‘Ku Zauna Cikin Maganata’
“Idan kun zauna cikin maganata, ku ne almajiraina na gaske.”—YOHANNA 8:31.
1. (a) Sa’ad da Yesu ya koma sama, menene bai bari a duniya ba? (b) Waɗanne tambayoyi za mu bincika?
SA’AD da Yesu Kristi, wanda ya kafa Kiristanci ya koma sama, ba shi da littattafai da ya rubuta a duniya, gini domin a tuna da shi, ko kuma dukiya da ya tara. Amma ya bar almajirai da kuma ƙa’idodi da dole ne almajiri ya cika su. A cikin Lingila ta Yohanna mun sami ƙa’idodi uku masu muhimmanci da Yesu ya ambata duk wanda yake so ya zama almajirinsa dole ne ya cika su. Menene waɗannan ƙa’idodi? Menene za mu yi domin mu cika su? Ta yaya za mu tabbata cewa mu kanmu mun ƙware mu zama almajiran Kristi a yau?a
2. Mecece ƙa’ida mai muhimmanci na almajiranci in ji Lingilar Yohanna?
2 Kusan watanni shida kafin mutuwarsa, Yesu ya je Urushalima ya yi wa’azi ga jama’ar da ta taru a nan domin ta yi Idin kwana bakwai na Bukkoki. Domin haka, da idin ya kai rabinsa, “daga cikin taron mutane dayawa suka bada gaskiya gareshi.” Yesu ya ci gaba da wa’azi, a ƙarshen idin, “mutane da yawa suka bada gaskiya gareshi.” (Yohanna 7:10, 14, 31, 37; 8:30) A wannan lokaci, Yesu ya mai da hankalinsa ga sababbi waɗanda suka ba da gaskiya, ya faɗa musu ƙa’ida mai muhimmanci na almajiranta, kamar yadda manzo Yohanna ya rubuta: “Idan kun zauna cikin maganata, ku ne almajiraina na gaske.”—Tafiyar tsutsa tamu ce; Yohanna 8:31.
3. Wane hali ake bukata domin mutum ya ci gaba da zama “cikin magana [ta Yesu]”?
3 Da waɗannan kalmomi, Yesu ba nufi yake yi ba cewa sababbin da suka ba da gaskiya ba su da bangaskiya ba. Maimakon haka, yana nuna musu ne cewa suna da zarafin su zama almajiransa na gaske—idan suka zauna cikin maganarsa, watau idan suka yi jimiri. Sun riga sun karɓi maganarsa amma suna bukatar su ci gaba a cikinta. (Yohanna 4:34; Ibraniyawa 3:14) Hakika, Yesu ya san cewa jimiri hali ne mai muhimmanci ƙwarai ga mabiyansa, saboda haka a maganarsa ta ƙarshe da manzanninsa, da aka rubuta a Lingila ta Yohanna, Yesu sau biyu ya ce: ‘Ku biyo ni.’ (Yohanna 21:19, 22) Kiristoci na farko da yawa sun yi haka. (2 Yohanna 4) Menene ya taimake su suka jimre?
4. Menene ya taimaka wa Kiristoci na farko suka jimre?
4 Manzo Yohanna, almajiri mai aminci na Kristi shekara saba’in, ya faɗi wani abu mai muhimmanci. Ya yabi Kiristoci masu aminci yana cewa: “Domin ku ƙarfafa ne, maganar Allah kuwa tana zaune cikinku, kuma kun yi nasara da mugun.” Waɗannan almajiran Kristi sun jimre, ko kuma sun zauna cikin maganar Allah, domin maganar Allah ta zauna cikinsu. Sun kuma ɗauke ta da muhimmanci ƙwarai. (1 Yohanna 2:14, 24) Haka ma a yau, domin mu ‘jimre har zuwa ƙarshe,’ muna bukatar mu tabbata cewa kalmar Allah tana zaune cikinmu. (Matta 24:13) Ta yaya za mu yi wannan? Misali da Yesu ya kafa ya ba da amsar.
‘Jin Magana’
5. (a) Waɗanne ƙasa iri dabam dabam ne Yesu ya ambata a wani misalinsa? (b) Menene iri da kuma ƙasa na misalin Yesu suke nufi?
5 Yesu ya ba da misalin mai shuki da ya shuka iri, an rubuta wannan a Lingila ta Matta, da ta Markus, da ta Luka. (Matta 13:1-9, 18-23; Markus 4:1-9, 14-20; Luka 8:4-8, 11-15) Sa’ad da ka karanta labarin, za ka lura cewa a misalin irin, iri ɗaya sun faɗi a kan ƙasa iri dabam dabam suka kuma ba da amfani dabam dabam. Ƙasa ta fari mai tauri ce, ta biyun kuma ba ta da zurfi, ta ukun kuma cike take da ƙayoyi. Ta huɗun, ba kamar saura ukun ba ne, tana da “kyau.” A bayanin da Yesu ya yi, irin, saƙon Mulki ne da yake cikin Kalmar Allah, ƙasar kuma tana nufin mutane ne masu zuciya iri-iri. Ko da yake mutanen da ƙasa iri dabam dabam ke kwatantawa suna da kamani, waɗanda ƙasa mai kyau take kwatanci suna da hali da ya bambanta su daga sauran.
6. (a) Ta yaya ƙasa ta huɗu ta misalin Yesu ta bambanta da saura ukun, kuma menene wannan yake nufi? (b) Menene yake da muhimmanci domin nuna jimiri namu na almajiran Kristi?
6 Labarin Luka 8:12-15 ya nuna cewa a duka misalai huɗun, mutane ‘sun ji maganar.’ Waɗanda suke da ‘zuciya mai kyau’ ba ‘jin magana’ kawai suka yi ba. Suka “riƙe ta, da haƙuri kuma suna bada amfani.” Ƙasa mai kyau saboda tana da laushi kuma tana da zurfi, ta ƙyale saiwar irin ta yi ƙarfi, kuma saboda haka, irin ya yi girma ya ba da amfani. (Luka 8:8) Hakanan, waɗanda suke da zuciya mai kyau sun fahimta, sun ga tamanin kalmar Allah kuma sun yi ƙwazo cikinta. (Romans 10:10; 2 Timothy 2:7) Maganar Allah ta zauna cikinsu. Domin wannan suka ba da amfani da haƙuri. Fahimtar tamanin Kalmar Allah tana da muhimmanci wajen nuna jimiri namu na almajiran Kristi. (1 Timothawus 4:15) To, ta yaya za mu samu fahimtar tamanin Kalmar Allah?
Yanayin Zuciya da Kuma Tunani Mai Ma’ana
7. Wane abu ne yake haɗe sosai da zuciya mai kyau?
7 Ka lura da irin ayyuka da Littafi Mai Tsarki yake haɗa da zuciya mai kyau. “Zuciyar mai-adalci ta kan yi tunanin abin da za ta amsa.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Misalai 15:28) “Bari batutuwan bakina, da tunanin zuciyata, su zama abin karɓa a gareka, Ya Ubangiji.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Zabura 19:14) “Binciken zuciyata kuma za ya zama na fahimi.”—Tafiyar tsutsa tamu ce; Zabura 49:3.
8. (a) Sa’ad da muke karatun Littafi Mai Tsarki, menene ya kamata mu guji yi, kuma menene ya kamata mu yi? (b) Wane amfani muke samu daga addu’a na bimbini a kan Kalmar Allah? (Ka haɗa da akwatin nan sun “Kahu Cikin Gaskiya.”)
8 Kamar waɗannan marubutan Littafi Mai Tsarki, mu ma muna bukatar tunani da kuma addu’a bisa Kalmar Allah da kuma ayyukansa. Sa’ad da muke karatun Littafi Mai Tsarki ko kuma littattafan Littafi Mai Tsarki, bai kamata mu zama kamar waɗanda suka je zagaya da suke hanzartawa daga wannan wuri zuwa wancan suna ɗauka hoton kome amma hankalinsu baya wurin ba. Maimakon haka, sa’ad da muke nazarin Littafi Mai Tsarki, muna bukata mu ba da lokaci mu tsaya mu more Littafi Mai Tsarki.b Sa’ad da muke bimbini a kan abin da muka karanta, kalmar Allah za ta taɓa zuciyarmu. Tana motsa zuciyarmu kuma tana gyara tunaninmu. Tana motsa mu kuma mu gaya wa Allah tunanin zuciyarmu cikin addu’a. Domin wannan, mannewarmu ga Jehovah za ta ƙarfafa, kuma ƙaunarmu ga Allah za ta motsa mu mu ci gaba da bin Yesu har a lokatai masu wuya. (Matta 10:22) A bayyane yake, bimbini a kan abin da Allah ya ce yana da muhimmanci idan muna so mu kasance masu aminci har ƙarshe.—Luka 21:19.
9. Ta yaya za mu iya tabbata cewa zuciyarmu ta kasance mai karɓan kalmar Allah?
9 Misalin Yesu ya nuna cewa da akwai matsaloli da za su hana iri a yin girma, watau kalmar Allah. Shi ya sa, domin mu kasance almajirai masu aminci, muna bukatar mu (1) gano matsalar da yanayin ƙasa marar dacewa ɗin ke wakilta da aka faɗa a misalin kuma (2) mu yi ƙoƙarin yin gyara ko mu guje ta. Ta wannan hanyar, za mu tabbata cewa zuciyarmu ta kasance mai karɓan iri na Mulkin kuma za ta ci gaba da ba da amfani.
“A Kan Hanyar”—Sun Shagala
10. Ka kwatanta ƙasa ta farko a misalin Yesu, kuma ka ba da bayanin abin da take nufi.
10 Irin ƙasa ta farko da irin ya faɗi “a kan hanyar” ne, inda aka “tattaka ƙarƙashin sawaye.” (Luka 8:5) Lallai ƙasa da take hanyar gona tana shan takun sawayen mutane. (Markus 2:23) Haka nan, waɗanda suka ƙyale je ka ka dawo na wannan duniya ya ɗauki lokaci kuma ya ci kuzarinsu za su shagala, da ba za su kasance da godiya ba ga kalmar Allah. Sun ji ta, amma sun kasa yin bimbini a kanta. Saboda haka, zuciyarsu ta taurara. Kafin su yi ƙaunarta “Shaiɗan ya zo ya amshe magana a zukatansu, domin kada su bada gaskiya su tsira.” (Luka 8:12) Za a iya hana wannan kada ya faru?
11. Ta yaya za mu kāre zuciyarmu daga zama kamar ƙasa mai tauri?
11 Da abubuwa da yawa da za a iya yi domin a hana zuciya daga zama kamar ƙasa marar amfani na kan hanya. Ƙasa da ake takawa kuma mai tauri zai iya zama mai laushi mai amfani idan aka nome kuma aka kashe hanyar da take wajen. Haka nan, ba da lokaci domin nazari da bimbini a kan Kalmar Allah za ta sa zuciya ta zama kamar ƙasa mai kyau, mai amfani. Abu mafi muhimmanci shi ne kada mu shagala cikin biɗan abubuwa na rayuwar yau da kullum. (Luka 12:13-15) Maimakon haka, ka tabbata cewa da akwai lokaci domin bimbini a kan “mafifitan al’amura,” na rayuwa.—Filibbiyawa 1:9-11.
“A Kan Marmara”—Tsoratawa
12. Menene ainihin dalilin da ya sa tsiro yake yin yaushi a ƙasa iri na biyun da aka ambata a misalin Yesu?
12 Da iri ya faɗi a kan ƙasa ta biyun, bai kasance ba kawai a sama sama kamar a kan irin ƙasa ta farkon. Ya yi saiwa ya tsiro. Amma sa’ad da rana ta fito, da tsiron ya sha zafin rana sai ya yi yaushi. Amma, ka lura da wannan bayani mai muhimmanci. Ainihin dalilin da ya sa tsiron ya yi yaushi ba domin zafin rana ba ne. Ko tsiro da ya fito a kan ƙasa mai kyau ma zai sha rana, amma bai yi yaushi ba—maimakon haka ya yi girma. To, menene bambancin? Yesu ya yi bayani cewa, “domin babu zurfin ƙasa garesu” kuma “ba su da laima.” (Matta 13:5, 6; Luka 8:6) “Marmara” tana hana saiwar iri ta yi zurfi domin ta samu laima da kuma ƙarfi. Tsiron sai ya yi yaushi domin ƙasar ba ta da zurfi.
13. Waɗanne irin mutane ne suke kama da ƙasar da ba ta da zurfi, kuma menene ainihin dalilin yadda suka amsa?
13 Wannan misalin yana nuni ga mutane da suka “karɓi magana da farincikin” kuma suka bi Yesu da himma na “ ’yan kwanaki.” (Luka 8:13) Sa’ad da suka fuskanci azabar “ƙunci ko tsanani,” sai su tsorata su rasa farin cikin da kuma kuzarinsu, sai su juya wa Kristi baya. (Matta 13:21) Amma ainihin dalilin tsoratar su ba hamayya ba ce. To, mabiyan Kristi miliyoyi suna jimre wa tsanani iri iri, duk da haka sun kasance da aminci. (2 Korinthiyawa 2:4; 7:5) Ainihin dalilin da ya sa wasu suke tsorata su ja da baya shi ne zuciyarsu da take kama da marmara tana hana su bimbini mai zurfi game da abubuwa masu kyau na ruhaniya. Saboda haka, ƙaunar Jehovah da maganarsa ba ta yi zurfi ba kuma ba ta da ƙarfin da za ta tsayayya wa hamayya. Ta yaya mutum zai iya hana irin wannan daga faruwa?
14. Waɗanne matakai ya kamata mutum ya ɗauka domin ya hana zuciyarsa daga zama kamar marmara?
14 Mutum yana bukatar ya tabbata cewa cikas masu kama da duwatsu, kamar su baƙin ciki mai tsanani, son kai da bai bayyana ba tukuna, ko kuma irin mugun tunani da ya samu zama cikin zuciyarsa. Idan kana cikin irin waɗannan cikas, iko da kalmar Allah take da shi zai iya kawar da su. (Irmiya 23:29; Afisawa 4:22; Ibraniyawa 4:12) Daga baya, addu’a tare da bimbini za su iya motsa “dasashiyar magana” cikin zuciyar mutumin. (Yaƙub 1:21) Wannan za ta ba da ƙarfi da za a jimre a lokacin karaya da kuma ƙarfafa domin a kasance da aminci duk da gwaji da ake fuskanta.
A “Tsakiyar Ƙayoyi”—Masu Zuciya Biyu
15. (a) Me ya sa ƙasa iri na uku da Yesu ya ambata musamman ya bukaci mu mai da masa hankalinmu? (b) Menene a ƙarshe ya faru da ƙasa iri na uku, kuma me ya kawo haka?
15 Ƙasa ta ukun, wadda take da ƙayoyi, musamman ta bukaci mu mai da masa hankalinmu domin a wasu hanyoyi ta yi kama da ƙasa mai kyau. Kamar ƙasa mai kyau, ƙasa mai ƙayoyi tana ƙyale irin ya yi saiwa ya tsiro. Da farko, babu bambanci tsakanin girman waɗannan sabon iri na waɗannan ƙasa iri biyu. Amma, da shigewar lokaci, yanayi ya canja da a ƙarshe ya kai ga shaƙe tsiron. Ƙasar ta cika da ƙayoyi, ba kamar ƙasa mai kyau ba. Sa’ad da sabon tsiron yake girma a wannan ƙasar, ya fuskanci gasa daga ‘ƙayoyi da suke girma tare da shi.’ Duk irin suka yi kokawar abinci, haske, da wuri na ɗan lokaci, amma a ƙarshe ƙayoyin suka fi ƙarfin irin kuma suka ‘shaƙe shi.’—Luka 8:7.
16. (a) Waɗanne mutane ne suke kama da ƙasa mai ƙayoyi? (b) A labarin Linjila uku, menene ƙayoyi suke nufi?—Dubi hasiya.
16 Wane irin mutane ne suka yi kama da ƙasa mai ƙayoyi? Yesu ya yi bayani: “Su ne sun ji, kuma cikin tafiyarsu sun shaƙe da sha’ani, da wadata, da annashuwa ta wannan rai, ba su bada wani amfanin kirki ba.” (Luka 8:14) Kamar yadda irin mashuki da kuma ƙayoyi suke girma lokaci ɗaya, haka wasu mutane suke so su ba da lokaci domin kalmar Allah da kuma “annashuwa ta wannan rai” a lokaci ɗaya. An shuka gaskiya ta kalmar Allah a zuciyarsu, amma ta fuskanci gasa daga wasu abubuwa da suke kokawa a mai da musu hankali. Zuciyarsu ta alama ta zama biyu. (Luka 9:57-62) Wannan yana hana su ba da isashen lokaci domin addu’a da kuma bimbini mai ma’ana a kan kalmar Allah. Ba su riƙe kalmar Allah da kyau ba saboda haka, ba su da ƙaunar da ake bukata domin a jimre. A hankali, neman abin da ba na ruhaniya ba suna rufe abubuwa na ruhaniya har su “shaƙe” su gabaki ɗaya.c Lallai ƙarasa ce ta baƙin ciki ga waɗanda ba su ƙaunaci Jehovah da zuciya ɗaya ba!—Matta 6:24; 22:37.
17. Me za mu zaɓa a rayuwa saboda kada ƙayoyi na alama da aka faɗa a misali na Yesu su shaƙe mu?
17 Ta wajen saka abubuwa na ruhaniya farko bisa abin duniya, muna guje shaƙuwa da azaba da kuma annashuwa na wannan duniya. (Matta 6:31-33; Luka 21:34-36) Kada mu yarda mu ƙyale karatun Littafi Mai Tsarki da bimbini bisa abin da muka karanta. Za mu samu ƙarin lokaci na mai da hankali da kuma yin addu’a da bimbini idan muka sauƙaƙa rayuwarmu yadda ta kamata. (1 Timothawus 6:6-8) Bayin Allah da suka yi haka—watau a ce, sun tuge ƙayoyin daga ƙasa domin su samu ƙarin abinci, haske, da kuma fili daga tsiro mai ba da ’ya’ya—suna samun albarkar Jehovah. Sandra ’yar shekara 26, ta ce: “Sa’ad da na yi bimbini a kan albarkata a cikin gaskiya, na fahimci cewa duniya ba za ta ba da abin da za a gwada da su ba!”—Zabura 84:11.
18. Ta yaya za mu zauna cikin maganar Allah mu Kiristoci kuma mu jimre?
18 A bayyane yake cewa dukanmu yara da manya, za mu zauna cikin maganar Allah kuma mu jimre mu almajiran Kristi kamar yadda kalmar Allah take zaune cikinmu. Saboda haka, bari mu tabbata cewa ƙasar zuciyarmu ta alama ba za ta yi tauri ba, marar zurfi, ko kuma ta cika da ƙayoyi amma ta kasance mai laushi kuma mai zurfi. A wannan hanya ce, za mu iya tsotsar kalmar Allah da kyau da “haƙuri kuma [mu] ba da amfani.”—Luka 8:15.
[Hasiya]
a A wannan talifin, za mu bincika ƙa’ida ta farko cikin waɗannan ƙa’idodi. Biyu da suka rage za a bincika su cikin talifofi na gaba.
b Domin ka yi bimbini na addu’a a kan abin da ka karanta cikin Littafi Mai Tsarki, za ka iya tambayar kanka, alal misali: ‘Ya bayyana halin Jehovah guda ɗaya ne ko fiye da haka? Wace nasaba take da shi da jigon Littafi Mai Tsarki? Ta yaya zan yi amfani da shi a rayuwata ko kuma in yi amfani da ita in taimaki wasu?’
c A labari uku na almarar Yesu a Linjila, azaba da nishaɗi na wannan duniya suka shaƙe irin: “Ɗawainiyar duniya” “ruɗin dukiya” “sha’awar waɗansu abu masu-shigowa” da kuma “annashuwa ta wannan rai.”—Markus 4:19; Matta 13:22; Luka 8:14; Irmiya 4:3, 4.
Menene Amsoshinka?
• Me ya sa muke bukatar mu ‘zauna cikin maganar Yesu’?
• Ta yaya za mu iya ƙyale kalmar Allah ta zauna a cikin zuciyarmu?
• Waɗanne irin mutane ne ƙasa iri huɗu da Yesu ya ambata suke kwatantawa?
• Ta yaya za ka sami lokaci domin ka yi bimbini a kan kalmar Allah?
[Box/Hoto a shafi na 18]
Sun “Kahu Cikin Gaskiya”
ALMAJIRAN Yesu da suka daɗe suna almajiranci suna tabbatar da cewa sun “kahu cikin gaskiya” da shigewar kowacce shekara. (2 Bitrus 1:12) Menene yake taimaka musu su jimre? Ka yi la’akari da wasu cikin kalamansu.
“Ina ƙarasa kowacce rana da karatun wani ɓangare na Littafi Mai Tsarki da kuma addu’a. Sa’an nan na yi tunani game da abin da na karanta.”—Jean, ta yi baftisma a shekara ta 1939.
“Bimbini a kan yadda Jehovah, wanda yake da girma sosai, yake ƙaunarmu ƙwarai yana sa in ji ina da kāriya kuma yana ba ni ƙarfi in kasance da aminci.”—Patricia, ta yi baftisma a shekara ta 1946.
“Ta wajen kasancewa da nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau da kuma shagala cikin ‘zurfafan abubuwa na Allah,’ na iya cin gaba da bauta wa Jehovah.”—1 Korinthiyawa 2:10; Anna, ta yi baftisma a shekara ta 1939.
“Ina karatun Littafi Mai Tsarki da littattafanmu na Littafi Mai Tsarki domin in binciki zuciyata da kuma muradina.”—Zelda, ta yi baftisma a shekara ta 1943.
“Lokatai da na fi jin daɗinsu sa’ad da na ɗan zagaya ne na yi wa Jehovah magana cikin addu’a kuma na gaya masa yadda nake ji.”—Ralph, ya yi baftisma a shekara ta 1947.
“Abin da nake yi da farko kowacce safiya shi ne na bincika nassosin yini kuma na karanta wani ɓangare na Littafi Mai Tsarki. Wannan yana ba ni wani sabon abin da zan yi bimbini a kai a ranar.”—Marie, ta yi baftisma a shekara ta 1935.
“A gare ni, ina jin daɗin tattauna littafi na Littafi Mai Tsarki aya aya.”—Daniel, ya yi baftisma a shekara ta 1946.
Wane lokaci kake yin bimbini da kuma addu’a a kan kalmar Allah?—Daniel 6:10b; Markus 1:35; Ayukan Manzanni 10:9.
[Hoto a shafi na 21]
Ta wajen sa batutuwan ruhaniya da farko, za mu iya “haƙuri kuma [mu] ba da amfani”