Ka Adana
Kana Yin Amfani da Waɗannan Ƙasidun?
Littafi Mai Tsarki—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
An wallafa ta don waɗanda ba su san Littafi Mai Tsarki ba sosai, musamman waɗanda ba Kiristoci ba ne
Yadda za a gabatar da ita: “Za mu so mu san ra’ayinka a kan abin da aka ambata a cikin wannan aya ta Nassosi. [Karanta Zabura 37:11, wanda aka ambata a sashe na 11.] Yaya kake tsammani duniya za ta kasance sa’ad da wannan annabcin ya cika? [Ka bari ya ba da amsa.] Wannan ne irin bege da kuma tagomashi da mutane daga dukan al’adu da addinai za su iya samu daga Littafi Mai Tsarki.” Ka karanta sakin layin da ke saman shafi na 3, kuma ka gabatar da ƙasidar.
Za ka iya gwada wannan: Idan kana gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa da wani da ba Kirista ba ne, ka yi amfani da ’yan mintoci a farko ko ƙarshen kowane nazari don ku tattauna sashe ɗaya na wannan ƙasidar don ya san abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki.
An wallafa wannan ƙasidar a yaren Efik da Turanci da Fulfulde da Hausa da Ibo da Isoko da Tiv da kuma Yarbanci.
Minene Yakan Faru Mana Sa’anda Muka Mutu?
An wallafa ta don waɗanda aka yi musu rasuwa
Yadda za a gabatar da ita: “Sa’ad da waɗanda muke ƙauna suka rasu, daidai ne mu yi tunanin inda suke ko kuma za mu sake ganinsu. Ka taɓa yin tunani game da wannan tambayar: Mene ne yake faruwa da mu sa’ad da muka mutu?” [Ka bari ya ba da amsa.] Sai ka karanta Ayuba 14:14, 15 kuma ka daɗa: “Wannan ƙasidar ta bayyana inda waɗanda muke ƙauna suke da kuma begen da suke da shi.”
Za ka iya gwada wannan: Ka buɗe babi na ɗaya kuma ka karanta sakin layi na 4, sai ka ce: “Idan na dawo, za mu tattauna amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da ga wannan tambayar.” Idan ka dawo, ku tattauna wasu sakin layi a babi na 9.
An wallafa wannan ƙasidar a yaren Efik da Turanci da Gun da Hausa da Ibo da Isoko da Tiv da kuma Yarbanci.
Za Ka Iya Zama Abokin Allah!
An wallafa ta don waɗanda ba su da ilimi sosai ko kuma ba su iya karatu sosai ba
Yadda za a gabatar da ita: “Kana zato cewa zai yiwu mu zama aminan Allah? [Ka bari ya ba da amsa. Karanta Yaƙub 2:23.] An wallafa wannan ƙasidar don ta taimaka mana mu zama aminan Allah, kamar yadda Ibrahim amininsa ne.”
Za ka iya gwada wannan: Ko a ziyara ta farko ko kuma sa’ad da ka koma ziyara, ka gwada yadda ake gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki ta wajen tattauna gabaki ɗaya ko wasu cikin sakin layin da ke darasi na 1.
An wallafa wannan ƙasidar a yaren Bariba da Efik da Turanci da Gokana da Gun da Hausa da Ibo da Isoko da Khana (Ogoni) da Tiv da kuma Yarbanci.
A Satisfying Life—How to Attain It
An wallafa ta don waɗanda ba sa bin wani addini
Yadda za a gabatar da ita: “Muna ziyararku domin mutane da yawa za su so su yi rayuwa mai gamsarwa. Dukanmu muna fuskantar matsaloli da za su iya sa mu baƙin ciki. Idan hakan ne, muna iya neman shawara daga wani dangi da muka amince da shi ko abokinmu ko kuma mu yi amfani da laburare ko kuma Intane. A ina ne za ka samu shawara mai kyau? [Ka bari ya ba da amsa.] Wasu sun yi mamakin samun shawara mai kyau a cikin Littafi Mai Tsarki. Ga misali. [Ka nuna wa mai-gidan babi na 2, kuma ka karanta ɗaya cikin nassosin da aka yi ƙaulinsu.] An wallafa wannan ƙasidar don ta bayyana yadda za mu ƙara yin rayuwa mai gamsarwa.”
Za ka iya gwada wannan: Idan mai-gidan ya karɓi ƙasidar, sai ka ce: “Mutane da yawa suna jin cewa Littafi Mai Tsarki yana cike da kurakurai. Idan na dawo, zan nuna maka wani misali da zai burge ka da ya nuna cewa idan ya zo ga batun kimiyya, Littafi Mai Tsarki ya faɗi gaskiya.” Idan ka koma, ku tattauna sakin layi na 4 a shafi na 12.
An wallafa wannan ƙasidar a Turanci.
The Origin of Life—Five Questions Worth Asking
An wallafa ta don matasan da ake koya musu ra’ayin bayanau a makaranta kuma za a iya amfani da ita sa’ad da ake tattaunawa da masu ra’ayin bayanau da masu shakka cewa Allah ya wanzu da kuma waɗanda ba su yi imani da Allah ba (Ba a wallafa wannan ƙasidar don a ba mutane sa’ad da ake wa’azi na gida gida ba.)
Yadda za a yi amfani da ita sa’ad da ake tattaunawa da mai ra’ayin bayanau ko kuma wanda bai yi imani da Allah ba: “Kusan dukan littattafan kimiyya a yau suna koyar da ra’ayin bayanau. Shin ka gaskata cewa ra’ayin bayanau ƙage ne ko kuma kana ganin cewa yanzu an amnice da shi a matsayin gaskiya? [Ka bari ya ba da amsa.] Don ka tsai da shawara mai kyau, na tabbata za ka yarda cewa ya kamata mu bincika batun sosai. Wannan ƙasidar ta ba da tabbaci da ya sa mutane da yawa suka gaskata cewa an halicce rai.”
Za ka iya gwada wannan: Idan ka je makaranta, ka bar ƙasidar a kan taburinka, ka ga ko za ta jawo hankalin wani cikin ’yan ajinku.
An wallafa wannan ƙasidar a Turanci.
Why Should We Worship God in Love and Truth?
An wallafa ta don masu bin addinin Hindu
Yadda za a gabatar da ita: “’Yan Indiya suna yawan roƙon Allah cewa ya sa su san gaskiya, kuma su samu wayewa.” Kana ganin yana da muhimmanci a bauta wa Allah cikin ƙauna da kuma gaskiya? [Ka bari ya ba da amsa.] Ga abin da Yesu ya ce game da wannan batun.” Ka karanta Yohanna 4:24. Sai ka karanta sakin layi na 4 a shafi na 3 kuma ka ba da ƙasidar.
Za ka iya gwada wannan: Idan mai-gidan ya karɓi ƙasidar, ka ce: “Wasu masu bin addinin Hindu masu hikima sun ce gaskiya tana ɓoye a cikin zukatanmu. Wasu kuma sun ce ana samun gaskiya a cikin nassi mai tsarki. Idan na dawo, zan so mu tattauna wata tambaya da aka yi a ƙarshen sakin layi na 3 da ke shafi na 4: ‘Daga ina ne za mu san ainihin gaskiya’”
An wallafa wannan ƙasidar a Turanci.
The Pathway to Peace and Happiness
An wallafa ta don masu bin addinin Buddha
Yadda za a gabatar da ita ga dattijo wanda ke bin addinin Buddha: “Wataƙila kai ma ka damu don ra’ayoyin da ba su dace ba da suke ko’ina a yau, da kuma yadda hakan yake shafan yaranmu. Me kake ganin ya sa lalata yake ƙaruwa tsakanin matasa? [Ka bari ya ba da amsa.] Shin ka san cewa an annabta cewa hakan zai faru a cikin littafin da aka rubuta tun da daɗewa kafin a kafa addinin Kirista da Hindu da kuma Musulunci? [Karanta 2 Timotawus 3:1-3.] Ka lura cewa wannan yanayin ya kasance duk da cewa an ci gaba da koyon abubuwa da yawa. [Karanta aya ta 7.] Bayanin da ke cikin wannan ƙasidar ya taimaka mini na fahimci gaskiya da yawancin mutane ba su taɓa sani ba. Za ka so ka karanta ta?”
Za ka iya gwada wannan: Idan ka koma ziyara a nan gaba, bayan ka sa mai-gidan ya soma son Littafi Mai Tsarki, ka nuna masa tambayoyi da ke bango na baya, kuma ka nuna masa hoton littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ka gaya masa cewa ka kawo littafin idan yana son ya gan shi. Ka nuna masa abin da ke cikin littafin, kuma ku tattauna sakin layi ɗaya ko biyu a cikin babin da ya zaɓa.
An wallafa wannan ƙasidar a Turanci.
Hanyar Rai Madawwami—Ka Same ta Kuwa?
An wallafa ta don mutanen Afirka
Yadda za a gabatar da ita: “Muna son mu san ra’ayinka game da wannan tambayar: Kana ganin dukan addinai suna koyar da gaskiya? [Ka bari ya ba da amsa.] Ana ƙirƙiro sababbin coci, kuma wasu suna iya tunani cewa Allah yana amince da bautar kowanne cikinsu. Amma, an yi mana kashedi a littafin Tasalonikawa 5:21. [Ka karanta.] Ka lura da abin da jimloli biyu na farko da ke shafi na 5, sakin layi na 3 a babi na 1 na wannan ƙasidar ta faɗa. [Ka karanta.] Tun da Allah bai amince da dukan addinai ba, yaya za mu iya sanin addini na gaskiya? Wannan ƙasidar za ta amsa wannan tambayar.”
Za ka iya gwada wannan: “Don Jehobah ya ƙaunace mu kuma ya kāre mu, dole ne mu bauta masa a hanyar da ta dace. Idan na sake dawowa, za mu tattauna tambayar da ke shafi na 19, ‘Allah Ya Yarda da Dukan Addinai Ne?’”
An wallafa wannan ƙasidar a yaren Efik da Turanci da Gun da Hausa da Ibo da Isoko da Tiv da kuma Yarbanci.
Ruhohin Matattu—Zasu Taimake Ka ne ko Kuwa Zasu Yi Maka Barna? Sun Wanzu Kuwa Da Gaske?
An wallafa ta don mutanen Afirka
Yadda za a gabatar da ita: “Mutane da yawa sun yi imani cewa matattu suna zuwa lahira, inda za su lura da abubuwan da mutane suke yi kuma su rinjaye su. Hakan gaskiya ne?” [Ka bari ya ba da amsa.] Sai ka karanta littafin Mai-Wa’azi 9:5, 10, kuma ka ce: “Idan wannan koyarwar ba gaskiya ba ce, su waye ne suke da’awa cewa sune ruhohin matattu? Wannan ƙasidar ta ba da amsar wannan tambayar.” Ka ba da ƙasidar.
Za ka iya gwada wannan: Idan mai-gidan ya karɓi ƙasidar, ka buɗe shafi na 13 kuma ka sa ya soma karantawa daga sakin layi na ɗaya. Ka yi alkawarin koma ziyara don ku ci gaba da tattaunawa.
An wallafa wannan ƙasidar a yaren Efik da Turanci da Gun da Hausa da Igala da Ibo da Isoko da Tiv da kuma Yarbanci.
Shiriyar Allah—Hanyarmu ta Samun Aljanna
An wallafa ta don Musulmai da ke zama a inda za su samu ’yancin yin nazarin Littafi Mai Tsarki
Yadda za a gabatar da ita: “Na san cewa Musulmai sun yi imani da Allah ɗaya da kuma dukan annabawa. Shin hakan gaskiya ne? [Ka bari ya ba da amsa.] Zan so na tattauna da kai game da wani annabi da ya annabta cewa za a mai da duniya aljanna. Bari na karanta maka abin da wannan annabin ya rubuta. [Karanta Ishaya 11:6-9.] Mutane da yawa suna mamaki yadda Allah zai yi wannan canji a duniya. Wannan ƙasidar ta nuna abin da annabawa suka ce game da wannan batun.”
Za ka iya gwada wannan: Idan mai-gidan ya karɓi ƙasidar, ka ce: “Nassi ya bayyana cewa a farko, mutum ya kasance a cikin aljanna. Idan mun sake tattaunawa, zan so na amsa wannan tambayar, ‘Ta yaya ’yan Adam suka bijire daga shiriyar Allah kuma suka yi hasarar aljanna?’” Sa’ad da ka koma ziyara, ku tattauna sakin layin da ya soma daga shafi na 6.
An wallafa wannan ƙasidar a Turanci da Hausa da kuma Yarbanci.
Cikakken Imani—Zai Sa Ka Yi Farin Ciki a Rayuwa
An wallafa ta don Musulmai waɗanda suke zama a yankin da za su samu ’yanci yin nazarin Littafi Mai Tsarki
Yadda za a gabatar da ita: Ka nuna hoton da ke shafuffuka na 16 zuwa 17 kuma ka ce: “Wannan yanayin ya yi dabam da abin da ake gani a duniya a yau. Kana tsammani cewa zai yiwu duniya ta kasance haka wata rana? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da alkawarin da Allah ya yi a cikin nassosi. [Ka karanta ɗaya cikin ayoyin da aka rubuta a cikin ƙasidar daga naka Littafi Mai Tsarki.] Wannan ƙasidar za ta taimaka mana mu samu cikakken imani cewa waɗannan alkawuran za su cika.”
Za ka iya gwada wannan: Sa’ad da ka kammala tattauna da shi a ziyara ta farko, ka ce wa mai-gidan ya zaɓi ɗaya cikin tambayoyin da ke bangon bayan ƙasidar. Sai ka shirya yadda za ka koma ziyara wurinsa don ku tattauna amsoshin tambayoyin da ke ƙasidar.
An wallafa wannan ƙasidar a Turanci da Hausa da Tiv da kuma Yarbanci.
Lasting Peace and Happiness—How To Find Them
An wallafa ta don mutanen ƙasar Caina
Yadda za a gabatar da ita: “Akwai matsaloli da yawa a yau da za su iya hana mu farin ciki. Mene ne zai taimaka maka ka yi farin ciki duk da matsalolin da kake fuskanta? [Ka bari ya ba da amsa.] Mutane da yawa suna farin ciki don bin gargaɗin Littafi Mai Tsarki. [Karanta Zabura 119:1, 2.] Wasu sun ce an rubuta Littafi Mai Tsarki don turawa. Amma ga abin da aka faɗa a nan. [Ka yi la’akari da sakin layi na 16 a shafi na 17.] Wannan ƙasidar ta tattauna yadda za mu samu salama ta dindindin da kuma farin ciki.”
Za ka iya gwada wannan: Idan mai-gidan ya karɓi ƙasidar, ka karanta jimloli uku na farko na sakin layi na 18 a shafi na 17 tare da shi kuma ka ce: “Idan na dawo, zan so na nuna maka abin da za mu iya yin begensa, bisa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa.” Idan ka koma, ku tattauna abu guda daga cikin bayanai da ke sakin layi na 6 a shafi na 30.
An wallafa wannan ƙasidar a yaren Caina da kuma Turanci.