“Ku Ba Da Tsohuwar Mujalla ko Wata Ƙasida da ta Dace da Mai Gidan”
A watanni da muka ba da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da kuma soma nazari a haɗuwa ta farko, an ƙarfafa mu mu “ba da tsohuwar mujalla ko kuma wata ƙasida da ta dace da mai gida” idan yana da littafin kuma ba ya son a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Me ya sa?
Ƙasidu da tsofaffin mujallu sun yi magana a kan batutuwa dabam-dabam da suka dace. Wani abu da ke cikin waɗannan littattafai zai iya taɓa zuciyar mai gidan. Saboda haka, sa’ad da kake shirya jakarka na wa’azi, ka saka ƙasidu dabam-dabam da tsofaffin mujallu. Idan ba ka da tsofaffin mujallu, wataƙila kana iya samun wasu daga kantar littattafai. Idan mai gidan yana da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwar? kuma bai yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi ba, kana iya nuna masa wasu cikin mujallun ko kuma ƙasidu da kake da su kuma ka gaya masa ya ɗauki waɗanda yake so. Bayan hakan, ka shirya ka koma ziyara. Wataƙila daga baya zai yarda a soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.