Wata Hanya na Yin Amfani da Ƙasidar nan Littafi Mai Tsarki—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
Mutane da yawa a yankinmu, musamman waɗanda ba Kiristoci ba ne, ba su san Littafi Mai Tsarki sosai ba. Wasu masu shela sun yi amfani da ƙasidar nan Littafi Mai Tsarki—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa? don su taimaka wa ɗalibinsu ya san Littafi Mai Tsaki sa’ad da suke nazari da shi da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Alal misali, wani ɗan’uwa ya gabatar da sashe na ɗaya na ƙasidar sa’ad da suke tattauna babi na uku na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Bayan hakan, sai suka tattauna wani sashe a ƙarshen kowane nazari da suka yi. Kana nazari da wanda bai san Littafi Mai Tsarki sosai ba ko bai sani ba kwata-kwata? Don ka taimaka masa ya koya game da ‘littattafai masu-tsarki waɗanda ke da iko su sa shi hikima don samun ceto,’ ka yi tunanin goyon bayan bayanin da ke cikin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da bayanin da ke cikin ƙasidar nan Littafi Mai Tsarki—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?—2 Tim. 3:15.