Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb17 Maris p. 5
  • Yadda Za a Yi Amfani da Ka Saurari Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za a Yi Amfani da Ka Saurari Allah
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Taimaka wa Mutane Su Saurari Allah
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Yadda Za A Yi Amfani da Sabuwar Ƙasidar Nan Albishiri Daga Allah!
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Ku Yi Amfani da Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! a Wa’azi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Wata Hanya na Yin Amfani da Ƙasidar nan Littafi Mai Tsarki—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
mwb17 Maris p. 5

LIVING AS CHRISTIANS

Yadda Za a Yi Amfani da Ka Saurari Allah

Ka Saurari Allah

An shirya ƙasidar nan Ka Saurari Allah don a yi amfani da hotuna wajen koya wa mutanen da ba su iya karatu ba muhimman gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki. Kowane darasi yana ɗauke da shafuffuka biyu da ke da hotuna da kuma alama da za ta nuna yadda za a yi amfani da hotunan ɗaya bayan ɗaya.

Ƙasidun nan Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada da Ka Saurari Allah suna da hotuna iri ɗaya. Amma rubutun da ke Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada ya fi yawa kuma ɗalibi da ya iya karatu zai iya amfani da ita. Masu shela suna yawan amfani da ita sa’ad da suke nazari idan ɗalibin yana amfani da Ka Saurari Allah. Yawancin shafuffukan suna da akwati da ke ɗauke da ƙarin bayani da za a iya tattauna bisa ga fahimtar ɗalibin.

Wata ’yar’uwa tana amfani da kasidar nan Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada yayin da dalibarta tana amfani da Ka Saurari Allah

Za ka iya ba da ƙasidar a kowane lokaci, ko idan ba ita ce littafin da ake rarraba a watan ba. Ka yi amfani da hotunan don bayyana labarin da ke Littafi Mai Tsarki. Ka yi amfani da tambayoyi don ka san abin da ke zuciyar ɗalibin kuma ka tabbata cewa ya fahimta sosai. Ku karanta da kuma tattauna nassosin da ke ƙarƙashin kowane shafi. Bayan kun kammala ƙasidar, ku yi nazarin littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? don ɗalibin ya cancanci yin baftisma.

Wani darasi a kasidar Ka Saurari Allah game da Adamu da Hauwa’u a lambun Adnin
    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba