Ku Gabatar da Saƙo a Hanyar da Zai Jawo Hankalin Mutane
1. Mene ne muka koya daga yadda Kiristoci na farko suka gabatar da saƙon Mulki?
1 Kiristoci na farko sun yi wa mutanen addinai da ƙabilu dabam-dabam wa’azi. (Kol. 1:23) Ko da yake dukansu suna wa’azi ne game da Mulkin Allah, yadda suka gabatar da saƙo game da Mulkin ya dangana ne da waɗanda suke yi wa wa’azi. Alal misali, sa’ad da Bitrus yake yi wa Yahudawa wa’azi, ya fara da yin ƙaulin annabi Yowel don ya san cewa Yahudawa sun yi imani da Nassi. (A. M. 2:14-17) Amma, ka lura da yadda Ayyukan Manzanni 17:22-31 suka kwatanta yadda Bulus ya tattauna da Helanawa. Wasu mutanen da muke yi wa wa’azi a yau sun yi imani da Littafi Mai Tsarki, saboda haka, za mu iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki yayin da muke yi musu wa’azi. Amma zai dace mu zama masu hikima sa’ad da muke wa’azi ga waɗanda ba su gaskata da Littafi Mai Tsarki ba ko kuma waɗanda ba Kiristoci ba.
2. Ta yaya za mu yi amfani da littattafanmu don mu taimaka wa waɗanda suka gaskata da Littafi Mai Tsarki da kuma waɗanda ba su yi imani da shi ba?
2 Ku Ba da Littattafai a Hanyar da Ta Dace: A wannan shekarar hidima, za a riƙa canja littattafan da muke wa’azi da su bayan kowane wata biyu kuma wannan sabon tsarin zai nuna mujallu da warƙa da kuma ƙasidun da za mu riƙa ba mutane. Ko da mutanen da ke yankinmu ba su gaskata da Littafi Mai Tsarki ba, za mu iya yin amfani da wani daga cikin littattafanmu ko warƙa sa’ad da muke tattaunawa da su don mu jawo hankalinsu. Wataƙila, ba zai dace mu karanta nassi ko kuma mu ambaci nassi kai tsaye a haɗuwarmu ta farko ba, amma idan mun lura cewa maigidan ya ji daɗin abin da muka ce, za mu iya dawowa da niyyar taimaka masa ya ƙulla dangantaka mai kyau da Mahaliccinmu kuma ya yi imani da Kalmarsa. A wani ɓangare kuma, idan muna wa’azi ga mutanen da suka gaskata da Littafi Mai Tsarki, za mu iya yin amfani da littattafanmu da kuma gabatarwar da muka saba yi. Hakika, za mu iya ba da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko Ka Saurari Allah ko kuma Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada a duk lokacin da ya dace, ko da ba su ne littattafan da ake ba da wa a watan ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne mu ba da littattafai a hanyar da ta dace.
3. Ta yaya zukatan mutanen da muke yi wa wa’azi take kama da ƙasa?
3 Ku Nome Ƙasar da Kyau: Zuciyar mutum tana kama da ƙasa. (Luka 8:15) Kamar yadda wasu irin ƙasa za su bukaci aiki tuƙuru saboda a noma su, haka ma zuciyar wasu mutane take, kafin gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki ta shiga, za ta bukaci a yi aiki sosai. Kiristoci na ƙarni na farko sun yi wa’azin bishara ga mutane dabam-dabam, kuma hakan ya sa su farin ciki matuƙa. (A. M. 13:48, 52) Mu ma za mu iya yin nasara idan muka mai da hankali ga gabatarwa da muke amfani da ita a wa’azi.