Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 7/12 pp. 2-3
  • Ku Taimaka wa Mutane Su Saurari Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Taimaka wa Mutane Su Saurari Allah
  • Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Za a Yi Amfani da Ka Saurari Allah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Yadda Za A Yi Amfani da Sabuwar Ƙasidar Nan Albishiri Daga Allah!
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Ku Yi wa “Dukan Mutane” Wa’azi
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Kana Yin Amfani da Waɗannan Ƙasidun?
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2012
km 7/12 pp. 2-3

Ku Taimaka wa Mutane Su Saurari Allah

1. Waɗanne ƙasidu ne aka fitar a Taron Gunduma na ‘Bari Mulkin Allah Ya Zo!’ kuma me ya sa suke da amfani sosai?

1 An fitar da sababbin ƙasidu guda biyu a Taron Gunduma na ‘Bari Mulkin Allah Ya Zo!’, wato, Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada da kuma wanda aka sauƙaƙa, Ka Saurari Allah. Tun da ƙasidun ba su da rubutu da yawa, za a iya fassara su da sauƙi kuma a cikin ƙanƙanin lokaci. A lokacin da aka fitar da wannan ƙasidar Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada a Turanci, an riga an ba da umurni a fassara shi cikin harsuna 431.

2. Su wane ne za su amfana daga waɗannan ƙasidun?

2 Su wane ne musamman za su amfana daga waɗannan ƙasidun? Ku yi la’akari da wannan yanayin da ke yawan faruwa a wurare dabam-dabam a faɗin duniya:

• Wani mai shela yana cikin tattaunawa da mai gida, wataƙila sa’ad da yake yi masa wa’azi ko sa’ad da ya koma ziyara, sai ya fahimci cewa mai gidan bai iya karatu ba sam ko kuma bai iya karatu ba sosai.

• Wani mai shela ya yi wa’azi wa mutanen da ba a fassara littattafanmu da yawa a yarensu ba ko kuma ba a fassara wani littafi a yaren ba sam; ko kuma yawancin mutanen da ke yankin ba sa iya karanta yaren da suka fi yi.

• Wani mai shela yana yi wa kurame wa’azi a yankinsa da yaren kurame.

• Wani mai shela ko kuma mahaifi yana so ya koyar da gaskiya wa yaro ƙarami wanda bai iya karatu ba tukun.

3. Yaya aka tsara ƙasidar nan Ka Saurari Allah?

3 Yadda Aka Tsara Su: Rubutun da ke cikin ƙasidar nan Ka Saurari Allah bai da yawa kuma yana da sauƙin ganewa, ƙari ga hakan, a ƙarƙashin rubutun, an saka Nassi da ke fitar da muhimman batutuwan da aka tattauna. Me ya sa? A ce wani ya ba ka ƙasidar da aka rubuta a yaren da ba ka iya karantawa ba, kuma wataƙila ma ba ka taɓa ganin haruffan da ke cikin ƙasidar ba. Shin, za ka so wannan ƙasidar ko da a ce yana ɗauke da hotuna masu kyau? Da ƙyar. Hakazalika, littattafan da suke da rubutu da yawa suna sa waɗanda ba su iya karatu ba su yi sanyin gwiwa. Domin wannan dalilin ne aka saka hotuna masu kyau a kowane shafi, kuma akwai alamun da ke nuna yadda za a tattauna hotunan bi-da-bi.

4. Yaya aka tsara ƙasidar nan Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada?

4 Ƙasidar nan Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada tana da hotuna iri ɗaya da Ka Saurari Allah. An tsara ta ne don yin nazari da waɗanda ba su iya karatu sosai ba ko kuma waɗanda suke koyon karatu. Mutumin da ke gudanar da nazarin zai iya amfani da ƙasidar nan Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada yayin da ɗalibinsa yana riƙe da ɗayan ƙasidar, Ka Saurari Allah. Kowane darasi ya soma ne da tambaya a gefen hagu daga sama, kuma an amsa tambayar a shafuffuka guda biyu da suka tattauna darasin. Hotunan suna ɗauke da bayanai da kuma nassin da za a karanta. Da yawa daga cikin shafuffukan suna ɗauke da akwati a ƙasa wanda ya ƙunshi ƙarin bayanai da kuma Nassin da za a iya tattaunawa, amma hakan ya dangana ne da ƙwarewar ɗalibin.

5. A wane lokaci ne ya kamata mu ba da waɗannan ƙasidun kuma ta yaya?

5 Yadda Za A Yi Amfani da Su: Za ku iya ba da kowace ɗaya daga cikinsu sa’ad da kuke wa’azi gida-gida ko kuma a duk lokacin da kun ga ya dace, ko da a ce ba su ne ake bayarwa a watan ba. (Duba akwatin nan “Yadda Za A Ba da Ƙasidun.”) Sa’ad da kuke koma don ku ziyarci waɗanda kuka yi musu wa’azi, kuna iya gabatar da ƙasidun ta wajen gaya musu cewa kuna da wani abu da kuke so ku nuna musu, sai ku ba su ɗaya daga cikin ƙasidun.

6. Ta yaya za mu yi amfani da waɗannan ƙasidun wajen gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki?

6 Tun da yake babu tambayoyi a cikin ƙasidar nan Ka Saurari Allah, tattaunawar ba za ta ƙunshi tambayoyi ana ba da amsoshi kamar yadda ake yi sa’ad da ake nazari da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ba. A kowace ƙabila, mutane suna jin daɗin sauraron labarai. Saboda haka, ku yi amfani da hotunan wajen ba da labaran Littafi Mai Tsarki waɗanda aka hure. Ku bayyana hotunan. Ku yi hakan a hanya mai ban sha’awa. Ku ba wa ɗalibin damar bayyana ra’ayinsa. Ku karanta nassin da ke ƙasan shafin kuma ku tattauna su da shi. Ku yi tambayoyin da za su sa ya bayyana abin da ya fahimta kuma ku tabbata cewa ya fahimci abin da kuke tattaunawa. Idan kuna amfani da ƙasidar nan Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada, ku karanta abin da aka rubuta a kowane hoto da kuma nassi da ke ƙarƙashin rubutun.

7. Ta yaya za mu iya taimaka wa ɗalibanmu su samu ci gaba?

7 Ku Taimaka wa Ɗalibin Ya Samu Ci Gaba: Muna fata cewa yayin da kuke tattaunawa da ɗalibinku, zai yi marmarin koya karatu don ya ƙara sanin Jehobah da kansa. (Mat. 5:3; Yoh. 17:3) Saboda haka, idan kuna amfani da ƙasidar nan Ka Saurari Allah kuma kun ga cewa ɗalibin yana son nazarin, za ku iya gaya masa cewa kuna son ku soma koya masa yadda zai yi karatu, sa’an nan ku soma yin amfani da ƙasidar nan Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada. Ko da wanne ne cikin waɗannan ƙasidu kuka gama nazarinta, hakan ba zai sa ɗalibin ya cancanci baftisma ba. Ya kamata ku ci gaba da nazarin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma wani littafin da ya dace wanda zai sa ya fahimci Littafi Mai Tsarki ciki-da-waje.

8. Me ya sa muke godiya don waɗannan sabbin ƙasidun da muka samu don wa’azi?

8 Wajibi ne mutane su saurari Allah Maɗaukakin Sarki idan suna so su rayu har abada. (Isha. 55:3) Kuma nufin Jehobah shi ne cewa “dukan mutane” har da waɗanda ba su iya karatu ba, su koyi yadda za su saurare shi. (1 Tim. 2:3, 4) Muna godiya sosai don waɗannan sabbin ƙasidun da za su taimaka mana mu koya wa mutane yadda za su saurari Allah!

[Akwati a shafi na 3]

Yadda Za A Ba da Ƙasidun

Ku nuna wa mutumin shafuffuka na 2 da 3, kuma ku ce: “Za ka so ka yi rayuwa a irin wannan yanayin? [Ku bari ya ba da amsa.] Allah ya yi alkawari a cikin Nassi [ko kuma Kalmarsa] cewa zai mai da duniya aljanna, inda za a yi zaman lafiya kuma talauci da rashin lafiya ba za su kasance ba. Ka lura da abin da ya kamata mu yi don mu cancanci zama a irin wannan yanayin. [Ku karanta Ishaya 55:3, wadda aka rubuta a saman shafi na 3.] Wurin nan ya ce mu “zo” wurin Allah kuma mu “ji” maganarsa. Amma ta yaya za mu saurari Allah?” Ku buɗe shafuffuka na 4-5, kuma ku tattauna amsar da shi. Idan mutumin ba shi da isashen lokaci, ku ba shi ƙasidar kuma ku yi masa alkawari cewa za ku dawo don ku tattauna amsar da shi.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba