shuki na asali da kuma wasu masu shelar Mulki da ba su sa hannu sa’ad da ake shuka iri ba sun girbe amfanin Mulki da ya sa aka samo wannan almajirin. (Ka karanta Yohanna 4:36-38.) Hakika, “mai-shuka da mai-girbi [za] su yi farinciki.”
Darussa Dominmu a Yau
18, 19. (a) Ta yaya maimaitawar kwatancin Yesu ya ƙarfafa ka? (b) Menene za a bincika a talifi na gaba?
18 Menene muka koya daga maimaitawar wannan kwatanci biyu da ke rubuce a Markus sura 4? Mun fahimci cewa muna da aiki, wato, aikin shuki. Bai kamata mu ba da hujja ko kuma mu ƙyale matsaloli da za mu fuskanta su hana mu yin wannan aikin. (M. Wa. 11:4) Ban da haka, muna sane da gata da muke da shi na zama abokan aiki na Allah. Jehobah ne ke kawo girma ta ruhaniya, yana sa albarka a ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu da kuma waɗanda suke saurara saƙonmu. Mun fahimci cewa ba za mu iya tilasta wa kowa ya yi girma a ruhaniya ba. Bai kamata kuma mu yi sanyin gwiwa ko kuma mu fid da rai idan girma ta ruhaniya ba ta zo da sauri ba. Abin ban ƙarfafa ne cewa ana gwada nasararmu da bangaskiyarmu ga Jehobah da kuma gata da ya ba mu na yin wa’azin “bishara ta mulki . . . domin shaida ga dukan al’ummai.”—Mat. 24:14.
19 Menene kuma Yesu ya koya mana game da girmar sababbin almajirai da kuma aikin Mulki? Amsar wannan tambaya na cikin kwatanci da ke rubuce a labaran Linjila. Za mu bincika wasu cikin waɗannan kwatanci a talifi na gaba.
[Hasiya]
a Ka yi la’akari da misalin hidimar Ɗan’uwa Georg Fjölnir Lindal a ƙasar Iceland da aka rubuta a Yearbook of Jehovah’s Witnesses, na shekara ta 2005 shafuffuka na 210-211, da kuma labarin amintattun bayi da suka nace a hidimarsu a ƙasar Ireland shekaru da yawa ba tare da wani sakamako ba, da ke Yearbook of Jehovah’s Witnesses na shekara ta 1988, shafuffuka na 82-99.
b A cikin wannan mujallar an bayyana cewa iri yana wakilta halayen mutane da za su girma a ruhaniya, wanda abubuwa na duniya suka rinjayi halayen. Amma, ka lura cewa a kwatancin Yesu wannan iri ba ya canja zuwa iri marar kyau. Sai dai kawai ya manyanta.—Ka duba Hasumiyar Tsaro, 15 ga Yuni , 1980, shafuffuka na 17-19.
c A Ayukan Manzani 12:10 ne kaɗai aka yi amfani da wannan furcin, inda aka yi maganar ƙofar ƙarfe ta buɗe “don kanta.”
Ka Tuna?
• Waɗanne kamani ne ke tsakanin shuka iri a zahiri da kuma wa’azin saƙon Mulki?
• Ta yaya Jehobah yake gwada amincin mai wa’azin Mulki?
• Wane kamani da ke tsakanin girma a zahiri da ta ruhaniya ne Yesu ya nanata?
• Ta yaya “mai-shuka da mai-girbi [suka] yi farinciki”?
[Hotuna a shafi na 15]
Waɗanda ƙasa mai kyau take wakilta suna yin wa’azin Mulki bisa ga yanayinsu da dukan zuciyarsu
[Hotuna a shafi na 16]
Allah ne ya sa su yi girma